← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 162

Sashe 139

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa, Wai Yazeed Yazeed dai Prince Yazeed a b’angaren bayi... Afujajan ta janyo alkyabbarta ta nufi b’angaren Bawan na kuma risina mata..

Tana isa sashen ta soma yatsine yatsine tana toshe hanci dan wari yake mata a cewarta... Taga wasu ‘yanmata guda biyu sunyi tsaye suna lek’en wani rub’ebb’en d’aki, da alama lek’en Yazeed d’in suke suna gulmarsa...
D’ayan har tana cewa “Ashe da rabon a samu kyakkyawan Bawa irin Yarima Yazeed..!” Ta had’iye sauran maganan nata sanda Raheemah ta k’araso wajen.. Gaba d’aya suka duk’a suna gaidata...! Da tsawa tace dasu duk su b’ace daga wajen kana Ta nufi cikin d’akin tsoro da Al’ajabi na kuma kamata..

Zaune taga Yazeed dirshan tamkar mutum mutumi bai um bai um um... Jiki na rawa Raheemah ke dubansa daga nan yanda take tsaye “Zeed..! Zeed is that you...?” Tai saurin k’arasowa had’ida duk’awa gabansa cikin tsananin rawar jiki, murya na rawa take furta “C’mon talk to me Yazeed, Wai da gaske kaine a nan..? Yazeed why..? kan mai zaka k’ask’antar da kanka ka kawo kanka cikin wannan dottin.. Look dubi everywhere is liking.. My Goodness you might catch infection here..!” ta k’arashe tana d’aga kai sama tana duban gajiyayyen d’akin a yatsine...

Lokaci guda Ta soma k’ok’arin mik’ar dashi tsaye tana furta “You don’t belong here Yazeed... Tashi mu tafi..”

Tarjewa yayi yak’i tashi... Raheemah Ta juyo tanai masa duban mamaki, lokaci guda Yazeed Ke furta “Let me be.. this is where I belong after all..! My life is completely ruined... I have nothing left Raheemah... I don’t want live anymore.. I’m sick and tired of this miserable life I’m living now... Pls end my life Raheemah, just kill me please..!” Ya k’arashe wasu irin hawaye na zubo masa...

Take Raheemah ma taji hawaye na zubo mata, lokaci guda take girgiza kai tana furta “No Zeed, this is not the end of it... Bazan barka a nan ba, You’re still that prince with so much pride and power..! Yazeed please ka tashi mu tafi..!”

Dubanta yayi da kod’add’un idanunsa kana yace “I’m worthless now, bazan amfani kowa ba, kowa guduna yake even my friends left me.. Kema nasan you’re just faking it... You love Mahmood, kawai dan babu yanda kika iya ne... And you’re doing all this out of pity... Kuma kin sani duk duniyar nan babu abinda nafi tsana kaman naga wani yana jin tausayina.. The moment na koma abin tausayi shikenan rayuwata ta k’are.. And that’s exactly what I’m now..!!” Ya k’arashe wasu hawaye na gangaro masa..

Raheema ta dubi hannayensa guda biyu tana mai tabbatar da abinda yake fad’i lokaci guda yake furta “But you still have me Yazeed.. I’m your wife ka mance...!”

Yai murmushi mai ciwo yace “Kar mu yaudari kanmu Raheemah.. Na tabbata daga yanzu jin kanki kike way too outside my world, we are not in the same league anymore... so please , just go and leave alone...!”

Share hawayenta tai tace “You know what I don’t give a crap about Mahmood anymore.. Kuma Wllhi sai na tarwatsa Farin cikin da yake k’ok’arin ginawa, kar ka damu Zeed zan d’aukar mana fansa kan wad’anda suka wulak’anta mu... Kuma sai kayi alfahari dani..! Tashi muje to your favorite place..”

Ta k’arashe tana mai kamosa ta d’agosa tsaye....

**

Ubandoma ya dubi Ja’afar sanda driver ya ida parking dalelliyar BMW X6 sai walk’iya take.. Yaci Uban gayu kana ganinsa Kaga d’an masu muk’ami... Ga wasu zuk’a zuk’an dogari har guda biyu biyedashi..
Ubandoma na daga b’angaren damarsa suka nufi ward d’in da aka ajesu Jamal bayan sunsha surgery an ceto rayuwarsu...

Gadajensu ne guda uku a jere, na Giwa daga farko sai na Jakadiya.. Na Jamal kuwa na daga d’aya b’angaren labule ne ya raba tsakaninsu...

SameenaAleeyou📚

SameenaAleeyou📚
*MUHIBBAH*

*80*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ko duban b’angaren da Giwa take Ja’afar beyi ba a cewarsa ziyaran na Jamal ne... Muryar Giwa ce ya soma masu sallama a galabaice sanda suka shiga Sai fad’in muggan abubuwan da tayi take... Idan tayi tayi sai ta k’ara da ihu tana fad’in ta shiga uku... Likitan ya dubi su Ja’afar da Ubandoma yace haka nan ta Kwana tana wanann sunbatu tunda aka fito da ita daga surgery... Gaba d’aya ta damesu ta cika masu kunnuwa... Ja’afar ya girgiza kai a hankali ba tareda ya furta komai ba, Ubandoma ne yace “Ai Izzatu Ta tapka ta’asa a doron k’asa dan haka duk abinda kace tanayi likita bazanji mamaki ba... Allah Ubangiji yasa mufi k’arfin zukatanmu..” Likita ya amsada Ameen... Can yanda Jakadiya Ke kwance Ubandoma ya k’arasa, shi kuwa Ja’afar yana nan jikin gadon Jamal yayi tsaye yana k’arema Jamal d’in kallo yanda ya koma abin tausayi lokaci guda... Likitan ya k’araso gefen Ja’afar ya tsaya yana masa bayanin ciwon Jamal d’in dan sosai k’unan nasa ya shiga deep harma ya d’ara na Giwa da Jakadiya da k’yar akai masa aiki aka samu fitsari Ke fita kad’an kad’an daga mafitsaransa a haka ma saida taimakon katata kafin ciwon nasa ya warke aga abinda hali zai, gaba d’aya ya koma tamkar wani halitta ta daban... Ja’afar ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yace “Yanzu Dr kanaga zai iya kaiwa yaushe kafin ya farka..?”

Dr yace “Ai ko d’azu ma ya farka, shi kuma duk farkawan da zai toh da tsinuwa da la’antar mahaifiyarsa yake tashi, kaji irin tashin hankali da wad’annan bayin Allah suke ciki..!”

Nanma girgiza kai kad’an Ja’afar yai yana mai kuma duban Jamal da tsoron duniya... Dr na matsawa da kad’an Jamal ya bud’e idanunsa yana duban Ja’afar dake tsaye kansa... Yai ma Jafar K’uri idanunsa suna rinewa zuwa ja... Cikin wane irin yanayin murya mai tsananin rawa ya furta “What brings you here..?! Kazo ne kaga yanda na koma..? Kazo ne ka tabbatar da idanunka..? Well, gani nan ga yanda na koma.. K’ask’antacce muskini saika zuba ruwa a k’asa kasha.. And don’t you dare think of taking my wife away from me, dan bazan tab’a bari hakan ta kasance ba.. Umaima tawa ce, she’s my wife, she and I are married.. You better stay away from my wife..!!” Ya k’arashe kaman zai finciko Ja’afar d’in sabida yanda yake tsananin tururi...

Tinda ya soma magana Ja’afar bai furta koda kalma ba har ya ida sunbatunsa cikin zuban hawaye, hannu Ja’afar ya zaro paper da pen cikin aljihunsa ya aje gefen Jamal fuskarsa a matuk’ar murtuk’e ya furta “Write..! Rubuta mata tun muna mu biyu nida kai..!”

Jamal ya dubi takardan ya kuma dubi Ja’afar yace “Do you think I’m that stupid, well you’re mistaken your Highness idan kana tunanin zanyi abinda kake umarta na... Never bazan tab’a rubutawa she’s mine..!”

Ciki wane irin huci Ja’afar ya kwanto da fuskarsa tamkar zai shak’o wuyan Jamal d’in yake furta “Don’t you test my patience..! Idan kana son kanka da lafiya ka rubuta tun muna mu biyu a nan wajen, don idan ba haka ba ni nan zan tabbatar maka ba kai kad’ai ne keda ilimin mugunta ba.. Bakaji azaba ba duk wannan rad’ad’in da kake ciki har sai ka bari ka shigo hannuna baka aikata abinda na umarceka ba.. Sannan ne zaka San the real meaning of the word pain..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci...

Ga tsananin mamakin Ja’afar murmushi saman fuskar Jamal ya gani irin na ko ajikina, lokaci guda yake furta “Babu abu mafi zafi da d’aci a duniyar nan da na fuskanta kaman rabuwa da rayuwata ta baya... So duk abinda zaka min duk kalan horon da zaka min na shirya amsan sa idan dai akan abu guda d’aya tak da ya rage min a duniyar nan ne.. Umaima ita kad’aice ta rage min kuma kaji na rantse maka ko kotun duniya zaka kaini gaban Alk’alin duniya saidai ka kaini amma bazanyi abinda kake umartana ba... Ka fahimta..?!” Ya k’arashe yana sakin huci...

Ja’afar d’inma huci kurum yake yana dubansa lokaci guda yake furta “You want battle..? Then I’ll give you war.. And don’t forget I’m the one with power now..!!” Daga haka mik’ewa yai ya nufi k’ofa cikin sassarfa kaman zai kifa k’asa yana iya sinkayo muryar Giwa tana fad’in “Ku kira min d’ah na Mahmood yazo ya kaini asibitin k’asar waje a sake mun fuska.. K’arya Izzatu tazo Ta shera masa, Mahmood d’ah na ne..!!”

Ko takanta Ja’afar baibi ba yayi ficewarsa... Ubandoma ne ma ya biyeta da furta “Hattara k’ask’antacciyar Baiwa, Butulu la’antar Allah da tsinuwarsa su tabbata gareki kin cutar da Sarauniya Giwar Amale Gimbiya d’iyar masu mulki... Allah dai ya kwashe miki mushirika..!”

Jakadiya tana kiran Ubandoma tana fad’in ya taimaketa ya canza mata d’aki kar zunuban Giwa da Jamal suci gaba da bibiyarta dan Ta tabbata yanda suke tsinema juna cikin d’akin bala’i na gaba nan tafe garesu.. Ya taimaka mata yasa likitocin su canza mata d’aki...
Ubandoma ya dubeta yace “Ni... Tare na ganku, dama duk wanda yace tukunyar wani bazai tafasa ba toh fa nasa ma ko zafi bazai ba... Allah ya kawo sauk’i Talle kar Ki damu na yafe marin da kika min bazan rama ba.. Kiji da wannan kawai.. Ni kinga tafiyata..!” Yasa kai ya shige yana fad’ida Ja’afar “Yarima gani nan tafe..!”

**

Koda sukaje club d’insu Yazeed k’in fitowa yai, Raheemah ta duk’a gabansa tana fad’in “Zeed ya kamata ka fahimci this is who you are now, if you accept yourself the way you’re that’s when people will accept you.. So just come out and stop hiding from your friends kaji koh..”

Da idanu kurum Yazeed ke dubanta kana ya furta “Bazan basu satisfaction d’in ganin downfall d’ina ba.. You know what Raheemah you’re just wasting your time... Bazan shiga wajen nan ba, I was once the king here, bazan tab’a shiga ciki a matsayin k’ask’antacce ba..!”

Raheemah Ta murmusa tace “But you’ve my company ba kai kad’ai zaka shige ba... Mu shiga kasha iska kad’an..!” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’arsa tsaye, ya d’anyi k’ara kad’an sabida ciwonsa da sukai masa tsami gashi yau d’in ba’ayi dressing ba...

Raheemah na rik’e dashi ta b’angare guda ya fuzge yana fad’in he can walk by himself... Saidai to their surprise suna isa spot d’insu Yazeed aka hanasu shiga...
Raheemah tace “Baku gane wanene bane.. Prince Zeed ne fah..”
Chapter 139 · 0% Book details