Sashe 40
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tare Fu’ad da Jamal suka amsa da Ameen kana Jamal ya d’an bud’e murya yace “Yaya a nawa shawarin kamata yai a tura Fu’ad can wani wajen yaje yai karatunsa zaifi bada himma samada idan yana gida...!”
Bai kai aya ba Fu’ad ya shiga girgiza kai tamkar mai k’aramin tab’in hankali yake furta “No... No I don’t want to leave.... Banso naje ko ina, no.. No... I wanna study here...!” Yana maganan yana girgiza kai yana rintse idanu had’ida kame kansa....
Saurin rik’osa Mahmood yai yana k’ok’arin calming nasa yake fad’in “Calm down Fu’ad... Babu wanda zai sakaka tafiya makarantar da bakaso kaji koh... Dik yanda ka zab’a nan zakiyi ka kwantar da hankalinka...!”
Fu’ad yai masa K’uri k’walla tab idanunsa yake furta “Thank you Yaya... Na gode Yaya Mahmood...!” Ya k’arashe yana mai kai masa runguma had’ida k’ank’amesa sosai kaman mai tsoron kada a rabasu....
Mahmood ya jinjina masa kai a hankali yana mai amsawa kana ya maidoda hankalinsa kacaukam kan Fu’ad dan shi bai yarda Fu’ad iyakacin gaskiyar Abinda yake son sanar dashi ya fad’i mishi, he can feel akwai abinda yake b’oyewa, yanaji cen k’asan zuciyarsa kaman akwai abinda yake tsananin damun yaron kuma yanaso ya fitar saidai baisan yaya zai ya fitar da abin ba.... But tinda yanzu Yana nan zai k’ok’ari ya taimaki d’an uwansa da izinin Allah....
Murmusawa Jamal yai yana mai dafa kafad’ar Fu’ad yake furta “I wish you all the best my brother... Idan ka zab’i yin karatu a nan then fine... Allah Ubangiji ya dafa maka k’anina...!” A tare Mahmood da Fu’ad suka amsa kana Jamal yai masu sallama ya nufi Parlorn Giwa....
Hannun Fu’ad Mahmood ya dafa a hankali kana ya ambato sunansa... Fu’ad ya d’ago yana dubansa.
Mahmood yaci gaba da fad’in “You know you can trust me right..?”
Fu’ad ya jinjina kansa a hankali alamun tabbatarwa kana Mahmood ya d’orada “And you can always count on me...!”
Nan ma jinjina kai Fu’ad yai... Mahmood ya gyara zamansa kad’an kana yace “Idan akwai abindake damunka kar kaji shakkun sanar dani kaji k’anina... Your big brother is here to listen..!” Ya k’arashe yana mai duban Fu’ad d’in cikeda tausayawa...
K’ak’aro murmushi Fu’ad yai kaman zai magana sai kuma ya rungume Mahmood d’in yana fad’in “I’m glad you are here now Yaya... Please don’t leave us kaji.. Kar ka sake komawa Spain ka barmu a nan, ina matuk’ar son kasancewarka a nan...!”
D’an bubbuga bayan Fu’ad yake yana mai furta “Bazan sake tafiya ba Fu’ad, zan zauna tareda ‘yanuwana a nan gaba d’aya kaji koh...!”
Fu’ad ya murmusa cikeda jin dad’i su duka biyun suna duban juna cikeda k’auna...
**
Jamal na ficewa bai zarce ko ina ba sai d’akin Giwa yanda suka k’ume su biyu d’in cikin d’aki..
Zuba masa idanu Giwa tai sanda yaci gaba da fad’in “Your little boy almost screwed up Maami... He almost ratted us out, if only ban isa akan lokaci ba... Nayi imani da Fu’ad ya bud’e bakinsa ya sanar da Yaya Mahmood komai, dik abinda muka aikata ranan hawan k’aramar sallah shekaru gomasha biyar da suka shud’e....!” Ya k’arashe yana sakin huci...
Giwa ta mik’e tana murza hannunta dake rufe cikin safa... “Jamal k’aninku baida hankali da wayo har yanzu, idan Mahmood yasan batun nan bazai tab’a yafe mana ba dikda cewa sabida ku gaba d’aya dukanku hud’u muka aiwatar da wannan abin, da bamu aikata hakan ba ina mai tabbatar maka d’ah na da yanzu an jima da koran mu cikin Masarautar nan, kana tinanin ba dan ina tsaye akan k’afata ba da yanzu ba’a d’aid’aitani a kassarani a Masarautar nan bane yanda akega duka ‘ya’ayan Sarki AbdulJabbar ni ce nan na haifesu gaba d’aya ku duka hud’un... Dik abinda muka aiwatar shekarun baya sabida nasaranku ne... Malami na ya tabbatar min duka ‘ya’yana sai kunyi sarauta tin daga kan Yayanku Mahmood har zuwa kan d’an autanku Fu’ad...”
Jamal ya d’ago yana dubanta cikin wane irin yanayi, lokaci guda ya furta “But Maami Yaya bai aikata laifin ba, shin ya za’ai shi d’in yai sarautar...?!”
Murmushi ta sakar masa tana mai shafa fuskarsa take fad’in “Kud’in kun wadatar ko Yayanku bai aikata ba zai sarauta tinda ku d’in kun aikata....!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta lokaci guda taci gaba da furta “Na sadaukar da abubuwa da dama sabidaku ‘ya’yana ciki harda wani b’angare na jikina...!” Ta k’arashe tana mai duban hannunta guda dake rufe cikin bak’ar safar nan....
Zaunar da ita Jamal yai yana mai furta “Karki damu Maami na fahimceki, babu uwar da bazatai komai dan ceton yaranta da cikar burinsu ba, wanann gidan shine asalinmu kuma shine tushen mu, dik abinda kikai kinyi ne domin amfanin ‘ya’yanki domin Ki rufawa ‘ya’yanki asiri domin Mu dawwama cikin wannan masarauta har k’arshen rayuwarmu kuma ban tab’a dana sanin yin duk wasu abubuwa da kike umartata ba... Ya Mahmood nasan bazai tab’a fahimtar hakan ba, he’d judge you... Shi d’in baisan cewa zama cikin gida na sarauta dole sai kanada shiri ba...!”
Murmushi Giwa ta saki a hankali tana mai duban Jamal, lokaci guda take furta “Kafi kowa fahimtata duk cikin ‘yanuwanka... Shisa nake matuk’ar k’aunarka nake ji dakai Gwarzo na.... Koda wasa kada ka bari Fu’ad ya sanar da Yayanku abinda muka aikatawa yarinyar nan SAUDATU da ahalinta....Munyi hakan ne domin KARE KARAGAR Masarautar nan, da bamu aikata hakan ba da yanzu mun jima da zama tarihi a Masarautar nan....!”
Jamal ya jinjina kai “K’warai kuwa Maami bazan tab’a bari Fu’ad ya sanar da Yaya ba, hasalima lokaci yayi da zamu d’aga Fu’ad daga cikin Masarautar nan, mu turashi makaranta cen wata k’asa mai nisa yanda zai nesa da gida..!” Ya k’arashe yana duban mahaifiyar tasa...
Mik’ewa tsaye tai tana dunk’ule hannunta dake rufe cikin bak’ar safar nan kana Ta shiga girgiza kai tana furta “A’a Jamal, banaso wani daga cikin ‘ya’ya na ya sake nesanta na, Fu’ad har yanzu yaro ne baida hankali k’wayoyin nan sun gama illata masa kwanya, ina tsoron mu turasa wata k’asa yaje ya aiwatar da suicide sanin kanka ne yasha attempting yin hakan a nan gida tin bayan abinda ya faru da wannan yarinya Saudatu da ahalinta...!”
Jamal ya fuzar da fuci a hankali kana yace “K’warai kuwa Maami my brother couldn’t get over it, Fu’ad gawwaki biyu ya tsallake kuma unfortunately Shi ya cakkawa Mutumin takwabi har ya mutu, Saidai baiyi hakan Da nufi ba k’ok’arin kub’utar da mutumin yake daga dakarun da na tura... Maami a wancan lokacin Fu’ad yaro ne d’an shekaru goma sha uku kacal a duniya, it was really a traumatic experience for him... Ban tab’a zaton zai iya rayuwa da Abinda ya rayu ba... Fu’ad ya wahala cikin wannan rayuwar Maami...!”
Jinjina masa kai tai a hankali abubuwan data aikata a Masarautar na kuma zuwa mata daki daki tin daga cin amanan da mijinta yai mata...Ta basa kyautar baiwarta a matsayin tukuici yaci amananta da Baiwar ya ‘yanta Baiwar Sannan ya auri Baiwar a bayan idonta a wani tafiya mai dogon zango da sukai shida Kyakkyawar Kuyanganta data mallaka masa....AbdulJabbar ya tozarta ta ya kuma ci mutuncinta ya wulak’antata sannan Bai cancanci yafiyarta ba even if in his death...!
Gimbiya Turai tafi k’arfin tayi kishi da baiwa, baiwarma ta Masarautar ta...!
Sannan kuma Wai ace Baiwar har ta riga haifawa mijinsu Magaji.... Inaa hakan sam bazai yuwu ba... Bazata tab’a bari jinin bauta ya k’wace mulki daga gareta ba koda kuwa cewa an ‘yanta mahaifiyarsa... Tabon bauta bazai tab’a shafewa a jininsu ba har abada...!! Ta k’arashe tinanin nata tana mai ci gaba da sakin huci...
**
A daren wannan rana Giwa ta ziyarci Tal’udu... Tana zaune kan jan daddumarsu Ta tsafi take ci gaba da fad’in “Idan SAUDATU na raye ya zama dole ka zak’ulota Tal’udu yanda ta shiga ta fita.. Babu kasawa babu fad’i a lamarina, saidai nasara da ci gaba...!” Ta k’arashe tana sakin huci...
Wani irin murmushi mai sauti Tal’udu yai yana mai buga turb’ayan dake gabansa... Wani irin jan k’ura ya tashi ya gauraye wajen gaba d’aya... Saida k’uran ya kwashe mintoci kana ya lafa..
Tal’udu ya dubi Giwa da firgitattun idanunsa “Babu wani haske gameda tak’aimemmen yanda yarinyar take a halin yanzu... Dama tun fari saida na miki kashedi muddin yarinyar nan ta kubce matsala ne Babba zai faru, kikai sake kika bari Ta kufce sannan yaranki suka miki k’arya cewa sun kasheta.... Idan har tana raye hakan nada tabbacin Mahmood zai zamto magajin Mahaifinsa... Sannan hakan zai kuma zamto dalili na rugujewarki..!!”
Gumi ya shiga tsartsafowa Giwa lokaci guda take furta “Yanzu miye abinyi gameda Mahmood..?!”
Murmusawa Tal’udu ya kumayi kana yace “WAMBAI.!!”
Giwa tai saurin d’agowa tana dubansa cikeda firgici...
Tal’udu yaci gaba da fad’in “Mabud’in fursunan sirri na wajen d’anuwan mijinki kuma idan har ya dank’awa Mahmood shikenan bazai tab’a dawowa hannunki ba JAFAR ka iya dawowa...!”
Yanzu kam kan Giwa ne ya soma kwancewa... Tai wuf Ta mik’e tsaye tana fad’in “Bayaga Jafar shin akwai wanda ya isa ya bud’e k’ofar da ni kad’ai Ke iya bud’ewa...?!”
“Kinyi kuskuren aminta da Wambai Turai... Keda Wambai tabbas kunyi tarayya wajen aikata wani laifi saidai kaman yanda na sanar dake zai iya zamewa yaci amanarki.... Kafin yaci amanarki kiyi maza ki aiwatar da wani abu kan Wambai, domin fitilar tsafi ta hasko min cewa akwai cin amana tsakaninku...!”
Huci kurum Giwa Ke sauk’ewa a hankali... Ta yaya Wambai zaici amanarta, ya zama dole ta b’atar dashi kafin a isa wajen... Bayan sun fice daga wajen Tal’udu ta komo d’aki nan ta umarci Jakadiya da tai mata kiran Waziri a waya....
Waziri na d’agawa Giwa ta amshe wayar cikin sauri tana mai sanar dashi cewa yai saurin cimma Wambai kafin Mahmood ya rigasu...
Waziri ya sanar da ita kada ta sami damuwa Mahmood bazai cimma Wambai ba, idanma ya cimmasa saidai ya cimma jana’izarsa....
Giwa ta saki murmushi cikeda jin dad’i Dan tasan Waziri bazai tab’a bata kunya ba har abada...
***
Kaman ko yaushe yauma nad’in buzaye yai ya nufi gidan Baba Wambai... Bak’on Buzu abinda ya sanarda Innani kenan Dan kar ta zargi wani abu... Wannan karon a parlorn Baba Wambai suka keb’e...
Baba Wambai ya tsaresa da idanu kana yace “Ina saurarenka d’ah meke tafe dakai wannan karon...?!”