← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 162

Sashe 8

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umaima Ta jinjina kai kana tace “Da alama ke d’in ‘yar baiwa ce.... Inaji a jikina zan k’aru dake sosai ko ince Masarautar nan zata k’aru dake sosai....” Ta k’arashe cikin sigar wasa...
A tare sukai murmushi mai d’an sauti kana Umaima tace “Bara naje na turo miki aike, nima zan shigo anjima kad’an.... Feel at home dan Allah kinji...”

Jinjina mata kai kurum Muhibbah tai had’ida kuma mik’a godiyarta a gareta...

Umaima na ficewa Muhibbah ta mik’e ta yaye tapkeken labulen tagar tana lek’en yanda k’wan wuta suka kuma k’arawa Masarautar kyau da tsari da shike almuru ya doso... Nan Ta hangi Fu’ad na fitowa Daga b’angaren Mahaifiyarsa kaman zai kifa da k’asa, yanayin data gansa ciki har yafi na ganinsa d’azu da tai... Tai saurin janyo alkyabbar Umaima wanda d’azu Ta barta a nan d’akin... Cikin sauri ta rufa alkyabbar akanta ta janyo hular ya sauk’o kusan idanunta kana ta d’an waiga gefe da gefenta, a hankali ta fito ta nufi hanyar da taga Fu’ad yabi cikin sand’a.....

SameenaAleeyou📚
[5/24, 9:28 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑*

*007*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Lokaci ne na almuru hakan yasa ko bayi ma jifa jifa kake gani, kowa yana k’ok’arin komawa mahutarsa ne.... Hakan yasa sam babu wanda ya lura da Muhibbah da tuni ta takewa Yarima Fu’ad baya.....

Sashe ne madaidaici ya shigo mai kyaun gaske, gini a jere masu kama da juna wanda ko ba’a fad’i maka domin yaran Sarkin akai, nan Muhibbah Ta hango Fu’ad ya shige d’aya daga cikin dogayen ginin...
Tana nan tsaye taji motsin mutum na dosowa cikin sashen... Gabanta ya yanke ya fad’i tai saurin matsewa jikin gini k’irjinta bai daina bugu ba, jin tafiyar take Tamkar mab’oyar da take aka nufa.... Jim kad’an sai hango mutum tai ya shige parlorn da taga Fu’ad d’in ya shige... Ta fito daga mab’oyarta cikin sand’a kana ta nufi saitin window d’in parlorn ta lab’e jiki tana lek’e...

Sosai ta hango Fu’ad na kuka tamkar k’aramin yaronda ya kasa jin lallashi... Yana tsugune gaban drawer dake jikin center table da akima parlorn ado dashi sai faman bincika drawer d’in yake yana kuka sosai, duk wasu tarkacen dake cikin drawer d’in jifa Fu’ad keyi dashi, gaba d’aya ya hargitsa wajen ya wargaza... Can ya ciro wasu magunguna cikin sachet yana k’ok’arin b’are ledar maganin... K’wayoyin sun kusan guda goma jikinsa na matuk’ar rawa musamman hannayensa da ya rik’e k’wayoyin dasu... Take ya d’aga kansa sama had’ida lumshe idanunsa masu zuban ruwa ya toshe hancinsa da hannu guda yana k’ok’arin watsa drugs d’in a bakinsa saiji yai an bigesu sun zube k’asa.... Ba Fu’ad dake k’ok’arin bud’e lumsassun idanunsa a hankali ba harta Muhibbah saida ta d’ago idanunta tana duban wanene ya hana Fu’ad aika ma cikinsa da k’wak’walwarsa wannan gubar....

Jamal ne tsaye ya hard’e rai sosai tamkar bai tab’a dariya ba, lokaci guda ya durk’usa suna fuskantar juna shida Fu’ad d’in....
Fu’ad ya matsa can jikin k’afar kujera yana tak’urewa waje guda yake fad’in “No...No no Jamal, I don’t want to live... I’m tired of living like this Jamal.. na gaji.....Na gaji Jamal....!” Ya k’arashe yana mai bin drugs d’in yana tattarosu tamkar dai mai tab’in hankali... Cikin zafin nama Jamal ya kamo fuskar Fu’ad yana fad’in “Look up Fu’ad, kalle ni nan....!” Ya k’arashe yana mai kuma matse fuskar Fu’ad da tuni har ya koma ja sabida tsananin damk’a da yasha....
Dole Fu’ad yai shiru sai duban Jamal da yake da idanunsa masu zuban ruwa, lokaci guda Jamal Keci gaba da fad’in “Now you’d do exactly as I say...!”
Girgiza kai Fu’ad yake da k’yar yana mai furta “No no Jamal... No...!!” Ganin bazai shiru ba ya sanya Jamal zaro wata sirinji na allura cikin aljihun wandonsa, lokaci guda yai injecting Fu’ad da allurar.... Kankace mai Fu’ad ya fad’o jikin Jamal tamkar sumamme....
Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Jamal yai kana ya rungume d’an uwan nasa sosai kaman mai tsoron kada a raba tsakaninsu.... Cikin rawar murya Jamal Ke furta “I’m sorry brother, I’m so sorry... I really don’t have a choice.... Ka yafe min Fu’ad....!” Ya k’arashe yana mai kuma k’ank’ame Fu’ad da har lokacin tamkar bai numfashi.... Lokaci guda Jamal ya mik’e ya aza Fu’ad a kafad’arsa kana ya nufi upstairs dashi, d’akinsa ya shigar dashi ya kwanyarsa saman gado, ya gyara masa kwanciyarsa sosai ya lullub’esa kana ya sauk’o k’asa ya tattare drugs d’in dake zube wajen... Saida ya tabbata ya tattare kaf drugs d’in kana ya saita kansa ya fice daga b’angaren Fu’ad....

Muhibbah dake lab’e bayan window a hankali Ta koma Ta jingina jikin bango tana maida numfashi a hankali... Meke faruwa...?” Fu’ad is living a miserable life... Meke faruwa dashi...?” Take taji b’angare na zuciyarta tana ayyana mata cewa ya cancanci fin haka, ya cancanci ya shiga k’uncin rayuwa fiyeda wanda yake ciki yanzu....Ta k’arashe tinanin tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali... Lokaci guda ta saita kanta kana ta fito daga b’angaren nasa....

Tana isowa sashen da aka sauk’eta kenan ta tadda Umaima tafe wasu kuyangi guda biyu na biye da ita d’aukeda manya manyan trays an rufe da k’yalle....
Muhibbah ta d’an sha jinin jikinta amma sai ta sami k’warin gwiwar dakewa kad’an...
Umaima dake bintada kallon mamaki ta bud’e murya tace “Hibba ina kika fito da magrib d’in nan...? Hope all is well...?”

Muhibbah ta murmusa kad’an kana tace “Gida na mulki da sarauta yanada gizo da kuma cika idanu, amma saidai dikda wannan gizo da cika idanu nasa idan wanda bai tab’a zama cikinta ba ya halarceta tabbas zaija yana matuk’ar k’aunar ya zaga cikin gidan ya baiwa idanunsa abinci.... Tsananin son naga yanda yanayin Fadar take ya sanyani fitowa, amma saidai koda na fito na lura dare ya sako Kai babu abinda zan iya gani... Sannan naji tsoron nai gamo da abubuwa na babban gida wanda da yawan mutane suka aminta cewa a cikin Masarauta ko wacce iri ne akwai d’inbin abubuwa da idanunmu bazasu iya gani ba... Allah yasa banyi wani laifi ba ranki shi dad’e...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarta...

Cikeda jin dad’in baiwan kalamai da Muhibbah kedashi saman harshenta Umaima ta girgiza mata kai kana tace “Bakiyi laifin komai ba sai guda d’aya...”
Muhibbah ta d’an d’ago tana dubanta tana jiran taji laifin nata, nan ta tina cewa Alkyabban Umaima ne jikinta, ta d’ago da zummar bata hak’uri saidai tuni Umaima ta katseta da fad’in “Laifinki shine kink’i ki daina kirana Ranki shi dad’e... Sunana Umaima, Ki kirani da Umaima kawai....”

Murmusawa kad’an Muhibbah tai tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana tace “Tuba nike bazan sake ba... Umaima....!”
Umaima ta jinjina kai kana tace “Shigar sarauta ta amsheki, kiso kiga yanda Alkyabba tai kyau sosai a jikinki....” Tai maganar fuska fal fari’a....
Cikeda jin nauyi Muhibba tace “I’m sorry na saka babu izini.....”
Umaima ta kuma murmusawa kana tace “Babu matsala dik lokacin da kike so zaki saka, hasalima hardai kina rayuwa cikin gidan nan zaki koyi saka kayan sarauta... Mu k’arasa ciki gobe idan Allah ya kaimu zan zagaya dake da kyau cikin Masarautar nan....”

Muhibbah ta d’an ware manyan idanunta kana tace “Da gaske...?”
Jinjina mata kai Umaima tai kana tace “K’warai kuwa zan zaga dake kiga ko ina... Allah yasa dai bakida makaranta goben....?”

Sai yanzu Muhibbah ta tina ashe Wai makaranta ne ya kawota garin... K’ak’aro murmushi tai kana tace “Satin nan akai resuming so babu wani karatu mai tsauri da za’ai...”
Umaima ta jinjina kai kana tace “Hakan na nufi kin amince kenan...”
Muhibbah Ta jinjina mata kai murmushi bai bar saman fuskarta ba... Lokaci guda suka sa kai suka k’arasa cikin madaidaicin parlorn kana bayin suka take masu baya...

***

Dare ya ratsa, k’afafuwa sun d’auke a cikin fada, bakajin komai sai kukan k’anan halittu wanda wasu idanu na basu iya hangosu cikin duhun dare... Dikda cewa Masarautar gauraye take da hasken fitilu da ya k’ara mata kyau....
Jakadiya ce ke gaba da ita, bak’ar Alkyabbace mai nauyin gaske tai mayafi dashi, baka iya hango komai sai alamun bak’in abu... A haka suka isa k’ofar, hannu tasa cikin wata k’aramar aljihu dake jikin bak’ar alkyabbar nan ta zaro wata ‘yar k’aramar mabud’i... Gini ne a zahiri domin kaw sam bazakai zaton wannan waje akwai k’ofa ba balle kai zaton har akwai mabud’i da zai bud’e ta har biladama ya ratsa Ta cikinta...Take ta soma fad’in wasu abubuwa tamkar yare lokaci guda ginin ke sauya launi alamun k’ofa na bayyana... Kafin ta k’arashe karanto surkullen nan k’ofa Ta bayyana... Mik’awa Jakadiya ‘yar makullin tai kana Jakadiya ta amsa ta bud’e... Abinda zai baka mamaki shine wannan waje da sam bazakai zaton akwai k’ofa wajen ba saigashi ya bud’e, sannan ba wannan kawai ba mataye ne cike a wajen, ‘yan mata daga kimanin shekaru goma sha hud’u zuwa ashirin da d’oriya, babu alamun namiji a wannan waje sai mata.... Da alama wata Al’umma Ke rayuwa cikin wajen...Suna shigewa matayen nan dake sanye cikin shiga iri guda suka risina gaba d’ayansu... Jakadiya da Giwa basu zarce ko ina ba sai wani k’aramin d’aki dake daga cen center....
Daga k’ofa Jakadiya ta tsaya dan bata shige cikin d’akin ba, yayinda Giwa ita kad’ai ta shige cikin wannan d’aki mai cikeda duhuwa... Wani jan darduma mai d’aukeda Tambarin Masarautar Giwa ta d’ale ta zauna... Zamanta babu jimawa saiga wani Dattijo ya bayyana gabanta, bak’ik’irin dashi gashi yai masa duguzun a jikinsa, idanunsa jajazir haka nan sumarsa gabaki d’aya fari ne sol... Murmushi maras kyaun gani saman fuskarsa yake dubanta....

Risinar da kanta tayi alamun gaisuwa kana tsohon ya yaryafa mata wani ruwa dake a hannunsa,bai daina mummunar murmushin nan ba yake fad’in “Nasan zakizo nan sabida ta bayyana kuma babu wani abu da ya faru a Fada face cecekuce tsakanin Yaranki...!”

Jinjina masa kai Giwa tai kana tace “Tal’udu...! Mun duba gabas da yamma kudu da Arewa babu wani abu bak’o da ya faru, sannan babu wani rai da aka rasa, Tal’udu kar kace min Cikin Yarana guda babu wanda zai gaji Karagar mulkin Masarautar nan...!” Ta k’arashe tana mai tsaresa da kyawawan idanunta wanda suke cike dam da butulciwa mak’aginta.....
Chapter 8 · 0% Book details