Sashe 9
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi mai sauti wannan karon Tal’udu yai maras dad’in sauraro kana ya janyo wata jaka ta fata ya baje jakar a k’asa... Take jakar ta koma tamkar tray ta fata ga yashi mai tsananin taushi akanta... Da yatsunsa guda biyu yasa ya zana alama kusan guda hud’u kewaye da juna kan ya zana wani abu tamkar karagar mulkin Masarautar a tsakiya...Ya d’ago yana duban Giwa da kyau kana ya kuma Sa yatsunsa biyu ya zana wani alama daga cen gefe...
Saida ya gyara zamansa sosai kana ya soma mata bayani...
“Kinga wad’annan alamu hud’u dana zana yaranki ne guda hud’u.... Wannan da yake tsakiya Karagar Mulki ne... Tabbas a cikin yaranki akwai wanda zai gaji mahaifinsa, sannan sarautar Masarautar nan bazata fice daga cikin jinin ahalin Sarki AbdulJabbar ba.... Toh amma....!” Shiru yai yana dubanta...
Giwa ta katsesa da fad’in “Amma mai Tal’udu..? Sannan shi wancan alaman da ka zana na menene.....?”
Murmusawa yai kad’an kana yace “Wancan alama ta k’arshe dana zana fitilar tsafi bata hasko min komai ba, tsantsan duhuwa ne mai gauraye da bak’in k’ura a wajen wanda yake nunida cewa dik d’anki da ya d’ale wannan Karagar Mulki toh fah mulkinsa bazai k’argo ba sannan duk wasu sirrika da kika bisne a Masarautar nan zasu bayyana... Zaki rasa mulkin Masarautar nan dake da ahalinki zaku zamto tamkar ba’a tab’a yinku ba... Abubuwa da dama zasu canza....!”
Katsesa Giwa tai da fad’in “K’arya ne wllhi.. Babu wani mahaluk’in da ya isa ya rabani da wannan gadon mulkin... Nida zuri’ata zamu ci gaba da mulkar Masarautar nan... Kawai ka sanar dani mai ka gani gameda bayyanar mahaukaciyar nan....!!”
Kai tsaye ya soma fad’in “Naga guguwa mai k’arfin gaske gauraye da bak’in k’ura a cikin gungun mayaka... Naga TAKWABI mai kaifin gaske sannan naga mashi da kibiya mai tsananin tsinin... Kinyi kuskure da kika bar wannan k’ofa d’aya tak a bud’e...!!!”
Giwa ta katsesa da fad’in “Wannan k’ofa kana nufin Ja’afar ne...?”
Murmusawa yai kad’an kana yace “Ba Jafaru bane amma ita wannan k’ofar da kika barta da gib’i ka iya zamtowa sanadin ‘Yanta Jafaru....!!!”
Daga haka dariya ya kwashe dashi mai mummunar sauti... Kan kace mai ya b’ace b’at kaman bashi a wajen.....
Giwa ta mik’e da k’yar gumi na karyo mata... K’ofofi guda goma shabiyar ne rus a jere a gefen d’akin Tal’udu, ko wata k’ofa a k’ulle take sai guda d’aya da take hangota a bud’e wanda duk randa ta shigo wannan gida haka nan take a bud’e....
A hankali ta furta “Muje Jakadiya...”
Babu musu Jakadiya tace “An gama Allah shi baki yawan rai....!”
‘Yan matan suka sadda kawunansu k’asa har saida su Giwa suka fice daga wannan gida da yafi kama da sansani....
Koda Giwa ta komo sashenta haka abubuwan saukaita mata yawo, batai mamakin ganin Jamal zaune hard’eda k’afofi alamun yana jiran dawowarta ba.... Domin kaw bazai tab’a bacci ba ba tareda ya nemi albarka mahaifiyarsa ba koda kuwa zai jira dawowarta har asubahi ne...
Yanayin da yaga mahaifiyar tasa ciki na tashin hankali ya sanyashi k’arasawa gareta ya tarota...
“Mamy...Mamy na meke faruwa....? Ina kika fito cikin daren nan...?”
Idanu ta zuba masa tana dubansa, lokaci guda ta shafi gefen fuskarsa kana tace “Babu komai masoyina... Ya ka baro d’an uwanka Fu’ad...?”
Fuzar da fuci Jamal yai a hankali kana yace “Karki damu Mamy zan kula da Fu’ad...”
Ta jinjina masa kai a hankali ba tareda ta kuma cewa komai ba,
Jamal ya d’an dubeta cikeda kulawa kana yace “Maami akwai wani abu ne..?”
K’uri tai masa kana ta muskuta kad’an tace “Jamal ka tabbata gaskiya ka fad’in gameda batun Ja’afar...?”
Wannan karon da gefen bakinsa ya murmusa kana ya tako zuwa gabanta a hankali... Durk’usawa yai nan gabanta kana yace “Ban tab’a miki k’arya ba Maami na dik abinda na sanar dake da gaske hakance Ta faru....!” Ya k’arashe murmushi kwance saman fuskarsa...
Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Giwa tai kana ta shafi gefen fuskarsa tace “Kaje ka kwanta D’ah na Allah shi maka Albarka...!” Ta k’arashe tana shafa sumarsa cikeda so da k’auna...
Jamal ya amsada “Ameen Maami na kana ya kuma mata sallama ya fice...
Giwa taci gaba da tinanin abububuwan da suka faru cikin Masarautar..
***
Ko kallo bata ishesa ba saima cire zobban hannayensa da agogo da yakeyi, ya zuba su saman bedside kana ya kwab’e rigar mulkin dake jikinsa kyakkyawar suffarsa Ta bayyana, Rahima tai saurin rintse idanunta tana tina yanda alak’arsu da Yazeed ya samo asali...
Gimbiya Raheema k’anwacega Gimbiya Zeenatu amaryar Sarki AbdulJabbar mai rasuwa... Su d’in ‘Ya’yaye ne ga Sarkin Akwanga wanda ke k’ark’ashin mulkin Sarki AbdulJabbar gaba d’aya dashike garin a k’ark’ashin k’asarsa take,...A lokacin da Rahima tazo Masarautar Jos bikin ‘yaruwarta Zeenat a nan tai gamo da mutumin da zuciyarta Ke muradin mallaka, wannan mutumi kuwa ba kowa bane face Yarima Mahmood AbdulJabbar, saidai kash abinda yai mata cikas shine Yarima Mahmood baida lokacin wata Mace face na iyalinsa Aliya.... Hasalima Auren mahaifin nasa ya kawosa k’asar bayan matsa masa lamba da mahaifin nasa yai da cewa lallai lallai sai ya halarci d’aurin aurensa da zai sake... A lokacin daga shi sai matarsa Aliya suka zosu Nigeria d’aurin auren Mai Martaba basu taho da Zahra ba a cewarsu tana makaranta, sannan bayan sunyi Abinda ya kawosu da kad’an suka kuma tattarawa suka koma Spain dikda cewa Giwa bataso d’an nata ya kuma tafiya ba amma babu yanda zatayi wannan tsinanniyar matar tasa d’iyar matsiyata tasan dan ita yake gudun gidansu dan yasan muddin yana Nigeria idan batasa ya rabu da wannan matsiyaciyar ba toh kuwa ko shakka babu aure zasu sake masa a Fada ‘yar asali ‘yar babban gida kaman yanda yake d’an manyan mutane....
Rahima bata sami hakan ba taci kuka har ta gode Allah dan Shi Yarima Mahmood baima San akwai wata halitta mai suna Raheema dake k’aunarsa ba... Tun bayan auren Maimartaba Sarki AbdulJabbar da ‘yaruwarta Zeenat tai sai tai zamanta a wannan masarauta da burin wata rana Mahmood zai dawo gida ya aureta dan bata cire rai ba, a wannan zaman da tai a masarautar suka k’ulla abota da Zuhra matar Yarima Yazeed domin zasuzo tsara da Zuhra, tasu tazo d’aya sosai hakan yasa daga abokai har suka koma tamkar aminai, so tari Yazeed yakan tsinci hirar matarsa Zuhra da Rahima yanda Rahima Ke sanar da ita irin k’aunar da takewa d’an uwansa Mahmood... Shak’uwar Raheema da Zuhra dai tai nisa sosai tamkar wasu ‘yanuwan juna, ko Akwanga Rahima ta tafi Zuhra taita damunta da waya kenan tana tambayarta yaushe zata dawo tsaban shak’uwa da aminci dake tsakaninsu musamman dashike Zuhra mutum ce mai Saurin yarda da d’anadam ga sanyin hali da kyakkyawar zuciya....
Wata ranan jumma’a Rahima Ta shigo b’angaren Zuhra da niyyan surprising d’inta dan ranan ta dawo daga tasu Masarautar.... Bata tadda Zuhra da yaran a k’asa ba sannan babu motsin mutane cikin sashen, sai tai zaton Ta sallami kuyangin ne dan wataran idan zatai baccin rana takan sallamesu idan da mai yin wani abu nasa na k’ashin kansa ma ya samu yajesa yai, sannan watak’ila yaran na makaranta basu dawo ba, hakan yasa kai tsaye ta haye d’akin Zuhra ta bankad’e k’ofar da k’arfin gaske tana mai furta “Surprise...!!!” Birki tai da kalaman nata ganin abinda idanunta suka gano mata...
Yana tsaye gaban gado jikinsa babu riga sai k’aramar towel dake rik’e hannunsa wanda da alama jik’akk’en sumarsa dake d’igan ruwa yake gogewa....
Rahima tai saurin rintse idanunta jiki na rawa take furta “I’m so...I’m sorry...I’m sorry please..!!” K’afarta har na hard’ewa take k’ok’arin juyawa saidai tuni taji an fizgota an dawo da ita cikin d’akin ta fad’o saman k’irjin mutum... Ta bud’e idanunta masu cikeda tsoro tana dubansa, saidai ga tsananin mamakinta shu’umin murmushin nan ne nasa saman fuskarsa... Lokaci guda kuma sai gani tai ya mugun had’e rai yana mai k’arewa fuskarta kallo idanunta zuwa bakinta...
Jikin Rahima bai daina rawa ba mak’ale jikin Yazeed... Lokaci guda kuma sai gani tai ya d’an murmusa kad’an kana yace “Malama idan zaki saki jikinki ki saki jikinki, ce miki akai bansan ke d’in ‘yar hannu bace... Sai wani k’ifi k’ifi da idanu kike min, sarai target d’inki kenan tinda kinsa every Fridays Zuhra na tafiya sashen Giwa da yara suyi mata yini shine kika kasa rik’e kwad’ayinki kika lab’ab’o kika hauro har sama kika kawo kanki yanzu zaki wani matse fuska tamkar tsoron gaske kike, ko ce miki akai bana lura da irin kallon maitan da kike bina dashi ne...” Ya kuma murmusawa da gefen bakinsa kana yace “You don’t play such games with Prince Yazeed sweetheart.... Abinda kikazo nema zaki samu, batai aune ba sai jin fuskokinsu tai sun had’e waje guda....
Rahima ta raina kanta ta kuma raina duk wasu mazaje da tai huld’a dasu a baya, ta yarda Yazeed k’arshe ne yanda yake a zahiri haka yake a shimfid’a, idan kuwa har bazata sami Mahmood ba tinda batada tabbacin zai dawo Masarautar dan haka ta zab’i taita maida kwad’ayinta da d’an uwansa Yazeed wanda takeji tamkar da Mahmood d’in take tare....
Saidai bayan komai ya lafa tsakaninsu ko takanta bai kuma bi ba saima ficewa da yai kaman babu abinda ya faru tsakaninsu, haka dai Rahima ta mik’e ta kintsawa Zuhra d’akinta can k’asar zuciyarta tana jin sam bata kyautawa Aminiyar tata ba... Tin Daga wannan lokaci haramtacciyar alak’a ta k’ullu tsakanin Yazeed da Rahima...
Tayi nisa cikin tinanin nan ta sinkayo muryarsa Cikin dakewa yana furta “
“Kinsan ba’a min yanga, so take that thing off....” Ya k’arashe yana mai kuma relaxing cikin gadon....
Jiki a matuk’ar sanyaye Rahima tasa hannu tana zame doguwar rigar dake jikinta hawaye basu daina gangaro mata ba.... Da gefen idanu yake dubanta har ta k’araso gabansa a d’arare tamkar mai tsoron taka k’asa, yau d’in ko idanunsa ta k’asa duba....
Saida ya kwashi dak’ik’ai yana k’are mata kallo daga nan yanda take tsaye kana ya bata izinin zama dan bata isa ta zauna saman gadon ba ba tareda yace tai hakan ba....Ta narka masa harara tana mai kuma ci gaba da share hawaye... A hankali ya mirgino gareta, Rahima na jin hannayensa cikin jikinta Ta fashe masa da kuka...
Da tsananin mamaki Yazeed ke duban sabon salon nata...