← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 162

Sashe 157

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rawar murya irinta mai kuka Fu’ad Ke furta “Inajin nid’in kaman ba d’aya bane daga cikin ahalin gidan nan.. Ina jin kaman ban cancanci zama ahalin gidan nan ba..!”
Saurin kamo hannunsa Ja’afar yayi yace “Of course you’re one of us.. You are a part of this family.. You’re our brother Fu’ad we share the same Father.. So don’t say those things kaji.. Kai ahalin gidan nan ne..!”

Kuka ya kufcewa Fu’ad, lokaci guda Ja’afar ya rungumosa shima hawayen na gangaro masa... Saida Fu’ad ya nastu kafin Ja’afar yace suje suyi wasan Doki Su gwada linzami...

Suka d’ale saman Dawakan suna duban juna murmushi saman fuskokinsu... Ja’afar ya dubansa yace “Ready...?”

D’an tsaresa da idanu Fu’ad yai yace “Ta yaya D’alibi zai gwada k’warewa da Malaminsa... Idan ban mance ba kai kake koya min Doki a baya...”

Murmusawa Ja’afar yai yace “Watak’ila D’alibin har Sai yafi malamin.. Lets do this..!” Ya k’arashe yana jan linzamin had’ida zaburan dokin... Take Fu’ad ma ya zabure nasa dokin yabi bayan Ja’afar a guje zukatansu cikeda annashuwa...
**
A b’angaren Muhibbah kuwa yau d’in su Mommy dasu Meenatu zasu tafi hakan yasa hankalinta ya karkarta zuwaga yin sallama dasu dukda cewa kuwa can k’asan zuciyarta tsananin kewar mijinta take.. Yinin ranan zubur basu had’u ba, batasan har haka take son mijinta ba.. Ta fara shakkun idan zata iya jure rashin ganinsa irin haka tinda yauma kenan akayi nad’in balle ace ya soma hidiman al’umma gadan gadan.. Ta lumshe idanunta a hankali tana tuna yanda a lokaci k’ank’ani Allah ya sauya mata k’addarar rayuwarta.. Wai yau itace Matar Sarkin wannan Masarautar.. Ta tuna sanda tazo Masarautar a k’ask’ance yau sai gashi Allah ya k’addari ta zamto matar Sarkin Masarautar gaba d’aya tabbas babu abinda ya gagari Allah... tana nan tana tinanin Ta sinkayo sallamansa... Zumbur ta mik’e tana duban k’ofa... Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yake dubanta.. Itama d’in murmushin ta sakar masa tana jin zuciyarta na wane irin fuzga... Ganinsa da tai cikin shiga irinta Sarki sak sai taga k’warjininsa ya kuma bayyana... Ta sadda idanunta a hankali tana k’ok’arin duk’awa gabansa dan kwasan gaisuwa... Cikin sauri ya tallafota had’ida mik’ar da ita tsaye.. Suna fuskantar juna hawaye na zirarowa daga cikin idanunta, da gaske yau babu Giwa kuma Mahmood ya d’ale KARAGA... Cikin hawaye take furta “Kaine Sarki.. Ka cancanci zama Sarki mijina.. Ina maka fatan alkhairi tareda addu’an Ibangiji yayi maka jagoranci..!” Ta k’arashe murmushi da hawaye gauraye saman fuskarta...

Tallafe da fuskarta yake furta “My love... My beautiful Queen.. I don’t need all this things... For me you’re all I want... And Wannan Kambin naki ne.. Idan akwai wanda ya cancanta ba kowa bane face ke..! Kece kika cancanci Karagar da Kambin domin kece kika yak’i Giwa da zaluncinta.. Kece kika shigo cikin Masarautar nan wanda yake gauraye da duhu kika haskaka shi da gaskiya.. Duhu ya yaye.. Haske ya bayyana... Ta sanadiyanki Allah ya kawo k’arshen Giwa da bak’in Mulkin zaluncin data gina cikin Masarautar nan..!” Ya d’anyi fasali hawaye na gangaro masa har lokacin yana tallafe da fuskarta.. A hankali yaci gaba da furta “Just like your name MUHIBBAH tabbas ked’in abar soyuwace ga duk wanda kika crossing path d’insa.. Ked’in kin zamto tamkar wata tsauni cikin Masarautar nan da rayuwarmu gaba d’aya.. Kin taka rawar gani cikin rayuwarmu gaba d’aya... Kinyi sadaukarwa da Dama dan ki tabbatar haske ya bayyana cikin Masarautar nan.. Thank you for coming into our lives..! Thank you for being mine..!” Ya k’arashe a hankali... Kukan da take k’ok’arin dannewa ya kufce mata.. Lokaci guda ta rungumesa tana kuka sosai... Saida tayi mai isanta Mahmood na lallashinta kafin ya kamo hannunta yace tazo suje.. Ta d’an dubesa sai kuma tace “Ina zamuje your Highness..?!”

Bai tankata ba har saida suka k’araso farfajiyan benen... Ya kaikaito da ita suna fuskantar juna lokaci guda kamo hannunta ya shiga janyota yana furta “Come I wanna show you something my Queen.. Turn around and close your eyes..!”

Ta d’an Ware idanunta tana tunanin mai zai nuna mata, lokaci guda tayi yanda yace d’in... Wani k’aton frame dake rufe da Farin k’yalle Mahmood ya bud’e kana yace ta juyo ta gani... A hankali take juyowa har ta sauk’e idanunta kan k’atoton frame d’in wanda zane ne na gidan Sarauta... Ta kame bankinta da hannayenta biyu tana duban yanda zanen ya tsaru... Ya tako a hankali ya tsaya daga bayanta had’ida d’aura hannayensa saman cikinta su duka biyun suna duban zanen yace da ita “Do you like it..?”

Kyakkyawan murmushi saman fuskarta tace “Of course I love it... It is so Beautiful..!”

Ya d’an kwanto da fuskarsa ya manna mata peck a gefen kumatunta kana yace “I’m glad you love it.. Kin gane ina ne..?”

Murmushin bai bar saman fuskarta ba tace “Is this also part of the exams your Highness..?”

D’an tab’e baki yai kad’an yana jinjina kai yace “Maybe..! Idan kin canka daidai na mallaka miki zanen kyauta idan kuma baki canka ba....!” Yai shiru bai k’arasa ba...
Ta d’an kaikaito tana dubansa... Sai kuma ta saki murmushi a hankali Ta furta “Masarauatr su Abbah ne.. Masarautar k’asar Benin...!”

Ya d’an yi K’uri yana duban waje guda har ta soma tunanin kodai bata canka daidai ba, Ta sinkayo muryarsa saitin kunnenta yana rad’a mata “Congratulations..!” Ta d’ago tana duban fuskarsa a hankali ta furta “Na gode..”
Girgiza mata kai yai yace “Ba irin wannan godiyan nake so ba”
Ta d’anyi rau rau da idanu tace “Wanne kake so Your Highness..?!”

Kunkuminta ya kuma kamowa suna fuskantar juna lokaci guda ya turo mata labb’ansa alamun ta sumbacesa..
Ta rintse idanunta sabida kunya.. Mahmood yace “Your Highness yaufa babu yanda zakije sai kin bani tukuwici na..” ya k’arashe yana mai kuma tura mata labb’an nasa.. Tace “Fine amma sai ka rufe idanunka..!”

“Well that won’t be a problem Rankidad’e..” Ya lumshe idanunsa yana jiran ta sunbacesa... Tai masa k’uri tana duban kyakkyawan fuskarsa, wani irin shauk’in k’aunarsa na fuzganta... Ido guda ya d’an bud’e kad’an jin Ta d’auki tsawon lokaci batai ba nan yaga fuskarta dab da nasa Sai faman rintse idanu take Zuciyarta na bugawa...Aiko a tare suka bud’e ido sanda fuskokinsu suka kusa had’ewa... Ta Ware idanunta tana k’ok’arin juyawa yai saurin rik’ota zatai magana yai ma bakinta marfi da nasa... Cak ya sureta ya nufi bedroom d’insa da ita yana nuna mata tsantsan k’aunarsa gareta...

**
Wai akace bayan wuya Sai dad’i sannan tsanani na tareda sauk’i... Al’amara sun soma daidaita cikin Masarauta tuni anyi nad’e nad’en sarauta, a b’angaren su Mommy Tunda suka koma gida kusan kullum sai tayi waya da d’iyarta Gimbiya Muhibbah... Ansar ma tuni ya d’auki matarsa Hameedah sun tare a gidansu.. Hankalin Mommy ya kwanta faranta Allah ya azurta yaran nata da zuri’a masu albarka...

A b’angaren Raheemah kuwa nadama yazo mata itama, musamman duba da yanda Yazeed ke mata wa’azi gameda duniya da rayuwar duniya.. Rayuwar da sukai kad’ai ya ishesu wa’azi a cewar Yazeed ya kuma rok’onta Ta taimaka Ta kirawo masa Mahmood ya gansa ya rok’esa gafara koda abinda zaiyi kenan na k’arshe a rayuwarsa domin kuwa Yazeed d’in ya zama weak sosai da ace zai iya tashi daga saman gadon jinyarsa da koda rarrafe ne zaije ya rok’i Mahmood da Muhibbah gafara... Raheemah na hawaye Ta dubesa tace “Banida tabbacin Sarki zai amsa gayyatarka amma Zanyi k’ok’ari na gwada koda Ta k’afar matarsa ce... Yazeed yai mata godiya kana ta fice hawaye....

Koda Ta iso masarauta Jakadiya ce tai mata iso wajen Gimbiya Muhibbah... Sosai Muhibbah taji tsoron yanayin da taga Raheemah ciki, duk ta kod’e ta jeme kaman ba Raheemar data sani ba...

Jiki a matuk’ar sanyaye Muhibbah Ke dubanta yanda ta duk’a gabanta tana cazgan kuka, lokaci guda take ci gaba da rok’on Muhibbar gafara... Muhibbah ta mik’ar da ita tsaye suna fuskantar juna, a hankali take furta “Raheemah ki daina rok’onta gafara irin haka ni baki min komai ba... Dukkanmu ‘yan adam ne kuma masu kuskure... Idan muka rok’i Allah gafara matuk’ar tuban gaskiya mukayi tabbas zai yafe mana koda kaifukan namu yakai yawan kumfan teku domin kuwa shi Allah mai yawan afuwa ne... Allah ya yafemu gaba d’aya kinji koh...!”

Cikin kuka Raheemah Ta rungumeta tana fad’in “Kinada zuciya mai kyau Muhibbah... Na gode na gode k’warai..!”

Muhibbah ta rik’o hannayen Raheemah cikin nata tace “Babu komai Raheemah...!”

Raheemah ta d’an jinjina kai tana duban Muhibbar sai kuma tace “Wani alfarma kuma nake so Kimin...”

Dubanta tai da mamaki kana tace “Wane alfarma kenan..?”

Raheemah taci gaba da fad’in “Akan Yazeed..!”

Take fuskar Muhibbah ya sauya ta zame hannayenta daga cikin na Raheemah...

Raheemah ta kuma share hawayenta tace “Nasan bai kamata na ambaci sunansa a gabanki ba amma babu yanda na iya ne Muhibbah.. Domin yana cikin tsananin jinya... Abinda yake buk’ata kawai shine yafiyarki... Muhibbah ki yafewa Yazeed dan Allah sannan ki rok’i Mai Martaba yaje yaga Yazeed domin banida tabbacin Yazeed zai iya fita daga asibiti... Please Muhibbah can you do this..?!” Ta k’arashe tana mai kuma kamo hannayen Muhibban cikin zuban hawaye...

Muhibbah da tuni itama hawaye sun fara gangaro mata, a hankali takai hannunta Ta goge hawayen... Tai k’ok’arin saita kanta kana tace “Fansa baida wani amfani Raheemah.. Tun lokacinda na watsar da k’uduri burin Fansar abinda suka aikata min na samu salama cikin zuciyata Raheemah... Na zab’i na bar komaiga mahaliccinmu yayi hukunci tsakaninmu... Raheemah I’m sorry I don’t know if I can still forgive him... I’m not really sure...! Amma na miki alk’awari zan rok’i Mai Martaba yaje yaga Yazeed kaman yanda kika buk’ata...!” Ta k’arashe hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta...
Cikin tsananin sanyin jiki Raheemah Ke jinjina kai tana furta “Na fahimceki, kuma na gode sosai... Thank you so much Your Highness..!” Muhibbah ta rungumota su duka biyun suna hawaye...

Koda Ta sami Mahmood da batun da fari k’in amincewa Yayi dan a cewarsa bayan abinda suka aikata mata baijin zai iya kuma had’a idanu Yazeed balle har ya yafe masa...
Chapter 157 · 0% Book details