← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 162

Sashe 132

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’akin dake gefe da nasa ya kaita ya kwantarta saman gado, ya d’an rank’wafo da wuyarsa kad’an sanda yake k’ok’arin ajiye kanta saman pillow, daidai saitin wuyarsa yaji kaman hucin numfashinta, ya karkato da fuskarsa yana duban nata fuskar yanda idanunta ke lumshe... Ya jima sosai yana duban fuskar nata da yanda jini ya d’an bushe ciwon da Jamal yaji mata, sosai ya runtse idanunsa sanda ya tuna ganin Jamal da yayi yana k’ok’arin auka mata wanda ba don Allah ya kawosa akan lokaci ba da ya aikata mata abinda suka aikata gareta shekarun baya, wancan ma da suka aikata duk tunowa da zai sai yaji kaman mashi ake caka masa a k’ahon zuciyarsa balle yanzu da yaga Jamal akan idanunsa na k’ok’arin aikatawa..! Sai faman dunk’ule hannunsa yake idanunsa na duban wani b’angaren zuciyarsa na kuma masa zogi yana murza zoben dake hannunsa, har saida yaji k’aran fad’uwar zoben saman tile kafin ya maidoda dubansaga zoben nasa..! A hankali ya mik’e ya nufi bathroom ya d’ebo ruwan d’umi kad’an a roba had’eda k’aramar towel ya zauna gefenta ya shiga danna mata goshinta dashi..! Yana danna mata towl d’in yana tuno duk abubuwan da suka faru tin daga lokacin da ya d’aurata saman dokinsa tana k’arama ranan Washe garin sallah da suka tsinceta, ranan da Giwa da ‘ya’yanta suka b’ata mata rayuwa..!

A hankali ya soma furta “I shouldn’t have left you alone with them..! I should have stayed..!” Muryarsa ya sark’e sabida tsananin rawa da muryar keyi, lokaci guda yake furta “Please Ki yafe min, Ki yafe min da ban tsaya na kaiki gida ba..!” Ya k’arashe yana mai k’ura ma fuskarta idanu fsukarsa dab kusan nata, hawayen dake mak’ale cikin idanunsa guda ya d’igo, ya d’iga a daidai saitin idonta, hawayen nasa ya ratsa ya shige cikin idonta wanda yasa idanun nata motsawa..! Idanunsa a lumshe hannunta guda rik’e cikin nasa ta soma k’ok’arin bud’e idonta..! A hankali take jin idanunta suna k’ok’arin bud’ewa, tana iya hango fuskarsa dururu, har sai da ida bud’e idon nata..
Cikin yanayin tsoro Ta soma k’ok’arin mik’ewa, Mahmood ya bud’e idanunsa Tar cikin nata idanun...
Zuciyarta yaci gaba da bugawa abubuwan da suka faru suna kuma dawo mata, yanzu ga Rankaidad’e zaune kusanta hannunta cikin nasa..! Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa, tsoron abubuwan da suka faru da wanda taji suka kuma dawo mata..! Numfashinta ya soma fita da sauri sauri tana mai kuma k’ok’arin fuzge hannunta daga rik’onda Mahmood d’in yai mata..! Bai saki hannun nata ba saima dad’a matse hannun nata da yayi cikin nasa...!

Tana gani yake k’ok’arin kwanto da fuskarsa kusan nata, idanunta suka kuma firfitowa waje tana k’ok’arin k’walla ihu yai amfani da d’aya hannun nasa ya toshe bakinta, saitin kunnenta yakai bakinsa had’ida rad’a mata “You’re safe now, you’ll always be safe... around me..! Stay here in bed and get some rest..! Likitarki zata K’araso nan bada jimawa ba..!!”

A hankali yake jin bugun zuciyar nata na raguwa alamun tsananin tsoron na d’an sakinta, idanunsu cikin na juna har lokacin hannun Mahmood na saman bakinta, har saida yaji natsuwa na sauk’o mata a hankali kana ya zame hannunsa daga saman bakinta..! Ta ja wani irin ajiyan zuciya tana mai dubansa har ya mik’e tsaye, tana gani ya ciro wayarsa a aljihu yana amsa kiran Turaki da alama maganar likitar suke..!

Mahmood na ficewa ta mik’e zaune da k’yar tana mai kuma jan wani dogon numfashin had’ida dafe kanta idanunta a rintse..!
Kusancinta da Rankaidad’e ya soma d’aure mata kai, a yau d’in tasan Shi baidaga cikin ahalin Giwa kuma shid’in d’ah ne ga yayar Mahaifinta amma kasancewarsa d’an uwanta bai halatta masa kusantuwa da ita har haka ba..! Tab’a k’ofar da akai ya sanyata saurin bud’e idonta da yai mata tsananin nauyi, wata mata ce ta gani wacce kaman tasan fuskarta a wani wajen, gefe da ita wata matar ce wacce ke sanye cikin shiga irinta likitoci...

SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*

*77*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Muhibbah tai K’uri tana duban matar wacce itama d’in ita take duba, tana mai takowa cikin d’akin a hankali..! Sai yanzu ta fahimci ko wacece wannan matar, mahaukaciyar nan ce data bata Taswira, wacce ta taimaka masu suka fice daga cikin Masarauta taredasu Ubandoma da Ja’afar, sannan itace Giwa ta sanar da ita cewa mahaifiyar Yarima Mahmood ne da kuma Ja’afar, ‘yar uwa ga Marigayi mahaifinta..! Take taji wasu irin hawaye suna zuwa idanunta, duk labarun zalunci da Giwa tayi ma wannan mata da ahalinta suka shiga dawo mata daki daki..! Tana gani matar dake zuban hawaye takai hannunta dake tsananin rawa tana shafa fuskarta, su duka biyun suna duban juna hawaye na gangaro masu... A hankali matar ta janyota cikin jikinta ta rungumeta sosai kuka mai k’arfi na kufce masu gaba d’aya, saida sukayi mai isansu kana ta kamo hannayen Muhibbah tana juyawa tana kuma kallon illahirin jikinta har zuwa fuskarta... Muhibbah dake sakin murmushi takai hannunta a hankali tana share hawayen matar, su duka biyu murmushi ne mai gauraye da hawaye saman fuskokinsu...

Hannayenta rik’e cikin na matar take tambayarta “Sun kuma cutar dake..?!”

Ta girgiza mata kai a hankali alamun a’a “Allah bai basu nasara ba..!” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya..
Lokaci guda taci gaba da fad’in “Ke ‘yaruwar.. Mahifina ne... Giwa ta fad’a min haka da bakinta, ta sanar dani abubuwa da dama, ciki harda yanda ta rabaki da ‘ya’yanki guda biyu... Rankaidad’e da Ja’afar ‘ya’yanki ne..! Haka tace..! Muje muje mu samesu mi sanar dasu..!!” Ta k’arashe a d’an rikice tana mai k’ok’arin sauk’owa daga saman gadon...

Hannunta Gimbiya Turai ta kamo ta zaunarta kana tace “Sun riga Sun San komai, asirin Izzatu ya gama tonuwa a cikin Masarautar nan..! Illahirin jama’an K’asar nan a halin yanzu sunsan wacece Izzatu da ta’asan da ta jima tana aikatawa shekara da sharkaru..! Allah shine abin godiya wanda ya k’addari sake had’uwarmu ya kuma cire fargurbi cikinmu..!!”

Muhibbah ta jinjina kai a hankali sai kuma tace “Inaso naje naga Umaima domin kuwa Giwa ta sanar dani cewa Umaima ‘yar uwatace wanda matar da mahaifina ya aura a lokacin da ya tafi nemanki ta haifa masa, Ta sanar dani yanda ta hallak’a mahaifiyar Umaima cikin wuta ta kuma tahoda Umaima cikin Masarautar nan..!!”

D’ago kan da zatayi ta hango Umaima na shigowa cikin d’ingishi hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta..! Muhibbah tana ganinta ta mik’e zumbur wasu hawayen na kuma gangaro mata, lokaci guda Ta soma takowa dukda rashin k’arfin dake jikinta, saida ta k’araso har gaban Umaima kana taja ta tsaya hawaye basu daina ambaliya a fuskokinsu ba.. Lokaci guda suka rungume juna suna masu ci gaba da sakin kuka..! Gimbiya Turai tai masu K’uri tana dubansu cikeda shauk’i, Allah sarki d’an uwa mai dad’i, a yau ahalin d’an uwanta Alfah sun had’e waje guda... Allah ya kuma had’asu gaba d’aya shin mai yafi wannan d’ad’i... Inama Alfah yanada rai yaga d’iyoyinsa Allah ya had’esu, tabbas Allah ya cika abin godiya mai yawan rahama ga bayinsa.. Yau ko babu Alfah Allah ya bar zuri’arsa a doron k’asa bayan duk kalan makircin da Izzatu tayi domin ta k’arar da ahalinsa a bayan k’asa... Tabbas Sara da sassak’a baya hana Gamji toho, Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ko ana shaho toh fah sai yayi, Ko a yanzu Allah ya d’auki rayuwarta ya cika mata burinta, ya had’ata da ‘aya’yenta guda biyu bayan tsawon shekarun nan sannan ya had’ata da ‘ya’yan d’anuwanta wanda zataga d’anuwanta a tattare dasu..!

Umaima da Muhibbah hannayensu rik’e cikin na juna suka zauna saman gado Umaima na fad’in “Nayi zaton bayan Giwa da ahalinta banida sauran dangi a duniyar nan kaman yanda Ta sanar dani, Ashe ba haka bane ita d’in hankaka ce mai maida d’an wani nata Domin ta cutar dashi, ita d’in ta k’ware wajen satan yaran mutane..! Taso tarwatsa ahalinmu sai Allah ya sake had’amu a cikin gidan nan, tin kallon farko da na miki Muhibbah naji ina k’aunarki ashe ked’in ‘yaruwata ce ta jini..! Alhamdulillah Allah ya nuna min ahalina na gaskiya, ba wannan azzalumar matar da d’anta da suka so cutar dani ba..!”

Muhibbah ta murmusa ta kuma kamo hannun Umaima tace “Hakance ta kasance dani sanda na soma tozali dake Umaima, Alhamdulillah.. Mun godewa Allah da baiwa wad’annan azzaluman damar cutar damu ba..!”

Umaima ta kuma murmusawa tana goge hawayen fuskarta take furta “Thank you Big Sis for saving me..!!”
Muhibbah tai mata K’uri jin ta ambaceta da big Sis, Ashe akwai rana irin wannan da zatazo ta ga jininta tayi zaton tun bayan rasa k’anwarta da tai bazata kuma jin wani ko wata ya ambaceta da ‘yaruwa ba sai gashi yau d’in taji haka... Tai saurin janyo Umaima cikin jikinta ta rungume suna matsan k’wallan Farin ciki..!

Likita ma saida ta matse k’walla ta dubi Muhibbah tace “Anya Rankidad’e ked’in patient ce kuwa, naga kaman da k’arfinki... Yanda aka d’ago min hankali na fito babu shiri ban zaci zan ganki haka ba..!”

Murmusawa Muhibbah tai tace “Lafiyata lou Dr, kaina ne kawai Ke min ciwo...!”

Dr ta jinjina kai tace “Naji dad’i da jin hakan, Allah ya k’ara lafiya..!” Ta ciro PCM cikin ‘yar jakan nata ta mik’a nata tace “Idan kinci abinci sai ki sha ki d’an samu bacci ki huta koh..!”
Nan ma jinjina mata kai Muhibbah tai had’ida mata godiya..!

Likita tai masu sallama sukai mata godiya gaba d’aya kana Ta fice..
wata Hadima ce ta shigo ta risina gaban Gimbiya Turai tai mata magana kaman mai bata sak’o... Yayinda Muhibbah da Umaima Ke ci gaba da tattaunawa Umaima na fad’in Ta bata labarin mahaifinsu da abubuwan da suka faru..!

Gimbiya Turai ta katsesu da fad’in “Yarana ku tashi muje koh..!”

Babu musu suka mik’e gaba d’aya Muhibbah na dafe da Umaima tana taimaka mata, a tare suka nufo downstairs, nan Muhibbah Ta fahimci b’angaren Rankaidad’e suke, bata dai ce komai ba har lokacin... Suka fito gaba d’aya yayinda wasu Hadimai guda uku suka risina masu alamun gaisuwa, lokaci guda sukai masu jagoranci zuwa masauk’in Muhibbah wanda Yarima Mahmood ya ajeta kafin su Giwa su kamata, Kaman bazata shiga ba taja Ta tsaya turus tana duban Umaima da Gimbiya Turai..
Chapter 132 · 0% Book details