Sashe 153
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Turaki ya girgiza kai yace “Ai wasu dai basu san illan cin dukiyar maraya ba, kuma k’alubalen da yanzu muke fama dashi kenan.. Wani yana Allah Allah nasa ya mutu ya hau kan dukiyar yayi babakere kuma karkaji da Wai idan ya cinye dukiyar nan bazai taimakawa marayun ba, basusan cewa wuta suke ci ma cikinsu ba..”
Ansar yace “Kaidai saidai kawai Allah ya kyauta duniyar Ta gama lalacewa da kwad’ayi da kuma rowa, mai kud’i baya tausayin talaka kansa da ‘ya’yansa kawai ya sani babu taimakekeniya tsakanin Al’umma, shima talakan baya tausayin kansa ga bak’ar hassada da k’eta da zai samu dama sai yayi zalunci... Hassda da k’eta had’ida bak’ar zalunci sun dabaibaye Al’umma ta yaya kuwa zamu zauna lafiya ba dole bala’u da musiba suyi yawa ba.. Kaidai kawai saidai muce Allah yayi mana maganin abun ya shiryar damu zuwaga tafarkin daidai.. Shi kuma Baffah idan Allah zaisa hakan ya zamto hanyar shiriyarsa ai abin mu godewa Mai Martaba ne daga ni har Hameedar domin kuwa duk kalan wa’azin duniyar nan da ka sani anyi wa Baffah akan kwad’iyin dukiya da jaraban son abin duniya.. Yanzu idan aka barsa haka nan gobe ma zai iya aikata abu makamancin hakan.. Ni naji dad’i da aka masa haka.. Allah yasa hanyar shiriyarsa kenan ..”Turaki ya amsa da Ameen kana ya k’arada “Mu k’arasa Masarautar koh..”
Ansar ya amsada “An gama Mai Sarauta..” Tare suka nufi Masarauta motarsu gaba a baya..
**
Suna shiga da Yawale motar suka gyara maza zamansa suna masu risinawa had’ida gaidashi.. Mamaki ya cika Yawale.. Yana ‘yan koke kokensa yana fad’in “Bintu shikenan ashe ba da rabon na miki sallama ba.. Ni kuma haka Allah ya k’addaro min.. Oh ashe dai ajalina ne yazo..!” Cak Yawale ya dakata da koke kokensa yana duban mutanen, cikin rawar jiki da rawar murya yace “Yal.. Yallab’ai nace ba.. Dama wllhi inaso ince maku na tuba.. In sha Allahu ni bazan sake aikata abu mai kamada haka ba.. Kuma kud’in auren yarinyar yana nan idan kuna so sai in baku.. Shikenan ku rabu dani salin alin in komaga iyalina.. Yallab’ai Iayalai ne dani nid’in..!” Ya k’arashe yana d’ago masu hannu alamun rok’o.. Babu dai wanda ya amsasa cikin su har suka shigo cikin Masarautar...
Tsaban tsoro da tsananin tashin hankali da Yawale ke ciki baima fahimci cewa Masarauta ce suka shigo ba.. Shidai damuwarsa kawai su k’yalesa ya tafi...
Suka isa wani b’angare nan cikin Masarautar aka bud’e masa k’ofa bayan driver ya ida parking... Guda d’ayan ya dubi Yawale ya risina yace “Muje Baba..”
Yawale yace “Na’am.. Toh toh.. Yallab’ai nace dai a duba lamarin kar a yanka ni wllhi Dattijo ne ni akwai iyalai.. Na baro iyalai gida..!”
Guda d’aya yace “Baba mu shiga daga ciki za’a baka sutura ka shirya sannan ka gudanar da sallar mangariba kafin a kaika kaga shugabanmu...”
Zuciyar Yawale Ta kuma tsinkewa, shikenan saima an shiryasa kafin akaisa ga shugaban mayankan.. Kaico son duniya irin nashi.. Bai tab’a nadaman kwad’ayi da son abinda duniya da yake irin na yau ba.. Wato ashe haka yarinyar nan Muhibbah taji.. Allah sarki ya cutar da ita.. Watak’ila ma har an yankata ansha jininta.. Yau gashi yanajin irin abinda taji.. Baisan ya akai ya isa cikin k’atoton parlorn na alfarma, dogari guda yai masa rakiya zuwa wani d’aki.. Yawale ya saki baki da hanci yana duban kayan alatu a wannan gida.. Nan fah ya mance da cewa mayanka aka kawosa sai jinjina mak’udan kud’ad’en da aka kashe a wannan tsararren gida yake wanda ya masa lak’abi da aljannar duniya.. A hankali yake furta “Wai dank’ari mak’ari Aradu wagga gini kinci kud’in kayukan bil’adama.. Allah kad’ai yasan Kayuka nawa akayi ginin nan dasu...!” Yai tsit kuma yana tuna Toh wato dai yanzu harda nasa kan za’a k’ara watak’ila sai gidan yafi haka tsaruwa idan aka k’ara da nasa kan... Ya cire hularsa ya shiga shafa kansa kaman mai auna size din kan nasa...
Ga tsananin mamakin Yawale kaya irinta masu mulki aka basa, kaya masu matuk’ar tsada harda rawani.. Ya juya kayan yana kuma furta “Ikon Allah kenan.. Su kuma wad’annan tufafi fah.. Toh kodai kar yasa ne.. Amma idan bai saka ba rabjejen mutumin nan idan ya kuma shigowa ya taddashi fah..? Wata zuciyar tace ai gwara ka saka kayan kafin su yanka ka ko banza ka tab’a saka kayan masu mulki irin haka... Yawale am ka shiga tarihi.. Ya k’arashe tinanin nasa yana kwab’e nasa gajiyayyun tufafin...
Koda Yawale ya fito zasu tafi fannin oga Sai rarraba idanu yake yana mamakin mutanen da suka kamosa sun sauya shiga sun saka jajayen tufafi masu ratsin koriya irin tufafin dogarai.. Mamaki ya cika Yawale musamman da suka fito yaga dogayen benen da suke ciki masu zubi da gidajen masu mulki.. Ikon Allah toh meke faruwa ne... Ya tambayi kansa cikin zuciyarsa... Yaga sunata shige mutane sahu sahu kama daga masu shiga irinta Bauta zuwaga masu shiga irinta muk’ami, yaga duk sanda zasu shige taron bayi sai an risina an gaidashi.. A’a Yawale naku fah Sai ya soma k’umewa yana wani jin kansa yana jinjina kai alamun amsawa.. Jin kansa yake yawa wani basarake... A haka suka iso babban Parlorn Mahmood wanda tsarinsa da kyaunsa yasha gaban wancan parlorn da aka soma sauk’an Yawale.. Ya saki baki da hanci yana kallon chandeliers ta ko ina sai wal wal suke kaman wani rana.. A fili yake furta kalman yabo ga wanann gida mai matuk’ar kyaun gaske...
Sanda zasu shiga asalin Parlorn da Mahmood Ke ciki yaji muryar Dogarai masu tsaron wannan k’ofar suna furta Gyara kimtsi..! Gyara kimtsi da kyau..! Had’ida masa maraba da isowa...
Yawale yaci gaba da Washe baki yana jinina kai... Suna shigowa parlorn ya hango wani kyakkyawan Basarake zaune saman kujera yasha kwalliya cikin tufafi irinta masu mulki, kallo guda zaka masa ka fahimci shid’in Basarake ne.. Gefe dashi saman darduma kuwa matsa ne guda biyu.. Bai ida tantance matasan ba saida ya k’araso sosai yaga ashe Ansar ne d’aya matashin d’ayan kuma kaman yaso ya gane fuskarsa.. Yawale ya k’arasa kusan Ansar yana furta “Yakubu..! Yakubu ina ne nan..? A ina muke..?”
Muryar Mahmood ya sinkayo yana furta “Barkada k’arasowa Baba..! Fadah tayi Farin ciki da tarban bak’uncinka..!”
Yawale ya kaikaito da k’yar yana so ya d’ago yanda yasan muryar.. lokaci guda yake duban Mahmood dukda tsananin gizo da k’wayar idanunsa ke masa.. Tabbas yaso ya gane wannan k’wayan idanu da karan hancin.. Ya shiga tuna a cikin nad’in Buzaye yaga wannan k’wayan idanun.. Zuciyarsa taci gaba da tsinkewa sanda ya kuma waigawa da sauri yana duban Turaki dake gefe wanda a zuwansu na farko shi babu nad’in Buzayen a tattaredashi..
Barde ya bud’e murya bayan Mahmood ya ida magana yana furta “Godiya yake Sarkin Sarakuna..! Dattijo yana godiya da karramawa Sarki...!”
Hannu na rawa Yawale ya shiga nuna Turaki yana furta “Yakubu gasu nan.. Wad’annan sune suka amshi auren Muhibbatu..! Alhamdulillah Allah ya nuna mana su.. Yanzu sai a warware aure kaga sai a fasa cinikin kaina...”
Barde dake tsaye daga gefe ya furta “Hattara Dattijo kana gaban Mai Martaba Sarki ne..! Hattara da kalamanka Dattijo Sarki baya saki.. Gimbiya Ta shigo gidan Alkhairi.. D’iyar masu mulki ce kuma matar masu mulki.. Jaaa zamanin Dogon Sarki...Sarki Mahmooda ibn AbdulJabbar..!”
Tinda Barde ya soma magana zuciyar Yawale ke ci gaba da tsinkewa... Meke faruwa..? Wannan mutumin Dama Sarki ne.. Gimbiya..? Wacece Gimbiya..? Muhibbar ce Gimbiya..? Yai saurin juyowa ga Ansar yana furta “Yakubu meke faruwa ne a nan.. Shin ina kasan mutanen nan..?”
Ansar yace “Baffah wannan Sarki ne.. Kuma shine ka aurar masa da Muhibbah b’adda kamanni yayi dan ya ceci Muhibbah daga gadar zaren dakaso k’ulla mata.. Shid’in d’an uwanta Baffah.. Muhibbah asalinta d’iyar masu mulki ce kuma ma d’an uwanta ka aurar da ita.. Gida Ta koma Baffah.. Shine yace azo dakai domin Masarauta tayi maka karramawa na musamman...” Ansar ya k’arashe murmushi saman fuskarsa..
Innalillahi wa Inna’ilaihi raji’un..! Tinda Yawale yake bai tab’a jin kunyar duniya irin wanda yaji yau ba.. Wato ashe haka al’amarin yake.. Dukda sanyin Ac dake circulating cikin parlorn bai hana zufa tsartsafowa Yawale ba.. Allah mai iko.. Yanzu ashe Dama wa Sarki ya aurar da Muhibbah.. Kai jama’a Kaicon hassada da son zuciya.. Mai za’ayi da hassada da k’yashi.. Ubangiji Allah ka tsarkake mana zukatanmu ka nisantamu da wad’Annan munanan d’abi’u.. Ai tuni hawaye suka soma zarya saman kumatun Yawale.. Ya kasa kaikaitowa ya dubi yanda Mahmood Ke zaune saima juyawa da yayi gaba d’aya ya basu baya hawaye naci gaba da gangaro masa..
Ansar ya rarrafo kad’an ya kamo hannayen Yawale yana fad’in “Baffah, ka juyo kayi ma Sarki gaisuwa sannan kai masa godiya...”
Girgiza kai kurum Yawale yake yana ci gaba da hawaye yake furta “Yakubu bazan iya ba.. Allah ya gani bazan iya juyo ba.. Kace ma Rankaidad’e ya yafeni.. Kace ma Gimbiya Muhibbah ta yafeni.. Wllhi sharrin zuciya ne da son abin duniya had’ida muguwar hassada da k’eta... Yakubu kace Rankaidad’e ya yafeni.. Na tuba wllhi..!” Kuka ya hana Yawale ci gaba da magana...
Turaki ya k’araso gabansa ya duk’a yace “Baba bakaima Sarki laifi ba.. Hasalima dan yayi maka godiya ya gayuaceka Fadah tareda karramawa..!”
Yawale da hawaye da gumi suka wanke masa fuska girgiza kai yake yana duban Ansar da Turaki yake furta “A’a.. Wllhi A’a ni ne nazo neman gafara da yafiya.. Kuyiwa Allah kuce Mai Martaba ya yafeni na tuba wllhi.. Itama Gimbiya ta yafeni...!” Yaci gaba da matsan k’walla.. Da k’yar Turaki da Ansar suka sa Yawale ya kaikato daga nan yanda yake duk’e yana fuskantar Mahmood..