Sashe 92
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda suka iso masarauta Mahmood ya tadda Zahra bacci ma take hankali kwancewa a d’akinta... Yai mata k’uri kaman mai tinanin wani abu, lokaci guda ya janyo mata k’ofan d’akin ya rufe... Yana ficewa Zahra ta bud’e idanunta a hankali tana sauk’e ajiyan zuciya lokaci guda tana addu’an Allah yasa Plan d’in Aunty Muhibbah yayi aiki akan Paa d’inta zai fasa Auren wannan mai suffar mayun.... Ta k’arashe tinanin nata tana mai darawa harda ‘yar tsallanta saman gado....
Mahmood na ficewa sashensa ya komo yanda ya tadda Zuhra zaune saman darduma alamun isowarsa take jira, har lokacin bata daina matsan hawaye ba....
Tana jin sallamansa tai k’ok’arin saita kanta had’ida risinawa Ta gaidashi...
Mahmood ya amsa cikeda tausayinta yasan tayi hak’urin zama da d’anuwansa... Can kujerarsa ya isa ya zauna kana ya soma fad’in “Zuhra, Yazeed mijinki ne kuma nasan kinyi hak’urin zama dashi tsawon shekarun da kukayi tare... Bazan hanaki yanke duk hukuncin da kikaso gameda ci gaba da zama dashi ba... Idan kin yanke hukuncin tura sak’o Masarautarku bazan hanaki ba sabida Ke aka zalunta, sannan idan kin yanke hukuncin komawa Masarautarku shima duk bazan hanaki ba... Kinada duk wani zab’i gameda ci gaba da zamanki cikin Masarautar nan... Idan har ni ne Sarki zan baki goyon baya d’ari bisa d’ari akan duk hukuncin da zaki yanke... Amma saidai inaso na miki wata tambaya Zuhra.! Shin ya akai kikasan abinda Ke wakana har kika tafi wancan gidan..?!”
Ta risina kad’an tana goge hawayen da suka kuma gangaro mata “Rankaidad’e sak’o na samu an turo min cikin wayata cewa Yazeed yana cikin wane yanayi naje na cecesa... Shine najeni nai wannan mugun ganin...!”
Mahmood yai shiru yana mamakin jin cewa itama batada masaniya gameda alak’ar Yazeed d’in da Raheemah..!
Jinjina kansa yai a hankali sai kuma ya d’an nusa yace “Kikace sak’o aka turo miki da bak’uwar lamba..?!”
Zuhra ta jinjina kanta a hankali “K’warai Rankaidad’e, sak’o aka turo min gashi ma ka gani..!” Ta k’arashe tana mik’a masa wayar....
Ya duba sak’on sosai kana ya ciro wayarsa yai comparing sak’wannin... Lambobi daban daban ne suka tura masu sak’on... Koda yayi dialing wannan lambar ma bata shiga... Watak’ila ma mai turo sak’on ya karya SIM cards d’in... Fuzar da fuci yai a hankali ya mik’a mata wayar... Ta tabbata Zuhra kanta batada masaniyan cin amanan da mijinta da k’awarta suke mata sai yau... Mutum gudace zata amsa masa tambayoyinsa itace d’iyarsa Zahra....
Ya d’anyi gyaran murya Murya kad’an yace “Sanda kika tadda Yazeed da Raheema sunada masaniyar naje wajen..?!”
Ta girgiza masa kai a hankali alamun a’a ta k’arada”Basu sani ba Rankaidad’e dan Raheemah har rok’ona take kada na sanar dakai don kar ka fasa aurenta..!”
Ya jinjina kai a hankali yace “Yayi kyau..!” Ya numfasa kad’an yace “Zan nemi wani alfarma a wajenki..!”
Zuhra tai saurin d’agowa tana saurarensa cikeda jin nauyin Kalmar alfarma da ya bid’a daga gareta yana Sarki, Allah yasa ba cewa zai ta yafewa Yazeed ba..! Tana tsaka da tunanin ta sinkayo muryar Mahmood d’in naci gaba da fad’in “Banaso Raheemah ko Yazeed susan cewa nasan wannan batu ko kad’an... Zaki Iya min wannan..?!”
Zuhra Ta jinjina kai tace “Bakada matsala Rankaidad’e... In sha Allah bazan tab’a sanar dasu cewa kasan komai ba...!”
Mahmood ya jinjina kai a hankali yace “Kina iya tafiya..!”
Ta risina tai masa sallama kana Ta fice jiki babu laka....
A hankali ya mik’e yana zaga parlorn nasa cikin taku d’aid’ai irinta masu Mulki....
**
Sauri sauri ta ida had’a kayanta kaf dan Allah ya gani bazata kuma kwana ko guda cikin Masarautar ba tinda Ta gama abinda ya kawota... Ta tabbata yanzu Mahmood bazai yarda da auren Raheema ba sannan Zuhra bazata ci gaba da zama da Yazeed a wannan masarauta ba... Auren Yazeed zai lalace Zuhra zata koma Masarautarsu tareda yaranta Yazeed zai zama baida kowa dan bayan abinda Mahmood ya gani bazai tab’a barinsa yayi sarauta ba... Kuma tayi imani idan maganan ya isa Masarautar su Zuhra babu Masarautar da zasu kuma yarda su baiwa Yazeed mata, shikenan martabansa ya zube... Zai rasa ahalinsa ya kuma rasa Sarautar, sannan Jamal ko yanayin da yake ciki ya ishesa Ta tabbata idan yayima Jakadiya horon da hankali bazai d’auka ba Umaima zatak’i amincewa da aurensa... Giwa kuwa halinda yaranta da MasarautarTa Ke ciki kad’ai ya isheta kuma tasan ko ba jima ko ba dad’e Ja’afar da Mahaukaciya Izzatu harmada Ubandoma zasu dawo sannan ne Giwa zata girbi duk abinda ta shuka...!
Ta saki murmushi a hankali kana Ta janyo jakan kayanta, sauri sauri ta fice daga cikin Masarautar...
Tsaye tayi daga can nesa tana k’arewa Masarautar kallo, a hankali ta furta “Alhamdulillah..! A yau ni Saudatu na kammala abinda ya dawo dani wannan Masarauta mai bak’in tarihi a gareni... Zan koma ga mutaneda suka amsheni suka maidani mutum bayan an wulak’antani anci mutuncina an tozartani...! Ni Saudatu Sabon shafin rayuwa zai kuma bud’e min tareda masoyina na gaskiya Dr Ansar..!!”
Ta saki murmushi a hankali kana tasa kai rik’eda jakan kayanta...
Sanda ta isa tashan mota ta samu babu motar da zata kuma tashi saidai Washe gari... Wata mata mai saida abinci bakin tasha ne Ta taimaka mata da wajen kwana zuwa Washe gari, Akai sa’a matar mai mutunci taceda ita budurwa kamanta haka bai tsari ta fito tashan motoci cikin dare ba sabida yanda duniyar Ta lalace, mugaye sunyi yawa wani dama kad’an zai samu sai ya cutarki... Muhibbah tai mata godiya sosai tace ta riga ta fito daga cikin makaranta ne kuma idan Ta koma baza’a bud’e mata shiyasa amma in sha Allah nan gaba zata kiyaye...
Taita mata godiya kan taimakon da tai mata... Washe gari kuwa motar sassafe tabi zuwa garin Bauchi...
**
Dandatson mutanen da ta ganine a unguwar tasu yasa gabanta mugun fad’uwa... Ko ba’ace ba taron d’aurin aure ne.. Toh auren wa ake d’aurawa..?! Tambayar da taiwa kanta zuciyarta naci gaba da tsinkewa...
SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH*
*58*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Bata iya bi Ta gaban masallacin unguwar tasu ba wanda yake babu nisa da gidansu hakan yasa mutane har k’ofar gidan nasu, ga kuma ababen hawan mutane a pappake Kota ina...
Cikin sauri ta canza hanya tabi ta k’ofar baya k’irjinta naci gaba da bugawa musamman data hango Ansar tsakiyan abokansu sunata d’aukan hotuna, yasha farar shadda k’al kaman wani Ango...
Jiki babu laka ta nufi cikin gidan ta nan k’ofar bayan yanda ta tadda Iya Larai na shanya...
Ganin babu mutane cikin gidan nasu ya d’an sauk’ar mata da natsuwa k’ila auren d’aya daga cikin abokansa ake a unguwar...
Suka gaisa da Iya Larai tai mata sannu da zuwa sai zolayanta take da fad’in “Amarya ta dawo Amarya Ta dawo...!”
Wad’annan kalaman Iya Larai d’in ya kuma haifar mata da fad’uwan gaba “Amarya kuma..?!” Ta nanata a hankali... Kardai hasashenta ya zamto gaskiya..?! Bata iya kuma tsayawa sauraren Iya Larai ba sai sa kai da Tai cikin gidan tana ganin hanya na had’e mata... Babban abinda ya kuma sanyar mata da jiki shine hango akwatuna da kayyaki barbaje tsakiyar parlorn da tai, Mommy da wasu k’awayenta guda biyu Anty Gudidi da Aunty Salamatu sai shirya kayayyakin suke wanda komai set biyu ne...
Aunty Salamatu fad’i take “Oh Ansar mai tagwayen mata... Kaga yaro d’an baiwa... Mommy dai sai murmushi take tana Allah san barka yayinda Anty Gudidi ke faman tab’e tab’en baki tana fad’in “Ni wllhi bansan dalilin da yasa kika aje tsintacciyar mage gidanki ba Murjah... Kuma Wai har k’i k’are kice zaki had’ata aure da d’anki... Tabd’im haka kawai babu wanda yasan asalinta, yarinya ta zauna ta tsara maku k’arya kun yarda.. Waima a wace duniyar kika tsintota ne..?!”
Mommy Ta katseta da fad’in “A’a Gudidi, Muhibbah ba tsintacciyar mage bace, d’iya ce kaman kowa... Sau nawa zance miki a hanyarmu Ta dawowa daga Lafia muka tsinceta can wajajen dajin garin Jos, wllhi abin tausayi b’arayin daji sun kashe Iyayenta makiyaya suka k’ona rigarsu da dabbobinsu itama suka biyota zasu kasheta Allah yasa muka tsinceta, lokacin Ansar na ajin k’arshe a Secondary sch hasalima d’aukosa mukaje can makarantarsa dake Nasarawa Lafia toh a hanya muka tsinceta, Ansar da Sabo driver na suka dage kan cewa mu taimaka mata... Muka d’aukota muka kawota gida mukai mata duk abinda ya dace har makaranta ta koma... Kuma ban tab’a danasanin rik’e Muhibbah ba musamman da yanzu zata zamto matar d’ah nah..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta...
Aunty Salamatu tace “Oh Allah sarki gaskiya Hajiya Murjah kinada zuciya mai kyau, Keda kika amshi musulunci daga baya har kin fimu da muka taso cikin musulcincin zuciyar imani... Allah k’ara ire irenku masu taimako babu dalili...!”
Aunty Gudidi Ta katseta da fad’in “Ba maganan imani ake a nan ba, maganar makomar d’anta muke... Wayasani koma B’arayin dajin sune iyayen yarinyar nan, haka kurum d’anki ya auri dangin ‘yanfashi azo ana haifa maki jikoki ‘yantadda babu gaira babu dalili... Shifa aure d’an asali ne... Asali ake jiye miki Murjah da abinda ka iya zuwa yazo in the future...!”
Daidai lokacin Muhibbah tai sallama jiki a sanyaye, Mommy Ta fad’ad’a murmushinta “A’a Hibbatu... Lale lale barkada sauk’a...!” Ta k’arashe cikeda fari’a...
Muhibbah na murmushi ta k’araso ta duk’a gabansu kanta a k’asa Ta gaidasu....
Mommy da Aunty Salamatu ne kawai suka amsa mata da sakin fuska ita kaw Gudidi a dak’ile Ta amsa mata tana aika mata muguwar kallo... Mommy tace “An gama jarabawar lafiya inji..?”
Muhibbah ta jinjina kai a hankali “Eh Mommy..!”
“Toh Masha Allah... Ubangiji ya baku sa’a... Kinga kin dawo a daidai ga kayyakin Ki nan da na ‘yar uwarki Hameedah...!”
Muhibbah dai bata iya cewa komai ba sai sadda kanta da Ta kumayi tana k’ak’aro murmushi da k’yar... Aunty Salamatu tace “Oh Murjah bakya bari ko d’an surkunta ya soma shiga tsakaninku ba... Duk kinsa tana jin kunya... Tashi Ki shige abinki..!”
Mommy Fad’i take “A’a babu wani surkunta tsakanina da d’iyata...!”
Gudidi Ta katse zancen da fad’in “Ke tashi kije kin wani zauna kin tsare mutane yaran yanzu babu kunya...!”
Muhibbah bata kuma cewa komai ba ta mik’e ta nufi ciki Mommy na fad’in maza tai wanka ta fito taci abinci....