← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 162

Sashe 10

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ke..!!” Ya daka mata uban tsawa, ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa, lokaci guda take furta “This is not good Yarima... Wllhi ni dama nayi zaton Yarima Mahmood bazai dawo bane nai zaton bazan tab’a samunsa ba shisa na biye maka... But wllhi na tuba daga wannan mummunar sab’on ni da aure nake son Mahmood, family nake so nidashi muyi building a sabon kingdom d’inmu...Pl....!”
Sauk’an marin da taji ne babu zato ya sanyata had’iye sauran kalaman nata...
Ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana duban Yazeed dake tsananin huci lokaci guda yake furta “Prince Yazeed AbdulJabbar can never be second option!!!... Ke kinyi kad’an kice a rashin wani kike taredani... And let me remind you this princess, idan kina tunanin jin kunyan idon duniya ne Toh ki sani a wannan duniyar babu wani abin jin kunya... Cos life itself is full of disappointment... Get out of my sight..!” Ya k’arashe yana nuna mata k’ofa...

Da tsananin tsoro take dubansa kana tace “Yazeed a daren nan zan fita, ka kuwaga time...?”

“I’ll be saying it twice if I said it again... Kuma kinsan bana maimaita magana....!”
Jiki a matuk’ar sanyaye ta fice dan tasan kad’an da aikinsa yasa ai waje da ita.... Haka ta fice cikin daren nan k’afa dik ya d’auke, domin a nan d’aya daga cikin guest house d’in marigayi Mahaifinsa suke akasarin had’uwarsu... Tana fitowa ta shige cikin motarta k’irar Mercedes Ta nufi Fada, batabi ta babban gate d’in Fada ba dan tasan komai ka iya faruwa dan haka ta k’ofar bayi tabi ta shigo cikin Masarautar.. Motarta ma a nan sashen bayin Ta barota, Haka nan take tafe tana waige waige tamkar mai tsoron kar wani ganta...
Muhibbah da ta kasa bacci dan idan ta tafi bak’on waje hakan ne Ke faruwa da ita a ranakun farko dan haka harabar masauk’inta ta fito tai zamanta tana bin taurari da suka haska sararin samaniya da kallo, lokaci guda tana tinanin Fu’ad da halinda ta gansa ciki..

Nan ta hango giftawar mutum, ta d’an mik’e kad’an tana kuma lek’awa tabbas mace ce kuma cikin shiga irinta alfarma nan ta hangeta ta shige hanyar da zai sadaka da wani sashen.... Jim kad’an sai hango hamshak’iyar jeep k’irar Ford tai ta shigo cikin Masarautar, ta nufi wani sashen gefen sashen dakeda tabbacin na Fu’ad ne....

Toh su waye wad’annan masu dawowa Fada cikin dare....? Tambayar da ya tsaya mata a rai....

SameenaAleeyou📚
[5/27, 10:42 AM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑*

*008*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tinda ya kwanta yake wasu irin mafarkai marassa kyau, da fari mafarkin matarsa Aliya da mahaifinsa yai, bayan yayi addu’a ya sake komawa wani mafarkin ya kuma tadashi... Wannan karon akan K’annensa guda Uku ne, abinda ya gani cikin mafarkin sosai ya tada masa hankali... Tsaye ya hangi Yazeed da Fu’ad rik’e da takubba a hannayensu ko wanne takwabin dake hannunsa na d’igar da jini wanda yake jajazir.... Sunayensu ya ambata cikeda tashin hankali ganin abindake rik’e hannayensu, cikin kid’ima ya nufi yanda suke a tsaye suna maida huci suna nunasa da takubban dake hannayensu lokaci guda suka fashe da dariya basu daina nunasa da takubban ba... Mamakin dariyarsu yake bayan abinda ya gani rik’e hannayensu, k’arasowar da zai kusansu sai hango wani d’aki yai a bud’e cikin jerin wasu d’akuna... Basu daina dariyar da suke ba har Mahmood ya nufi cikin d’akin mai tsananin duhuwa.... Saidai yana shiga d’akin ya hango mahaifiyarsu zaune saman gadon sarautar masarautarsu... K’irjinsa yaci gaba da bugawa sanda ya hango d’an uwansa da yakeda tabbacin ya fita zakka cikin sauran ‘yan uwan nasa durk’ushe kan wata yarinya sai darza mata wuk’ar yake... Ga jini na kwarara amma da alama bata mutu ba.... Cikin zafin nama ya ambato sunan Jamal da k’arfin gaske, saidai ko gizau Jamal bai ba saima ci gaba da darza mata takwabin da yake... Tsalle Mahmood yai ya finciko Jamal don ceton yarinyar amma mai..? Yana d’agosa saiji yayi an luma masa takwabi a cikin cikinsa... Mahmood ya rik’e cikinsa yanda jini ke malala a k’asa.. Ya d’ago yana duban ‘yan uwansa guda Uku rikeda takubban saidai bazaice ga wanda ya caka masa ba cikinsu, maida dubansaga mahaifiyarsu dake zaune saman Karagar mulkin yai saidai wannan karon matarsa Aliya ya gani ba mahaifiyarsu ba...Hannu yake mik’a mata alamun neman taimako amma inaa batai ko gizau ba tana nan zaune saman Karagar mulkin saima sakin dariyar da take mai firgitarwa... A hankali yake ji numfashinsa na d’aukewa jikinsa na zamewa har saida ya fad’o kan yarinyar da Jamal ya gama yankata da takwabi, su duka biyu jini na malala daga jikkunansu.... A daidai wannan lokaci ne ya farka daga baccin cikeda tsananin tashin hankali... Addu’o’in da sukazo bakinsa kawai yake iya karantawa had’ida jero hasbunallah wa ni’imal wakil... A hankali yake jin natsuwa na sauk’o masa cikin zuciyarsa... Hannu ya mik’a ya kunna side lamp kana ya dubi k’aramar agogo dake gefen bedside ya nuna k’arfe 4:30am, anata kiraye kirayen assalatu... Shafe fuskars yai da duka hannayensa biyu kana ya mik’e ya nufi bathroom ya d’auro alwala, shimfid’a abin sallah yai amma ko tsayuwar sallar saiji yai ya kasa... Ya zauna nan bakin gado abubuwan na kuma zuwa masa... Wannan wane irin mafarki ne mai cikeda rud’ani da kuma tashin hankali.... Mai wannan mafarki yake nufi...? Take yaji wani b’angare na zuciyarsa na raya masa _Akasarin munanan mafarkai Daga shed’an ne ka nemi tsari da kariya daga shedan.._ Ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya yana mai kuma shafe fuskarsa, tabbas ‘yan uwansa bazasu iya kashe ran wani ba koda bawa ne balle nashi.... Ya fuzar da fuci a hankali yana neman tsari daga shaid’an da kuma munanan abubuwan da ya gani a cikin baccinsa... Ya jima zaune wajen har saida ya soma jiyo kiran sallar asubahi... Ya mik’e ya d’auki cazbaha da k’aramar littafin azkar d’insa na hisnul Muslim kana kana ya nufi masallacinsu dake nan cikin Masarautar....
Nan cikin masallacin ya tadda Jamal zaune yana wurdi da alama sallar nafila ya ida yana jiran k’arsowar imam a tada sallar asuba... Yarima Mahmood ya saki murmushi a hankali natsuwa na sauk’o masa, tabbas wannan mafarki nashi daga shed’an ne... Of all people bazai yuwu ma ace Jamal ne zai caka masa wuk’a ba... Nan ya k’arasa had’ida zama gefen Jamal d’in... Suka sakar ma juna murmushi kana Jamal ya mik’a masa hannu alamun masabaha... Zamansa da kad’an kaw Imaam ya shigo suka tada sallah....
Bayan an ida sallah ne suka jera suna fitowa a tare suka nufi b’angaren mahaifiyarsu... Suna tafe Yarima Mahmood ya d’anyi gyaran murya kad’an kana ya dubi Jamal yace “Nikam har yanzu Yazeed na nan da halinsa na k’in zuwa sallah...? Naga tinda na dawo bana ganinsa a jam’i and Fu’ad ya akai yau bai fito sallah ba...?”

Murmusawa kad’an Jamal yai wanda murmushin d’abi’arsa ce kana yace “Babu abinda ya canza da Yazeed Yaya... Fu’ad kuma baijin dad’i ne shisa baka gansa ba...”

Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali suna tafe cikin kamfacecen masarautar nasu da duk yanda suka gifta sai bayi sun risina Sun gaidasu.... A haka suka iso sashen mahaifiyar tasu...
Jakadiya ce Tai masu iso kana suka shiga suka taddata zaune saman abin sallarta da alama itama sallar Ta ida tana gabatar da wurdi...

A jere sukai zama irinta rak’umi saman Darduma dake a saitin mahaifiyar tasu wanda dama dominsu darduman yake aje wajen, dik sanda suka shigo gaisheta a nan suke zama...

Ta ida addu’o’inta suka shafa a tareda yaran nata, murmushi fal fuskarta take dubansu....Tsananin k’aunarsu na ratsa dik wani kafa na jikinta, Mahmood ne ya soma gaidata sannan Jamal... Ta amsa masu cikeda so da k’auna had’ida shi masu albarka... Daga nan ne take sanar dasu jiya Galadima ya sanar da ita cewa Yau d’in da yammaci zasuyi zama kan maganar wanda zai gaji mahaifinsu Sarki AbdulJabbar mai rasuwa...

Sosai suka natsu suna sauraren Mahaifiyar tasu sanda taci gaba da fad’in “Sadauki..!”
Yarima Mahmood ya d’ago yana dubanta, Giwa taci gaba da fad’in “Na riga na zab’eke matsayin wanda ni nakeso ya gaji mahaifinku, toh amma Galadima ya tabbatar min cewa cikin masu neman sarautar nan harda Majidad’i d’an d’an uwan mahaifinku Wambai da kuma biyu daga cikin yaran Marigayi Talba mai rasuwa, sannan da shi kanshi Chiroman gari yana neman Karagar Masarautar garin nan... Dan haka ni a nawa b’angaren na tsaida kai, kuma na tabbata king makers bazasu bani kunya ba, domin kaw daga Galadima har Waziri a b’angaren mu suke, kuma sunyi Na’am cikin masu neman sarautar Masarautar nan babu wanda ya dace ya maye gurbin mahaifinku sai kai Sadauki....” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta, yayinda Jamal yaci gaba da jinjina kai yana furta “Tabbas Maami, Yaya shi kad’ai ya dace ya gaji Abbah... Cikin duka wad’anda kika lissafo, sannan dama ance kyaun d’a ya gaji mahaifinsa... Kuma idan har sarauta ya fice daga gidan nan haka munaji muna gani za’a sallamemu mu bar Fada mu koma cen wani k’auye a nad’amu hakiman k’awye... Yaya you’re the rightful heir to the throne... Kai ka cancanta ka d’ale wannan karaga...!” Ya k’arashe yana duban d’an uwan nasa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa....
K’uri Mahmood yai masu yana dubansu kana ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana mai shafe fsuksrsa da tafukan hannunsa, ta yaya zai sanar dasu ba abinda ya dawo dashi Masarautar nan ba kenan.. Ta yaya zai sanar dasu ba neman mulki bane gabansa, ta yaya zai sanar dasu abinda ya dawo dashi yasha bambam da abinda suke tinanin shi ya dawo dashi.... Muryar Giwa ya sinkayo tana ci gaba da fad’in “Kai nake sauraro d’ah na nasan bazaka bani kunya ba...!”
K’ak’aro gajeren murmushi yai irinta masu mulki kana ya soma fad’in “Allah shi taimaki Giwar Sarki AbdulJabbar, Allah shi taimaki Mai babban d’aki... Allah shi taimaki Gimbiya Turai d’iyaga Sarki Jamaludden na k’asar Benin, La princesa de benin (the Princess of Benin), La reina de jos (the Queen of Jos)... Mi hermosa madre (Kyakkyawan mahaifiyata) Allah yaja zamaninki...!!”

Tinda ya soma mata kirari take dubansa da murmushi saman fuskarta, hannu tasa ta shafi fuskarsa kad’an k’walla tab idanunta... Tana matuk’ar k’aunar Mahmood, akwai wani abinda ya banbanta dashi cikin ‘yan uwansa...
Chapter 10 · 0% Book details