← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 162

Sashe 147

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Tana tsaka da kukan taji hannayen mutum saman arms d’inta.. Cak ta had’iye kukan nata sakamakon jiyo dadd’an k’amshinsa da tai wanda yayima k’ofofin hancinta sallama...

Mahmood ya mik’ar da ita tsaye, har lokacin bata daina ajiyan zuciya ba, ta kuma kasa d’ago idanu ta dubesa..

Mommy ta mik’e sad’af sad’af ta fice ta basu waje, kyakkyawan murmushi saman fuskarta.. Hadimar Gimbiya Turai taceda Mommy ta biyo bayanta dan Tuni Gimbiya tace ai mata iso...

Parlorn ya rage saura Mahmood da Muhibbah, kanta saman k’irjinsa ta kasa d’agowa sai ajiyan zuciya da take...

Kaman mai rad’a yake furta “Maiyasa kike kuka, ba Abinda kike so na baki ba..?!”

Kasa cewa komai tai dan har lokacin ajiyan zuciya take... Mahmood yaci gaba da fad’in “Na cika miki alk’awarinki na baki abinda kika jima kina so ..!”

Sai Sannan ta d’ago pale eyes d’inta ta dubesa, shid’inma ita yake duba, lokaci guda yace “Oya open it.. Bud’e ki karanta dan nasan baki karanta ba...!”

Yanda Yai maganar a tsare ya kuma sanyar mata da gwiwa, Ta mak’e masa kafad’a tace cikin rawar murya.. “Ni banaso naci jarabawar..!”

Sosai ta basa dariya amma ya tsime yace “Don’t you want be brave again..?”
Ta kuma mak’e masa kafad’a..
Ya murmusa kad’an har lokacin tana cikin k’irjinsa hab’arsa saman kanta da shike ya d’arata a tsawo, lokaci guda yaci gaba da furta “Bakisan cewa Sarki baya sab’a alk’awari ba..? Sunnan Sarakuna ne yin magana d’aya tak.. Dan idanma baki bud’e ba ni zan sanar dake da bakina..!”

Hawaye suka kuma gangaro mata, sharad’in saki shine idan bata karanta da idanunta ba ko kuma idan bai fad’a mata da bakinsa taji ba Tabbas bata saku ba shiyasa ma tak’i karantawa..

Muryarsa ya kuma katse mata tunani “Hibbah open that envelope and read now..!” Cikin tsananin dakewar murya yayi maganar..

Tasa bayan hannunta ta share hawayen da suka kuma zubo mata, lokaci guda Ta shiga warware envelope d’in hannayenta na matuk’ar rawa... Zuciyarta naci gaba da tsananta bugawa...
Cak Ta tsaya da abinda take sakamakon sinkayo muryarsa da tai yana fad’in “Idan kin gama karantawa Jakadiya tana jiranki a k’ofa..!” Daga haka bai kuma cewa komai ba ya fice cikin taku irinta masu mulki hannayensa hard’e Ta baya..

Muhibbah ta lumshe idanunta, wasu hawayen suka gangaro mata, Wato ma Jakadiya ce zatai mata rakiya zuwa k’ofar Fadah.. Aiko ya bari dai tayi sallama da ‘yaruwarta Umaima da kuma Ummi...
Lokaci guda tasa d’aya hannunta tana share hawayenta take furta “Enough Muhibbah, ya isa haka... Ina amfanin zama da mutumin da bai k’aunarki.. Tinda ya zab’i ku rabu, fine, sai ku rabu d’in.. He’s not worth a single drop of your tears..!” Lokaci guda ta shiga warware takardan a hankali..

Cak Ta tsaya tana kuma nanata abinda ta gani saman takardan, a hankali Ta furta...
“DNA test result..!”

Idanunta suka sauk’a k’asa, sunanta take gani ga kuma sunan Zahra... Zuciyarta tai wani irin tsinkewa... A fili take furta “70% matched..!” Kenan itada Zahra are related... Kusanci mai tsanani wanda zasu iya kasancewa sun had’a both iyaye.. Kenan Zahra ‘yaruwarta ce da suka fito ciki guda, mahaifiyarta da mahaifinta aune suka haifi Zahra... Take taji duniyar na juya mata.. Ta dafe kujera a hankali ta zauna tana kuma juya takardan.. Nan wata takardan Ta fad’o tai saurin d’auka Ta warware da zummar karantawa..

Daidai lokacin Ummi, Mommy da Umaima suka shigo...

SameenaAleeyou 📚
[10/5, 6:23 AM] +234 703 881 5154: *MUHIBBAH*

*84*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Takarda ce mai k’unshe da bayanan komai gameda Zahra... Hawaye basu daina zubowa daga idanunta ba take ci gaba da juya takardan, ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansu d’aya bayan d’aya, sud’inma ita suke duba hawaye saman fuskokinsu... Umaima ta d’an dafe hannunta guda tace “Go ahead Sis, read it... Read..!” Ta k’arashe murmushi da hawaye saman fuskarta...

A hankali Muhibbah ta jinjina mata kai kana Ta soma karantawa
Chapter 147 · 0% Book details