Sashe 95
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mahmood ya kuma katsesa da fad’in “And what makes you so sure itada Yazeed basu san juna ba....?? Maybe she’s helping him in some ways.....! Waht if itada Yazeed are lovers,maybe d’aya ce daga cikin ‘yan matansa da yake cin amanar matarsa dasu.... wayasani ma ko ya d’aukota ya aje cikin Masarautar nan ne just to ruin me, and they used my own daughter to bring me down....! And after she learns yana cin amanarta da Raheema shine ta fallasa Raheema kuma kar ka mance mun tab’a kub’utarta hannun Yazeed,maybe Yazeed gaskiya yake fad’i ba raping d’inta yaso yi ba... Maybe dama sunsan juna tuntuni... Is her way of getting back at him shiyasa ta tona asirinsu shida Raheema...!! I was such a stupid for believing in her..!!” Ya k’arashe yana sakin huci mai wane irin zafi yanaji zuciyarsa kaman tana rarrabewa gunduwa gunduwa, lokaci guda yasa hannu ya daki jikin gini zuciyarsa na kuma masa d’aci...
Turaki yai shiru Dan bayan tabbatarwa da sukai Muhibbah ba d’aliba bace a makarantar kaman yanda tace Mahmood yanada duka damar da zai zargeta da komai, wacce har tai k’arya irin haka baida lasisin da zai kareta dukda cewa shi sam zuciyarta bata aminta da cewa Muhibbah mutumiyar banza bace musamman da ya fahimci abokinsa ya aukawa soyayyarta wanda bai tab’a ganinsa cikin irin wannan soyayyar ba koda kuwa zaita denying...
Turaki ya d’an shafi fuskarsa da duka hannayensa biyu yana mai tsare abokin nasa da idanu wanda sosai yake iya hango tsagwaron b’acin rai kwance saman fuskarsa... Shi zai iya cewa ma bai tab’a ganin hakan daga garesa ba... Ya d’an nusa kad’an yace “What are you suggesting your Highness..?!”
Wane irin duba kurum Mahmood yai masa ba tareda ya kuma cewa komai ba yai hayewarsa sama...
Turaki yabi bayansa da kallo tausayinsa na kuma lullub’esa Dan yayi imani sosai ya kamu da san yarinyar sai gashi tayi breaking zuciyarsa tun ba’aje ko ina ba....
Bai ida tunanin ba ya hango Mahmood ya sauk’o cikin shiri irinta Buzaye...
Turaki ya mik’e babu shiri yana dubansa baki sake....
“Bak’on Buzu kuma Rankaidad’e..?!” Turaki ya fad’i yana duban Mahmood d’in dake k’arasowa cikin parlorn....
Lokaci guda yaci gaba da furta “Ai na zaci an rufe shafin Bak’on Buzu tuntuni Rankaidad’e...?!”
Har lokacin bai tankasa ba saima k’arasawa jikin babban mirror na alfarma dake gefe daga nan cikin parlorn yana gyara nad’in buzayensa....
Lokaci guda ya soma furta “Jikina yana bani Baba Wambai bazaice na nemeta itada zata linking d’ina to all the answers I’ve been looking for a banza ba, watak’ila itada Yazeed sun jima suna shirya abubuwa akaina... Idan ban samu amsoshin a wajen Yazeed na ita zan iya samu a wajenta...!”
Turaki ya jinjina kai yace “Toh yanzu ina muka nufa Rankaidad’e..?!”
Ba tareda ya dubesa ba yace “Bauchi..!!”
Saida gaban Turaki ya fad’i, ya d’ago taintsiyar hannunsa yana duba time...
“Rankaidad’e da dai mun bar tafiyar zuwa gobe, Idan muka tafi yau zamuyi dare sosai a hanyar dawowarmu...!”
Mahmood ya katsesa da fad’in “Are you coming or not..?!”
“A’a yanda kace hakan za’ai Your Highness..!” Turaki ya fad’i yana mai take masa baya...
Babu wanda yaga ficewarsu ko hadimin Mahmood d’in baisan Sun fice ba hasalima da motar Turaki sukai amfani suka fice.
**
A b’angaren Jakadiya kuwa neman duniya anyi ba’a sameta ba cikin Masarautar, hankalin Giwa yakai k’oluluwa wajen tashi... Wai meke faruwa da ita ne..? Daga wannan sai wancan.... Yau kwana biyu kenan babu Jakadiya babu dalilinta kuma babu wanda yasan yanda take... Gashi Giwa ta hana a yad’a Labarin b’acewar Jakadiyar Dan bata so ya isa ga Mahmood balle har aje ga tono ina Ubandoma ya shige tinda shima ba’a gansa ba... Gashi Tal’udu ya mata iyaka da sashensa balle Takai masa kokenta na abubuwan dake faruwa da ita... Tashin hankali daga wannan sai wancan... Ita duk tsoron ta kar dai Ubandoma ne ya zago ya sace Jakadiya tinda tayi imani yana tareda Ja’afar da kuma Izzatu mutanen da suke barazana ga rayuwarta... Tayi imani randa duk suka bayyana cikin Fada Toh fah kashinta ya bushe...
Taci gaba da zaga cikin d’akin nata yanda Jamal ya shigo ya taddata...
Daga can gefe ya zauna yana k’are mata kallo dan da alama bataji shigowar tasa ba...
Ya d’anyi gyaran murya kad’an yana mai daidaita zamansa had’ida aje sandarsa Ta crutches...
“Maami Wai meke damunki ne..?!” Ya tambaya cikeda kulawa...
Giwa Ta juyo tana dubansa da mamakin yaushe ya shigo ko k’aran sandarsa bataji ba....
“Gwarzona na yaushe ka shigo..?!” Ta tambaya cikeda kulawa...
“Maami tun d’azu fah na shigo, inata miki magana amma kinyi nisa duniyar tunani... Maami meke damunki duk kika fice a hayyacinki haka... Tell me is there something I can do to help..?!”
K’ak’aro murmushi Giwa tai Ta k’araso kusan d’an nata Ta zauna, hannunsa ta dafa kad’an tace “Meyasa abubuwa suke faruwa yanda bana so Jamal... Meyasa komai yake nema ya sukuruce min...? Nayi zaton inada k’arfin zuciya da k’arfin hali, Maiyasa nakeji kaman na zamto mai rauni.... Jamal babu Ubandoma, yaci amanata ya gudu da mahaukaciyar nan da kuma Jafaru... Yanzu kuma an wayi gari Jakadiya ta b’ace itama... Jamal idan na rasa Jakadiya tamkar rayuwata na rasa..!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Jamal yai shiru yana duban mahaifiyar tasa sai kuma yace “Maami har haka Jakadiya Keda mahimmanci wajenki..?!”
Giwa ta nusa tace “Bazaka gane bane Jamaluddeen, Jakadiya tasan sirrika na da yawa wanda b’acewarta tashin hankali ne a gareni...!”
Jamal ya tsareta da idanu sai kuma ya d’an gyara zama yace “Maami akwai wasu sirrikan da kike b’oyewa ne wanda Jakadiya ta sani ni ban sani ba...?!”
Tambayar da ya haifarwa Giwa da fad’uwan gaba tinda tasan yaran nata basu san cewa ta salwantar da shigabanta bane ta maye gurbinta, yaranta basu san cewa ita d’in baiwa bace k’ask’antacciya maras ‘yanci... Shiyasa duk yanda zatayi dole tayi komai Dan ganin itada ahalinta sun tabbata cikin wannan masarauta tunda basuda yanda yafi masu nan...!
Ta girgiza masa kai a hankali alamun a’a tace “Iyakacin abinda ka sani sune Jakadiya ta sani amma duk randa ya isa kunnen Yayanku Mahmood zai tsaneni a matsayina na mahaifiyarsa dole duk yanda zamuyi mu aje Jakadiya a k’ark’ashin ikon mu Jamal..!”
Yai shiru had’ida tsurama waje guda idanu tamkar mai tunanin wani abu...
Giwa ta tsaresa da idanu tana karantarsa, Ta d’an muskuta kad’an tace “Jamal... Anya kuwa babu abinda kake b’oye min..? Kodai kasan wani abu gameda b’acewar Jakadiya..?!”
Jamal yai shiru ba tareda ya amsata ba... Giwa Ta mik’e tana fad’in “Jamal ina Jakadiya..? Mai kai mata..?!”
D’agowa yayi yana dubanta sai kuma ya kauda fuskarsa zuwa d’aya b’angaren “Maami Jakadiya macuciya ce cin amanarki take a bayan idanunki shisa nake hukunta ta..!”
Giwa ta shiga tafe hannaye tana salati babu shiri tace dashi maza ya kaita taga Jakadiya....
**
BAUCHI
Mommy tai jigum tana sauraren Baffah Yawale yanda yaci gaba da fad’in “Haba ni nasan za’a rina, wannan yarinya da kika d’auko kika aje gidanki tsintacciyar mage ce, a tunaninki irin na mata taimako kikayi gashi nan da idanunki kin gani, Allah ya bud’i bakinta da kanta Ta sanar dake k’arya ta miki a baya... Allah kad’ai yasan yawan sauran abinda take b’oye miki.... Ki gode ma Allah da ya fargar dake kafin ki kaiga aikata babban kuskure na aura ma d’anki wannan yarinya maras asali balle tushe...!”
Kaman daga sama suka sinkayo muryar Ansar yana fad’in “Dukda rashin asalinta naji na gani na amince Ina sonta a haka... Ni ne nan zanyi zaman aure da ita ba d’aya daga cikinku ba, so ni nakeda alhakin zab’awa kaina macen da ta dace Tai zama matata kuma uwar yaran da zan haifa gaba.!”
“Ansaar.!!!!” Mommy ta daka matsa tsawa tana mai mik’ewa tsaye...
Ansar bai daina huci ba yake furta “Mommy Ki k’yaleni na fad’I gaskiya, wannan mutumin yazo yana poisoning zuciyarki da kalamansa na son zuciya..!”
Momy ta katsesa da fad’in “Nace kamin shiru... K’anin mahaifin Naka kake wa magana haka...? Ansar I didn’t raise you to become like this... Rashin kunya ba halinka bane kada ka fara kan wannan mak’aryaciyar yarinyar..!!”
Ansar na tsananin huci yake girgiza kai yana duban mahaifiyarsa, lokaci guda yake furta “Mommy shin zaki bari son zuciya ya rufe miki ido..? Mommy Muhibbah bata miki komai ba, Mommy don’t judge her akan abinda bakida masaniya akai... Mommy ki bari nai miki bayani na tabbata zaki fahimci komai..!”
“Shut up.!! Kamin shiru nace... Bana buk’atan naji komai, kuma bana so na fahimci komai... The only abinda na sani shine bazaka auri yarinyar nan ba period.!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci..
Shima Ansar d’in huci yake idanunsa na kuma kad’awa, lokaci guda yake furta “Fine..! Haka kikace Mommy..? Kin mance same mutanen da suka k’yamaci aurenki da Daddy sabida ke tibabbiya ce same mutanen suke tunzuraki ki aikata abinda zakizo kina danasani daga baya... Mommy why can’t you open your eyes and see the truth...! Toh wllhi kinji na rantse miki.... ina mai tabbatar maku idan har baku d’aura aurena da Muhibbah ba wllhi bazan zauna da yarinyar da kukeso ba, zaku aura mata wofi ne Dan wllhi tafiyata zanyi ku nemi ni ku rasa..!!”
Marin da Mommy Ta wankesa dashi ne ya sanyashi dakatawa da magana, ya d’ago dafe da k’uncinsa yana dubanta, Baffah Yawale ya mik’e ya tsaya a tsakiya yana duban Mommy yake fad’in “Kiyi hak’uri Murja... Har yanzu dai Yakubu(Ansar) yaro ne... Baisan menene daidai da abinda ba daidai ba... Kiyi hak’uri abi abun a sannu....!”
Mommy na hawaye take nunawa Ansar k’ofa “Get out... Get out before I lost it all on you... Fita nace..!!!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata....
Ansar ya aikawa Baffah Yawale wani duba kana yasa kai ya fice kaman zai kifa da k’asa...