Sashe 23
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duban da Giwa tai masa ya sanyashi had’iye sauran kalaman nasa... Take Ubandoma ya soma karanto sunbatu cikin zuciyarsa yana mamakin Wai Jakadiya ce zata mare sa.... Aiko bai ida tinanin ba yaji sauk’ar wata jahilar mari a k’uncinsa wanda saida ya tafiyar masa da jinsa da ganinsa na wasu dak’ik’ai...
.
Ya dafe k’uncinsa a birkice yana kuma sadda kai k’asa yana fad’in “Tuba nake Allah shi taimakeki... Tuba nake sarauniyar Masarautarmu... Ki yafeni Giwar Amale...!”
Giwa ta kuma takowa gabansa kad’an cikeda mulki da isa kana tace “Ka sanar dani Ubandoma shin kunje wani wajen ne...?!”
Ya girgiza kai cikin sauri yana mai furta “Allah shi taimakeki tare muke a masallaci toh sai ya bani damin kud’i na rabawa mabuk’ata da musakai dake zama bakin masallaci... Daga nan na nemeshi na rasa Rankishi dad’e... Ko k’yallinsa ban kuma hangowa ba...!” Ya k’arashe yana mai kuma sadda kai k’asa har yanzu rik’e yake da k’uncinsa yanda Jakadiya Ta shata masa mari...
Taci gaba da huci tana aika masa muguwar kallo, lokaci guda take ci gaba da fad’in “Sabida Mahmood d’in Aljani ne shiyasa zakace ya b’ace maka ko... Sau nawa zan sanar dakai koda wasa kada ka kuskura ka bari Mahmood ya b’acewa ganinka... Dik yanda Mahmood zai kasance ya zamana kaima kana wajen... Toh kan mai zaka Zo min da batu irin wannan...?!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci lokaci guda ta juya ta bada baya tana mai fad’in “Ubandoma..!!! Zaka karb’i horona mai tsanani idan har abu makamanciyar haka ta kuma faruwa...!!”
Ubandoma ya kuma zubda kai k’asa yana mai ban hak’uri da neman gafarar Giwa, jikinsa har wane irin karkarwa yake...
Alamu da ido taima Jakadiya kana Jakadiyar ta bud’e murya tace “An sallameka Ubandoma... A kiyaye ayi kuma hattara....!!”
Ubandoma ya kuma risinawa yana mai mik’a godiyarsa tareda tabbatarwa Giwa hakan bazai kuma faruwa ba...
Yana ficewa Giwa ta dubi Jakadiya dake zube k’asa a wajen kana tace “Jakadiya..!”
Jakadiya ta kuma risinawa had’ida d’ago jannu guda alamun jinjina kana tace “Allah shi taimakeki...!”
Giwa taci gaba da fad’in “Mai kike tunani kan Yarima Mahmood...?!”
Jakadiya Ta kuma risinawa kana tace “Allah shi baki yawan rai Yarima Mahmood yaro ne mai biyayya tun tasowarsa...!”
Giwa tai shiru tamkar mai nazari kana tace “Mai kike tunani idan ya tsananta bincike...?!”
Wannan karon a firgice Jakadiya ta d’ago tana duban Uwar gijiyar tata kana ta kuma maida kanta k’asa, cikin daburcewar murya take furta “Bazai fahimci komai ba Rankishi dad’e... Amma saidai... Ina tsoron ranan da zai tono sirrikan da muka jima da aza masu k’as.....”
Batakai aya ba Giwa ta dakatar da ita da fad’in “Jakadiyaaa.!!”
Cikin sauri Jakadiya ta rik’e labb’an bakinta duka biyu tana mai furta “Tuba nake Allah shi taimakeki... Yarima Mahmood bazai tab’a tono komai ba... Amma Rankishi dad’e idan har ya tabbata Sarki na gaba komai ai ka iya faruwa....!”
Wannan k’asaitaccen murmushi Giwa tai kana tace “Inada manufata da yasa nake so lallai lallai shine zai d’ale Karagar mulkin a daidai wannan lokaci.... Tal’udu bazai tab’a min K’arya ba Sarautar bazata fice daga cikin Ahalin Mijina ba....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin murmushi had’ida kishingid’a cikin gadon mulkinta....
***
Da tsananin mamaki Turaki ke dubansa hannu a kunkumi, lokaci guda yake furta “Unbelievable..! Wai dan Allah your Highness kaine haka...? Shikenan daga Spain ka koma Niger....!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa...
Mahmood yace “Ina ka aje motar...?”
Turaki yai masa nuni da motar dake pake tsallaken kwalta...
Yarima Mahmood yace “Muje da Allah kafin wani yai noticing d’inka ma...” Bai ko jira amsar Turaki ba yasa kai ya nufi motar...
Turaki yabi bayansa da kallo yana furta “Mahmood mai abin mamaki...” Lokaci guda ya girgiza kai yana mai sakin murmushi kana yabi bayan abokin nasa....
Daidai nan motar Majidad’i D’an wajen Baba Wambai mai neman sarautar Ta shigo kwanar... Bayan Turaki kawai ya hango ya gane abokin Yarima Mahmood ne... Toh mai ya kawo abokin Yaima Mahmood gidansu...? Kardai Mahmood ne ya turosa wajen Mahaifinsa dan su kuma saye zuciyar Mahaifin nasa su kuma karkatar da ra’ayinsa... Lallai Mahmood baisan ko Shi d’in wanene ba har yanzu... Bazai yuwu ya shiga tsakaninsa da mahaifinsa ba ya hanasa amshe gadon sarautar Kakansu da Uban Mahmood yai fin k’arfi wa mahaifinsu....Toh idan za’a tashi Masarautar wllhi sai ya amshe mulkin gidan daga hannun ‘ya’yan Abduljabbar.....
Da wannan tunani ya isa Gida, ko parking mai kyau bai ida ba ya fito yana tafe yana sakin huci kaikaice tafashesshen Koko ne....
Ya iske ma’aikatan gidan tsakar gida suna gaidasa ko ci kanku baice dasu ba ya nufi b’angaren mahaifiyarsa tamkar zai kifa da k’asa, yana tafe yana k’walla mata kira...
“Innani..! Innani..!! Innani...!!!”
Budurwa mai kimanin shekaru 26 wacce ke kwance bisa kujera mai d’aukan mutum uku itace Ta amsa masa da fad’in “Kai Yaya irin wannan kira saikace Aunty Jamila ce ko kuma Yasir ko Nimra ne ka rasa d’aya cikinsu.. Ni wllhi ka razanen...!” Ta k’are ashe baki a ture..
Majidad’i yace “Ke Juwairyya ni ba sa’anki bane zakiyi ma sarki magana haka ne...?”
Juwariyya ta zaro ido waje had’ida k’ame baki “Tabb Yaya ai wllhi dama hak’ura Kai dan...” Batakai aya ba ya bige bakinta yana fad’in “Sai na karyaki na sake jin kince banyi zubin sarakuna ba... Ina Innani take...?!”
Juwariyya na k’unk’uni rik’eda bakinta ta nuna masa hanyar bene....
Daidai sanda Majidad’i yakai dubansaga b’angaren benen
Dattijuwar mai k’aramin jiki irin masu suffan mafad’atan nan ta fito tana gyara d’aurin kwali take fad’in “Yaya Wai yaya akai ne...Sarkin gobe Kai kuma fah, lafiya daga Ina haka.. Waye ya b’ata maka rai inyi...?!”
Juwariyya dai ficewa tai tana ci gaba da k’unk’uni...
Lokaci guda kuma ta lab’e jikin k’ofa tana sauraran tattaunawan Yayanta da Mahaifiyarta..
Majidad’i na sakin huci yake fad’in “Innani uban mi ya kawo Mahmood gidan nan...?”
Innani ta dafe k’irji tace “Mahmuda fah... A’a badai shi ka gani ba don baizo gidan nan ba...”
Majidad’i bai daina tururi ba yake fad’in “Ba yanzu naci karo da abokinsa waje ba...!”
Innani dafe da k’irji take girgiza kai kana tace “A’a bakadai duba da kyau ba... Yo Mahmuda yazo gidan nan yamin mai balle har abokinsa...!”
“Ai dama ba wajenki zaizo ba wajen tsohon nan mai d’aure masa gindi da zigasa zai zo shi....!”
Innani ta girgiza kai tace “Kai Majidad’i ka b’ata gani, yau bak’o guda Babanka yayi tun wayewar gari kuma bak’on Buzu ne... Ka kwantar da hankalinka Majidad’i ko Mahaifinka baya so sai kayi sarauta kaji koh... Haba ni da na tabbata Mahmood da ‘yan uwansa kashe juna zasuyi sabida fitinan son mulki.... Kaga cikin sauk’i zakayi sarauta.. Su Turai a fice a bamu waje, yanda nake ‘yar tsurut d’in nan haka zan fitar da Giwa daga gidan wayaga cinnaka ta kori Giwa...!!” Ta k’arashe tana mai fashewa da dariya...
Yayinda d’an nata ya bita da kallo yana mai ci gaba da sakin huci a hankali...
Juwariyya na gama nad’e komai ta koma gefe ta zaro wayarta take ta shiga neman layin Raheema...!
***
Kasancewar duk daren Juma’an k’arshen wata Ahalin Giwa na hallara gaba d’aya a sashenta da daddare don cin abinci a farfajiyan b’angaren nata yanda ake k’awata wajen da manyan dardumai da kuma pillows na alfarma had’ida k’awata wajen da ado da kwalliya irinta alfarma yasa sai shirin fita taron suke..
Muhibbah ta dubi Umaima da mamaki kana tace “Kuma Wai Hakan a’adan gidan nan ne... Toh maiyasa ni zanje tinda Ahalin cikin gidan nan ne kawai Ke hallara...”
Umaima tace “Ke bak’uwarmu ce dan haka har zuwa lokacinda zaki tafi ki bar gidan nan ki dinga lissafin kanki cikin Ahalin gidan nan, ai dai kinji mai Maami tace, bazataji dad’i ba idan bata ganki wajen ba....”
Muhibbah tai shiru tamkar mai nazari, hakan na nufin zata had’u dasu kaf d’insu kenan a daren nan.... What if ta kasa jurema hakan har tai wani abinda zata fallasa kanta..? Take taji b’angare na zuciyarta na k’arfafa mata gwiwa da fad’in zaki iya Saudat....
D’agowa tai ta d’an dubi Umaima murmushi saman fuskarta kana tace “Shikenan na amince zanjeni...”
Umaima ma Ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa ko kefa yanzu naji batu...” Take Umaima ta fito masu da kaya irinta mulki da sarauta tace shi zasu saka...
Muhibbah ta dubeta ta dubi kayan... Kafin tai magana Umaima tai saurin katseta da fad’in “Don’t say anything Hibbah... Tashi kawai ki shirya bara nayi wanka Zahra ma na shiryawa already....” Ta k’arashe tana mai fad’awa bathroom yanda Ta bar Muhibbah tsaye nan cikin closet d’in rungume da lallausar Cotten lace kalar ja anyi masa ado da duwatsu masu d’aukan idanu anyi mata d’inkin doguwar riga irin mai bajewa daga k’asa... Ga wani mayafi mai k’yalk’yali da d’aukan idanu jikin kayan... Murmusawa Ta d’an kumayi kana ta saka rigar kaman yanda Umaima Ta buk’ata....
Ya Subhanallah! Sosai rigar ya zauna jikinta, ita kanta saida ta jita wane iri cikin kayan... Ita kanta saida ta yaba kyaun da kayan yai a jikinta sanda ta dubi kanta jikin marfin wardrobe d’in da yake zallan madubi ne...
Tsaf Ta ida shirinta ta nufo parlor sai watsa k’amshi take, ita kanta tasan tayi kyau dukda babu kwalliya a fuskarta....
Tai tsaye a parlorn tana kallon wani hoton zane na ginin gidan sarauta dake lank’aye jikin garu nan cikin parlorn tsakanin D’akin Umaima da Zahra....
A haka Umaima ta gama shirinta itama ta fito..
Tai tsaye tana duban Muhibbah dake bin zanen ginin da kallo cikeda nastuwa tamkar mai nazarin wani abu.... Umaima ta k’araso tana fad’in “Wai dama Kina tsaye a parlor...? I thought kina tareda Zahra...”
Ta murmusa kad’an had’ida juyowa tana duban Umaima da Ta fito cikin shiri kana tace “Ina tsamman Zahra bata gama shiri ba dan banga fitowar Kuyangarta ba...”
Umaima Ta jinjina kai a hankali tana duban hoton zanen gidan Sarauta da Muhibbah ta tsaresa da idanu kana tace “Wannan hoton Yarima Jamaludden naji dashi sosai... Kyautarsa aka basa sanda yai rakiyawa mahaifinsa zuwa wata masarauta a cen k’asashen nahiyar Yamma...!”