← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 162

Sashe 162

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yai tsaye yana dubanta yanda take bacci hankali kwance ga Baby a gefenta. A hankali ya k’arasa ya duk’a gaban gadon.. Yai mata K’uri yana duban fuskarta da yai fayau dashi.. A hankali ya sumbaci goshinta yana mai duban fuskarta kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.. A hankali take bud’e idanunta har ta sauk’esu saman kyakkyawan fuskarsa.. Suka sakar ma juna murmushi, lokaci guda yakai hannunsa guda yana shafa fuskarta, a hankali yake furta “How are you feeling my Queen..?!”
Hannunsa Ta sakale cikin nata had’ida sumbatar hannun nasa tace “Good.. I’m feeling Good my King.!” Murmushi bai bar saman guskokinsu ba suke ci gaba da duban juna cikeda so da k’auna.. Mahmood ya zauna gefenta kad’an kana yasa hannu ya d’auki jaririn dake kwance gefenta Sai wutsil wutsil yake alamun ya tashi bacci.. Ya sumbaci yaron a goshi yana mai lumshe idanunsa.. Muhibbah tai masu K’uri tana godiya wa mahaliccinta da ya lullub’eta da wannan rahama bayan iftila’in rayuwa data fuskanta kala kala wanda bata tab’a tsammanin rayuwa zata sauya mata irin haka ba..

Ya shiga jijjiga yaron daketa k’ok’arin tsala kuka yana lallashinsa yake furta “C’mon Champ, Paapa is here.. Are you hungry..? Or do you wanna go horse riding my prince .. Shiii is okay, Maama is still weak ka barta Ta huta kaji koh..!” Ya k’arashe yana mai jijjiga yaron a kafad’arsa.. Sosai ya birge Muhibbah tai masu K’uri tana dubansu murmushi saman fuskarta.. A haka Mahmood yaita jijjiga yaron har ya koma bacci... Ya d’ago yana duban Muhibbah da tai masu K’uri ya d’an kashe mata idanu guda yace “You can go back to sleep now shima yayi bacci..!”

Murmusawa tai kad’an tace “I never knew Sarki ya iya raino haka..”
Kusan kunnenta ya matso kaman mai rad’a yace da ita “Ni kuma yanzu waye zai raine ni tunda sun rufeki a nan..Inaga dai k’arshe zan karb’i tayin da aketa min daga garuruwa daban daban ne..!” Ai bai kai aya ba tai kicin kicin da fuska kaman mai shirin kurma ihu tace “Your Highness Ummi fah zata iya shigowa yanzu kawai ka tashi kaje.. ai dama nasan ku sarakuna baku iya zama da mace guda.. So nasan wataran zakayi ai ko an maka tayi ko ba’a maka ba..” Ta k’arashe fuska a tamke kaman ba ita ba..
Ya d’an murmusa kad’an yace “Allah huci ran Gimbiya Giwar Amale...Duk suyi zamansu I don’t need to do what other Kings are doing, To me you’re more than enough my Queen..!” Ya k’arashe idanunsa cikin nata.. Ta murmusa kad’an cikeda kunya..
Shima murmushin yai yace “Wai dama haka kikeda kishi ne..?”
Murmushin ta kuma yi tana mai sanne kanta... Ya ajiye Jaririn gefenta kad’an yana mai dubansu su duka biyu.. Lokaci guda Muhibbah tace “Wanne suna zaka saka masa have you thought of the name..?”

K’uri yai mata ya kuma duban yaron kana yace “You choose the name.. Duk wanda kike so..!”
Tai murmushi a hankali kana tace “Mahmood..! Mahmood (Hamdaan)..!”

Yai mata k’uri yana dubanta kana yace “Yarima Mahmood Hamdaan ibn Mahmood..! Wow what a beautiful name.. Na gode da aka min Takwara..!”
Ta matso kusansa a hankali ta saka hannunta cikin nasa lokaci guda take furta “Ka cancanci fiyeda haka my King.. Ka haskaka min rayuwata a lokacinda nayi zaton babu wani haske da zai kuma bayyana cikin rayuwata.. Ka dawo min da Farin cikin dana rasa a rayuwata ko ince Wanda banyi zaton zan samu ba bayan iftila’in da ya auka min.. You’re not just my king Your Highness..! You’re my world..!”
Murmushi saman fuskarsa ya sumbaci goshinta zuwa labb’anta.. Lokaci guda yake furta “Manzon Allah S.A.W yana cewa _Aldunya mata’un.. Duniya jin dad’i ne.. Wa khairu mata’uddunya.. Mafi alkhairin jin dad’in duniya Almar’atussaliha.. Itace mace Ta k’warai.._ Ni nayi dace da samun mafi alkhairin jin dad’I na duniya wacce nake fatan har a aljannah ta zamto wannan jin dad’in nawa.. I love you so much My Queen..!” Ya k’arashe yana mai rungumeta had’ida lumshe idanu.. Su duka biyu suka jima cikin jikin juna kaman kar su rabu da juna har saida suka soma sinkayo kukan Yarima Hamdaan kafin Mahmood ya sassauta rik’on da yai mata.. Ya d’auki yaron ya mik’a mata, Ta shiga bama yaron abincinsa Mahmood na tayata cikeda nuna kulawa da k’auna..

Ranan juma’a akayi shagulgulan rad’in sunan Yarima Mahmood Hamdaan.. Akayi wasan Dawakai a Fadah aka buga Tambura aka busa algaita.. Kowa na son barka da Yarima da mahaifiyarsa yanda suka amshi kyauttuka kama daga kan Mai Martaba har izuwa sauran ahalin gidan.. Suna yayi albarka an cika sosai su Mommy dasu Gudidi duk sunzo harmada matar Ansar wacce itama nata cikin ya d’an soma fitowa dashike tafiyar ba wani mai tsawo bane kuma da lafiyarta shiyasa Mommy Ta amince suka taho gaba d’aya... Harta Raheemah ma tazo suna daga can masarautarsu...

Kaman yanda yake a tsarin gidan daren Jumma’an aka had’a hamshak’in Royal Gathering, kowa yai shiga Ta alfarma harta da jariri Yarima Hamdaan shima ba’a barsa a baya ba.. Yana rungume hannun Kakarsa Gimbiya Turai.. Muhibbah tai tsaye daga can saman benen Mahmood tana hango yanda aka hallara gaba d’aya Masarautar.. Hasken wuta ya gauraye ko ina tamkar rana.. Ta lumshe idanunta tana godiya wa mahaliccinta da wannan baiwa da ya lullub’esu dashi.. A hankali taji alamun Rankaidad’e Ta bayanta yanda ya rungumota had’ida d’aura hab’arsa kad’an saman kafad’arta.. Su duka biyun sukai k’uri suna kallon yanda Ahalinsu ya cika da albarka.. Zahra tana video call da Fu’ad tana nuna masa Prince Hamdaan, Fu’ad sai wasa ma yaron yake ta cikin waya kaman yana ganinsa, Umaima da Ja’afar wasu love birds d’in suna daga gefe suna zuba nasu love d’in...

Allah ya raya Yarima Hamdaan..!

Mahmood ya kuma matseta cikin jikinsa yana shak’an k’amshinta mai sanyaya zuciya..
Murmushi kwance saman kyakkyawan fuskarta take ci gaba da duban illahirin fad’in Masarautar, a hankali Ta furta “Hamdaan katheeran Ya Rabb..!”

Nima a nan na tayata da furta ALHAMDULILLAH..!

*A nan na kawo k’arshen wannan littafi nawa mai taken MUHIBBAH.. Ina rok’on Allah ya yafe min kurakuren dake ciki, fad’akarwan dake ciki Ubangiji ya amfanemu dashi baki d’aya..Ameen..!*

*Bazan iya ajiye alk’alamina ba tareda na mik’a godiyata da jinjinata a gareku ba d’imbin masoyana.. Hak’ik’a kun nuna min k’auna dani da wannan labari nawa mai taken Muhibbah.. Idan babu ku babu Muhibbah...A duk yanda kuke a fad’in Duniyar nan ina k’aunarku nima.. Ubangiji ya bar k’auna...*

*Sameena Ke maku Fatan Alkhairi...*

SameenaAleeyou📚
Chapter 162 · 0% Book details