Sashe 76
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jakadiya tai saurin girgiza kai tana mai kuma risinawa “Allah shi baki yawan rai kinfi gaban dodanniya annurinki da k’warjininki ya cika wajen nan gaba d’aya..!” Ta k’arashe tana d’ago babbar yatsarta alamun jinjina... Cikin zuciyarta kuwa cewa take ai kinfi gaban dodanniya a munin halitta yau d’in...
Ta kuma risinawa tabi bayan Giwa dake kuma rufe fuskarta cikin bak’ar alkyabbarta...
Mahmood dake tsaye sararin farfajiyan sashensa nan ya hangi mutane suna tafiya cikin bak’ak’en kaya... Kafin ya ankare sai wulk’awansu ya gani bai kumaga yanda suka nufa ba... Toh su wanene wad’annan..? Take tinanin abinda ya gani kwanakin baya ya dawo masa... Mutumin da ya tab’a gani cikin Masarautar da bak’ak’en kaya... Toh su kuma wad’annan su wanene... Shin su waye suke shawagi cikin dare a Masarautar..? He needs to find out..! Ya k’arashe tinanin nasa yana mai kuma k’arema fad’in Masarautar kallo daga can sama yanda yake tsaye...
Zanen ginin gidan Sarauta da Wambai ya basa ya d’auko ya k’urama taswiran idanu sosai yana son fahimtar wani abu abinka da mai ilimin sanin sirrikan zane iri da kala... A hankali ya saka yatsar hannunsa guda yana bin wani layi dake jikin zanen, yaita bin dik wani hanya da layin ya ratsa har saida ya iso mahad’an layin yanda dogon layin ya tsaya... Da alama layin ba’a nan zai k’are ba, duk yanda akai akwai ci gaban wannan zanen dake rik’e hannunsa... Toh ina zai samu...?! Yai shiru tamkar mai nazari... A hankali ya ninke taswiran ya maidata ma’ajiyarta ya aje....
**
Juyi taketa faman yi saman gado amma babu bacci babu alamunsa, tayi salloli tayi addu’o’i amma duk dai baccin bai Zo mata ba... Idan ta rintse idanunta shi take hangowa sanda ya fito daga babban Zauren taro kwantattun k’walla cikin idanunsa, Ta mik’e ta zauna sosai tana tina tun Farin had’uwarsu sanda ya d’aurata saman dokinsa tun tana k’aramar yarinya, ta tuna had’uwarsu ta farko bayan komawarta da nufin tarwatsa ahalinsu, ta tuna sanda ya saving rayuwarta a cikin museum sanda ya tureta katako ya fad’i kansa...Ta tina kub’utar ta da yai yau d’in a hannun Yazeed.. Ta tuna yanda ya kawota har gida ya tabbata she’s safe...! A hankali ta kuma lumshe idanunta wasu hawayen suka gangaro mata... Shin Maiyasa rayuwa haka..? Maiyasa mutanen kirki suke shan wahala... Yanzu shikenan ta janyo mutumin da yafi kowa cancanta da mulkin Masarautar zai rasa sarauta kuma ya rasa d’iyarsa... Maiyasa ta mishi mummunar zato...? mutumin da tun farkon had’uwarsu bai mata komai ba sai d’inbin alkhairi..? Anya zata iya yafewa kanta abinda ta aikata garesa..? Tabbas zata rayu da guiltiness ne tsawon rayuwarta..! Ta koma jikin gado ta kwanta wasu hawayen masu tsananin d’umi suna kuma gangaro mata...
Ta mik’e a hankali ta isa jikin jakan kayanta ta ciro zanen ginin gidan sarautar nan da mahaukaciyar nan ta bata, tai K’uri ma zanen tana kallo... Toh wacece mahaukaciyar nan da har sunanta ta kira alamun ta santa, sannan Maiyasa ta bata wannan Taswiran...? Tabbas tanada unfinished job a wannan masarauta, duk yanda akai mahaukaciyar nan tanada dalilinta na mallaka mata wannan Taswiran... Toh amma meye dalilin nata...? Babban tambayar ma a nan shin wacece wannan mahaukaciyar..? Ta kuma lumshe idanunta a hankali had’ida fuzar da fuci mai d’umin gaske... So many reasons for her to go back to that Kingdom... K’uri taima zanen tana kuma karamtarsa Dukda cewa ba fahimtar wani abu tai gameda zanen ba....
**
MASARAUTA
Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Yazeed dake ci gaba da jinjina mata Kai alamun tabbatarwa “Uncle what exactly do you mean...? Uncle ban fahimceka ba..! Mai kake nufi...?!”
Yazeed ya kamo kafad’un Zahra ya zaunarta saman kujera ya tsaya sosai gabanta yace “Zahra gaskiyar kenan... Mahaifiyarki ba itace ta haifeki ba... Ni nan da kike gani naji tattaunawarsu da Yaya na Mahmood before they left for Spain....!”
_Flash Back_
Yazeed yaci gaba da fad’in “Cikin dare naga shigowar motarsa cikin Masarautar nan, nabi bayansa a hankali dan na kula da yanayinsa kaman akwai abinda yake b’oyewa... Aikuwa to my surprise sai gani nai ya fito da jaririya lullub’e cikin zani ya shige cikin sauri alamun baiso wani ya gansa... Nabi bayansa har zuwa sashensa ba tareda yayi noticing d’ina ba... Aliya dake zaune parlor tana jira dawowarsa, tana jin an tab’a k’ofa ta dubi time k’arfe biyu da rabi na tsakar dare... Share hawayen da suka gangaro mata tai ta mik’e tana jiran shigowarsa... Yana shigowa ta daskare tana duban abin mamakin da Yarima Mahmood ya shigo mata dashi...
“Yarima... Mai nake gani hannunka..? Ina ka fito da jariri cikin daren nan....?!”
Aliya tace cikin rashin fahimta...
K’arasowa yai ya mik’a mata yana furta “Karb’eta ki ganta, ba jariri bane, jaririya ce... And I named her after my grandmother, Maman mai Martaba.. Na sanya mata sunan Fatima Zahra...!”
Yai maganar yana mai duban jaririyar kyakkyawan murmushi saman fuskarsa...
Kukan da Aliya ke dannewa yaci k’arfinta “Yarima... A ina ka samu jaririya, wacece mahaifiyarta..?!”
Ya d’ago yana duban Aliya “She’s my daughter... And you’re her mother... D’iyarki ce Aliya, inaso ki rik’eta matsayin d’iyarki kuma har abada kada ki tab’a ce mata ba kece kika haifeta ba...!”
“Yarima dan Allah ka sanar dani ina ka samo yarinyar nan...!!”
Cikin d’aga murya yaceda Aliya “I told you she’s my daughter... ‘Yata ce ita d’in ‘yata ce, banida lokacin maki duk wani bayani... We’re leaving to Spain in a couple of days... Bana so kowa yasan da jaririyar nan cikin gidan nan... Not even Jakadiya... Bazasu San da labarinta ba har sai mun kuma dawowa k’asar nan wani lokaci... A lokacin zamuyi introducing d’inta matsayin d’iyarmu da muka haifa can Spain... Kin fahimta..?!”
Aliya na hawaye Ta amshi jaririyar tana kallo, wane ikon Allah kallo d’aya taima jaririyar taji shauk’i na k’aunarta, kaman sunada connection haka taji koda shike Mahmood yace d’iyarsa ce k’ila sabida soyayyar da take masa yasa taji take itama son yarinyar ya shigeta...
Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Yarima Mahmood lokaci guda take furta “Nai maka alk’awari zan rik’eta tamkar ni ce na haifeta, bazata tab’a sanin ba nice mahaifiyarta ba... Ta zamto tawa kaman yanda kake nawa, Zahra d’iyarmu ce ni da kai Yarima...!!” Ta k’arashe tana mai rungumar jaririyar hawaye na gangaro mata...
Yarima Mahmood ya k’arasa ya rungumesu gaba d’aya yana mai furta “Kud’in ahalina ne... Ahalin da zamu rayu a Spain, cikin rayuwa mai ‘yanci ba tareda an tak’uramu da maganar bin dokoki na gidan sarauta ba.. Zamu rayu kaman yanda sauran mutane suke rayuwa babu tak’uri da nauyin bin dokoki irin na gidan sarauta... I promise to make you both happy... In sha Allah.. You two are my world..!” Ya k’arashe yana mai kuma matsesu cikin k’irjinsa....”
Yazeed yana kaiwa aya ya kuma juyowa yana duban Zahra da tuni hawaye sun wanke mata fuska.... Ya k’araso gabanta ya duk’a yace “Zahra d’ago ki kalleni... Na aje wannan abu cikin zuciyata tsawon shekarun nan... But I know ko ba dad’e ko ba jima watarana zaki sani... As they say no secret remains hidden forever.... Mahmood ya b’oye miki haka ne dan watak’ila watarana zaki iya zama magajiyarsa... Amma kuma kinsan ko a shari’a d’an da aka haifa bata hanyar aure ba baida gadon Mahaifinsa... Mahmood yaji tsoron rasa Magaji a Masarautar nan shiyasa ya b’oye miki sabida Ke kad’ai ce k’wall magajiyarsa.... Zahra yau kinsan abinda mahaifinki ya jima yana b’oye miki tsawon rayuwarsa... Yanzu abinda ya rage miki shine kije ki tambayesa wacece mahaifiyarki... Da wacece yaci amanar Aliya har ya haifeki ta k’azamar hanya..!!” Ya k’arashe cikin karaji....
Mik’ewa Zahra tai tana kuka sosai take furta “So wannan shine dalilin.... Wannan shine abinda ya jima yana b’oye min... Paa ka cuceni, kazalunceni... Ka lalata min rayuwa... Na tsaneka na tsaneka...!!” Ta k’arashe cikin fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya...
Yazeed yai K’uri yana duban yanda Yarinyar Ke kuka tana furta Ta tsani Mahmood... Muguwar murmushin nan nasa saman fuskarsa yake ayyanawa cikin zuciyarsa “That’s it Mahmood... K’arahenka yazo... Na tabbata zaman Masarautar nan zai gagareka... I’m getting rid of you at last.. Yarima Mahmood..!!” Ya k’arashe yana mai kuma gyara tsayuwarsa zuciyarsa nai masa wani irin sanyi....
**
Tafiya kurum take tana had’a hanya bataji bataji bata gani... Raheema dake tafe zata nufi sashen Yazeed wajen k’awarta Zuhra nan ta hangi Zahra ta nufi sashen mahaifinta tana kuka sosai... Lokaci guda Raheema ta fasa shigewa b’angaren Zuhra tabi bayan Zhara cikin sauri....
Yana tsaye tareda sabon Hadiminsa Barde yana basa umarni kan wasu abubuwa Zahra ta shigo kaman wacce aka jefota... Duban Barde yai ya basa umarnin tafiya kana ya maidoda hankalinsa ga Zahra wacce Ke tsananin huci...
“Princess meke faruwa... Ya na ganki haka..?!”
“Paa tell me the truth... Who’s my real mother..?!!” Tai maganar cikin tsananin dakewar murya...
Zuciyarsa ta yanke lokaci guda, ya kuma duban Zhara da mamaki kana yace “Zahra lafiyarki... Where did you get that idea from... Tell me ina kika samo wannan gurb’attacciyar tunani...?!” Yai maganar cikin tsawa
Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tace “Paa please na rok’eka, babu wani nok’e nok’e it’s over, na riga nasan komai, nasan Maa ba ita ta haifeni ba... I’m your daughter with another woman right..? So tell me wacece mahaifiyata...!!”
“Get out Zahra... Fita nace kafin ranmu gaba d’aya ya b’aci...!!”