← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 162

Sashe 19

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hakali yake takowa cikin d’akin, cikin takunsa mai cikeda charisma yayinda zuciyar Muhibbah yaci gaba da bugawa da sauri da sauri cikin sakanni... Sai murza sark’ar dake hannunta take ba tareda ta iya koda motsa wuyarta ba balle tai tinanin juyowa....
Tana jin sanda Zahra Ke furta “Aunty Hibbah meet my Paa...!”

Zuciyarta taci gaba da tsinkewa, bugun zuciyarta ya k’aru.. Batasan ta yanda zata soma juyawa tai idanu hud’u da wannan azzalumi ba and act like nothing ever happened.... Tana tsaka da tinanin ne sallaman Umaima ya katsesu....
Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali...

SameenaAleeyou📚
[6/5, 7:51 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*014*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Umaima ta shigo tana mai fad’ad’a murmushinta “Yaya barka da shigowa...” Ta fad’i cikeda risinawa...
Jinjina mata kai yai daidai sanda wayar salulansa ta d’auki ruri, abokinsa Turaki ne mai kiran... Dan haka kai tsaye ya juya ya fice daga d’akin...
Muhibbah ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’ida bud’e lumsassun idanunta... Umaima ta k’araso tana fad’in “Sorry na barki ke kad’ai a parlor Prince F ya rikeni da hira, ashe kin hauro nan...”

Muhibbah ta rausayar da idanu kana tace “Eh mana, kin barni ni kad’ai salon naje na b’ata a wannan k’atoton gidan... Allah yasa ban shige wani wajen ba nai karo da d’akin patient d’ita...”

Umaima da Zahra suka d’anyi tak’aitaccen dariya a tare cikeda jin dad’i kasancewa da juna Umaima na fad’in “Kar ki damu babu wanda zai saceki cikin Masarautar nan...”
Suka kuma darawa a tare

Rahima dake lab’e jikin k’ofa k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi ganin wannan mayyar k’awar Umaimar mai bak’in shishigin tsiya tareda Zahra... Allah ya gani bata k’aunar yarinyar nan.. Bata iya shiga ba sai juyawa da tai zuciyarta na mata zafi...

A b’angaren Yarima Mahmood kaw tinda Turaki ya sanar dashi isowarsa bai kuma dawowa d’akin Zahra ba dan tini ya samu Ubandoma ma na jiransa daga waje, yasan isowar Turakin zai sanar dashi..
Hakan sai yafi wa Muhibbah dan harga Allah batajin tayi shirin fuskantar babba cikin azzulaman ‘ya’yan sarki AbdulJabbar a yau bayan karon da tai da Yazeed da kuma zancen Fu’ad da Umaima da ta sinkaya...
Dik surutun da Umaima da Zahra keyi da alama hankalinta bai taredasu... Tafi bada mahimmanci ga duban k’ofa kaman mai jiran shigowar wani... Cikin zuciyarta take sak’awa, tinda ba Yazeed bane ba kuma Fu’ad bane Giwa Ke tattaunawa da, tabbas da Jamal kenan take tattaunawar, a shi take bada umarnin zartar da wani abu... Mai kenan..? Meye take umartan Jamal yai da wannan kakkausar murya irin haka...? Idan bata b’ata ji ba kaman taji Giwa na cewa kaje ka duba ka gani ko har yanzu na raye... Wannan statement shi take ta nanatawa cikin zuciyarta har lokacinda sukai karo da Yazeed.... Waye Giwa take bada umarnin aje a duba ko Yana nan a raye... Could it be mahaifinta ne...? Kardai Abbanta ne tsawon shekarun nan yana cikin Masarautar nan basu kashe shi ba...? Ya zama dole tabi bayan Jamal taga yanda Giwa ta aikesa...?! Bata ida tinanin ba taji Umaima na dungurinta tana fad’in “Hibbah Wai ina kika tafi munata tambayarki...?”

K’ok’arin saita kanta Muhibbah tai kana tace “Kinsan na baro wayata cen sashen bak’i kuma munyi da Mummy zata kirani toh ko shakka babu nasan tana kan nemata yanzu haka....”

Umaima ta d’an girgiza kai tace “A’a Gaskiya bai kamata ki k’yale Mummy taita kiranki no response ba, zatai tinanin ko wani abin ne ya sameki... Kinsan iyaye da nuna damuwarsu musamman idan sun tura yara makaranta... Ki tashi kije ki d’au wayarki gaskiya...”

Murmusawa Muhibbah tai kana tace “Toh shikenan ga patient d’ina na barta hannunki amana...”
Suka murmusa gaba d’aya kana Muhibbah ta mik’e ta fice Zahra na labartawa Umaima yanda Muhibbah ta bata magani cikin dad’in rai ba tareda taji d’acin maganin ba...

**
Gimbiya Zeenat ce hankice a parlornta na alfarma, bayi guda biyu sai aikin tausan k’afafunta dake bisan manyan pillows na sarauta suke... Shigowar Raheema fuska a tamke yasa Gimbiya Zeenat umartan kuyangin nata da su fice su basu waje... Babu musu kuyangin suka mik’e sukai kaman yanda uwar gijiyar tasu ta umarta...

Raheema ta zauna saman kujera sai cika take....
Aunty Zeenat ta d’ago tanai mata wani irin duba kana tace “Ke kuma fah.. Wannan kumbure kumburen na minene... Ince kina cen kina kula da d’iyar mijinki... Meye kuma zaki shigo kina kumbura fuska..?”

Raheema ta d’an kuma tura baki gaba tana kuma tab’e fuska kana ta dubi ‘yar uwar tata tace “Aunty wata mayya ce ta shigo Masarautar nan take neman shige min hanci da k’udundune.... Wllhi bakiga yanda take rawar k’afa kan ahalin Masarautar nan ba musamman Zahra... Aunty tsoro nake kar wannan shegiyar yarinyar Zahra tasa mahaifinta ya auka wa soyayyar wannan mayyar tinda dama yarinyar bak’ar munafuka ce dan na lura tamkar bata k’aunar alak’ata data mahaifinta....!” Ta k’arashe tana kuma tura baki gaba...

Tsegege Gimbiya Zeenatu ke dubanta kana ta murmusa kad’an cikeda k’asaita sannan taci gaba da fad’in “Dad’ina dake Raheema wauta, Ke yanzu har akwai macen da zata baki tsoro akan Mahmood... Mutumin da matan ma basa gabansa, mutumin da har yanzu mutuwar matarsa bai gama ficewa daga jikinsa ba... Ni wannan wauta naki da yawa take Raheema saikace ba d’iyar Saraki kike ba, sam Bakida jarumta... Har yaushe zaki tsaya wata banza can Ta baki tsoro Yo ni ba don inason cimma burina wajen ganin kin auri Mahmood ba yaushe zan tsaya ina biyayyawa Giwa...Toh wllhi ki bud’e kunnuwarki da kyau ki saurareni... Idanma baki son Mahmood wannan Ke ta shafa iayakacin abinda na sani shine idan za’a kashe rai a Masarautar nan sai kin aure Mahmood dan yanda na zamto ‘yar kallo cikin Masarautar nan auren Mahmood da zakiyi shine zai dawo min da Martaba ta ya kuma d’aga darajata, don na tabbata da zaran Mahmood ya zama Sarki Ke kuma kin zamto matar Sarki Toh fah mulki ta dawo hannunmu sai yanda mukai da Giwa cikin Masarautar nan, da Sarki da Uwarsa dik zasu dawo k’ark’ashin mulkin mu....Tunda ban haifa Sarki ba don haka dole na zamto Sirkar Sarki, dole ta ko wanne hanya nasan yanda zanyi mulkin Masarautar nan Ta dawo gareni... Kuma hanya d’aya kenan tak shine ki auri Mahmood...!” Ta k’arashe tana zaro idanu waje...

Raheema tai shiru tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali, k’aunar Mahmood na kuma fizgarta, dik yanda za’ai bazata tab’a bari wata tazo Ta rusa mata Farin cikin data jima tana k’ok’arin ginawa ba koda kuwa wann shegiyar d’iyar tasa bataso.... Da wann tunanin ta mik’e ta nufi d’aki shiryawa dan zuwa ganin Yarima Mahmood...

**
Turaki ya kuma gyara zama yana mai kurb’an drink d’in dake rik’e hannunsa kana ya nusa kad’an yace “Toh yanzu what are you suggesting your Highness...?”

Yarima Mahmood ya fuzar da fuci a hankali kana yace “I don’t know Turaki... Is getting more complicated... Na rasa ta ina zan b’ullowa al’amarin... Waye zan fara tuhuma..? Ta ina zan fara bincikawa... Sannan waye zan yarda dashi cikin Masarautar nan...?”

Shiru ya d’an gifta tsakani kana Turaki ya d’an gyara zamansa had’ida fitowa daga cikin kujera sosai “A gaskiya your Highness ko ni ban goyi bayan ka amince da kowa cikin Masarautar nan ba... I’m sorry to say not even your brothers...It might sound ridiculous but gaskiyar kenan... Kuma kaman yanda Baba Wambai yace, if you really want to get to the bottom of all this, Toh fa sai ka zamto shugaba a Masarautar nan... Idan har kana tunanin mutuwar Matarka nada nasaba da mutuwar mahaifinka bazaka tab’a ganowa ba har sai ka zamto kaikeda mulkin Masarautar nan....”

Yarima Mahmood yai shiru yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa had’ida fuzar da fuci a hankali... Lokaci guda abubuwa da dama ke ziyartan kwanyarsa... Mafarkin da yai da ‘yan uwansa harma da mahaifiyarsa, Sannan Maiyasa Giwa take so ya auri k’anwar matar mahaifinsa... Maiyasa yake jin can k’asan zuciyarsa bai aminta da wannan had’i da suke k’ok’arin yi ba... Maiyasa yake jin abubuwa da dama basa tafiya daidai cikin Masarautar... Tabbas ya kamata ya saka zancen Baba Wambai a ma’auni, bai kamata ya k’yale Yazeed ya d’ale Karagar Mulkin ba har dai yanaso ya samo amsoshinsa....

Turaki yaci gaba da fad’in “Mai kake gudu cikin sarauta Mahmood... Kana tinanin sirrin da ka b’oyewa d’iyarka shekara da shekaru na iya bayyana ne... Is that what’s holding you back...?” Ya k’arashe cikeda kulawa...

Kaikaitowa yai wannan karon yanaima Turaki wani irin duba kana ya soma fad’i cikin karaji “She’s never going to find out.... I won’t allow that to happen... I’ll protect that from happening, no matter the cost..!!”

Shiru Turaki yai ba tareda ya kuma cewa komai ba dan yasan wanene abokin nasa idan ransa ya b’aci... Bai kuma kawo zancen ba sai ma shiru da yai yana karantar Mahmood d’in da ko ba’ace ba lissafi da sak’e sak’e yake cikin zuciyarsa... Turaki ya girgiza kai cikeda tausayin abokin nasa....

***

A nan yanda ta mak’ale take jiran fitowar Jamal, Ta kusan minti talatin mak’ale a nan wajen tana ganin masu kaiwa da komowa amma bataga koda k’yallin Yarima Jamal ba... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai kuma lek’awa... Har saida ta cire rai bazataga giftawansa ba ta hango wani mutum sanye cikin bak’in kaya mai tsananin duhuwa ya nufo ta yanda take, baka iya hango fuskarsa don ya rufe da bak’ar hula mai yanayi da hular sanyi... Baka hango komai sai alamun mutum... Sosai k’irjinta ke tsananin bugu zuciyarta na tambayarta wanene wannan... Tana gani mutumin ya nufi wata hanya ga walk’iya da har yanzu akeyi had’ida tsawa mai k’arfin gaske... Take taji zuciyarta tana son ganin yanda wannan mutumi zai jesa... Lokaci guda ta sad’ad’o ta fito daga mab’oyar nata ta nufi mutumin cikin sand’a dikda cewa tafiyar mutumin yafi kama da sassarfa tamkar mai tafiya cikin iska dan har b’acewa ganinta yake.....

Dikda tsananin tsoro da ya ziyarci zuciyarta hakan bai hanata bin bayan wannan mutumin da bata iya hango komai nasa face bak’in tufafi....
Chapter 19 · 0% Book details