← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 162

Sashe 39

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dubansa Giwa tai ba tareda ta furta komai ba kana ta nufi wata k’ofar yanda zai fitar dakai sararin veranda dake a saman benen...

Suna shigewa Giwa ta kuma dubansa kana tace “Ina saurarenka Yazeed mai kuma Mahmood yai wannan karon...?”

Yazeed ya kuma fuzar da fuci kana yace “Kan mai zaice zai saka CCTV cameras cikin Masarautar nan..? Maami hakan karya dokan masarauta ne, cin amanan tsari da tarihin Masarautar nan ne... Sannan wulak’anta babban gida irin wannan ne... Yanzu inada tabbacin cewa kin yarda Mahmood bashi ya cancanci gadon sarautar nan ba, tin yanzu tin bai d’ale Karagar ba gashi nan yana nema ya kawo sauye sauye cikin Masarautar nan... Yana nema ya rusa ya lalata duk wasu al’adu na cikin gidan nan tin shekara da shekaru... Yana neman ya kawo mana d’ab’un Yahudu da Nasara cikin Gidan... Maami Masarautar nan bazata tab’a amincewa da wannan ba sam..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci...

Giwa da taji wani irin gumi na neman keto mata, duban Yazeed Ta kumayi kana tace “Bakaji da kyau ba Yazeed... Ta ya Mahmood zaizo da batu irin wannan cikin Masarautar nan, tin iyaye da kakkani ba’a tab’a zuwa da batu mai kama da wannan ba... Hakan wulakanta ahalin gidan nan ne..!!” Ta k’arashe cikin tsananin tashin hankali...

Kaman daga sama suka sinkayo muryar Yarima Mahmood yana fad’in “A’a Maami hakan ba wulak’anta ahalin gidan nan bane... Hakan na nufin tsare ahalin gidan nan ne... Kuma babu gudu babu jada baya, kaman yanda ka fad’i Yazeed tabbas za’ai instilling cameras cikin Masarautar nan ta ko wane b’angare domin tabbatar da tsaro cikin Masarautar.... Abubuwa da dama Sun faru cikin Masarautar nan kuma suna kan faruwa, misalin mutuwar mahaifina da akace heart attack ne yai ajalinsa, mutuwar matata wacce gawarta kawai aka sinkaya cikin d’aki... Sannan b’acewar Ja’afar da har yau babu shi babu dalilinsa... Don’t you think duka abubuwan da na lissafa sunada connection...?!” Ya k’arashe d’aukeda alamun tambaya hannayensa hard’e Ta baya yayi tsaye gaban Yazeed su duka biyun suna fuskantar juna... Babu alamu ko gizau na shakku da tsoro a tattareda Mahmood...!

Giwa kuwa tuni kanta ya soma juyawa, hankalinta yakai k’ololuwa wajen tashi, batai zaton Mahmood went far har haka ba... Lallai tayi gangancin raina capabilities d’in wannan d’an mijin nata... Mai zatai yanzu kafin Mahmood ya tono sirrikan gidan, shin anya batai ganganci uzzura masa ya dawo Nigeria ba..? Ya zata dawo dashi yazo yana yak’arta... Karfa maganan Tal’udu ya tabbata cewa Mahmood yak’i ya dawo yai da ita, dole tasan abinyi... Dole tasan yanda zatai ta takawa Mahmood birki da wannan shiri nasa da yakeyi... Muryar Yazeed ta sinkayo yana fad’in “And kana tinanin kashe maka matarka akai cikin Masarautar nan...? Ko kana tinanin kashe mahaifinmu akai...?!”

Mahmood ya katsesa da fad’in “Everything is possible a gida irin wannan, d’ah zai iya kashe Uba dan ya gaji Kujeran mulkin mahaifinsa...!!”

Cikin murya mai yanayi da kuka Giwa ta katsesa da fad’in “Haba Sadauki ya zakake magana haka..? So kake kace cikin ‘yanuwanka wani ne ya kashe mahaifinku dan ya gaji sarauta... Shin akan wannan mulkin ne rabuwar kai da zargi ke neman shiga tsakaninka da ‘yanuwanka, shin zargin ahalinka kake da alhakin mutuwar mahaifinku da matarka... Sadauki ban zaci haka daga gareka ba... Da zuciya d’aya nai muradin ka dawo ka amshi jagorancin Masarautar nan a matsayinka na babban Magajin mahaifinku... Da ace nasan abinda zai dawo dakai kenan rabuwar kawunanku da ahalinmu da banyi burin ka dawo ba... Bana nufinka da komai daga kai har ‘yanuwanka sai alkhairi amma bazan so naga kawunanku ya rabe ba... Mahmood kaine Babba cikinku kai ya kamata ace ka had’a kan ahalin nan sai gashi kana k’ok’arin rabawa tin ina raye balle ace Babu ni... Nayi zaton I can count on you koda bayan raina ashe nayi kuskure..!!” Ta k’arashe cikin kuka kana ta nufi saman d’aya daga cikin kujerun shak’atawa dake baje fsrfajiyan Ta zauna tana hawaye...

Dafe kansa kad’an Mahmood kana ya nufi Giwa ya duk’a gabanta, cikin kwantar da murya yake fad’in “Maami baki fahimci ne... Please karki mun mummunan fahimta...”

Katsesa tai da fad’in “Banaso na fahimceka Mahmood... Ka bani kunya, a koda yaushe nida mahaifinku mun zaci kaine zakabi yanda yake tafiyar da mulki da kyawawan d’abi’unsa da halayyarsa, kuma kaine zaka had’a kan ahalin gidan nan... Ashe munyi kuskure, na godewa Allah da mahaifinka baiga rana irin wannan ba tabbas da wannan maganan Naka shi zai kashesa fiyeda bugawan zuciya..!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin kuka daidai lokacinda Jamal ya shigo....

Jiki a matuk’ar sanyaye ganin mahaifiyarsu na hawaye dan ba k’aramin abu Ke sakata kuka ba, sannan ga Yayansu Mahmood duk’e gabanta ga kuma Yazeed nan tsaye gefe yana sakin shu’umin murmushin nan nasa, ya sakasu gaba yawa TV...

Jamal ya dubi Yazeed yana tambayarsa meke faruwa “Yazeed what’s going on here... Why’s Maami crying..?!” Yai tambayar cikin tsananin tashin hankali...

Yazeed bai daina murmushin ba saima gyara tsayuwarsa da ya kuma yi yana fad’in “Why not ask your beloved brother... The one you all think is a saint, I’m sure yanada ansar da zai baka don na tabbata shine dalilin zuban hawayen mahaifiyarmu...”

Da mamaki Jamal ke duban Mahmood da tuni ya mik’e tsaye yana aikawa Yazeed wane irin firgitaccen duba...

Jamal ya d’an tako kad’an yana duban Mahmood yake fad’in “Yaya mai Yazeed yake fad’i... Shin da gaske sabida kai Maami Ke kuka...?!” Kafin Mahmood yakaiga basa amsa suka sinkayo muryar mahaifiyar tasu tana fad’in “Jamal Yayanku zargin ahalin nan yake... Yana zargin ahalinsa da alhakin mutuwar mahaifinku da matarsa gashi har yana k’ok’arin dasa na’urorin cameras da zasuke hasko masa abinda ke wakana cikin gidan nan dikda ya sani cewa yin hakan wulak’anta Martaban Masarautar nan ne..!” Ta k’arashe tana mai kuma matsan k’walla...

Lokaci guda Jamal ke duban Mahmood yana fad’in “No Yaya you can’t do that... Yin hakan tozarta al’adu da tarihin Masarautar nan ne... Yaya idan akan mutumin da kake tinanin ka gani jiya cikin Masarautar nan ne shisa kake yunk’urin aiwatar da wannan abu bana tinanin nima zaka sami goyon bayana... Ko wane masarauta Yaya sunada d’abi’a da kuma tasu al’adun... Abinda kake shirin yi kaman bud’e duk wasu sirrika na Masarautar nan ne da wasu kafi na tun iyaye da kakanni... Yaya I’m sorry but I don’t agree with you either..!” Ya k’arashe yana mai k’arasawa ga mahaifiyarsu ya rik’o hannunta yana fad’in “Maami muje ki huta, this isn’t good for your health..!”

Mahmood yabi mahaifiyarsu da kallo har suka fice kana ya maidoda dubansa ga Yazeed wanda ke ci gaba da sakin shu’umin murmushi, lokaci guda Yazeed d’in ke furta “Slowly slowly Yaya...I’ll prove to everyone that I’m better than you, sannan ni ne nan na cancanci Karagar nan, na fara daga cikin gida zan isa har izuwaga wad’anda sukeda alhakin nad’a sarki a Masarautar nan...!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi kana yasa kai ya fice...

Fu’ad dake tsaye daga k’ofa mugun kallo suka aikawa juna shida Yazeed har Yazeed d’in ya fice kana Fu’ad ya k’arasoga Yayansa Mahmood...

Murmushi suka sakarma juna Fu’ad d’in na k’ok’arin gaidashi, ko ba’ace ba Kasan Mahmood k’arfin hali kurum yake...

Kai a risine Fu’ad ke fad’in “Yaya dan Allah kayi hak’uri da Yazeed da halayyan da yake maka... Baka cancanci hakan ba...!”

D’an dafasa Mahmood yai murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake fad’in “Is Ok Fuad, nasan Yazeed tun yarinta... So babu wani d’abi’a nashi da yake Sabo a idanuna... Kar ka damu kaji koh...!” Ya k’arashe yana d’an buga kafad’anshi...

Jinjina kai Fu’ad yai a hankali kana yace “Yaya dama akwai abinda nake so na fad’a maka...!” Wanann karon cikin tsananin nuna damuwa yai maganar, tsoro da tashin hankali kwance saman fuskar Fu’ad...

Mahmood yai masa K’uri kana yace “Ina saurarenka Fu’ad mai kake son sanar dani...!”

SameenaAleeyou 📚
[7/4, 7:09 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*027*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Kasa magana Fu’ad yai sai duban Mahmood da yake da idanunsa wanda tuni sun sauya launi... A hankali Mahmood ya dafasa “Fu’ad... Brother are you alright...?!”

A hankali Fu’ad ya jinjina kansa yana mai k’ok’arin had’o kalamai saman harshensa... Daidai nan Jamal ya k’araso yana sakin murmushi had’ida aikawa Fu’ad wani irin duba... Yarima Mahmood yace “Fu’ad ina saurarenka menene zaka sanar dani..?!”

Fu’ad ya soma k’ok’arin saita kansa sabida irin duban da Jamal Ke aika masa, tuni ya soma ‘yan kame kame... Mahmood ya dafa kafad’arsa kad’an “Fu’ad, ka natsu ka sanar dani abinda kake son sanar dani....”

Jamal ne ya katse zancen da fad’in “Yaya our little brother here wanted to tell you that he’s going back to school, zai koma makaranta yai karatunda baiyi ba a baya... Right Fu’ad...?!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa yana mai tsare Fu’ad d’in da idanu...

Fu’ad ya d’an shafa kansa kad’an yana duban Jamal, lokaci guda ya jinjina kai a hankali “Eh haka ne... Haka ne Yaya, na yanke shawari ina so na koma makaranta...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya...

Mahmood ya d’an dafasa kad’an cikeda tausayinsa kana ya janyo dokin wuyarsa irin yanda babban wa keyiwa k’ani suka nufi wasu kijeru na shak’atawa dake nan farfajiyan suka zauna...

“Fu’ad nayi matuk’ar farin ciki daka yanke shawarin komawa makaranta... Kuma zan baka goyon bayana d’ari bisa d’ari kaji koh... So tell me, wane makaranta ne ka yanke shawarin komawa...?”

D’an fuzar da fuci kad’an Fu’ad yai kana yace “I haven’t decided yet Yaya, ban zab’i makaranta ba tukuna...”

Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali kana yace “Ka zab’i dik yanda kake so kuma a ko wacce k’asa... Saidai a shawarce nafi so kayi karatun naka a nan gida Nigeria, if possible ma a jami’ar garin nan ta yanda bazakai nesa da gida ba...!”

D’an dubansa Fu’ad yai cikeda k’auna kana ya jinjina kai yace “In sha Allah Yaya, and this time around I won’t disappoint you...!”
Mahmood ya kuma murmusawa yana mai buga kafad’an Fu’ad a hankali kana yace “Yayi kyau Fu’ad... May Allah always be with you...!”
Chapter 39 · 0% Book details