← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 162

Sashe 62

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tinda ya fito daga Zauren taron tafiyar kurum yake ba tareda yasan yanda yake jefa k’afafunsa ba... Kallo guda zakai masa ka fahimci yana cikin matsananin tashin hankali had’ida b’acin rai... Tafiyar kurum yake yana dukan k’asa da k’afafunsa yake ratsa cikin Fada, dik wanda ya gansa a haka sai yasha jinin jikinsa ya k’ame ya risina saidai shi Mahmood d’in baima kula da kowa, gani yake tamkar shi kad’ai ne tareda matsalolinsa cikin Masarautar... K’arfin halinsa yasa yake k’ok’arin danne abindake tasowa daga can k’asar zuciyarsa amma kam shi kansa yasan ana gab da kaisa mak’ura a Masarautar...

Raheema da fitowarta kenan daga sashen Gimbiya Zeenat Ta hangi Yarima Mahmood tafe ya nufi sashensa, yanayinsu ya bala’in tada mata hankali...
Ta dubi Hadimarta Mashkura da a yau d’in ita ke take mata baya... Jinjina mata kai tai alamun tana iya tafiya bata buk’atarta...
Mashkura na shigewa Raheema tasa kai tabi bayan Mahmood... A daidai k’ofar sashensa Ta cimmasa, tai gyaran murya kad’an had’ida risinawa kaman yanda tarbiyan babban gida yake “Barkada yammaci Your Highness..!”

Duba d’aya yai mata ya watsar Dan har yanzu ba Wai sun koma normal bane tun bayan tattaunarwarta da Juwariyya da ya sinkaya....
Raheema ta kuma gyaran murya kad’an tace “Rankaidad’e akwai abinda ke damunka ne... Kai hak’uri na tunk’aroka ba tareda iso ba... Yarima I just couldn’t help it... Ganinka haka ya d’aga min hankali.. Definitely nasan something is wrong... Zan iya taimakawa da wani abu....?!” Ta k’arashe tana k’ifk’if da idanu had’ida rau rau da fuska alamun nuna damuwa....

Dubanta yai na wasu ‘yan dak’ik’ai, ba tareda ya furta koda kalma guda ba yasa kai ya shige sashensa....
Raheema ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai ayyanawa cikin zuciyarta, wannan damarta ne to win Mahmood back zatai duk yanda zatai ta tabbata shid’in ya kuma zama nata a yau d’in... Murmushi Ta saki kana tasa kai Ta shige cikin sashen nasa...

Tsaye ta hangesa ya bada baya yana duban window, hannayensa hard’e Ta baya... Raheema ta k’arasa Kai a k’asa yawa mutumiyar arziki...
Saida ta kuma yin gyaran murya kad’an kana tace “Yarima there’s something I need to tell you... Ka cancanci ka sani...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

A hankali ya kaikaito yana dubanta, kanta a k’asa taci gaba da fad’in “Nasan ba lallai ka kuma yarda dani ba Yarima... I did something behind your back... But believe me nayi komai ne don amfaninka kuma with pure intentions... Yarima I did all that for you, sabida Farin cikinka... I hope abinda zan fad’a maka yanzu zaka yarda dani... Kuma ba Dan na saye zuciyarka ko wani abu mai kamada hakan ba... Zan fad’a maka ne because I care about you... And I love you...!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata cikin yanayi mai ban tausayi....
Ganin yayi K’uri yana dubanta ya sanyata samun daman ci gaba da magana...

“Yarima akwai wasu mutane da suke maka k’ulleliya a bayanka, mutanen da suke son ganin downfall d’inka... Ni da idanuna na gansu a asibiti sanda naje duba Baba Wambai, su biyu d’in basa jituwa sam amma da na gansu a tare nasha mamaki..!”

Katseta yai cikin kakkausar murya da fad’in “Raheema...! Mai kike son cewa, just spell it out once and for all, su waye kike magana akai...!!”

Jinjina kanta tai a hankali kana tace “It’s your brother Yazeed and Majidad’i... I saw the of them together, they were conspiring against you... Naji da kunnuwana suna cewa zasu kaika k’asa by every means...!” Ta k’arashe tana zaro idanu waje had’ida jinina kai alamun tattabatarwa....

Tinda ta soma magana yake dubanta ba tareda ya janye idanunsa ba, ga wani irin gumi dake tsartsafowa daga goshinsa, take idanunsa suka kad’a sukai jazir haka nan fatar jikinsa, kana iya hango yanda yake sakin huci cikin wane irin yanayi... Idanun Raheema suka sauk’a kan hannayensa da tuni ya damk’esu jijiyoyin sunyi rud’u rud’u... Baiso ya yarda da zancen Raheema Dan shi ba mutum ne mai d’aukan magana haka kurum ba tareda k’wakk’waran hujja ba... Amma bayan abinda ya faru yanzu a Zauren taro baijin akwai sauran hujja da yake nema... Bai kuma furta komai ba sai ficewa da yai kaman zai tashi sama...

Jamal da Fu’ad dake tafe haraban Masarautar hango Yayan nasu a haka yasa suka dubi juna... Fu’ad yaceda Jamal meke faruwa..?

Girgiza kai kurum Jamal yai alamun shima bai sani ba.... Fu’ad yace “Mu k’arasa muji...!”

Babu musu Jamal ya jinjina masa kai sukabi bayan Mahmood...!

**

Giwa na tsaye gaban Yazeed tana ci gaba da sakin huci take furta “Har abada muddin Yayanka na raye bazakai saurata shi ya rasa ba Yazeed... Yazeed mai kake so ka zama..? Shin maiyasa kake neman ka raba kan ahalinmu...! Yazeed ka d’ago idanu ka dubeni ka sanar dani dik abinda Ubandoma ya fad’i k’arya ne kai ka tsara masa Mahmood bazai aikata haka ba..!!”

Giwa bata rufe baki ba Mahmood ya banko k’ofa ya shigo cikin yanayin da basu tab’a ganinsa ciki ba... Jajayen idanunsa masu cikeda b’acin rai ya sauk’e kan Yazeed kan kace mai yayi tsalle ya cakumo wuyan Yazeed ya masa wani irin damk’a da duka k’arfinda Allah ya huwace masa....
Cikin kakkausar murya mai firgitarwa yake furta “I have warned you time without numbers... Do not cross me Yazeed... Now tell me what’s your role in all this..! Talk to me Yazeed..! Talk...!!!” Ya k’arashe yana kuma jijiga Yazeed da iyaka k’arfinsa...

Giwa da gaba d’aya duniyar ta juye mata ga wane irin rawa da illahirin jikinta keyi, gaba d’aya ta kasa furta komai sai wane irin karkarwa jikinta keyi...
Daidai nan su Jamal da Fu’ad suka shigo... A d’ari Jamal ya isa garesu yana k’ok’arin janye Mahmood yake calming d’insa amma inaa tamkar baiji saida matse Yazeed yake yana wane irin huci... Tuni idanun Yazeed sun furfito waje tamkar an matse mage a buhu....

Giwa cikin rawar murya mai cikeda firgici had’ida tashin hankali take furta “Mahmood kar ka kashe d’an uwanka... Ka sakar masa wuya, ka bashi dama yayi bayani...!”

Bai sakesa ba sai jijiyoyin jikinsa dake kuma fitowa rud’u rud’u... Dik iyaka k’ok’arin Jamal da Fu’ad wajen janye Mahmood sun kasa, koda wasa basu tab’a ganin wannan side d’in nasa ba basu tab’a sanin cewa yanada zuciya har haka ba...

Har saida Giwa ta fashe da kuka tana janye Mahmood tana fad’in idan zai iya kashe d’anuwansa Yazeed Toh itama kawai ya shak’e mata wuya ya fara da ita....

A hankali yake sassauta rik’onda yayiwa Yazeed har ya cikasa gaba d’aya... Yazeed ya zube gefe yana haki sosai had’ida gumin azaba...

SameenaAleeyou📚
[8/9, 11:27 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*42*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

D’agowa Yarima Mahmood yai ya dubi Giwa na d’an wani lokaci kana ya furta “Kiyi hak’uri Maami... I’m sorry...!” Daga haka waigowa ya kumayi yana aika muguwar kallo wa Yazeed da har yanzu bai iya mik’ewa ba... Bai kuma cewa komai ba ya fice daga sashen gaba d’aya....
Jamal yai saurin k’arasawaga mahaifiyarsa ya taimaka mata ta suka shige d’aki yana mai k’ok’arin calming d’inta... Parlorn ya rage saura Fu’ad da Yazeed..

Fu’ad kaw girgiza kai kurum yai yana duban Yazeed “Wannan shine abinda nake jiye maka Yazeed, raininka da wulak’ancinka ya soma yawa...!”

Katsetsa Yazeed yai da fad’in “Don’t you dare lecture me you idiot... Kaje ka sami wancan mahaukacin Yayan naka shi yake buk’atan lecture sama dani tinda cikin mu biyun shine criminal, ya kashe Wambai tareda taimakon Hadiminsa sannan ya zago yana so ya kashe Hadimin nasa before he rats him out... Kuma Wllhi abinda yayi mun baici banza ba sai na koya masa hankali... No one messes with Prince Yazeed AbdulJabbar..!” Ya k’arashe yana sakin huci da haki had’ida sosa wuyarsa da tuni fatan tayi jazir...

Sai yanzu Fu’ad ya fahimci meke faruwa... Gajeren murmushi yai yace “Kafi kowa sanin cewa zancen da kake babban k’arya ne Yazeed, ko ka mance cewa cikin dukanmu hud’u shine ba criminal ba... The three of us are criminals, we are the criminals Yazeed, You Jamal and I...Kuma cikinmu gaba d’aya shi kad’ai ya cancanci zama Sarki sabida ba’a Sarki criminal...!”

Katsesa Yazeed yai da fad’in “Shut up! Just Shut the hell up Fu’ad... Kai mahaukaci ne k’waya ya gama illata maka kwanya... Baka da sauran amfani Fu’ad, dakai da babu a Masarautar nan duk d’aya ne... Kai gwara ace babu kaima at least bazaka dinga jawo mana abun kunya da wannan haukar Naka ba wanda bakada ranan warkewa...!”

K’walla masu zafi suka ciko idanun Fu’ad lokaci guda... Ya shiga dunk’ule hannayensa sabida tsananin b’acin rai...
Yazeed kuwa abinda yakeso kenan yai provoking d’insa, take ya saki shu’umin murmushin nan nasa da gefen baki... Ya mik’e tsaye da k’yar ya matso dab gaba Fu’ad saitin kunnensa yake rad’a masa... “You’re useless Fu’ad, bakada amfani... Babu wanda yake sonka sabida kai psychopath ne, ko budurwar da kake mutuwar so ka kasa samun amincewarta Fu’ad... You’re nothing but a failure Fu’ad...! Just accept the fact bazaka tab’a birge kowa ba Fu’ad... Not even your Criminal brother Mahmood..!!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi had’ida d’an buga kafad’an Fu’ad d’in...

Bai kuma tsayawa sauraren kowa ba yasa kai zai fice yana mai ci gaba da sosa wuyarsa... Fu’ad dake tsananin huci hannu yasa ya damk’o hannun Yazeed ya dawo dashi baya...
Chapter 62 · 0% Book details