Sashe 58
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tai k’ok’arin tarttaro natsuwarta gaba d’aya, murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskrta “Your Highness... Barka da yammaci.!” Tai maganar tana mai daidaita tsayuwarta...
Kaman bazaice komai ba har wannan lokacin, sai dubanta da yake daga nan yanda yake tsaye hannayensa hard’e Ta baya... Gaba d’aya sai tajita ba daidai ba, zuciyarta yaci gaba da bugawa da sauri sauri... Maiyasa yake dubanta haka..? Kodai ya karanceta ne ya soma zarginta... Kai inaa hakan bamai yuwa bane, musamman yanzu data soma samun hanyar da matsalanta zai warware.. She can’t allow someone to get suspicious of her...Tai saurin d’ago idanunta aiki nan idanunsu ya sark’e waje guda.. Fuskar nan nasa tamau... Ta had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’oshi ya kasa shigewa....
Gyaran murya Tai kad’an tana k’ok’arin had’o kalamai saman bakinta “Tuba nake your Highness... Na zaci kowa zai iya ziyartan Zauren ajiya na.....” Burki tai ma kalaman nata ganin ya soma d’ago k’afafunsa yana takowa cikeda k’asaita... Zuciyarta taci gaba da bugawa ganin ita yake nufowa... Tai saurin lumshe idanunta tana k’ok’arin karanto duk addu’an da yazo bakinta...
Dai dai gabanta Mahmood yaja ya tsaya har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya yai k’uri ma labb’anta yanda take motsasu a hankali alamun tana karanto addu’a, a hankali yake k’arewa fuskar nata kallo tin daga labb’anta zuwa karan hancinta har zuwa idanunta da suke a lumshe masu cikeda tsoro... Wani irin yarr yaji gaba d’aya illahirin jikinsa... Yanayin da ya jima baiji hakan ba a tsakanin lokacin... A hankali ya janye idanunsa daga barin duban nata, cikin takunsa mai cikeda k’asaita ya soma takawa har ya isa gaban wani k’aton hoto mai k’unshe da zanen mutane cikin shiga irinta mulki da sarauta... Ya kafe hoton da idanu hannayensa hard’e ta baya...
“Halittanmu baisha bambam da mutanen da sukazo kafin mu ba, saidai halayya da d’abi’unmu sun banbanta...Wani zamani muke ciki wanda cin amana da yaudara, zalunci da k’eta su sukafi jagoranci sama da kyawawan d’abi’u masu nagarta...!” Ya k’arashe yana mai juyowa...
Tinda ya soma magana take k’ok’arin bud’e idanunta a hankali har Ta ida waresu...
Daga nan yanda yake tsaye yai gyaran murya kad’an yace “Having curiosity aroused..?!”
K’ak’aro murmushin da yafi kama da yak’e tai ta d’ora saman labb’anta “K’warai your Highness... Masarauta mai cikeda d’inbin tarihi da kyawawan d’abi’u had’ida al’adu irin haka... Babu wanda zaiso ya shigo cikinta ya tafi ba tareda ya yi dubi da wad’ann kyawawan hikayoyi da suka aje Martaban Masarautar har Ta kawo tsawon wannan lokaci...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta..
Baisan dalili ba amma tunda ta soma magana yakejin kumatunsa na motsawa kad’an sihirtaccen murmushi da ba lallai ka fahimci hakan ba shine sama fuskarsa tasa...
Ya d’an gyara tsayuwarsa yana dubanta sosai, saida yai taku kaman guda uku, sai kuma yaja ya tsaya “You seemed so sure...?!” Ya fad’i yana dubanta....
Ta kuma murmusawa kad’an tana mai k’arasawa jikin wani k’atoton zane mai d’aukeda hoton wani basarake sanye da rawani da alkyabba wanda ko ba’a ce ba kasan dadd’en zane ne... Tasa hannu tana shafa wasu rubutun da akai k’asan zanen da haruffan ajami na Arabic... Lokaci guda taci gaba da furta “An samu Masarautar ne ta hanyar nagartattun mutane wanda jajircewarsu da k’wazonsu had’ida gaskiyarsu da son gaskiyarsu sune suka had’u suka kafa Daular... Kuma da sannu al’umman Masarautar zasuyi fatan magadansu suyi koyi da kyawawan d’abi’u masu nagarta irin nasu... Fata mai kyau a koda yaushe yana tafiya tareda Al’umma nagartacciya ce Rankaidad’e...!” Ta k’arashe tana mai juyowa gareshi...
Kai tsaye bazaice ya fahimci duka abubuwan data fad’i ba, amma har k’asan zuciyarsa yake jin kalaman nata.... Ya isa jikin k’atoton hoton ya tsaya gefe da ita, su duka biyun suna duban hoton... Cikin kalmomi da basu shige uku zuwa biyar ba ya fad’i k’arnin da aka kafa Daular a tak’aice...
Ta karkato kad’an tana dubansa murmushi saman fuskarta... Lokaci guda tace “Ka iya bada labari your Highness... Kodai History ka karanta...?”
Duban da yai mata ya sanyata had’iye sauran zancen nata tana mai furta “Tuba nake Rankaidad’e...!”
Baice komai ba sai soma takawa da yai zauren na amsa sautin duk wani aje k’afarsa da zai a k’asa mai cikeda charisma...
Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai furtawa cikin zuciyarta _Muhibbah nemi abinda ya kawoki kafin lokaci ya k’ure miki.._ Take ta hangi wani dogon shelf d’aukeda manyan takardu da littafai, ta waiga gefe da gefe bata hangi Mahmood ba hakan ya bata daman k’arasawa jikin shelf d’in cikin sauri tana dubawa a hankali...
A yayinda shima Mahmood d’in tsaye yake ta bayan shelf d’in yana bincika takardu wanda zai iya kamanceceniya da zanen gidan sarauta da Wambai ya damk’a masa...
A tare suka hango wani littafi mai tarihin gaske, ba tareda sun sani ba sai kai hannunsu sukai lokaci guda kowanne cikinsu na son ya d’auki littafin.... K’irajensu ne suka buga sakamakon jin hannayensu da sukai cikin na juna sun sark’afe waje guda...
Muhibbah tai saurin zaro idanu waje zuciyarta naci gaba da bugawa.... Hannunsa guda yasa ya matsar da littafan da cikin shelf d’in dan tabbatarwa idanunsa cewa hannunta ya rik’e...
Sukai tsaye suna duban juna ta cikin shelf d’in... Muhibbah ce ta soma yunk’urin janye hannunta cikin tsananin rawar jiki, saidai fuzge hannunta da zatai k’atoton ma’ajiyan takardun ya dawo kanta....
Suka d’aga idanu suna duban katakon yanda ya nufota... Tsayuwa kurum tai had’ida dafe kanta tana jiran mai aukuwa ya auku.. Lokaci guda ta saki wane irin k’ara... Bata ankara ba sai ji tai ya bangajeta gefe guda katakon ya fad’o kansa...
Muhibbah dake zube gefe dafe bakinta tai da duka hannayenta biyu tana mai kuma firfito da idanunta waje ganin bata ko hango Yarima Mahmood sai k’uran shelf d’in nan da ya fad’o kansa.... Gaba d’aya k’ura ya turnuk’e wajen..
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai zuciyarta Ke nanatawa... A d’ari ta mik’e ta nufo wajen tana ambato sunansa amma shiru bai amsa ba, zuciyarta ya kuma tsinkewa... Take taji hawaye na neman ciko idanunta... Ta shiga k’ok’arin janye shelf d’in daga kansa tana kiran sunansa amma inaa shiru babu amsa... Hawaye na gangaro mata take kuma k’ok’arin janye k’atoton katakon da ko motsa sa bata iya yi... A hankali k’uran Ke lafawa yanda Ta soma hango fuskarsa da k’ura ya lullub’e idanunsa a lumshe....
Cikin azama taci gaba da k’ok’arin janye katakon tana furta “Yarima..! Yarima please wake up... Dan Allah ka tashi..!!”
**
Yazeed ya kuma relaxing cikin gadon yana mai rakata da idanu shu’umar murmushin nan nasa saman fuskarsa...
Raheema ta margino cikin k’irjinsa tana shafa fuskarsa a hankali take furta “You seems to be in a good mood Your Highness... Fad’a min sirrin...” Ta k’arashe cikin salo tana mai fatan ya zayyano mata komai gameda shirinsu shida Majidad’i kan Mahmood cikin zuciyarta...
Sumarta yake shafawa a hankali murmushin bai bar saman fuskarsa ba “Well, I’ve every reason to be in a good mood... Soon enough burina zai cika..!”
Raheema Ta kuma gyara kwanciyarta sosai tana mai dubansa take furta “Wow... Da gaske.. Ba dai burinka na zama sarki ba..!”
Yai murmushi da gefen bakinsa yana mai dubanta da wutsiyar ido wannan karon “Very soon komai a Masarautar nan zai zamto yana k’ark’ashin iko na... Kowa zai zama yana k’asa dani... Sai abinda nace kuma sai abinda naga dama za’ayi... Ciki harda Yaya na Mahmood..!” Ya k’arashe muguwar murmushin saman labb’ansa...
Raheema Ta kuma zama sosai tana dubansa lokaci guda tana k’ok’arin karantarsa... “Tell me... Mai kake shiryawa...?!”
Da wutsiyar idanu ya kuma dubanta wannan karon ma... “Sabida kije ki fad’awa Mahmood..?”
Ta d’an sha jinin jikinta kana tace “Ban gane naje na fad’awa Mahmood ba... Mai kake nufi Zeed..?!”
Murmusawa ya kumayi lokaci guda ya mik’e yana mai zura tufafinsa yake furta “Drop the act Princess... You can’t fool me... Na gane nufinki...And believe me bazakiji komai daga bakina ba... Kinyi kuskure da kikai underestimating d’ina... You might be a woman but Prince Yazeed AbdulJabbar ya shige duk makircin wata mace Sweetheart..!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi had’ida zira zobbansa yasa kai ya fice...
Gimbiya Zeenat dake lab’e jikin staircase tana ganin shigewan Yazeed ta fuzar da fuci a hankali.. Ta rasa Raheema wace irin kariya ce mai take samu wajen wannan watsettsen Yazeed d’in da ta tabbata ko sarautar ce bazai tab’a yi ba... A fusace Ta nufi d’akin da Yazeed ya fito yanda Ta tadda Raheema na shirin fitowa...
Fincikota tai Ta dawo da ita baya tana fad’in “Shige ki Fada’ min uwar mai kuka gamayi Keda watsettsen can...!!”
**
Duk iyaka k’ok’arinta Ta kasa janye katakon, gaba d’aya itama ta jigata, tuni ta kwab’e alkyabban jikinta tana k’ok’arin had’o duka k’arfin da Allah ya huwace mata ganin Ta ceci rayuwar Mahmood... Ganin dai bazata iya janye katakon ba ya sanyata saurin nufa k’ofa neman agaji... Saidai wani tashin hankalin shine ta kasa koda motsa k’ofar ne abinka da ginin zamanin da mai aminci.... Ta shiga dukan k’ofan tana kiran taimako nan ma shiru dan yanda ginin Keda matuk’ar zurfi da tsawo zai wuya na waje ya iya saurarenka...
Sabbin hawaye suka kuma ciko idanunta, yanzu idan ya mutu nan no one would believe cewa ba ita ta kashesa ba.... She can’t let him die here...! Lokaci guda ta koma da baya tana mai ci gaba da k’ok’arin janye k’kk’arfan katakon mai minci... Da k’yar da nishi ta samu ta d’an matsar da katakon.. Lokaci guda tana mai kuma ambato Yarima, daidai nan Mahmood ya soma tari da atishawa alamun yana fitar da k’uran da ya shak’a.... Muhibbah tai hamdala cikin zuciyarta tana mai ci gaba da k’ok’arin janye katakon take furta “Rankaidad’e ka tashi... Alhamdulillahi... Sannu Rankaidad’e...!”
Hannu yasa da k’yar ya matsar da katakon daga kansa yana mai k’ok’arin mik’ewa da k’yar had’ida kakkab’e k’uran dake bisa jikinsa... Sai faman sannu take masa fuska fal damuwa, harda ‘yar murmushin da bata San ya subce mata ba...
Ta kuma matsowa kusansa kad’an tanai masa sannu... Ido ya d’ago yana dubanta wanda ya sanyata stepping back kad’an...
Lokaci guda yake furta “Are you hurt..? Did something happen to you..?”
Saurin girgiza masa kai tai alamun a’a.. “I’m fine your Highness, babu abinda ya sameni... We need to get out of here...”