← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 162

Sashe 31

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cen wane b’angare mai duhuwa suka had’u shida Giwa Jakadiya na take mata baya....Duba guda yai mata ya d’auke kansa sai faman sakin huci yake...

Giwa taci gaba da takowa cikeda k’asaita....

“Yaya kukayi da d’ah na Mahmood Waziri...?!” Ta tambaya cikeda izza...

Saida ya kuma fuzar da fuci kana yace “D’anki ji yake shi d’in kaman wani sarki ne...Doka da Umarni yake bani tin yanzu Ina a matsayin Wazirin mahaifinsa....!”

Giwa ta murmusa cikeda k’asaita kana tace “Na d’an lokaci ne Waziri.....!”

Dubanta Waziri yai a kaikaice kana yace “Kin tabbata na d’an lokaci ne.... Shin kinada masaniyan cewa Yarima Mahmood ya soma tono diddigin abubuwa... Mai zai faru sanda ya isa k’arshen k’urya...?!”

Murmushi Giwa tai kana tace “Mai ya tambayeka...?”

Waziri ya gyara tsayuwarsa yana mai furta “Matarsa, mahaifinsa da kuma Jafaru...!!”

Nan ma murmushi Giwa Ta kumayi kana tace “Toh mai zai dameka Waziri bacin bamuda alhakin mutuwar matarsa dana mahaifinsa a wuyanmu.... Kaima kasan wakeda alhakin Mutuwar Maimartaba da Aliya...!” Ta k’arashe wani murmushin saman fuskarta...

Waziri yai mata K’uri kana yace “Kin tabbata Jafar baya raye....?”

Cikeda isa Giwa Ke kuma murmusawa kana tace “Jafar ya zama tarihi tinda jimawa...!”

Waziri ya jinjina kai kana yace “Allah yasa gaskiya kike fad’i, domin kuwa Jafar shi kad’aine yasan hanya da kuma launin mabud’in kurkun dake k’ark’ashin Masarautar nan, wanda tonoshi na nufin k’arahenmu ne... Dan nayi imani Yarima Mahmood sawa zai a fille kawunanmu koda kuwa Ke d’in mahaifiyarsa ce...!!”

Giwa Ta kuma murmusawa kana tace “Anyima kurkukun rufinda har abada bazai kuma bud’ewa ba....!”

Waziri ya murmusa kad’an kana yace “Kar kiyi gaggawa Turai domin kaw mabud’an wannan kurkuku mijinki ya mallakama wani wanda har yau bamu San ma waye ya mallaka ba...”

A harzuk’e Giwa ta d’ago tana dubansa kana tace “Inada tabbacin ma Jafar ya mallaka shiyasa na b’atar da Jafar.... Na kuma rufe bakin Jafar rufuwa ta har abada....!!!”

Waziri ya kuma jinjina kai kana yace “Allah yasa bakiyi kuskure ba wannan karon... Zan wuce na duba Gimbiya Zeenatu...!!”

Giwa Ta murmusa kana tace “Zeenatu Karen farautarmu... Kaje kaji da mai tazo wannan karon...!”

Waziri ya d’an murmusa kad’an kana yace “Tana nan tana haukarta akan mulkin Mahmood.... Da ace tasan tarkon da kika d’ana mata na tabbata da tayi yanda tayi ta fitar da kanta da kuma ‘yar uwarta daga wannan masarauta...!!!” Ya k’arashe mummunan murmushi saman fuskarsa...

Giwa Ta murmusa cikeda k’asaita kana tace “Gimbiya Turai bata yima kowa alkhairi face tanada nufinta akansa....Zeenatu da ‘yaruwarta tabbas sun fad’a Tarko na... Tabbas Alhakin mutuwar Mahmood zai rataya ne a wuyansu... Zasu fice daga cikin Masarautar nan suna k’ask’antattu... Kaga na kashe tsuntsu biyu ko nace uku da Dutse d’aya tak..!!” Ta k’arashe mummunan murmushi saman fuskarta...

Waziri ya murmusa kad’an kana yace “Mahmood mai Uwa... Tabbas kin cika Uwa Ta gari...!!”

Giwa Ta kuma murmusawa kana tace “Na masa d’aurinda sam babu mai warwaresa...!!” Ta k’arashe dikda cewa cen k’asan zuciyarta kalaman Tal’udu ne Ke mata Yawo cewa wannan gudan jinin bai shiga cikin tandun tsafi ba kuma dik a ta dalilin wannan tsinanniyar yarinyar Saudatu....
Take tinanin Mahaukaciya Izzatu ya fad’o mata, lokaci guda Ta dubi Jakadiya dake cen gefe kana tace “Jakadiya...!”

Jakadiya ta k’araso cikin sauri had’ida zubewa k’asa tana mik’awa Giwa jinjina...

Giwa taci gaba da fad’in “Yau da dare zamu kaiwa Izzatu ziyara...!”

Jakadiya ta jinjina kai cikeda girmamawa tana mai amsawa shigaban nata...

Waziri da Giwa sukaima juna wane irin duba kana Waziri yace “Na k’agu naga Yazeedu kan Karagar nan...!”

Murmusawa Giwa ta kumayi kana tace “Na d’an lokaci ne kad’an... Masarautar zata zama mallakinmu gaba d’aya...!”
Suka kuma murmusawa a tare kana Waziri yai masu sallama yayi shigewarsa....

***

Misalin k’arfe tara da rabi na dare ta shigo b’angaren nata, ta soma gudanar da shirye shiryenta na bacci, bayan tayi wanka da alwala ta tada sallah tai shafa’i da wutiri kaman yanda yake a al’adarta... Tana zaune saman abin sallah tana tinanin yanda al’amara Ta kaya yau tsakaninta da Fu’ad ga kuma fargaban abinda ka iya zuwa yazo tsakaninta da Yazeed, sannan ga rashin yarda da juna da take so Ta k’ulla tsakanin Mahmood da d’iyarsa, kaman daga sama taji ana knocking a k’ofar parlor... Bata kawo komai ba dan a zatonta Umaima ce ko wata Kuyanga ce ‘yar aike... Dan haka ba tareda wani damuwa ba ta isa ta bud’e k’ofar....
Saidai mutumin data gani ne tsaye k’ik’am a bakin k’ofar yai mugun bata shock.....

Sameena📚
[6/22, 1:05 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*022*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Kallon kallo suke ma juna su duka biyun, idanun Yazeed ko k’yaftasu baiyi dikda cewa Allah yasa bata cire Hijab d’in data ida sallah dashi jikinta ba.... Take ta tuna kalaman da ya fad’i mata d’azu da safe, kardai yazo ya tona asirinta ne... Ga wani irin mayen kallon da yake binta dashi... Ganin idan tai wasa zata iya b’ata komai dan gaba d’aya ji take kaman wuta ne Ke cin illahin jikinta da wannan irin duban da Yazeed Ke mata, d’aya daga cikin mutane biyar d’in da tafi tsana a duniyar ta... Lokaci guda tai K’ok’arin tattaro nutsuwarta kana ta d’an saki murmushi “Your Highness... What brings you here...?!” Ta fad’i murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskarta...

Har lokacin bai furta komai ba sai k’are mata kallo da yake ci gaba da yi.... Lokaci guda kuma yasa kai ya shigo cikin parlorn k’irjinta sai bugawa yakeyi da sauri da sauri ganin Yazeed ya kutso Kai cikin parlorn kai tsaye... Tai saurin jada baya don tabbas idan bata matsa ba zai bangaji jikinta ne... Ta had’iyi abinda ya tsaya mata da k’yar a mak’oshi kana ta d’ago tana dubansa....
Ko gizau babu a tattredashi....

Baibi takanta ba saima k’arasawa da yai ya zauna saman kujera irin zaman da masu mulki suka fayeyi...

Muhibbah tai saurin kauda fuskarta gefe tsan tsan tsanar wannan halitta naci gaba da wanzuwa cikin zuciyarta....

Har wannan lokaci Yazeed bai furta koda kalma ba saima ci gaba da murza zobban hannunsa da yake yi... Gaba d’aya sai ta d’an daburce don yanzu kam abin Yazeed tsoro ya soma bata amma dole tai jarumtar kauda tsoron kodan tsira da mutuncinta domin kaw sam bazata bari Yazeed ya kamata ba, bari Ta b’ullo masa a k’wararriya....
Ta sauk’e fuci a hankali kana ta saki murmushi mai kyau wannan karon...

Jikin k’aramar fridge ta isa ta d’auko masa bottle water harda glass cup Ta kawo Ta ijiye gabansa, kujerar dake cen gefe ta k’arasa ta zauna, k’afafu d’aya bisa d’aya... Lokaci guda take furta “To what do I owe the honor your Highness...!” Tai maganar tana mai rausayar da idanu had’ida girgiza k’afafunta dake d’aya bisa d’aya....

Murmushi ya sakar mata wannan karon yana mai dubanta, kaman bazaice komai ba sai kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “I can see you’re well trained... Tabbas kin K’ware a fanninki...!”

Ta kuma dubansa ba tareda ta fahimci Ina ya dosa ba.....Saida ya lank’wasa k’afarsa guda wannan karon kana yace “Tell me, a ina kika tsaya..? Mai da mai kikai discovering zuwa yanzu..?!”

Gabanta yai wane irin fad’uwa... Ta d’ago dara daran idanunta da suka k’ara girma lokaci guda tana dubansa... Shikenan Yazeed ya gane ko ita wacece... Su duka biyun suna duban juna, k’irjinta sai fat fat yake... Kai no bazata bari ya kamata ba, she will play his game.... Lokaci guda kuma ta saki murmushi kana tace “Excuse me your Highness, but I don’t get you... What exactly do you mean...?!”

Shu’umin murmushinsa ya saki kana yace “Kin fini sanin mai nake nufi...Aren’t you a spy....!?”

Wane irin ajiyan zuciya ta sauk’e jin bai fahimci cewa itace Saudatu ba... Lokaci guda ta kuma sakin murmushi kana tace “A spy...? Where’s that coming from your Highness...?!”

Mik’ewa tsaye yai had’ida maida hannayensa baya, lokaci guda itama Ta mik’e tsaye....

Saida Yazeed ya kuma daidaita tsayuwarsa kana ya soma fad’in “Daga Masarautar su matata kike... Sun turoki domin ki bincika irin zaman da Zuhra keyi a Masarautar nan....Am I right...!”

Harga Allah dariya yaso bata jin yanda gaba d’aya tinaninsa ya karkata.... Murmushi mai bayyana hak’wara wannan karon tai tana mai d’an rufe bakinta da yastun hannunta, dariyar take d’anyi har wannan lokacin....

Yazeed yai tsaye yana dubanta, lokaci guda take d’an k’ok’arin saita kanta kana tace “Oh I’m sorry your Highness, but you’ve that got that wrong....Do I look like a detective to you Rankashi dad’e...? I’m here to study... Karatu nake a nan, you can have me investigated if you wish.... But wait..!”

Ta k’arashe tana mai dubansa sosai wannan karon... Shid’inma ita yake duba musamman labb’anta da k’wayan idanunta... Lokaci guda Muhibbah taci gaba da fad’in “Mai yasa zakai tinanin ni ‘yar bincikece... Akwai wani abu ne da bakaso Masarautar su matarka su sani gameda kai..?!” Ta k’arashe tana mai rage girman idanunta....

K’uri yai mata kaman mai tinani, kana ya saki murmushi da gefen bakinsa had’ida daidaita tsayuwarsa “You expect me to believe that...? Well I don’t buy that... I’m not the kind of prince that can be easily fooled... But be grateful you’re beautiful... Idan kinaso ki fanshi kanki, kinada abinda zaki iya fansar kanki dashi ba tareda kin fuskanci horo da k’ask’anci daga Masarautar nan ba...!” Ya k’arashe yana mai k’arasowa dab kusanta had’ida mata kallon k’urilla....

Dikda bugu da k’irjinta keyi hakan bai hanata k’ok’arin tattaro natsuwarta ba... Tai k’ok’arin janye jikinta ta matsa daga kusansa lokaci guda take furta “I’ve got nothing to be afraid of your Highness... Like I told you, idan kana so zaka iya yin bincike akaina and clear all your doubts...!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta....

Miyau ya had’iya da k’yar kana ya d’anyi gyaran murya yace “If you’re really telling the truth, idan har gaskiya kike fad’i, baki tinanin ya kamata Ki samawa kanki Yarima a Masarautar nan wanda zai zamto garkuwa a gareki kafin ki gama karatunki ki tafi...?!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa...
Chapter 31 · 0% Book details