Sashe 159
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aiko Jamal dake biye dasu dafe da sandarsa sannan ya kuma dank’wafewa sabida k’unan wutan da yayi.. Aiko Dogaran nan suna bada hanya shima ya duk’a yana rarrafawa da hannayensa had’ida janyo sandarsa a hankali har ya samu ya shige cikin d’akin hannayensa rik’eda almak’ashi har guda uku wanda ake masa dressing dasu.. Dukda azaban zafin da yakeji amma sabida taurin zuciya bai fasa jan jiki har ya tsinta kansa cikin d’akin.. A yayinda hankulansu gaba d’aya yayi kan Giwa dake ambato sunan Sadauki kaman yanda take kiran Mahmood d’in, a daidai wannan lokaci Jamal yai k’ok’arin mik’ewa saman sandarsa Sai ciza labb’a yake sabida azaban da yakeji... Mahmood da idanunsa ke kan Giwa yana ganin halittar data koma Sam bai kula da Jamal ba wanda ya saita almak’ashin yana sakin huci zai cakkawa Mahmood a k’ahon zuciya... Daga nan yanda yake tsaye can bayansu dafe da sandarsa yake fad’i cikin zuciyarsa.. A yau zaka bak’unci lahira Mahmood.. Wannan karaga bazaka tabbata akai ba kaman yanda Ubana Tal’udu ya fad’i a yau zan gajesa zanyi ajalinka nayi ajalin Mulkinka.. Zan cikawa Mahaifiyata burinta sannan na tabbatar da kalaman mahaifina cewa Mulkinka Bazai k’argo ba....! Yana ida tunanin ya saita bakin almak’ashin masu tsananin tsini dai dai saitin k’ahon zuciyar Mahmood yai majajjawa ya jefasu a tare....
SameenaAleeyou 📚
[10/10, 7:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
_(MAY 2021)_
*88*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Yazeed da shi kad’ai ne yake iya hango Jamal da abinda yake k’ok’arin yi... Dan hankalin Mahmood gaba d’aya naga Giwa yayinda Fu’ad da Ja’afar suka bama Jamal d’in baya hakan yasa bazasu iya ganinsa ba...Wani irin k’arfi ne yazo ma Yazeed yai tsalle daga nan saman gadonsa ya isa ya hankad’a Mahmood gefe ya tare masa makamin da Jamal ya jefa masa ai kuwa take guda biyun suka cakki wuyansa suka huda, guda d’aya ya karjesa a k’irji amma babu Wai na wuyan sun huda masa wuya sun b’arka masa mak’ogoro, take ya zube a k’asa jini ya shiga fita daga bakinsa har hancinsa... Mahmood ya tallafosa ya fad’o saman hannunsa yana ambaton sunansa yayinda Giwa Ta k’walla wani irin k’ara tana ambaton sunan Yazeed itama... Ja’afar da Fu’ad a tare suka juya suna duban wanda yayi wannan aika aika wanda target d’insa Mahmood ne... Aiko Jamal yana ganin sun waigo ya shiga jada baya cikin sauri dafe da sandarsa..Mahmood ya shiga fad’I masu cikin tsananin tashin hankali su kira Dr, a d’ari Ja’afar yabi bayan Jamal da tuni ya fice bayan ya shime dogari guda da sandarsa sannan ya cakka ma guda d’aya scissors a wuya... Can Ja’afar ya hango Jamal yana k’ok’arin guduwa Ta k’ofar baya... Cikin wane irin doka kira yace dashi “Jamaaaal..!!” Aiko Jamal yana hango Ja’afar ya k’ara sauri, take Ja’afar ya nad’e hannun rigarsa yabi bayan Jamal a guje...
Jakadiya wacce dama tana biye dasu a rakub’e saidai sanin batada ‘yancin shiga d’akin ya sanyata tsayawa daga waje tana ganin abindake faruwa Ta sami zarafin shigowa cikin d’akin itama... Aiko Giwa tana ganinta tace da ita maza ta fitar da ita taga Jamal d’inta kar su kamasa su kashesa... Jakadiya zatai magana Giwa ta katseta da fad’in ta fitar da ita taga Jamal d’inta kar wani abu ya samesa ba k’oshin lafiya bane dashi...
Haka Jakadiya ta shiga turo Giwa suka nufo waje...
Yazeed da jini ke zuba daga cikin jikinsa kwance yake saman cinyar Mahmood yana so yai magana amma babu hali... Cikin d’igan hawaye Mahmood Ke dubansa yana fad’in “Just hang in there Yazeed... Zaka samu lafiya in sha Allah, Fu’ad yaje kiran Likita yanzu zasu shigo su dubaka... Just stay with me kaji...!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin k’arfafawa Yazeed d’in gwiwa... Daidai lokacin Fu’ad da Dr suka shigo cikin tsananin sauri tare da wasu nurses biye dasu...Fu’ad ya isa ya dafa kan Yazeed yace “Brother zaka sami lafiya In sha Allah...!” Shidai Yazeed bai iya furta masu komai ba Sai dubansu da ido da yake...
Sauri sauri Fu’ad ya fice dan ya cimmasu Jamal da Ja’afar....
Dr da nurses suka amshi Yazeed daga hannun Mahmood suna fad’in “We’d take it from here your Highness...!” A hankali Mahmood ya jinjina masu kai kana ya fito waje yana jiran su gama duba Yazeed d’in su fito masa da bayanai, Allah ya gani ko motsawa daga wajen bazai iya ba har Sai yaji a wani hali Yazeed yake...
A can waje kuwa Jamal ya haye can k’ololuwar saman wani bene uncompleted building dake a nan cikin asibitin yana duban Ja’afar dake k’ok’arin cimmasa yana lek’a k’asa Dan babu wajen tsira wajen gudu ya k’are... Saidai yayi tsalle ya fad’o k’asa... Ja’afar ya d’anyi surrender hannayensa duka biyu a sama yake fad’in “Don’t Jamal.. Don’t jump, it’s over... Just turn yourself in...!!”
Cikin huci Jamal ke fad’in “I rather die than na tsaya na tafi prison ko na zamto bawanka.. Gwara na kashe kaina da na zamto bawanka Ja’afar..!!!”
Ja’afar ya jinjina kai a hankali yace “Please don’t Jamal, don’t kill yourself, just surrender now...!”
Daidai lokacin Fu’ad ya k’araso saman benen, ya tsaya gefen Ja’afar shima yana duban Jamal dake yunk’urin fad’awa daga saman ginin...
Fu’ad ya shiga girgiza kai yana k’ok’arin K’arasowa kusan Jamal d’in yake furta “Please Jamal, don’t, don’t think of doing that...!”
Cikin zuban hawaye Jamal Ke dubansa yana fad’in “No Fu’ad... Babu sauran rayuwa a gareni, bazan tsaya na zamto Bawa a gidan dana girma cikinsa matsayin Yarima ba.. Bazan tsaya na kalli matar da nake matuk’ar son kasancewa da ita ta k’are da wancan Bawan ba..!” Ya k’arashe yana nuna Ja’afar lokaci guda yaci gaba da furta “Just take care of Maami please Fu’ad.. Duk abinda tayi tayisu ne sabida mu.. Nida kai da kuma Yazeed.. Bata da kowa sai kai Yanzu, dan Allah ka kula da ita kaji..!” Ya k’arashe cikin zuban hawaye... Fu’ad d’in ma cikin zuban hawaye yake furta “You can still choose to do what’s good Jamal, please don’t kaji..!” Ya k’arashe yana kuma matsowa a hankali yana so ya rik’o Jamal d’in ya hanasa fad’awa..
Sandarsa ya d’ago ya dafe gini kad’an yana nuna Fu’ad da sandar yake fad’in “Don’t come near me Fu’ad idan ba so kake mu fad’a tare ba.. Just stay right there.. Maami still needs you, take care of her kaji.. Tell her I love her, and I do everything for her...! Goodbye Fu’ad... Goodbye brother! Yana ida fad’i haka ya ci gaba da takawa da baya da baya har ya isa k’arshen ginin... Fu’ad ya nufosa a guje yana k’walla kiran sunansa inaaa tuni Jamal ya fad’a da baya... Suna jin sautin k’aran da ya saki alamun wani abu ya sokesa kafin ya k’arasa k’asa...
Giwa da k’arasowarsu kenan Ta hangi wannan tashin hankali Jamal d’inta ne Rodin gini ya sokesa ya huda cikinsa... Ta saki wane irin k’ara mai tsananin gaske tana duban wannan tashin hankali...
Fu’ad da Ja’far suka k’arasa cikin sauri yanda suka hango Jamal a k’asa k’arfen da ake ginin dashi ya hudasa... A tare sukai saurin rintse idanunsu had’ida dawowa da baya.. Ja’afar yai saurin rungume Fu’ad wanda tuni ya zama out of control sabida ganin wannan kayan tashin hankali da yayi...
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Kowa farkonsa ya sani bai San k’arshensa ba.. Ya Allah ka bamu k’arshe mai kyau kasa muyi mutuwa mai kyau ..Ameen..! Yau ga bak’ar zuciya takai Jamal ga kashe kansa, hukuncin wanda ya kashe kansa kuwa babu shi babu rahamar Ubangiji domin ya mutu kafuri ne...
A daidai gaban Giwa ya fad’o.. Babu abinda zata iya yi, ko motsawa ta isa garesa bazata iya ba sabida Jamal d’in ya riga ya nakasata da allurar da yaso nakasa Muhibbah dashi.. Haka Giwa tanaji tana gani taga d’anta mafi soyuwa a gareta wanda suke duk wani dirty works d’in tare kwance a k’asa cikin jini, yanda suka halak’a mutane da dama ba tareda wasu nasu sun Iya yin komai ba yau ga Jamal d’inta itama kwance gabanta kuma babu abinda zata iya akai... Rayuwa kenan ka shuka alkhairi domin ka girba mai kyau...
A can cikin asibiti ma likitoci sunyi all they could amma da alama lokacin Yazeed ya riga yayi, Jamal yayi sanadiyan mutuwar Yazeed sannan shima ya kashe kansa...
Mahmood ya buk’aci ya shiga yaga gawan Yazeed.. Yai tsaye saman kansa hawaye na gangaro masa.. Lokaci guda ya shiga tuno rayuwarsu na baya, sun kasance basa jituwa tsawon rayuwarsu yau sai gashi Yazeed d’in ya sadaukarda rayuwarsa gareshi, sai gashi ya zamto shine mutum na k’arshe da ya gana da Yazeed d’in kafin ya bar duniya.. Take wani irin kuka mai k’arfi yazowa Mahmood, ya kifa kansa gefen Yazeed d’in yana kuka sosai, lokaci guda yake furta “Allah ya yafe maka Yazeed.. Allah ya yafeka Brother..!” Ya k’arashe yana mai dafa tafin hannunsa saman goshin Yazeed...
Hankula sun tashi sosai, kan kace mai labari ya isa masarauta.. Wannan kayan tashin hankali da yawa yake, yau babu Yazeed babu Jamal... Innalillahi wa Innalillahi raji’un.. Ya Allah ka bamu jarabawar da zamu iya ci... Idan Kaga Fu’ad dole ne ma ya baka tausayi saidai ko kusa Ja’afar bai bar side d’insa ba tun bayan da abun ya faru.. Kullum Ja’afar na taredashi yana kwantar masa da hankali... Yau kwanaki bakwai kenan da mutuwar Yazeed da kuma Jamal Fu’ad yai sallama ya shigo Babban Gwani... Ya risina ya gaida Mai Martaba...
Mahmood yace dashi “Fu’ad an fito..?”
Fu’ad ya jinjina masa kai a hankali yace “Eh Rankaidad’e na shirya, flight d’in k’arfe shabiyu na rana ne..”
Sarki Mahmood ya jinjina kai a hankali yace “Da kyau..! Mun riga munyi magana da mutanenmu na can Spain d’in komai an gama shirya maka, da zaran ka isa zasu nemeka..”
Fu’ad ya risina ya kuma yima Mai Martaba godiya kana ya k’arada “In sha Allah nayi maka alk’awari zan nastu na k’arasa karatuna... In sha Allah..”