← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 162

Sashe 84

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

K’uri yayi mata da kannararren idanunsa kana ya murmusa yace “Bakida hurumin fitar damu daga cikin wannan gini da muka riga muka gina alk’aryarmu cikinta... Kuma tinda kikace haka daga yau na barki da iyawarki har sai ranan da kika shiga taitayinki da kyau... Abubuwa suka kuma kwab’e maki... A lokacin Ke da kanki zaki nemi hanyar alk’aryarmu Ki rasa..!” Ya k’arashe yana mai buga mata sandar tsafin akanta... Giwa ta saki wani irin k’aran azaba had’ida rik’e kanta lokaci guda tana mai rintse idanunta sakamakon ji da tai tamkar wuta aka watsa mata cikin illahirin jikinta sabida tsananin azaba... Bud’e idon da zatai ta ganta a gefen Jakadiya Tal’udu ya cillosu waje...

Jakadiya ta k’arasa da sauri tana taimakawa Sarauniyar tata, ta d’agota sosai tana tambayarta “Rankidad’e ya akai...?! Mai ya faru...?!!”

Cikin tsananin tashin hankali Giwa Ke furta “Jakadiya.. Jakadiya Ina cikin tsaka mai wuya, Tal’udu yana neman ya juya min baya...!”

Jakadiya ta nusa tace “Nifa inaga k’arfin tsafinsa ne ya soma k’arewa Rankidad’e.. Kinsan fah duk abinda yakeda rai dole yana tsufa, ilimin tsafin Tal’udu ne ya soma gushewa sabida tsufa... Rankidad’e Allah ne kad’ai mai dawamammen iko kan komai da kuma kowa, shi kad’ai ne rayayye wanda buwayarsa baya gushewa... Anya Rankidad’e lokaci baiyi ba da zamu tuba, mu nemi yafiyar wad’anda muka zalunta..!!!”

Batakai aya ba Giwa Ta katseta da fad’in “Har abada Giwa bata fad’uwa k’asa...Ke Jakadiya kin tab’a jin ance miki Giwa ta fad’i k’asa idan ba mutuwa tayi ba..!! Toh Babu gudu babu jada baya.. Babu abinda zan fasa... Da sannu zuciyar Tal’udu zata huce... Shige muje...!!”

Jakadiya da tin labarin Izzatu da taji jikinta yai matuk’ar yin sanyi a hankali ta soma takawa tabi bayan Giwa tamkar Kazan da ruwa ya shanye... Harga Allah a firgice take da Al’amarin Giwa.. Giwa ta shige duk tinaninta a baya... Suna tafe ne suka hango Jamal na dogarawa da sandar crutches d’insa, sai ‘yan waige waige alamun baiso ai noticing d’insa....

Giwa ta dakata kad’an had’ida dakatar da Jakadiya ma... Suka mak’ale gefe suna duban Jamal da hanyar da yabi... Giwa taceda Jakadiya su bi bayansa...
Sannu a hankali suka dinga bin bayan Jamal har suka shigo wani sunk’urumin waje da su kansu basusan da wajen ba cikin Masarautar...

Yana shigewa cikin d’akin suka take masa baya... Hankali tashe Jamal ya k’arasa jikin k’arfen da ya d’aure Jafar da sark’ok’i, babu Jafar babu alamunsa sai sark’ok’insa zube wajen... Hankali tashe Jamal ya duk’a yana d’aga sark’ok’in dan tabbatarwa idanunsa... Tabbas babu Jafar babu alamunsa saiko magensa da yake zuwa taredasu guda biyu a wajen suna kalatan sauran abincin da ya rub’e a wajen... Jamal ya shiga girgiza kai yana mai furta “No no this isn’t happening..!”
Juyowar da zai sukai ido hud’u da mahaifiyarsa, ga Jakadiya tsaye bayanta kanta a k’asa....Ya mik’e zumbur yana dubanta...
“Maami mai kikeyi a nan... Ta yaya har kika iya biyoni...?!”

“Ba wannan zaka tambayeni ba Jamal... Bayani zakamin meke faruwa a nan... Wanene ka ije cikin wannan waje...? Don’t tell me Izzatu ka aje tsawon lokacin nan da muke nemanta...?!”

Jamal dake asibiti a ‘yan kwanaki baimada masaniyar b’acewar Mahaukaciya Izzatu ya d’an tab’e fuska yace “Maami I don’t know what you’re talking about...!”

Giwa dake sakin huci Ta matso kusansa sosai ta kama kafad’unsa da k’arfin gaske tana furta “Jamal tell me the truth, idan ba Izzatu ka aje cikin wajen nan ba waye ka aje... Kamin magana talk to me...!!” Ta k’arashe tana mai jijjigasa...

Shaye da mamaki yake dubanta yanda tai masa wane irin damk’a tana jijjigasa da iyaka k’arfinta tashin hankali maras misaltuwa bayyane saman fuskarta...Fincika yai yana furta “Enough Maami, let me go... I don’t know what you’re talking about... For crying out loud I just got out of the hospital ta yaya zansan abinda kike fad’i...!!”

Cikin kid’ima da d’imauta Giwa Ke fad’in “Toh idan ba Izzatu ba waje ka aje cikin wajen nan..? Waye ka aje a wajen nan Jamal.. Ka bud’e bakinka kamin maganaa..!!!” Ta k’arashe cikin wane irin tsawa tana mai kuma jijjigasa...

Da k’arfin gaske ya fincike jikinsa yana mai sakin huci yake furta “It’s Jafar..!!! I kept Ja’afar here... And and I’m afraid he’s escaped...!!!”

Jiki a matuk’ar sanyaye Giwa ta sakesa tana dubansa da tsananin mamaki... Wai Jafar ya aje cikin wajen nan tsawon shekara guda harma da watanni da yayi bai cikin Masarautar ashe Yana nan Jamal d’anta ya b’oyesa...
Cikin rawar muryar Giwa Ke furta “Jafaru fah... Jafaru fah kace Jamal..? Shin ba ka sanar dani ka kashesa ba..? Mai kuma kake sanar dani yanzu..?!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

“I couldn’t kill him... As much as I wanted to kill him, I just couldn’t, bansan dalili ba but na kasa kashesa... Na ajesa a wajen nan tsawon shekara guda ina azabtar dashi Ta hanyar injecting d’insa da kuma drugging nasa da miyagun k’wayoyi...!”

Giwa dake tsaye tana duban d’an nata tamkar wacce ruwa ya shanye Ta nanata abinda ya fad’i kana ta d’aurada “Kan mai zaka ajesa a nan idan ba gamawa dashi zakai ba..?!”

A hasale yace da ita “Na tsanesa, na tsane wannan k’ask’antaccen Bawan... Especially idan na gansa tareda Umaima... Maami duk abinda nai masa it’s because of her... Zan Iya yin komai akanta... That’s how much I love her..!!” Ya k’arashe yana sakin huci...

Cikeda tsoro Giwa take dubansa, lallai ta yarda shid’in d’anta ne, zai komai kan abinda yake so kaman yanda zatai komai kan abinda take so... Jamal bai rage mata komai ba hardai zai iya aje mutum yana azabtar dashi tsawon shekara guda, can k’asan zuciyarta kuma sai taji dad’i da ya d’auko wannan hali nata ko Babu komai zai iya tsayuwa yaga ya sami abinda yake so koda bata raye ne... Saidai a halin yanzu tashin hankali ne take fuskanta tinda da alama Jafar ya gudu....

Bata ankara ba sai sinkayo muryar Jamal tai yana fad’in “Someone helped him escaped Maami, kinga hujin da akaima garun nan....!!”

Daga Giwa har Jakadiya suka k’arasa suna kallon ramin da aka huda... Jamal ya murmusa kad’an yace “Tabbas a d’akin dake gefe da wannan aka b’oye Mahaukaciyar da kike fad’i Maami... Kuma sun taimaka ma junane itada Jafar suka gudu...!”

Giwa da kanta gaba d’aya ya kwance, girgiza kai ta soma tana furta “Izzatu babu hankali jikinta bazata iya taimakama wani har su gudu ba..!”

Jamal yai shiru tamkar mai nazari sai kuma yace “Jafar must be very weak, sabida azaban da yasha a nan... Bazai iya taimakama wani ba shima... Toh Who helped them escape...?!”

Baikai aya ba Giwa Ta basa amsa da fad’in “Wanda ya rufe Izzatu a wancan d’akin shi ya taimaka masu suka gudu..!”

Jamal yace “Waye shi Maami... Ki fad’a min sunansa yanzu na gama dashi..!”

Giwa tace “Wanda yafi kowa sanin lungu da sak’o dake cikin Masarautar nan.. UBANDOMA..!!”

Lokaci guda Ta ambato sunan Jakadiya...

Jakadiya da tinda suka soma magana hankalinta bai jikinta sakamakon ji da tai Jafaru da Izzatu sun kub’uta tasan ko shakka babu k’arshensu yazo kenan... Dan idan asiri ya bayyana tayi imani itakam tsire wuyarta tsaf da ayi a matsayinta na baiwa da taci amanan Iyayen Gidanta...

Jin bata amasata ba ya sanyata kuma doka mata kira... A firgice Jakadiya ta amsa da “Allah shi taimakeki..!!” Ta zube a wajen zuciyarta naci gaba da tsinkewa....

Giwa tace “Maza kije kizo min da Ubandoma yanda duk ya shiga ya fita... Ki sanar da Sarkin Dogarai yau kada ya shigo cikin Fada face yana tareda Ubandoma... Idan ba’a samesa ba azo da ‘ya’yansa... Kinji abinda na fad’i..!!?”

Jakadiya ta had’iyi miyau da k’yar, kanta a k’asa take furta “An gama ya Shugabata...! Allah ya huce zuciyar Giwar Amale...!!”
Daga nan mik’ewa tai cikin sauri tabi ta hanyar da suka shigo....

Giwa da Jamal suka jera suma suka fito su duka biyun, kowa da abunda yake sak’awa cikin zuciyarsa....

Suna isowa sashen Giwa Jamal ya dubeta yace “Maami idan an kamo Ubandoma I’ll be the one to punish him... Zai d’and’ani kud’arsa...!”

Giwa ta fuzar da fuci tana dunk’ule hannu take zaga cikin d’aki lokaci guda tace “Ni kaina bansan irin horon da zan masa..!”

Jamal ya murmusa yace “Ki barni dashi, ni ne Gwarzonki Maami kuma na tanadi muggan horo da zanyima wannan k’ask’antaccen Bawan....!!”

Giwa ta jinjina kai tace “Nasan bazaka bani kunya ba Gwarzona... Zan baka Ubandoma kayi duk abinda kaso dashi, idan kaga dama kada ka ragar masa ruhi...!!”

Jamal yai wata murmushi da gefen bakinsa yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa cewa muddin ya damk’o Ubandoma zaiji jiki, zai masa horo fiyeda wanda yayima Ja’afar, tabbas ba’a shiga gonarsa a wanye lafiya... Dik manyan syringe na zira ma dabbobi da yaita huda jikin Jafar dashi mai sauk’i ne akan irin horon da ya tanadarwa Ubandoma muddin yayi ganganci shiga hannunsa....

**
Chapter 84 · 0% Book details