Sashe 17
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba Wambai ya kamo hannun Mahmood suka zauna saman wata itaciya... Saida yai gyaran murya kana ya soma fad’in “K’warai kuwa ni ne gaba da mahaifinka a haife, amma a b’angaren cancancanta ya fini, shi yayi karatu mai zurfi boko da islama ni kuwa banyi boko ba, kuma sanin kanka ne a halain da muke ciki yanzu karatu na zamani na taka muhimmiyar rawa cikin rayuwarmu gaba d’aya, k’anina ya had’a komai da ya cancanta ya rik’i Karagar Masarautar nan, yanzu kuma da babu shi kaine magajinsa... Sannan Ina wajen sanda Allah yaiwa mahaifinku kuma d’an uwana cikawa.... Mahmood idan baka amshi sarautar nan ba kana kallo sarautar zata fice daga k’ofarmu, kana gani dai Talba da ‘yanuwansa sun k’wallafi ransu kan wannan muk’ami... Kuma abinda baka sani ba shine, Ina mai tabbatar maka mahaifinka kashesa akai dik akan wannan Mulki... So kake burinsu ya cika su amshe mulki daga hannun ahalin AbdulJabbar... Na tabbata bazakaso haka ba....!” Ya k’arashe yana dafe da hannayen Mahmood idanunsa k’unshe da damuwa...
Mahmood ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Wambai kana yace “Kashe mahaifina akayi akan neman mulki...? Su waye suka kashe shi...?!”
Wambai ya gyara zamansa kana yaci gaba da fad’in “Mahmood akwai sirrika da dama da suke lullub’e cikin bak’in duhu a Masarautar nan... Ka jima baka Masarautar nan, akwai abubuwa da dama da suka faru...”
Yarima Mahmood ya katsesa da fad’in “Shin mai ka sani gameda mutuwar mahaifina..? Shin mutuwar mahaifina nada alak’a da mutuwar matata..? Wad’annan amsoshin na dawo nema Masarautar nan amma ba mulki ba...”
Baba Wambai Yai murmushin cin nasara kana yace “Alhamdulillahi yanzu ka dawo hanya... Idan har kana son samun amsoshinka sai kanada k’arfin mulki a hannunka, idan ya kasance kaine wanda Allah ya d’aura masa nauyin gudanar da al’amaran cikin Masarautar nan toh fah ina mai tabbatar maka zaka sami amsoshinka cikin sauk’i... Amma muddin kace bincike zakai a gida irinta mulki da sarauta ba tareda kanada wadataccen ilimi gameda al’amran dake aukuwa cikin gidan ba to zaka b’ata ne a hanya ko kuma a b’ataddakai, Mahmood a gida irinta sarauta an b’atar da mutane da dama wanda har yau babu d’uriyarsu....Mahamuda, Kai tinani akan abinda muka tattauna, Ina mai tabbatar maka hardai Ina d’aya daga cikin masu nad’a sarki a wannan masarauta bazan tab’a saka hannu a zab’i wani matsayin sarki ba kai ba..!”
Sauk’e ajiyan zuciya Yarima Mahmood yai kana ya mik’e tsaye lokaci guda... Ya d’an kaikaito yana duban Baba Wambai kana ya jinjina kai a hankali yace “Shikenan Baba... Zanyi tunani, na gode K’warai....!”
Wambai ya jinjina kai kana yace “Allah shi maka Albarka...!”
Yana k’ok’arin mik’ewa abinka da jikin tsufa Mahmood yai saurin tallafa masa ya mik’ar dashi tsaye...
Daga yanda Muhibbah ke lab’e ta gama sauraren tattaunawarsu tana kallon yanda Yarima Mahmood Ke rik’eda wannan Dattijo suna tafe, Mai yasa yake nunawa kaman wani shid’in mutumin arziki ne... Maiyasa yake nuna tausayi da jin k’ai cikin Al’umma bayan tasan ba haka yake ba.. Mugu ne azzalumi ne... Wanda sukai tarayya shida ‘yanuwansa wajen ruguza rayuwarta data ahalinta.... Take ta kuma jin tsanar Mahmood dana ‘yan uwansa da uwarsu kanta na kuma mamaye illahirin ruhinta, abubuwan da Ta gama ji bazaisa ta janye k’udirinta ba, tayi imani sune azzaluman cikin Masarautar ba wasu daban ba, they cannot be victims, Ta tabba sune azzaluman... Tasa baya hannu Ta goge hawayen da suka zubo mata kana ta fito cikin sand’a, lokacin a idda ruwa saiko d’an yayyafi kad’an kad’an...
Tana isowa d’aki kwab’e jik’akk’en kayan jikinta tai kana Ta fad’a bathroom had’ida sakar ma kanta shower, ta rintse idanunta sanda take hango Mahmood cikin k’wayar idanunta yana taimakawa Dattijon nan yawa wani mutumin arziki... Kuma rintse idanunta tai da k’arfin gaske ganin wani b’angare na zuciyarta na neman amincewa tabbas Mahmood mutumin kirki ne... Sauri sauri ta gama wankan nata ta d’auro alwala dan already magrib ya gabato... Tana fitowa ta shirya tsaf cikin wani cotton material sea green d’inkin doguwar riga da yai matuk’ar amsar jikinta... Ida shirinta da kad’an wayar Mummy ya shigo mata ta d’aga cikeda kewan gida....
Bayan sun gaisa Mummy Ke tambayarta karatu... Jiki a sanyaye Muhibbah ta amsa mata dan gani take kaman bata kyautawa Mummy ba b’oye mata babban al’amari iri wannan da tai... Har suka ida wayar jikinta a matuk’ar sanyaye yake, bugu da k’ari tinda taji tattaunawar Mahmood da Baba Wambai ta kuma jin rauni sosai daga wani b’angare na zuciyarta wanda bata tab’a jin irin hakan ba tun sanda ta sanyawa ranta k’udirin d’aukan fansa daga wajen wad’anda suka zalunceta....
Tai lamo cikin kujera tana mai lumshe manyan idanunta a hankali... Kiraye kirayen sallan magrib da aka soma ya sanyata mik’ewa dan gudanar da nata sallan... Bayan ta ida ta d’auko alk’ur’ani tana karantawa, take ta kuma jin wani irin rauni na ratsa illahirin b’argo da tsokanta, taji wasu irin hawaye suna k’ok’arin ciko idanunta... Tabbas Alk’ur’ani maganin dik wani gyambo ko k’ulli ne dake a cikin zuciya, kuka sosai Muhibbah keyi ba tareda ta iya ci gaba da karatun ba...
Wani irin rauni takeji can k’asar zuciyarta, tai lamo saman abin sallar had’ida lumshe idanunta hawaye masu tsananin d’umi suna kuma gangaro mata, Ta tina sanda ya tambayeta da muryarsa mai cikeda k’warjini had’ida dad’in saurare murmushi saman kyakkyawan fuskarsa
_”Kina son kiga wasan dawakin ne...?”_
Ta jinjina masa kai a hankali kana yace
_Ya sunanki_
_Saudatu_ Ta fad’i tana wage baki cikeda jin dad’i tana kuma gustiran apple d’in da ya bata...
Ya murmusa a hankali kana yace
_Zo na d’auraki saman dokin_
Ta tina sanda sauran ‘yan uwan nasa keta dariya suna nunata da yatsa...
Wannan tunani da Muhibbah keyi ya sanyata saurin bud’e idanunta zuciyarta na mata tsananin zogi, a fili Ta furta “Mayaudari ne, yaudarar mutane yake da kyawawan d’abi’unsa, dashi yai amfani suka cimma burinsu kan k’aramar yarinyar da bataji ba bata gani ba...
Take taji wani b’angare na zuciyarta na raya mata, karki janye k’udirinki, kar Ki d’agawa d’aya daga cikinsu k’afa.. Ruin them all, expose them and take them down.... Ta k’arashe tana mai goge ragowar hawayen da suka zubo mata, sallaman Umaima ya sanyata saurin mik’ewa had’ida saita kanta kaman babu abinda Ke wakana...
“Ke Wai baki gajjiya da zaman d’aki...Kinga taso mu tafi b’angaren Giwa d’iyanin muci dinner a cen....” Umaima ta fad’i daga nan yanda take tsaye...
Saida ta d’an rausayar da idanunta kana tace “Yo naga dai gidan sarauta ai zaman d’aki da kulle ya gada ko ba haka ba... Kinga dama ke nake jira muje na duba jikin Zahra, tana raina tin d’azu...”
Umaima ta d’an girgiza kai kurum tana mai janyo hannunta tana fad’in “Iyanin Ki amsa kiran Ya Mahmood..!”
Saida k’irjinta ya buga jin tace ta amsa kiran Mahmood, harga Allah ta mance Wai yana kiranta... Banda guntun gulma mai zai mata, yaji da abubuwan da suke gabansa, tabbas da ace yasan wacece ita da kuma k’udirin da ya kawota wannan masarauta ko mai irin sunananta bazaiso ji ba balle ya buk’aci ganinta...
Wani tapkeken parlor suka soma shiga, babu kowa cikinsa sai manya manyan standing ac daketa faman aikinsu suna huro ni’imtaccen sanyi... Hotuna ne a jere a parlorn sahu sahu na ahalin Sarki AbdulJabbar mai rasuwa....
Muhibbah tai k’uriwa hoton da yake daga center... Yaran Sarkin ne su duka hud’u cikin hoton, dukansu cikin shiga irinta mulki da sarauta, k’asaitaccen murmushi irinta ‘ya’yan sarauta kwance saman fuskokinsu, idanunta suka waiga gefe kad’an nan ta hango wani hoton, su duka hud’u amma wannan suna yarane masu k’ananun shekaru wanda tsaf ta gane fuskokinsu domin kaw sanin da tai masu kenan....Tai K’uri tana duban hoton zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri....Ji take tamkar ta rarumi koma minene ta tarwatsa hoton dashi, so take ta finciko hoton daga ma’ajiyinsa ta zane fuskokinsu tai masu lamba mai muni wanda suma har abada bazai shafe daga tarihin rayuwarsu ba kaman yanda sukaima nata rayuwarta lamba...Take ta dunk’ule hannayenta duka biyu tana mai ci gaba da sakin huci a hankali....
Sam bata ko kula da Umaima da ta fice ta wani k’ofar tana amsa kira a waya ba...
Waige waige ta soma sanda ta tabbata babu kowa cikin parlorn sai ita kad’ai saiko na’urorin nasara.... Nan ta hangi matakalan haurawa bene daga gefe, ta soma takawa a hankali ta nufi benen dikda tsananin bugu da k’irjinta keyi, ita kanta ta sani abinda takeyi abune mai matuk’ar had’arin gaske....
Abinka da gini irinta sarauta nan ta hangi dogon corridor da yake open, ga k’ofofi birjit iyaka ganinka.... Ta rasa ta wane k’ofar zata soma bi, lumshe idanunta tai tana ambato Allah da neman taimakonsa, Ta bud’e idanunta a hankali tana jin k’warin gwiwa na zuwa mata... Cen ta hangi wani k’ofa da yake daga center, zuciyarta tafi amintar da tabi wannan k’ofa... A hankali cikin sand’a had’ida d’an sauri ta nufi k’ofan, ta d’an tura a hankali tana lek’awa, shima d’in wani hamshak’in parlor ne maiji da tsari... Tabbas ana baza mulki a wannan gida, Ta fad’i haka cikin zuciyarta.... Cikin sand’a ta kutsa Kai cikin parlorn, saidai shigarta Keda wuya Ta soma sauraron wasu muryoyi.... Tai saurin k’arasawa yanda take sauraron maganan, tabbas muryar Giwa ce dan bazata tab’a mance wannan azzalumin murya a dodon kunnenta ba, tana iya sauraro muryan d’aya daga cikin yaranta suna tattaunawa saidai bazatace ga wanene suke maganan ba cikin yaran nata dan gaba d’aya yaran murya kala guda Ke garesu, na Mahmood ne kad’ai ta d’an banbanta dan dik ya fisu gwab’in murya mai cikeda k’warjini... Hakan ya tabbatar mata da d’aya daga Cikin k’annensa Giwa ke tattaunawa....
Bataji gaba d’aya abinda suke tattaunawa akai ba amma tabbas taji Giwa na basa umarnin aiwatar da wani abu.... Jin kaman ana k’ok’arin tab’a k’ofa ya sanyata saurin sad’ad’owa ta fito k’irjinta na tsananin bugu.... Sauri sauri ta nufo dogon open corridor d’in nan tana tafe tana waigawa baya bata ankara ba saiji tai ta bige mutum ta fad’o cikin jikinsa....
SameenaAleeyou 📚
[6/5, 7:51 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*013*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*