← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 162

Sashe 74

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Huci kurum Raheema take tana mai furta “K’arya kake Mahmood bazai tab’a min haka ba, ni yake so... Hasalima shi ba mai kula mata bane baida wannan lokaci.....!” Batakai aya ba taji Yazeed ya damk’o wuyarta da k’arfinda Allah ya hore masa, cikin huci yake furta “Ni kike kira mak’aryaci... Sai na karya wuya ki a wajen nan naga gatanki...!!”

Raheema sai firfito da idanu waje take tana k’ok’arin janye hannun Yazeed daga wuyarta, tana rok’onsa Allah Annabi ya sakar mata wuya kada ya kasheta cikin muryarta da bai fita sosai... Saida tai Laushi yayi jifa da ita gefe.. Ta fad’i k’asa tana tari da k’yar a hankali dan kar a jiyota, tanayi tana sosa wuyarta...
Tsuka ya buga kana ya k’araso yanda take ya shiga janyota kaman kayan wanki yayi jifa da ita daga cikin d’akin kana ya maida k’ofa ya rufe... A d’ari Raheema ta mik’e ta nufi downstairs cikin sauri dan kar Zuhra ta fito ta ganta.. Tana tafe tana sosa wuyarta da har lokacin zogi yake mata....

**

BAUCHI

Suna zaune itada Mummy a parlor, tv na aiki lokaci guda Mummy na sorting wasu takardu dake gabanta yai sallama ya shigo da alama daga asibiti yake....
Mummy tace “Likita an dawo..?” Tai maganar tana aje wasu takardun gefe had’ida zare Farin gilashi na k’arin k’arfin gani daga idanunta....
Ansar ya jinjina kai yace “Eh Mummy mun sameku lafiya...?”

Ta amsa masa kana ya gaisar da mahaifiyar tasa yana mai satan duban b’angaren da Muhibbah take ko zatai masa magana amma shiru batace komai ba, Mummy na hankalce dasu dan tinda rana da Iya Larai ta kirata ta sanar da ita dawowar Muhibbah da kuma abinda ta gani babu yanda batai ba Muhibbar ta sanar da ita abinda ke faruwa amma sai ce mata tai babu komai lecture free week suke shisa tazo gida..

Muhibbah ta mik’e tana furta “Mummy zan duba Iya Larai a kitchen...”

Dakatar da ita Mommy tai da fad’in “Dawo nan Muhibbah, Zo ki zauna...!”

Babu musu da ta dawo mazauninta ta zauna fuskarta babu walwala, har lokacin Ansar bai daina satan kallanta ba...

SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*

*48*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Dubansu duka biyu Mommy tai kana tai gyaran murya kad’an tace “Ina saurarenku.. Can anyone explain what’s going on here..? And don’t even think of lying to me Dan Larai ta kirani ta sanar dani komai..!”

Muhibbah tai saurin d’ago idanunta masu rauni tana duban Mommy da sam babu walwala tattareda ita...
Jin sunyi shiru su duka biyun yasa Mommy kuma fad’in “What’s wrong with the both of you... Kai Ansar kaine Babba Wai meke faruwa ne..? Meke faruwa tsakaninku..?!”

Ansar ya fuzar da fuci kad’an yace “Mommy is nothing serious, Kinsan Iya Larai da exaggerating abu...!”

Galala take dubansa kana tace “I see, ni zaka rainawa hankali... Tunda nake daku ban tab’a ganin ka dawo aiki Muhibbah batai maka sannu da zuwa ba duk fad’a da fushin da zakuyi da juna, nasan ba abu ne mai sauk’i zaisa shigowarka ya sanyata ficewa daga parlorn nan ba... Amma idan kunce haka, tsakaninku ne, kuyi sulhu da kanku banso tun yanzu na dinga shiga fad’arku..” Ta dubi Muhibbah da har lokacin jikinta a sanyaye yake tace “Tashi kije abinki kinji d’iyata..”
Muhibbah ta jinjina kai a hankali tace “Toh Mommy, kana Ta mik’e Ta wuce jiki a sanyaye Ansar na satan kallanta...

Tana shigewa Mommy ta maidoda hankalinta sosaiga Ansar tai gyaran murya ta kirawo sunansa...
Ya amsa cikin risinawa, Mommy taci gaba da fad’in
“Ni ba ma wannan ba d’azu Baffanka Yawale yaje har office ya sameni da batun saka maku rana, nace masa sai nayi shawari da duka yarana biyu naji yaushe suke so a saka bikinsu...!” Tai maganar tana mai maida glasses d’inta had’ida janyo wasu takardun...

Cikin wane irin bugawan zuciya Muhibbah dake k’ok’arin shigewa corridor taja ta tsaya d’agowa tana duban Mommy daga can yanda take zaune cikin parlor, ta kuma dubi Ansar da annuri tuni ya cika fuskarsa, lokaci guda yake furta “Mommy Baffah Yawale da kansa yake fad’in a saka mana da Muhibbah, kenan yanzu ya amince na aureta..?!”

Sauk’e ajiyan zuciya tai kad’an tace “Ya amince amma Yana nan akan bakansa na aura maka d’iyarsa Hameeda, idan ka amince da sharad’insa sai a aura maka su biyun rana guda...!”

Cikin k’unan rai Ansar ke furta “Wai Mommy Baffah Yawale wane irin mutum ne shi, Wai ana aure dole ne... Nace bana son wannan yarinyar, bana sonta ko ana so dole ne... Mommy ni fah Muhibbah kawai nake so, kuma ita kad’ai ta isheni... In fact banida ra’ayin Auren mata biyu sabida nasan duk macen dana had’ata da Hibbah bazan tab’a mata adalci ba... Haka kawai bazan kai kaina wuta ba Mommy... Nidai ki fad’a masa bana son d’iyarsa...!”

“Kai rufe min baki, bansan rashin kunya... Da kake gaya min sak’o kake bani naje na fad’a masa... Kana gani tun daga tasowarka kawo girmanka irin gwagwarmayar da nayi da mutanen nan akanka... Babu yanda basuyi ba sai Sun karb’eka daga hannuna tun bayan rasuwar mahaifinka amma na jajirce na hanasu nace babu mai rabani da d’ah na dan na tabbata cikinsu babu wanda zai baka future mai kyau... Ansar babu irin wulak’anci da ban gani ba daga wajen dangin mahaifinka ganin sun karb’eka daga hannuna amma na shanye komai, naita gwagwarmayar rainonka ganin ka sami ingantacciyar rayuwa... Babu irin sunayen da basu dangantaka dashi ba sunce ka zama D’an mace, sunce na maisheka had’e, sunce K’abila ta sace d’an Ard’o...Har cewa sukai zan maidaka Arne cikin ‘yan uwana Arna, wanene wanene amma duk na shanye nace naji na gani ni ce nan zan raineka da dad’i da babu dad’i... Toh amma yau dashike ka girma ka zama mutum gashi suna son had’a iri da had’e... Toh amma shi mutum ka tura masa aniyarsa... Hamida da mahaifiyarta basuda matsala, yarinyar tanada hankali da hali irin na mahaifiyarta... Dan ka aureta ni inaga ba wani matsala bane kuma inada tabbacin baza’a sami matsala daga Muhibbah ba...”

Ansar dake k’ok’arin danne b’acin ransa yace “Mommy a gaban idonki mutumin nan yace bazai barni na auri Muhibbah ba sabida batada asali... Shine yanzu zaice ya amince na aureta dan kawai na auri d’iyarsa... Toh gaskiya Mommy ni bazan iya auren d’iyarsa ba... Maganan gaskiya kenan, kawai ni za’a tak’urani ne... I’m sorry Mommy but gaskiya I can’t...!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye zuciyarsa naci gaba da tafarfasa...

Kallo mahaifiyar tasa Ta bisa dashi har ya b’acewa ganinta, ta girgiza kanta a hankali tana mai ci gaba da abinda take...
Muhibbah kuwa d’aki ta shige ta fad’a saman gado tana kukan da ita kanta bata San dalili ba... Kodashike dalili da yawa zai iya zama sanadin kukan nata... Bayan gwagwarmayar da suka sha da dangin mahaifin Ansar na ganin sun koreta ma daga gidan gaba d’aya wanda badon Allah yasa Mommy mace ce jajirtacciya wacce ke tsaye kan k’afafunta da sun jima da yin sanadin barinta gidan musamman da suka fahimci soyayya da shak’uwar dake tsakaninta da Ansar... Bayan duka wannan yanzu at last wanda yafi kowa k’ullatanta da kyaranta ya amince Ansar ya aureta amma kuma wai da sharad’in zai auri d’iyarsa, rana guda za’a d’aura masu aure...Bayan wannan kuma gacan halinda ta baro Zahra ciki a masarauta wanda duk abinda yaje yazo tsakanin Yarima Mahmood da d’iyarsa itace sila... Har abada bazata tab’a samun kwanciyar hankali ba sanin cewa ta b’ata tsakanin d’iya da mahaifi... Ita duk bama wannan ba yau da taji da kunnuwarta ana maganan saka masu rana da Ansar ji tai kwata kwata bata muradin auren, tana ki can k’asan zuciyarta bazata iya rayuwa dashi matsayin miji ba...Shin yaya zatayi... Menene abinyi..?! Ta lumshe idanunta wasu hawayen suka kuma gangaro mata, hijabi Ta janyo ta zira ta fice ta k’ofan baya ana kiraye kirayen sallan Isha ta nufi layin bayansu gidansu k’awarta Meenatu...

A parlor ta tadda Meenatu da k’annenta suna kallon shirin film a zeeworld yayyensu maza na shirin fita sallah suna masu fad’an suma su tashi su shige suyi sallah su bar kallon nan... Muhibbah ta gaisa dasu Yaya Huzaifa kana Ta nufo cikin parlorn...

Meenatu na ganinta ta tafi da gudu tanai mata oyoyo had’ida tambayarta sauk’an yaushe... Tai aya tana duban idanun Muhibbar dake d’aukeda alamun kuka... Janyo hannunta tai suka nufi d’aki tana tambayarta lafiya meke faruwa...

Muhibbah ta kuma saka hannu ta goge hawayen da suka ziraro mata “Meenah komai ma ya faru...!”

Meenah Ta gyara zama tace “Ban gane ba, Kina nufin a sch d’in..A can Jos d’in... Kinga kin ma tuna min jiya a Islamiya Malam Ayuba Ke tambaya kwana biyu baya ganinki nace masa ai kin tafi makaranta Jos zaki k’ara karatu zakiyi Bsc Nursing... Toh.. Wai meke faruwa ne Hibbah..? Ni kinsa duk jikina yayi sanyi..!” Ta k’arashe cikeda kulawa...

Ta Sauk’e ajiyan zuciya a hankali tace “Meenah ba makaranta na tafi Jos ba...!”

Meenatu ta dubeta da tsananin mamaki “Ba makaranta kika tafi ba... Toh ina kika tafi....?!”

Cikin muryar kuka take furta “I went there for a mission Meenah... And everything now is a complete messed up...!”

Jiki a sanyaye Meenatu ta zauna gefenta “Hibbah you’re scaring me...Wane irin mission kuma Ni Saamina....?!”

Cikin zuban hawaye take furta “Zan fad’a miki komai k’awata... Zan fad’a miki harda labarin da baki sani ba game dani... But for now dan Allah so nake ki sanar dani ya kake gane kana son mutum...?!”

Meenatu Ta rausayar da idanu kad’an tace “Toh yau kuma Keda kanki kike tambayar haka ta Yaya Dr... Bayan ked’in tuni kin tsaida gwani...?!”

Muhibbah ta lumshe idanunta a hankali had’ida fuzar da fuci tace “Haka nayi zato a baya... Bayan abubuwan da suka faru dani a yau, inajin shakkun abubuwan da naji a baya... Please tell me Wai ma mecece ita soyayyar nan..?”
Chapter 74 · 0% Book details