← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 162

Sashe 54

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K’wank’wansa k’ofan da suka sinkayo ne ya sanya Waziri komawa da baya kad’an ya wani risina kaman mutumin arziki yayinda Giwa ta k’arasa saman kujera tai zamanta...

Jakadiya ce ta shigo cikin d’ingishi ga fuskarta gaba d’aya a kumbure sai tururin man zafi ne Ke tashi a jikinta... Waziri yaima Giwa sallama yayinda Jakadiya ta k’araso tana mai gaida Waziri...

Kallo guda Giwa tai mata ta ayyana cikin zuciyarta lallai Jakadiya ta daku wajen mahaukaciyar nan, amma ya suka iya haka dole zasu sake komawa har Izzatu ta bud’i baki ta sanar dasu yanda zasu sami Saudatu kafin tayi ajalin mulkinta...

Jakadiya ta zube da k’yar tana nishi take gaida Giwa... Giwa ta amsa a dake ko sannu da jiki Jakadiya bata sami darajan wannan ba wajen Giwa...

Murya a dake Giwa Ke fad’in “Jakadiya wajen Izzatu muka nufa..!”

Gaban Jakadiya ya yanke ya fad’i, ta d’ago kumburarren idanunta tana duban Giwa tsoro dabaibaye saman fuskarta “Allah shi baki yawan rai matar nan fah zata iya kisa... Anya bazamu k’yaleta..”

Batakai aya ba Giwa ta aika mata wani irin muguwar kallo, lokaci guda take furta “Yaushe kika fara sanar dani abinda ya kamata nayi Jakadiya...?!”

“Tuba nake Allah shi taimakeki... Ayimun aikin gafara..!!” Ta k’arashe tana mai sadda kai...

Giwa Ta kauda fuskarta gefe tana mai furta “Zamuje muga Izzatu daren yau dan haka Ki shirya...!”

‘Yan hanjin Jakadiya suka kuma kad’awa, cikinta ya bada wani sautin k’ara, Allah ya gani ko sunan Izzatu taji an ambata yanzu sai gabanta ya fad’i...
Tamkar ta kurma ihu haka ta daure tana amasawa Giwa murya cikin inda inda....
Kana ganin Jakadiya kasan ba har cikin zuciyarta take maganar ba akan dole takeyi...

**

Tafe yake cikin mota hannunsa duka biyu saman steering wheel, har lokacin itada Fu’ad yake hangowa cikin idanunsa, maiyasa tunanin ya kasa barin zuciyarsa, maiyasa suka kasa b’ace masa daga k’wayan idanunsa... Maiyasa ma abin Ke damunsa in a any case...! Ya d’an fuzar da fuci kad’an yana mai dukan steering wheel da hannunsa maras ciwon.... Yana k’ok’arin saka trafficato kenan ya d’ago idanunsa yana duban mirror nan ya hangi wata mota tamkar tana biye dashi... Idan bai b’ata gani ba wannan motar tun fitowarsa daga masarauta take biye dashi... Speed ya rage kad’an kana ya canza hanya...
Yana ganin mai motar ma yai slow kad’an yana k’ok’arin juyawa...

Mahmood ya murmusa kad’an yana mai ci gaba da driving d’insa...

Kai tsaye gidan Turaki ya nufa ya kirawo Turakin yace dashi gashi nan tafe ya fito haraban gidan kawai ya jirasa dan ba shiga zai ba...

Turaki ya fito waje yana jiran isowar Mahmood.. Jim kad’an Mahmood ya k’araso, Turaki ya isa da kansa ya bud’e masa gate...

Mahmood ya shigo cikin gidan yai parking motarsa a parking lot... Turaki ya nufo garesa yana tambayarsa meke faruwa...

Dubansa Mahmood yai yace “Bani car keys d’inka...”

Turaki ya dubesa da mamaki saidai baice komai ba ya nufi cikin gidan, Jim kad’an ya fito da key ya damk’a masa...

Mahmood ya amsa cikin sauri kana ya nufi ma’ajiyan motar Turaki..

Turaki ya d’an k’araso yana tambayarsa meke faruwa

Kaikaitowa Mahmood yai yace “Kaikam zamuyi magana idan na dawo, just make sure mota ta bata fice daga cikin gidan nan ba..!”

Jinjina masa kai kurum Turaki yai yana mai furta “Do you want me to come with you..?”

Girgiza masa kai kurum Mahmood yai yace “Kar ka damu kaidai kawai kayi yanda nace...”

Turaki ya jinjina masa kai yana mai masa fatan sauk’a lafiya...

**

Mahmood yana fitowa daga gidan Turaki bai zarce ko ina ba sai asibiti wajen Baba Wambai kaman yanda likitan ya sanar dashi cewa Baba Wambai ya farka amma sunan Mahmood d’in kurum yake ambata tinda ya farfad’o shisa bai kirawo kowa ba sai shi...

Mahmood ya k’araso cikin sassarfa yanda Likitan tuni ya tareshi... Tare suka nufi cikin d’akin Mahmood na tambayarsa ya jikin Baba Wambai...

Suna shiga d’akin ya hango Wambai kwance idanunsa na kallon sama... Mahmood ya k’arasa cikin sauri yana ambaton sunansa... Lokaci guda yakai hannunsa ya dafa saman na Wambai yana mai furta “I’m here Baba...!”

Baba Wambai da idanunsa Ke duban sama a hankali yake kuma ambato sunan Mahmood da k’yar cikin muryarsa da bai fita sosai tamkar ta ‘yan koyo, lokaci guda yake k’ok’arin ciro wani takarda k’asan matashinsa... Mahmood yai masa K’uri yana duban abinda Baba Wambai keyi... Lokaci guda ya d’ago hannunsa dake tsananin rawa rik’eda wata ‘yar takarda ya aza saman hannun Mahmood....

Mahmood ya rik’e takardan yana juyawa a hankali daidai sanda Majidad’i da mahaifiyarsa suka shigo d’akin a kid’ime....

Saidai shigowarsu Keda wuya Wambai ya soma wane irin numfashi tamkar ransa zai fice cikin jikinsa.....

Dr ya k’araso da sauri yana mai umartansu da su fice su basu waje domin su duba jikin Wambai....

Majidad’i kuwa sai fuzga yake yana ambaton sunan mahaifinsa... Nurses sai turasa waje suke yana tarjewa... Mahmood ne ya kamo hannunsa yana k’ok’arin fitar dashi yayinda Majidad’in ya d’ago jajayen idanunsa yana duban Mahmood cikin wane irin huci....

SameenaAleeyou 📚
[7/28, 9:43 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*37*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Turaki yai turus yana duban Mahmood da ya koma tamkar babu laka jikinsa... Lokaci guda kuma yai saurin basa hanya yana fad’in “Shigo daga ciki Your Highness...!”

Babu musu Mahmood yasa kai ya shigo cikin parlorn ya k’arasa ya zauna saman kujera, har lokacin bai iya ceda Turaki komai ba...

Glass of water Turaki ya mik’awa Mahmood d’in yana fad’in “Have some water..”

Nan ma babu musu ya amsa ya kurb’a kad’an... Turaki ya k’arasa ya zauna saman kujera mai kallon na Mahmood d’in....

“Talk to me Your Highness... Meke faruwa..? Ya jikin Baba Wambai..?”

Sumarsa ya shafa da duka hannayensa biyu had’ida fuzar da fuci a hankali “Dole na bar cikin asibitin Turaki...That idiot almost creates a scene there regardless of his father’s condition....!”

“Kana nufin Majidad’i...?”

“Who else..!” Ya bashi amsa yana mai kuma kurb’an ruwan...

Fuzar da fuci kad’an Turaki yai sai kuma yace “Allah dai ya baiwa Wambai lafiya ya tashi kafad’unsa, jikina na bani ta hanyarsa zaka sami wasu amsoshin da ka jima kana nema...”

Bai rufe baki ba Mahmood yakai hannunsa cikin aljihu tamkar wanda ya tina wani abu, nan ya ciro takardan da Wambai ya damk’a masa ya shiga warwareta...
Turaki yai masa K’uri yana duban yanda yake ware takardan...

Tas ya warware yana duban hoton zanen gida tamkar na sarauta.... Ya jima yana duban hoton yana k’arema zanen kallo...

“What’s that..?!” Turaki ya tambaya...

Ba tareda ya amsa masa ba ya mik’a masa zanen... Turaki ya amsa yana juya zanen mai wahalan fasaltuwa... Ya d’ago ya dubi Mahmood “Ina ka sami wannan...?”

“Wambai ya bani before na bar asibitin...!”

Turaki yai shiru yana mai kuma duban zanen.. “Kaman ginin gidan sarauta..” ya fad’i yana mai kuma juyawa...

Mahmood ya jinjina masa kai alamun tabbatarwa... “Bansan mai yake nufi da dank’a min wannan zanen ba, amma koma menene nufinsa nasan zanen nada matuk’ar mahimmanci..!”

Turaki ya jinjina kai yace “K’warai kuwa,and probably it might link you to all the answers you’ve been looking for...”

Mahmood ya dubesa kad’an kaman zaice wani abu sai kuma ya linke zanen ya tura cikin aljihu, ya d’ago ya dubi Turaki “Ya labarin neman Jafar... Have you found something yet...?”

Ya girgiza masa kai a hankali “Dik yanda nake tunanin abin zaizo da sauk’i ya wuce haka... But kar ka damu ina nan ina bincike...”

Mahmood ya kuma jinjina kai a hankali...

Turaki ya d’an kuma muskutawa yace “Wai mai ya faru ka aje motarka a gidan nan ka fita da tawa..?”

Dubansa da gefen idanu Mahmood yai yana mai kuma kurb’an ruwan dake hannunsa, saida ya kwashi wasu dak’ik’ai kana yace “I noticed Someone was following me... Dole nai branching a gidanka dan ya rasani... I’m sure ko wanene Ubangidansa yana can yana basa bad news..!”

Turaki ya murmusa kad’an yana mai duban Mahmood da har lokacin juya cup d’in dake hannunsa yakeyi ya k’urama waje guda idanu... Ba komai yake hangowa ba face Fu’ad da Muhibbah... Ya d’an lumshe idanunsa a hankali had’ida fuzar da fuci lokaci guda yake kauda fuskarsa zuwa wani b’angaren... Sosai yake so ya yakice tinanin amma ya kasa...

Gyaran murya kad’an Turaki yai yace “But your Highness are sure babu wani abu dake damunka kuma... You seemed preoccupied..”

Mahmood ya dubesa kad’an ya kuma kauda kai gefe, bayan shud’ewan wasu dak’ik’ai ya mik’e yana furta “With everything that has been going on you still ask me that question..... I’ll go ahead Zamuyi magana anjima... Keep me posted idan akwai abinda ya canza regarding the search for Jafar...”

Turaki ya jinjina masa kai a hankali yana mai furta “An gama Ranakashi dad’e...”

Har saida yakai k’ofa ya juyo yana furta “Aff kaga na mance ban tambayi Madam da yara ba...”

Turaki ya murmusa kad’an yace “Daga baya kenan Your Highness, bayan kayi nisa duniyar tunanin Gimbiya Raheema.. Toh Madam da yara duk suna lafiya, gobe suke cika sati guda a Jalingo, inaga cikin satin nan zanjeni na d’aukosu dan duk gidan ya min girma gwara su dawo hutun ya isa haka...”

Sai wannan lokacin Mahmood ya murmusa kad’an yace “Ashe dai kaid’in gawro kake...!” Yai maganar yana k’ok’arin had’o kalaman wanda daji kasan bai saba ba...

Turaki ya murmusa kad’an yana mai mik’ewa tsaye danyiwa abokin nasa rakiya, lokaci guda yake furta “Na shigo layinku Rankaidad’e for the time being muji yanda kukeji tunda kak’i kaba da himma kan batun Auren nan naka...!” Yai maganar yana sosa kai...

Mahmood dai murmusawa kurum yai without saying a word... Turaki ya kasa gane cewa shid’in ba aure ne ko soyayya ne ya dawo dashi ba... Yanada babban dalilinsa, dalilin kuwa shine to find answers and get justice ga wad’anda aka zalunta cikin Masarautar....

**

Wani jahilin mari Waziri ya kuma sauk’ewa d’an Aiken nasa wanda Ke bibiyan Mahmood... “Ashe kai shashasha ne ban sani ba, ta yaya Mahmood d’in zai b’ace maka... A iska yake tafiya kokuwa....!”
Chapter 54 · 0% Book details