← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 162

Sashe 152

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gimbiya Zeenat ta dubeta galala tace “Bak’in ciki kike so nayi.. Mutanen da suka mana halacci, yau da sunso bayan irin k’ulle k’ullen da mukai cikin Masarautar nan da sun koremu daga cikin Masarautar nan...Amma basuyi ba suka amshe mu hannu bibbiyu... Yau ko Masarautarmu kinaji kina ganin wulak’ancin da suka mana a lokaci aurenki sai gashi su Sun amshe mu Sun mance duk abubuwan da mukai a baya.. Ke nayi bak’in ciki na mai bayan wanda Allah ya riga ya d’agasa kai baka isa ka karyasa ba.. Ya kamata ki d’auki darasi cikin abubuwan da suka faru a Masarautar nan... Yau Ina Giwa da ahalinta..? Babu su kaman an shafesu a doron k’asa wasu ma sun fara mancewa dasu tun basu bar duniyar ba.. Toh ita rayuwa haka take, abinda ka shuka shi zaka girba.. Kiyi wa’azi ma kanki Raheemah, kiyima kanki karatun ta nastu tin kinada ikon yin hakan... Idan kuma rikici zakici gaba da janyo min cikin Masarautar nan toh gaskiya banida zab’in da ya shige na sallameki daga cikin Masarautar nan.. Ko ki tafi kibi mijinki can b’angaren Bayi kokuma ki koma can Masarautar mu wanda nasan bayan abubuwan da suka faru da k’yar idan zasu amsheki...”

Baki sake Raheemah ke dubanta hawaye na gangaro mata “Aunty ni zaki kora cikin Masarautar nan..?”

“K’warai kuwa idan dai fitina zaki jazamin... I won’t hesitate to throw you away.. Dan haka gwara tun wuri Ki zaba, ko ki natsu ki zama mutumiyar kirki ko ki kama gabanki..!”

Tana ida fad’in haka tasa kai Ta nufi d’aki yanda k’awayenta Ke jiranta, sune su keta tayata shirya kyaututtukan...
Raheemah ta zauna dirshan tana matsan k’walla, yau itace Aunty Zeenat take cewa zata koreta daga Masarauta kaman wata shara.. Lallai ta yarda rayuwa ta sauya... Da k’yar ta Iya mik’ewa ta fice ta nufi Sashen Gimbiya Turai...

Tana isa ta tadda Hadimai masu kai komo a sahen Ta shiga tambayarsu ina zataga Muhibbah..

Hadima guda d’aya Ta dubeta sama da k’asa kana tace “Mai kikace..? Gimbiya Muhibbah ce kike zare Sunana ta babu wani girmamawa..?!”

Raheemah dake sakin huci tace “A wajenku ne take Gimbiya.. Nida Muhibbah ‘yar lek’en asiri na santa kuma dashi zan kirata..!” Bata kai aya ba Hadima guda ta matso zata d’auketa da mari, wacce take gefe ta dakatar da ita... Hadimar tace da kin barni na wanketa da mari dan batada wani maraba damu matar Bawa ne a cikin Masarautar nan, matar Yazeed ce..!”

Dukda hawaye da suka ciko idanun Raheemah sabida wulk’anci da wad’annan Hadiman suke mata, bai hanata hura hanci tana nunasu da yatsa tana fad’in “Zaku sani.. Duk sai kun yaba wa aya zak’inta zakusan kun shiga hurumin da ba naku ba k’ask’antattun bayi kawai..!”
Hadiman basu daina bata amsa da fad’in batada wani maraba dasu d’in ba..
Umaima da Zahra ne suka taho zasu shige sunci uban gayu irinta yaran masu mulki wanda kallo guda zaka masu kaso sake kallonsu nan suka tadda Raheemah na rikici da wad’annan Hadiman...

Umaima ta katsesu da tambayan ba’asin abinda Ke faruwa..

Hadima guda d’aya tace “Rankidad’e Wai wannan matar Bawan ne tazo nan zatai rashin kunyawa Gimbiya kuma Giwar Masarautar nan matar Amale ...Shine muke son koya mata tarbiyan Bauta tunda itama cikinmu zata shigo yanzu, ai Bawa take aure..”

Harga Allah yanda Hadimar Ke magana taso baiwa Umaima dariya.. Amma tai k’ok’arin saita kanta sanda ta sinkayo muryar Raheema tana fad’in har abada bazata tab’a zama jinin Bauta ba... Umaima tai alamawa Hadiman cewa su tafi su basu waje su barsu da Raheemah.. Babu musu suka risina sukai yanda Umaima tace...

Umaima ta dubi Raheemah tace “Kiyi hak’uri da abinda Hadiman nan sukai miki, Kinsan...”

Katseta Raheemah tai da fad’in “Where’s Muhibbah.. I need to speak to her right this instant..”

Umaima bata kaiga bata amsa ba Zahra Ta k’araso gabanta rik’eda kunkumi.. Tana duban Raheemar daga sama har k’Asa lokaci guda take furta “Ba ko wace shara bace take iya ganin Sarauniya kai tsaye.. Dan haka bazaki samu ganinta ba, Ki b’ace a nan kafin na saka wad’ancan Hadiman su b’atar dake da k’arfin gaske..!” Ta k’arashe tana ware manyan idanunta..

Zuciyar Raheemah taci gaba da tururi, ta yunk’ura zata cakumo Zahra take fad’in “Ke yarinyar nan wllhi yau sai na cire miki rashin kunyarki tsaf naga gatanki dan ko Ubanki bazai iya k’watanki ba...!”

Umaima tai saurin shiga tsakiya, yayinda Zahra taci gaba da fad’in “Ya riga ya miki nisa nisanda sai gani daga nesa... Saidai Ki k’are da auren Bawa..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta...

Umaima ta girgiza kai tace “Raheemah ki tafi kawai, bazaki samu ganin Muhibbah ba.. Just go please..”

Zahra ta kuma katseta da fad’in “Har sai kin rok’eta Sis..? Ai kawai wad’ancan Hadiman zamu sa suyi mata bugun surfe a turmi...! Zaki b’ace ne ko sai na kirasu..?” Zahra ta kuma fad’i cikin daka tsawa wanda saida ‘yar muryar tata ta firgita Raheemah.. Babu shiri ta juya da baya tana jin zuciyarta na mata wane irin d’aci...

Tana shigewa Umaima ta dubi Zahra tana girgiza kai, lokaci guda kuma suka tintsire da dariya a tare musamman da suka dubi yanda Raheemah Ke buga sauri tana waige waige tsoron kar hadiman nan su capkota...
Zahra ta tab’e baki tace “Allah dai ya ceci Paa wannan matar a naira goma aka baka ita an cuceka wllhi.. Can ta k’arata wutsiyar rak’umi yayi nesa da k’asa Paa d’ina ya d’ara ajinta.. Saidai a k’are a fannin Bayi..!”

Umaima Ta janyo hannun Zahran tana fad’in “Yarinyar nan bakida da Dama, ni ko shige muje Meenatu naga missed call din Meenatu nasan yanzu haka Sistu Ke nemata..”

“An gama Rankidad’e..!” Zahra ta fad’i harda ‘yar risinawarta... Suka kuma murmusawa a tare kana suka shige...

**

Yamma Lis suka iso bayan Yawale ya gama baccinsa, yaji Ac yasha bacci harda su miyaun bacci...
Ansar na ida parking bai tashesa ba saida ya ciro wayarsa yai making call yana fad’in gasu nan sun iso... Yana zaune gefe yana duban Yawale dake ci gaba da baccinsa harda su gwarti yanda kasan wanda ya kwana bai bacci ba... Jim kad’an wata Mota bak’a k’irar corolla ta iso tai parking gefe.. Ansar ya d’an bibbigi kujerar da Yawale yake bisa wanda har kwantar masa da kujeran Ansar yai dan yaji dad’in yin baccin... Ya bibbigi kujerar yana furta “Mun iso Baffah..”
Yawale ya mik’e zaune da k’yar yana mutsuka idanunsa wanda har lokacin da sauran bacci ciki.. Lokaci guda yake furta “Mun iso Yakubu...Oh Yakubu wannan wane irin gida zamuje da sai yanzu muka iso.. Kodai Habuja muka taho zaka yanka min tikin kujerar Makkah na sauk’e farali bana..”

Ansar bai amsasa ba sai bud’e masa marfin Mota da yayi yace “Baffah gasu nan..!”

Ai a d’ari Yawale ya kuma ware idanunsa yana sake murtsukasu ganin k’artai da yayi tsaye bisa kansa sun rurrufe fuskokinsu da bak’ak’en masks...

Jiki na rawa Yawale ya soma furta “Kalu Innalillahi.. Yakubu mai zan gani..? Ina ka kawoni..? Su waye wad’annan..?!”

Ansar yace “Baffah ba kud’i kake so ba shiyasa ka saida Muhibbah, Toh ai wad’annan da kake gani sunji labarinka kana saida yaranka da sunan aure shine suka taho suna nemanka, sud’in masu cinikayyan bil’adam ne.. Da suka sameni nace ‘ya’yan Naka sun k’are dan Ta k’arshen kenan ka aurar min shine suka bani kud’in kanka mukayi cinikin kanka dasu.. Yanzu haka zan kaima Innah kud’in kanka tinda da dai ace ka saida sauran yaranka mata k’anana gwara ace babu kaid’in.. Gwara a sayar dakai.. Yara kuma k’annen Hameedah zan rik’esu in sha Allahu.. Amma ka gama saida Bil’adama Baffah..” Ya k’arashe yana fad’in ku d’aukesa..

Cikin kuka had’ida tsananin tashin hankali Yawale yake fad’in “Kamin rai Yakubu.. Nifa k’anin mahaifinka ne..! Kuma ita wancan yarinyar ai ba jininmu bane, Kai kana tunanin zanyi haka ma ‘ya’yan ciki na ne..! Dan Allah ka rufa min asiri dama akanta kawai nayi haka kuma bazan sake ba..!” ya k’arashe yana kuma zillewa had’ida daka tsalle yana son k’wacewa daga hannun mutanen...

Ansar ya dakatar dasu ya dubi Yawale yace “Auho sabida ba ‘yarka bace shine ka zab’i ka cutar da ita koh.. Ka bayarda ita ga mutanen da baka San daga duniyar da suke ba ka aura ma d’iyarka saurayinta koh..? Toh ai d’ah na kowa ne Baffah.. Muhibbah d’iyarka ce tinda kaine alwalinta.. Kawai kaje Allah yajik’anka Baffah.. Allah yasa k’arshen wahalan kenan.. kar ka damu zan kula da iyalanka in sha Allahu..! Ku tafi dashi..!” Ya k’arashe yana kuma masu umarni..

Yawale yaci gaba da tsalle yana kokawan k’wace kansa yake fad’in “Kamin rai Yakubu.. Kaji k’aina Yakubu.. Wllhi na tuba.. Na tuba bazan sake ba..!” Inaa tuni gardawan mazan sun jefa Yawale cikin mota mai lullub’e da tint..

SameenaAleeyou 📚
[10/9, 1:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*86*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Gefe ya koma yanda Turaki Ke tsaye yana dariyar Baffah Yawale da Dogaran da suka b’adda kama suka sauya tufafi harda rufe fuskokinsu da masks... Turaki yace “Gaskiya Likita baka kyautama surkinka ba.. Ya zaka sake had’a idanu da d’iyarsa..?”

Ansar ya murmusa kad’an yace “Mai Sarauta kenan, ai ni nasan halin Baffah tinda tin ina k’aramin yaro Babana ya rasu.. Babu irin karan tsaye da Baffah baiyiwa rayuwata data mahaifiyata ba duk akan abinda Babana ya bari, ba don Allah ya rufa asiri Mahaifiyata tsaye take kan k’afafunta ba wajen neman abinda zata rufa mana asiri da yanzu Allah kad’ai yasan yanda rayuwata zata kasance sabida Yawale ya handame duk wani abinda mahaifina ya bari da ka sani...”
Chapter 152 · 0% Book details