Sashe 155
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta jinjina masa kai a hankali alamun eh..
Cikin kashe murya yace “You sure..?”
Nan ma jinjina masa kai tai.. Goran fresh milk da ya shigo dashi ya shiga bud’ewa yana furta “But still you’ll drink this..!”
Ta d’an marairaice fuska tace “Nifa na k’oshi your Highness..”
Bai daina abinda yake ba, cikin tsarewa yake furta “Do I need to remind you your Highness, ko kin mance ba’a gardama a Fadah.. so just open your mouth and drink all this.. I need an empty bottle.” Ya k’arashe yana mai matso da goran saitin bakinta.. Yana furta “If you don’t drink this zamu sake sabon jarabawa yanzun nan.. So just drink it..!”
Kaman zata kurma ihu haka ta lagnab’e kanta waje guda.. Yanda ya tsareta da rikitattun idanunsa ya sanyata bud’e bakinta a hankali tana mai shan madaran da k’yar.. Bata wani sha sosai ba tace ta k’oshi saidai Mahmood bai k’yaleta ba saida ya tabbata tasha sosai.. Ya gyara zamansa sosai yana dubanta kana yace Ta shiga bathroom tayo alwalwa tazo suyi sallaha.. Jikinta a matuk’ar sanyaye Ta mik’e Ta nufi closet, cire alkyabbar jikinta tai ta lank’aye kana ta nufi bathroom ta d’auro alwala kaman yanda ya umarceta.. A nan closet d’in ta tsaya duba hijab yanda ta samesu a shirye a anjesu a mazaunansu.. Ta d’auko wani dogo har k’asa mai ruwan k’asa ta zira kana ta komo cikin d’akin yanda Ta hangi bayansa yana shimfid’a masu abin sallah.. Jallabiyarsa fara k’al sai d’aukan idan take.. Tai tsaye a wajen tana dubansa.. A hankali ya kaikaito yana dubanta yanda tai tsaye nan wajen.. Ya sakar mata murmushi kana ya soma takowa gaba gareta.. Hannayenta ya kamo yana duban kyakkyawan fuskarta dake duban k’asa... A hankali ya matso da ita cikin jikinta had’ida manna mata kiss a goshi, Muhibbah ta lumshe idanunta a hankali tanajin sauk’an labb’ansa had’ida hucin numfashinsa saman goshinta... Murya can k’asa ya furta “Lets pray mu kuma godewa Allah da wannan babban Ni’imah da ya lullub’emu dashi..!” Ta jinjina masa kai a hankali har lokacin k’asa take duba, ya shiga janyo hannunta tana binsa kaman rak’umi da akala har saida suka isa saman abin sallar tasu.. Mahmood yai masu limanci suka sallaci raka’a biyu na nuna godiya kaman yanda yazo a sunnah... Ya kuma kama forehead d’inta ya karanto addu’an neman alkhairi da tsari... Daga nan janyota cikin jikinsa yai yana mata tambayoyin da suka shafi addininta musamman b’angaren fiqhu tana basa amsa daidai gwargwado, dukda wani irin bugu da zuciyarta keyi.. Yanda yake mata tanbayoyin cikin sigan raha har sai ya sanya ta soma sakin jiki dashi.. Idan Ta basa amsa sai yai murmushi yace ashe dai zata lashe wannan jarabawar..! A haka dai salon jarabawar tasu Ta soma sauyawa.. Tun tana fahimtar tambayoyin Sarkin nata har dai ta kasa banbance yaren da yake mata jarabawar da ita... Tabbas wannan jarabawa yafi duk sauran jarabawar da yai mata a baya... Dare ne mai matuk’ar mahummanci a gareta kaman yanda yake a wajen ko wacce d’iya mace.. Saidai in her own case can k’asan zuciyarta tanajin kaman ba haka zai kasance a gareta ba bayan tuna tsautsayi da iftila’in da ya faru da ita da tai... Dukda kuwa cewa Angon nata zallan k’aunarta yake nuna mata... Sosai ta k’ank’ame bedcover tana kuka da duka zuciyarta harda shesshek’a.. Wanda hakan ba k’aramin karyar masa da zuciya yai ba... Tausayinta gauraye da k’aunarta na kuma ratsa duk wani k’ofa na zuciyarsa... A hankali ya matso kusanta ya janyota cikin jikinsa... Kaman zatai magana amma kuka ya hanata.. “Shiii!” Ya furta yana mai kwantar da kanta cikin k’irjinsa, lokaci guda hawayen zafin zuciya ya d’igo daga cikin idanunsa zuwa cikin sumarta...A hankali yake fad’in “Don’t say a word..! I love you.. I love you so much.. I love everything about you... Just stay right here..!” Ya k’arashe yana mai sumbatar cikin sumarta had’ida lumshe idanunsa... Wani hawayen ya kuma d’igo masa.. Allah ya gani baida tabbacin zai tab’a yafe wa su Yazeed... A wanann dare Mahmood ya tabbatar mata shid’in masoyinta na gaskiya ne.. Haka yaita tarairayanta yana nuna mata soyayyarsa mai tsuma zuciya..
Safiyar washe gari idan Ta tina abubuwan da suka faru saidai ta kulle fuskarta taita sakin murmushi a hankali.. Anya ma zata iya sake had’a idanu da Rankaidad’e..? Ta shiga girgiza kai ita kad’ai tana mai kuma sakin wani murmushin a hankali.. Gaba d’aya jiyan ya juye mata tamkar dai ba Rankaidad’e data sani ba, ko ina sarautar tasa suka tafi oho.. Ta kuma murmusawa a hankali tana tuno kalamansa a gareta... Murmushi bai bar saman fuskarta tayi k’uri ma hasken hantsi take furta “Allah ya tsare mun kai Rankaidad’e..!” Ta k’arashe tana mai kuma lumshe idanu tsan tsan k’aunar mijinta na fuzganta....Shige da ficen Hadimai da take saurarowa daga downstairs ya sanyata mik’ewa a hankali Ta nufo k’asan nan kuwa Ta tadda su Meenatu da Umaima shigowarsu kenan suma.. Meenatu ta shiga zolayarta da fad’in Amarya baki laifi ko kin koda kin k’ona Karagar Sarki..”
Bata amsata ba Sai hararar da take jifanta dashi...
“Tuba nake Rankidad’e kar kisa Dogarai suyi majajjawa dani...”
Sai sannan Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Kedai bazaki bar hali ba... !”
Meenatu tace “Ina kuwa zan bari Rankidad’e, ni yanzu haka ma zuwa nai na miki sallama anjima zamu tafi..”
Muhibbah Ta zaro idanu waje tace “A’a Haba banson rashin M.. Ai dai zaki jira ayi nad’in sarauta...”
“Anya kuwa Toh Bandai San mai Mommy zatace ba dan dama kwana biyu Mama ta bani..”
Muhibbah Ta katseta da fad’in “Ba sai na kira Maman ba nace a barki kiyi sati..”
Meenatu Ta zaro idanu tace “Sati.! Ai sai kisa Sarki ya koreni garinmu babu shiri..”
Umaima ce ta k’araso waya mak’ale kunnenta tana fad’in “Eh Ummi ta tashi lafiya.. Muna can side d’in nata ma.. Okay I’d make sure she eat..” Daga sallama sukai Ta zauna daga gefe tana fad’in “Surkarki ta kira tana tambayan ko kinyi breakfast, nace mata kar ta damu muna nan a nan, we’d feed you if we had to tinda hidiman sarauta ya hana Angon zana balle ya kula da amaryar tasa..!” Ta k’arashe cikin sigan zolaya... Suka d’an dara gaba d’aya Muhibbah na fad’in “Zaki sani ne..” daidai lokacin Mommy dasu Aunty Gudidi sukai sallama ga Kuyangi biyedasu nik’i nik’i da kaya.. Gudidi na baiwa Hadiman umarnin yanda zasu aje kayan.. Su Gudidi abin nema ya samu sai bada doka da order ake..
**
A b’angaren Mahmood ma yanda take yau d’in babban rana ce a gareshi kaman yanda daren jiya ya zamto babban dare mai cikeda alkhairai a gareshi, yanajin kaman bazai iya amsar shugabancin nan ba domin kuwa ko shakka babu Sarautar ya shige hakkinsa.. Kamata yayi ace yanzu yana tareda amaryarsa yana tarairayarta amma gashi wannan hidimar sarautar ya hana faruwan hakan, shi gaba d’aya ya soma tantama idan zai amshi mulkin...
Isowar Turaki ya katse masa tunanin nasa... Barde ya shigo ya zube yai gaisuwa kana ya sanar da zuwan Turaki... Mahmood ya basa izinin shigowa...
Daga yanda Turaki ya gansa ya fahimci abokin nasa ango yake, dan kyakkyawan annashuwa na musamman kake hangowa saman fuskar tasa mai cikeda gizo...
Tun kafin Turaki yakaiga mik’o gaisuwarsa Mahmood ya soma fad’in “Ba’a Turaki da yaro..!”
Turaki ya duk’a yana masa jinjina yake furta “Rankaidad’e..!”
Mahmood ya kuma fad’in “Ba’a Turaki da yaro..!”
“Rankidad’e.. Godiya nake..!” Turaki ya kuma fad’i yana masa jinjina murmushi saman fuskarsa... Lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Galadima ya sanar dani komai ya kammala fitowar ka kawai ake jira Rankaidad’e.. Already an bud’e Babban Gwani (Fadan Mai Martaba Sarki) anyi all the necessary arrangements.. Sarakun yankinmu na kusa sun soma isowa.. Hakimai da manyan masu muk’amin cikin masarauta duk sun hallara kaid’in ake Jira Rankaidad’e..” Ya k’arashe yana mai kuma d’ago masa yatsa alamun jinjina...
Mahmood yai shiru tamkar mai nazari wanda har saida yasa Turakin d’gowa yana dubansa...
A hankali Mahmood Ke furta “Im not sure Turaki.. I think I’m having a second a thought...!”
Turaki ya d’an dubesa da mamaki yace “Ban gane ba your Highness..!”
Mahmood yaci gaba da fad’in “I just want to be with my wife.. That’s all Turaki... Babu hidimar sarauta babu damuwar komai..”
Turaki ya d’an fuzar da huci yace “But your Highness..”
Katsesa yai da fad’in “Can’t you see I’m stuck here... Turaki I can’t do this anymore.. I’m stepping down..!” Ya k’arashe yana murza zobban dake hannunsa..
Turaki ya d’an fuzar da iska kad’an yace “I understand where you’re coming from Your Highness... But ya kamata ka fahimci girma ne ya hau kanku both you and your wife, dole ku sadaukar wasu lokutan naku ga al’umma.. Your Highness you can’t back down now.. I mean ya zamuyi da d’imbin manyan mutanen da aka gayyata.. Mai zamu fita mu sanar dasu..?!”
Mahmood ya shafe fuskarsa a hankali had’ida fuzar da huci “Just come up with something.. Whatever, ko kuma a nad’a wani ba dole sai ni ba..”
Baikai aya ba Turaki ya katsesa da fad’in “But you’re their choice.. Kaine zab’in mutane.. People chose you.. I’m sure you don’t want to disappoint your People... Babu wanda yafi cancanta sama dakai your Highness.. Na tabbata ita kanta Muhibbah bazata so jin haka daga gareka ba balle Ja’afar da mahaifiyarka.. Please do this for them.. for your people.. And for me as well..!” Ya k’arashe cikin tsananin rauni...
Mik’ewa Mahmood yai suna duban juna shida Turakin... Lokaci guda yake furta “Ko da yaushe kana tare dani, through good times and worse... Ka wuce aboki a wajena Turaki.. You’re my brother, kai d’in d’an uwa ne a wajena... Today I want to thank you from the bottom of my heart...For everything...” Katsesa Turaki yai da fad’in “That’s what brothers are for... Bani da buk’atan kamin godiya your Highness.. Fata ne shine Allah ya sanya maka albarka a aurenka ya kuma yi maka jagoranci a shugabancinka.. Allah ya shiga al’amaranka abokina..!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa harda ‘yar guntuwar hawaye cikin idanunsa...
Su duka biyun murmushi suke suna duban juna suna sauraro yanda Sautin algaita da tambura ke kuma gauraye d’aukacin Masarautar ...
A haka Ja’afar ya shigo ya taddasu ya sanar dasu komai ya kammalla su ake jira...