← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 162

Sashe 49

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Giwa Ta kuma jefa mata tambayar Ina Saudatu...? Saidai abinka da mai tab’in hankali dariya Izzatu ta kuma fashe masu dashi tana mai furta wani magana da yafi kama da gwalamniya kasancewar babu harshe cikin bakinta...

Giwa ta sauk’e nannuyan ajiyan zuciya, lallai akwai aiki ja a gabanta idan har za’ace mahaukaciya kuma bebiya ce zata sanar da ita duniyarda Saudatu ke rayuwa... Wannan wane irin al’amari ne...? Bata tab’a zaton Izzatu zata zamto mata k’adangaren bakin tulu ba... Ta yaya za’a ce sa’arta na tareda Izzatu... Ta sauk’e fuci a hankali sanda Jakadiya ke furta “Allah shi baki yawan rai inaga mu k’yaleta haka nan na yau kuma har sai zuwa wani lokaci... Inaga da kad’an da kad’an idan muna bijiro mata da zancen har Allah zaisa mu dace ta bud’i baki ta sanar damu...!”
Ta k’arashe tana mai kuma k’ank’an da kai gaban Giwa...

Badon Giwa taso ba Ta mik’e tana mai ci gaba da duban Izzatu dake sakin murmushi cikin yanayin fuskarta da ya cika da datti da kuma daud’a....

Duban Jakadiya Giwa tai ta mata alama da cewa su fice... Babu musu Jakadiya tabi umarnin uwar gijiyarta...

Sam Muhibbah bata ankara dasu Giwa da tuni sun nufo k’ofa gadan gadan ba, hankalinta da tinaninta yayi nisa wajen tunanin shin wacece wannan mahaukaciyar, maiyasa Giwa ta ajeta a wannan sunk’urumin d’akin sannan mai take zuwa yi wajen wannan mahaukaciya... Ya kamata tasan wacece wannan mahaukaciyar....

Kaman daga sama taji alamun tab’a k’ofa babu shiri tai saurin komawa da baya k’irjinta naci gaba da bugu...

Giwa ce ta d’anja ta tsaya sanda taji tamkar akwai alamun mutum a wajen... Jakadiya ta d’ago tana dubanta, lokaci guda Giwa ke furta “Jakadiya, kin tabatta mu biyu ne a wajen nan bamuda wani d’an rakiya...?”

Jakadiya Ta waiga gefe da gefe kana tace “Rankishi dad’e mu biyu ne rak saiko Izzatu dake cikin d’aki...!”

Giwa Ta d’anyi Jim tana mai kuma karantar wajen.... Lokaci guda ta kaikaito sosai tana mai k’arewa d’akin Izzatu kallo... Babu shiri Muhibbah ta zame daga jikin k’ofar ta shige cikin d’akin dan tabbas idan Giwa ta matso sosai zata iya ganinta jikin k’ofar...

Giwa ta dubi Jakadiya tace “Jakadiya ban yarda babu kowa a nan ba mu koma da baya...!”

Babu musu Jakadiya tabi umarnin uwar gijiyarta...
Duk addu’an da yazo zuciyar Muhibba yinta kurum take.... Ta sadakar shikenan Giwa da Jakadiya Sun kamata, kaman daga sama taji an janyota Ta baya... Zuciyarta ta kuma tsinkewa sanda taga mahaukaciyar nan ne Ta rik’eta sosai ta b’oyeta k’asan gadon katakon da aka d’aureta bisa....

Tana jin sanda su Giwa suka dawo da baya suna masu k’arewa d’akin kallo na wasu dak’ik’ai... Giwa taceda Jakadiya ta bincika ko ina har k’asan gadon Izzatu...
Zuciyar Muhibbah ta kuma tsinkewa shikenan Sun kamata an gama... Tai saurin rintse idanunta had’ida toshe bakinta da duka hannayenta biyu...

Jakadiya na k’ok’arin duk’awa Izzatu tai tsalle Ta mak’uro Jakadiya tanai mata wani irin duka wanda da kaga mai yinta kasan babu hankali a tattaredashi...

Giwa ta Wato ido waje don basusan Izzatu likamau tayi ba ashe dai ba d’aure take ba... Bugun Jakadiya take tamkar wacce aka aikota bataji bata gani...Jakadiya na sakin k’aran azaba...
Giwa kanta saida ta firgita da irin bugunda Izzatu keyiwa Jakadiya tasan ko shakka babu idan ta gama da Jakadiya kanta zata hauro tunda ba hankali bane jikinta...

Ai tuni Giwa ta soma jada baya Jakadiya na fad’in ta ceceta... Inaa Giwa ko takan Jakadiya batabi ba ta fice da baya da baya tana waige waige... Da k’yar da mak’yark’yata Jakadiya ta samu ta k’waci kanta hannun Izzatu ta fito a guje babu shiri amma kam ko shakka babu Ta daku irin bugun da akewa dawa idan an ciro daga gona...
Haki kurum Jakadiya take d’ankwali a hannu haka ta nufo waje tana gumi da haki had’ida d’ingishi...

Suna ficewa Izzatu ta duk’a ta yaye mayafin k’asan gadon nata yanda Muhibbah ke b’oye ciki....

Jikin Muhibbah ya d’auki rawa ganin irin bugunda taiwa Jakadiya kardai itama ta lallasa mata nata bugun... Saidai ga tsananin mamakinta murmushi ta sakar mata kana ta mik’a mata hannu alamun tana jira ta mik’o nata hannun ta fito da ita...

Dukda rawa da jikin Muhibbah keyi hakan bai hanata jarumtar mik’awa mahaukaciyar nata hannun ba... A hankali take janyota har Ta fito da ita daga k’asan gadon... Sukaima juna K’uri su duka biyun... Sai yanzu ne Muhibbah ke iya tantance mahaukaciyar da ko shakka babu Dattijuwa ce sannan da alama ta jima a wannan yanayi sabida daud’a da jikinta yayi sosai, data k’urawa mahaukaciyar idanu sai ta fahimci farar fata ce ba bak’a bace dan ga alamun asalin kalarta Ta ramin idanunta da kuma k’ark’ashin kunnuwarta ashe bak’in datti ne ya rufe mata fata har ya zamto tamkar wani layer....

“AUDOTU” (SAUDATU) abinda mahaukaciyar kenan Ta fad’i cikin kalamanata da basa fita sosai...

Gaban Muhibbah ya yanke ya fad’i jin wannan mahaukaciya tamkar sunanta taji Ta ambata...

Muhibbah ta d’ago firgitattun idanunta tana duban mahaukaciyar wacce tuni ta kuma sakar mata murmushi....

Hannun Muhibbah taci gaba da janyowa har suka isa jikin shirgin kayanta, itada dai Muhibbah bata dawo daidai ba har wannan lokaci saima bugu da k’irjinta Ke ci gaba da yi... Tana gani mahaukaciyar ta soma bincike kayayyakinta... Can k’asan kayan ta ciro wani zane mai yanayi da zanen dake lank’aye parlon su Umaima... Gaban Muhibbah ya kuma yankewa ya fad’i... Mai wannan zane yake nufi....?

Batakaiga samo amsa ba taji sauk’ar takardan a hannunta mahaukaciyar ta mallaka mata ta dunk’ula mata sosai cikin hannunta tana mai ci gaba da sakin murmushi... Lokaci guda kuma Ta koma mazauninta Ta zauna, Ta rarumo ledar bredin da jiya Jakadiya da Ubandoma suka kawo mata Ta barka ledar ta hau mamuk’ar bredin kaman mai tsoron kar wani ya k’wace...

Muhibbah ta tsaya daga yanda take tai mata K’uri don ba kowa ta tina mata ba face Mahaifiyarta... Haka mahaifiyarta Ke tsananin k’aunar bread shine abincin da yafi soyuwa a gareta a lokacinda take raye.... Ta lumshe idanunta a hankali sanda take jin wasu hawaye daga can k’asan idanunta suna yunk’urin fitowa...

Jin kaman alamun tafiyan mutane ya sanyata saurin saita kanta kana ta nufi k’ofa sauri sauri wannan zanen na damk’e cikin hannunta ta fice daga cikin d’akin tana mai kuma waigowa tana duban mahaukaciyar nan itama mahaukaciyar idanunta k’yam akan Muhibbar har Ta fice...

A haka Muhibbah ta nufi d’aki, har lokacin bata dawo daidai ba, abubuwan da suka faru suna kuma dawo mata... Musamman da Ta tuna taji kaman matar nan Ta ambaci sunanta... Toh wacece mahaukaciyar nan...? Ya akai ta santa...? Shin wacece ita..? Ta k’arashe tunanin nata tana mai bud’e wannan taswira da mahaukaciyar ta damk’a mata... Tai k’urima zanen ginin tana mai kuma k’are masa kallo... Lallai ya zama dole tasan yanda za’ai tai comparing wannan zanen da wanda Ke lank’aye parlorn su Umaima, idan har sun zmato iri guda toh ko shakka babu akwai wani b’oyayyen sirri tattareda zanen...! Ta k’arashe tinaninta tana mai kwanciya rigingine saman gado... Ta janyo wayarta tana mai k’ok’arin neman layin Ansar... Saidai kira kusan sau uku tai bai d’aga ba... Sai sannan ta duba time taga dare ya d’anja sosai dan haka bata kuma kiran nasa ba barshi har sai zuwa safiya...

**

Kafin Washe gari iyaka buguwa Ubandoma yayi laushi a hannun Majidad’i... Idan Kaga Ubandoma dole ya baka tausayi irin yanda bugu ya sauya masa halitta... Kankace mai labari ya bazama Fada cewa an kama Ubandoma a gidan Wamabai... Wannan labari ba k’aramin d’aga hankalin Giwa da Waziri yai ba... Mai yakai Ubandoma gidan Wambai... Shin kodai munafuntarsu yake... Shin kodai shid’in ya amintada Mahmood ne...? Bacin haka ma Uban wa yake aiki Tunda dai sunsan su basu aikesa gidan Wambai ba..
Shi kuwa Mahmood mamaki abin ya dinga basa... Shin mai yakai Ubandoma gidan Wambai..? Shin kodai yasan cewa shine bak’on Buzu...? Ya zaci Ubandoma aminatccen hadiminsa ne, kenan Ubandoma na munafuntarsa ne..? Yayi daidai da bai aminta dashi ya bud’e masa wasu sirrika nasa... Tabbas zarginsa ya tabbata wannan gida ba kowa ba abin yarda bane... Kenan zata iya yuwa wasu sunyi amfani da kusancin dake tsakaninsa da Ubandoma dan yai masu aiki.... Lallai ya zama dole ya k’ara taka tsantsan kuma Ubandoma zai fad’i abinda ya kaisa gidan Baba Wambai da kuma wanda ya turasa...
Da wannan tunanin Bawa guda ya k’araso ya zube gabansa yai gaisuwa kana ya k’arada “Allah shija zamaninka an tafida Ubandoma Gidan Yarin wucen gadi dake nan cikin Masarauta Dan a tsaresa...!”

Jinjina kai Yarima Mahmood yai a hankali alamun amsawa... Lokaci guda ya haura sama domin shiryawa dan ya zama dole ya gana da Ubandoma a yau d’in....

****

A daidai k’ofar shiga masarauta Yazeed da Majidad’i suka had’u...

Yazeed ya fad’ad’a murmushinsa sanda yake k’ok’arin k’arasowa dab da Majidad’in... Bayan sun gaisa ne Yazeed yai gyaran murya cikeda k’asaita “Ashe an kama b’era... Bravo gaskiya kayi k’ok’ari Partner... I’m so proud of you..!” Ya k’arashe yana mai tafe hannu a hankali shu’umin murmushi kwance saman fuskarsa...

Murmushin Majidad’i ma yai kana yace “Idan nasa abu a gaba bana fasawa har sai naci nasara domin ni d’in mai sa’a ne a koda yaushe...!” Ya k’arashe cikeda ziga kansa...

Shu’umin murmushin bai bar saman fuskar Yazeed ba ya d’an kwanto da fuskarsa kad’an saitin kunnen Majidad’i “Kar kayi gaggawa Abokina domin tafiya ce mai tsawo a gabanka...!”

Majidad’i ya murmusa kad’an yana mai duban Yazeed yake furta “At least yanzu na nuna maka what I’m capable of....Kai kuma fah shin ka nuna wani jarumta...?!”

Murmusawa kad’an Yazeed ya kumayi kana yace “Ta yuwu a idanunka kaga kaman ka fini k’arfin jiki... Amma saidai ni inada k’arfin tunani wanda zan iya yak’an tawaga guda da wannan tunanin nawa...!!”

“Ban gane mai kake nufi ba...!” Majidad’i yace yana duban Yazeed d’in...

Kafad’arsa kad’an Yazeed ya buga kana ya kuma matso da fuskarsa dab kunnen Majidad’i “Waye kake tunanin ya umarci Ubandoma da ya shiga Gidan Wambai...?!”
Chapter 49 · 0% Book details