← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 162

Sashe 13

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Jakadiya na kasa aminta Mahmood zai b’oye min babban al’amari irin wannan... Da ace wani na umarta ya gudanar min da aikin tabbas da zan amince aikin bai yuwu bane... Tabbas da zan amince Aliya bataci saiwar nan ba... Amma da hannuna na bata ta kuma ci dan bana fatan had’a iri da dangin bayi wanda basu gaji komai ba face bauta... Na kuma tabbata nayi aikin yanda Tal’udu ya umarta.... Toh ya akai bayan tafiyar Mahmood da Aliya k’asar Spaniya zasu dawo da d’iya... Kuma tabbas Tal’udu ya tabbatar min cewa yarinyar jinin AbdulJabbar ce...Shin ya akai aka haifeta bayan na tabbata da kaina Aliya bazata tab’a haihuwa da d’ahna Mahmood ba... Jakadiya wannan dalili yasa sam banajin k’aunan yarinyar cikin raina... Akwai wani rufeffen sirri gameda al’amarin yarinyar....Idan har ba Aliya bace ta haifeta toh hakan na nufin Mahmood ya haifeta da wata mace kenan...? Shin wannan dalili yasa yake gudun mulki...?” Ta k’arashe tana duban Jakadiya daga nan yanda take tsaye hannayenta hard’e ta baya...

Jakadiya dake risine gabanta k’asa, girgiza kai tai a hankali kana tace “Allah shi taimakeki kina ganin Yarima mai jiran gado zai aikata babban laifi irin wannan...? Bana tunanin zai aikata babban abun kunyaga Masarautar nan irin haka... Idan har akace yarinyar nan ‘yar gaba da Fatiha ce toh fah kinsan wannan bak’in fenti sai ya shafi ahalin Marigayi Mai Martaba gaba d’aya... Wannan dalili ka iya janyowa Sarauta ta fice cikin gidan nan Allah shi baki yawan rai....!”

A matuk’ar harzuk’e Giwa ta waigo tana watsawa Jakadiya firgitaccen kallo “K’arya ne... Wannan k’Arya ne Jakadiya... Shiyasa sam bazan tab’a bari magana mai kama da haka ya bayyana a Masarautar nan ba... Na gommaci ace wannan yarinyar jinin ‘yantacciyar baiwa ce akan ace sakamakon abin kunya ce... Bazan tab’a bari sunan zuri’ata ya b’aci ba Jakadiya....!!”

Jakadiya ta shiga jinjina kai cikin sauri tana mai furta “Wannan haka yake Allah shi taimakeki... Allah huci zuciyar Giwar Amale... Allah shi baki yawan rai shugabata.. Ki jima kinayi zuri’arki su jima sunayi... Mulkin k’asar nan taki ce ya Shugabata...!!!” Ta k’arashe tana d’aga babbar yatsawa Giwa daga nan yanda take duk’e alamun jinjina...

Giwa ta kuma sakin huci tana mai ci gaba da zagaya d’akin take ci gaba da fad’in “Na zab’i maganan ta zauna a haka, hardai bayyanarsa na nufin tarwatsa kan ahalina ne da mulki na...!”
Jakadiya ta kuma jinjina kai tana mai furta “Allah shi baki yawan rai har abada wannan magana bazai fito ba...!”

Giwa tai K’uri ma waje guda tana tinanin tabbas Yazeed ka iya sanin wani abu gameda al’amarin amma for now ta zab’i ya zauna a haka, akwai lokacinda ya dace maganar ta bayyana idan ma haka d’in ne... Ta k’arashe tinanin nata tana mai ci gaba da zagaye tapkeken d’akin nata...

**

“Yaya Muhibbah K’awatce, karatu take a nan asibitin koyarwa, batada wajen sauk’a shine nai mata masauk’i a Masarautar nan...”

Jinjina kai yai a hankali yana mai kuma takowa kad’an kana yai gyaran murya yace “Yayi kyau... Ina take yanzu...?”Ya k’arashe yana mai zama gefen Zahra

Umaima ta d’anyi gyaran murya kana tace “Tana cen b’angaren bak’i dake bayan sashen Maami..”
Jinjina kai ya kuma yi kana yace a tak’aice “Ina son ganinta...”

Umaima murmushi fal fuskarta tace “Alright Yaya zanje na sanar da ita...”
Jinjina mata kai kurum yai ba tareda ya amsata ba kana ta fice tana mai fatan samun lafiyawa Zahra...

Murmushi kad’an Zahra tai kana tace “Tanada kirki sosai Paa...”
Ya murmusa kad’an yana mai shafa sumarta lokaci guda yake furta “Akwai yanda Ke maki ciwo...?”
Ta girgiza kai alamun a’a... Sai kuma taci gaba da fad’in “Please stay here with me Paa...”

Dafa kanta ya kumayi kana yace “I’m here baby, I’m not going anywhere.. Okay...”

Jinjina masa kai Ta kuma yi murmushi bai bar saman kyakkyawan fuskarta ba... Ya sumbaci goshinta a hankali yana mai furta “I love you...”
Cikeda k’aunar mahaifin nata take furta “I love you too Papa...” Taita tina lokaci da dama da suke k’asar Spain... Saidai dikda jarumtarsa da k’warewa wajen b’oye dik wani abindake damunsa, zata iya karanto damuwa cikin idanunsa... Tin bayan rasuwar mahaifiyarta ya canza sosai amma wannan karon zata iya cewa akwai wani babban abin kuma dake damunsa, zatai iyaka k’ok’arinta wajen gano ko mai ke damun mahaifinta sannan dikda k’arancin shekarunta zatai k’ok’arin kawar masa da damuwar tinda baida wacce ta fita bayan mahaifiyarsa a halin yanzu.. Babu Maama d’inta dan haka bazataso taga mahaifinta cikin damuwa da tashin hankali ba... Suna nan a haka Rahima ta shigo cikeda d’imauta tana tambayar mai ya sami Zahra...

Zahra kaw tamkar wacce akai mata albishir da ajalinta, Rahima na shigowa ta kauda kanta gefe had’ida rausayar da idanunta tana fad’in kalamai cikin harshen spanish a hankali...

***
Ida wayarta da Ansar bada jimawa ba Umaima ta turo k’ofa ta shigo... Lokaci guda ta rungume Muhibbah tana fad’in “Kin cancanci yabo da godiya Hibbah, harta likitan da ya duba Zahra ya fad’i hakan... Zahra taji dad’I sosai da agajin gaggawa da kika bata... Ba don Ke ba ciwonta could’ve been worse... Thank you Hibbah...”

Gajeren murmushi Muhibbah tai kana tace “You don’t need to thank me Umaima, I only did what’s right... After all, haka aikin mu ya gada... And haka ya kamata dik d’an Adama ya kasance, ka taimaka a lokacinda kakeda halin yin hakan... Besides this is nothing compared to taimakon da kuka min, kuka bani wajen zama kukai welcoming d’ina cikin masarautarku...I’ll be forever be grateful..”

Murmusawa Umaima ta kumayi kana tace “Aff Kinga kafin na manta Ya Mahmood yace yana son ganinki...”

Ambato sunansa da tai ya kuma haifar mata da fad’uwan gaba, lokaci guda tai k’ok’arin dakewa had’ida zaro idanu waje kad’an kana tace “Allah yasa ba wani laifi naiwa Yarima ba....!”
Umaima ta d’an dungureta kad’an kana tace “Kinjiki da wani batu kuma... Kinga idan babu abinda kike tashi muje, nasan by now Giwa ma ta sauk’o k’Asa....”

Muhibbah ta mik’e tana mai gyara zaman alkyabban dake jikinta kana tace “Amma kafin nan sai mun k’arasa kin ida zagawa dani dik yanda ya kamata...”

Umaima ta zaro idanu waje kana tace “Aw sai mu k’yale Yaya na jira... Babban Yarima guda...?!”

Rausayar da idanu Muhibbah tai a hankali kana tace “Yarima shike son ganina bani Ke son ganinsa ba, a duk lokacinda yamin zan amsa kiransa... Dan haka nace sai mun k’arasa zagaye Fada, saidai kuma idan Yarima zai min mulkin kama karya ne... Dan na tabbata ko wani d’an adam yanada right d’insa koda kuwa k’ask’antaccen bawa ne...”

Girgiza kai kurum Umaima tai tana murmusawa kana tace “Kuma kinada gaskiya ta wani b’angaren... Amma nan goyi bayanki ba wannan karon sai don hakan kika zab’a....”
Suka murmusa a tare Muhibbah na fad’in “Naji na amince... Tinda jikin Zahra da sauk’I abinda ake so kenan... Komai zai biyo bayan wannan...!”
“Zancenki haka ne ..” Umaima tace sanda suke fita....

SameenaAleeyou📚
[5/31, 11:08 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*010*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Da mamaki Umaima Ke duban Muhibbah “Ke kaw mai zaki gani a sashen bayi...?”
Murmusawa kad’an Muhibbah tai kana tace “Ranki shi dad’e bayi na taka muhimmiyar rawa a kowace masarauta, sannan dik Masarautar da babu b’angaren bayi bai kai a ambacesa da sunan masarauta ba... Bayi suke gina masarauta, sune k’ashin bayan ko wani masarauta sannan ko wacce masarauta na alfahari da tulin bayin da take dashi, idan babu bayi babu masarauta... Bayi sune cikar Fada....”
K’uri Umaima tai mata har takai aya kana ta jinjina kai a hankali “Kedai ko da yaushe baki rabo da hujja mai k’wari.. Tinda kince haka muje na kaiki....”
Muhibbah ta jinjina mata kai murmushi saman fuskarta...
Suna tafe sukazo shige Bargan dawakan Sarki.... Su duka biyun yanayinsu ya sauya sanda suka doso wannan waje... Umaima taja Ta tsaya tana duban wani spot a nan cikin Bargan dawakan Maimartaba yayinda Muhibbah tai saurin d’auke idanunta tana mai k’ok’arin saita kanta sabida wasu irin hawaye masu d’umi da suka ciko idanunta lokaci guda.... Saida ta tabbata ta saita kanta kana ta d’an dubi Umaima da har lokacin duban wannan b’angaren take “Wannan fah... Ina ne nan...? Ga dawakai masu kyau da d’aukan idanu gwanin ban sha’awa...!”

Hannu Umaima ta saka tana goge hawayen da suka gangaro mata cikin sauri dan bataso Muhibbah ta fahimci wani abu, lokaci guda take furta “Nan Bargan Maimartaba kenan, yanda ake aje dawakansa...” Tai maganar a tak’aice...
Dafata kad’an Muhibbah tai kana tace “Are you alright..? Akwai wani abu ne... Ki sanar dani dan Allah...” Ta k’arashe cikeda kulawa...

Umaima ta k’ak’aro murmushi kana tace “Babu komai Hibbah mu k’arasa...”
Hannunta Muhibbah ta rik’o had’ida girgiza kai har lokacin damuwa ne k’arara saman fuskarta kana tace “No Umaima, ban yarda babu komai ba, tinda mukazo wajen nan yanayinki ya canza, dan Allah ki sanar dani idan akwai wani abu ne... Hardai kin amince ‘yaruwa kika d’aukeni...!” Ta k’arashe cikin tsananin kulawa dan san jin taji ko menene...
K’ak’aro murmushi Umaima tai kana tace “Wannan waje yana tina min shi... Yana tuna min irin zallan soyayyar da na nuna masa dikda cewa yasha jadadda min bai tab’a sona ba... Zuciyarsa mallakin wata yarinya ce k’arama wacce suka rabu ba tareda su duka biyu sunsan ma’anan soyayya ba a wancan lokacin... Ta tafi da zuciyarsa ta bar gangan jikinsa cikin Masarautar nan... Yasha jaddada min kar nayi gangancin fad’awa soyayyarsa dan bazan samu ba... Dikda sanin cewa shi d’in bawa ne hakan bai hana zuciyata afka ma soyayarsa ba domin kaw ita soyayya batasan bawa ba bata San Y’antacce ba, faruwa take a wani lokaci da sam baka shiryawa aukuwarta ba...!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata...

Muhibbah da k’irjinta Ke ci gaba da tsananin bugu, dafa Umaima tai kad’an kana tace “Kiyi hak’uri ba nufi na bane na sakaki kuka....!”
Umaima ta girgiza kai kad’an tana mai sakin murmushi “Babu komai Hibbah, Ja’afar ya riga ya zama tarihi a gareni domin kaw yau shekara guda kenan da barinsa Masarautar nan... An wayi gari aka nemesa aka rasa dan yasha jadadda min dama lokuta da dama dik daren dad’ewa zai fice ya nemo SAUDATU koda kuwa hakan na nufin bijire ma iyayen gidansa ne... “
Chapter 13 · 0% Book details