Sashe 154
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Turaki ya d’anyi gyaran murya kad’an bayan shud’ewar wasu dak’ik’ai kana yace “Alhamdulillah..! Mun gode ma Allah da yasa ka fahimci kuskurenka Baba.. Ina kuma fata wannan ya zamto wa’azi gareka da masu hali irin naka... Ka aurawa Mai Martaba macen da yake matuk’ar k’auna a lokacinda kake da ikon aurartaga waninsa dan haka ka cancanci kyauta daga Masarauta dukda cewa da wani nufi kayi hakan cikin zuciyarka.. Allah yasa wanann ya zamto izna a gareka damu baki d’aya.. Kar dan ka samu dama akan mutum kace zaka cutar da rayuwarsa baka San mai gobe zata haifar ba..!”
Cikin rawar murya had’ida rawar jiki Yawale Ke furta “Wannan gaskiya ne.. Wannan gaskiya ne Rankaidad’e.. Allah dai yayi mana tsari da sharrin zuciya..” ya saci duban Mahmood yana mai kuma duk’awa had’ida d’ago babbar yatsa yake furta “Godiya nake Allah shi taimakeka..! Tuba nake Allah shi baka yawan rai.. Ja zamaninka angon Gimbiya Hibbatu d’iyar albarka..!” Shi kansa Mahmood saida Yawale yaso basa dariya.. Ansar da Turaki suka murmusa a hankali kana Ansar ya dubi Mahmood wanda shima gajeriyar murmushi ne saman fuskarsa yace “Your Highness zan tafi dasu masauk’i idan kamin izini..”
Mahmood ya jinjina kai yana mai alamawa Turaki da ya k’araso.. Turaki ya matso yana sauraron sak’on da yake basa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa... Ko da gani kasan bazai shige kyautukan karramawa yake umarta a baiwasu Yawale...
Sukai masa sallama had’ida godiya kana suka fice tareda rakiyar Turaki.. Yawale yana fad’in shidai so yake yaga Murjah yayi mata murnan wannan babban al’amari mai dad’in ji sannan idan da hali ma yaga Gimbiya Hibbatu ya nemi yafiyarta da gafararta ya kuma mata murnan wannan babban abin arziki da ya sameta...
Sun sami ganin Mommy harma da Muhibbah kasancewar a daren za’a rufeta a lalle kaman yanda yake a al’adarsu sai kuma Washe gari akaita d’akinta kai tsaye bayan an rufa mata Alkyabba Ta amarci, nan Yawale yayita neman afuwa a wajenta, shima Ansar ya rok’eta Gafaran abinda yayi mata da Mahmood.. Fadah ta kuma cikada albarka.. Su gudidi ba’a sama ba’a k’asa an samu karamci Sune kan gaba wajen saka Amarya a lalle.. Sai pictures ake ana watsawa social media ko wanne picture da Gudidi zata maka status sai tayi caption maiji da lafiya tace gasu waje kaza Iyayen matan Sarki.. Mommy dai saidai ta kalleta ta murmusa tace oh su Gudidi budurwar zuciyar na nan dai ba’a girma ma hidiman social media.. Gudidi tace ah zamaninsu ne dole su shana ina ta tab’a zaton zata zamto k’awar Maman Matar Sarki da kansa.. Hidima yayi hidima ta ko wanne b’angare sai son barka..
Washe gari tun bayan ida sallan asubahi tambura da algaita Ke tashi cikin masarauta, lokutan sallah ne kurum yake sanyasasu tsagaitawa ana idar kuwa sautin algaita zaici gaba da tashi.. Matayen masu Mulki dasu Mommy harma da Gimbiya Zeenat su suka raka Amarya Muhibbah sashen mahaifiyar mijinta Gimbiya Turai.. Sai gud’a mata suke, nan aka rufa mata sabuwar Alkyabba k’ar mata naci gaba da gud’a .. Masu zuba turare nayi masu rawa nayi.. Masu fatan Allah sanya albarka nayi.. Zigazigai kuwa Sai kod’a Amarya da ango suke harma da uwar angon da Marigayi mahaifin Amarya Wato Yarima Alfah.. Duk wannan hidima Raheemah na k’ume a d’aki tana sharb’an kuka dan akan kunnuwanta komai ke faruwa saidai ko fitowa ta k’asa saidai kawai taga pictures a status din Umaima.. Ko asibti wajen Yazeed ta kasa komawa, tana nan k’ume a d’aki tana cazgan kuka..
Su Zahra dasu Umaima dasu Meenatu suma dai da alama ‘yan team d’in Aunty Gudidi ne ‘yan ayi pictures a tura status ne... Sai pictures suke Meenatu na turo ma K’awayensu da basu samu halarta ba.. Kai saidai ace Masha Allah komai ya tafi yanda ya kamata... Su Mommy sukai mata rakiya har sashenta dake nan cikin Masarautar yanda komai kama daga finiture zuwa duk wani abin buk’ata na cikin sahen a tsakanin satin Rankaidad’e yasa akayo order.. Allahu Akbar yau dai ga Muhibbah cikin d’akinta sosai suka rungume juna itada Mommy suna kuka su Gudidi da Aunty Salma Sai basu baki suke.. Mommy ta kuma mata nasiha kan rayuwa da abinda ya shafi zamantakewa na aure domin kuwa sabon babin rayuwa zata soma.. Daga bisani sukai mata sallama kowa ya koma masauk’insa...
Tana nan zaune tana tinanin rayuwarta tin daga farkon abinda ya sameta a wannan masarauta har zuwa had’uwarsu da Rankaidad’e da yanda Allah ya k’addari faruwan abubuwa... Sam batasan lokaci yaja ba tana nan zaune taji k’amshin turarensa nayima hancinta sallama.. Ya zauna gefenta kad’an yana mai tsareta da idanu har lokacin fuskarta rufe take cikin alkyabbar.. Zuciyarta taci gaba da tsinkewa jin ya zauna gefenta.. Hannunta guda dake aje saman gadon ya kai nasa hannun ya d’aura saman nata.. Lokaci guda yai amfani da d’aya hannun ya yaye alkyabbar dake rufe fuskarta.. Yai mata K’uri yana duban yanda hawaye ke kuma gangarowa daga cikin idanunta... A hankali yake furta “I thought kuka ya k’are tunda baza’a sake jarabawar ba..Unless kuma kina so a sake..?” Ya k’arashe tamkar bashin yai maganar ba ‘yan yatsun hannunta cikin tafin hannunsa...
Ta saki murmushi a hankali tana mai sanne kai had’ida mak’ale kafad’a, ya murmusa kad’an wannan karon yace “Have you eaten..?”