← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 162

Sashe 14

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashinta ne ya sark’e lokaci guda... Take taji jiri na neman Kaita k’asa, duniyar taci gaba da juya mata... D’an uwa ta d’auki Ja’afar bata tab’a zaton shak’uwarsu yakai munzanin soyayya mai k’arfi haka ba... Maiyasa Ja’afar zai tafi ya bar Masarautar nan a lokacinda ta dawo kuma lokacin da tafi buk’atar kasancewarsa cikin Masarautar... Shin kodai yanada masaniyar abinda azzaluman cikin Masarautar nan sukai masu ne itada iyayenta...? Idan har kuwa yanada masaniya tabbas zai iya sanin mai akai da mahaifinta da har yau bata san wane hali yake ciki ba... Shin kashesa akai..? Ko kuwa dai Yana nan cikin wannan masarauta... Tabbas Ja’afar zata iya samun wasu amsoshi daga wajen Ja’afar idan har yanada masaniyar abinda akai masu... Toh amma Ina Jafar...? Ta ina zata soma nemansa bayan babu shi cikin Masarautar... D’an dungurinta da Umaima tai ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi... Ta saki murmushi a hankali kana tace “Kinga kallon dawakan nan ya d’auke hankali na...”
Umaima ta murmusa kana tace “Ai naga alama... Mu k’arasa ko...”
Muhibbah ta jinjina mata kai kana suka nufi b’angaren bayi... Suna tafe Umaima naci gaba da mata bayani... Sun kusan nufa gate d’in bayin kenan Umaima ta hango Rahima sai buga sauri take ta nufi wani b’angare nan cikin sashen bayin yanda tai parking motarta daren jiya... Mamaki ya d’an kamata ita kaw mai ya kawo motarta k’ofan bayi....?
Muhibbah ta sauk’e idanunta a yanda Umaima ke duba... Lokaci guda take furta “Wacece wancan... Batai kama da bayi ba, mai ya kawota b’angarensu...?”
Umaima ta d’an girgiza kai kana tace “Rahima ce k’anwar Aunty Zeenat..”
Muhibbah tace “Matar da Yarima Mahmood zai aura...?”

Umaima ta jinjina mata kai alamun eh kana taci gaba da fad’in “Toh amma mai ya kawo motarta nan...? Kinga mu k’arasa wajenta sai nai introducing naku...”
Babu musu Muhibbah tabi Umaima suka nufi Rahima dake k’ok’arin shigewa mota, sai waige waige take tamkar maras gaskiya....
“Rahima..!” Muryar Umaima ya daki dodon kunnuwanta, abinka da maras gaskiya sai ta firgita, ta juyo cikin sauri tana dubansu... Lokaci guda kuma ta d’an saki murmushi kana tace “Haba Umcy wllhi kin razanani....” Tai maganar tana d’an dungurin Umaima da car keys d’inta...
Umaima ta murmusa kad’an saidai kafin Takaiga bata amsa suka sinkayo muryar Muhibbah tana fad’in “Yo miye abin tsoro Keda kike kusa da Dakurun sarki idan ma hari aka kawo Masarautar...?” Tai maganar cikin sigar wasa tamkar itada Rahimar sunsan juna.... I zuwa wannan lokaci Umaima kam Ta soma Sabo da halin Muhibbah, ita kaw Rahima da tsananin mamaki take duban budurwar da tai maganan wacce sam kallo guda tai mata taji ko kad’an bata kwanta mata ba....
Murmushin yak’e ta saki kana tace “Toh wa ya sani ko harin ta cikin k’asa aka kawo wanda Dakaru bazasu ankara ba...!” Tai maganar tana juya idanu...
Daga Muhibbah har Umaima murmusawa sukai kana Umaima tace “Rahima ga k’awata Muhibbah ku gaisa.. Muhibbah wannan itace Rahima ko nace our big Aunty, matar Yaya Yarima Babba...” Wannan kirari da Umaima tai mata ya sanyata sakin murmushi tana kuma jijjiga had’ida gyara tsayuwarta tana jin tabbas ta isa....
Muhibbah ta murmusa kad’an tana yaba kyaun halitta da Allah yayiwa Rahima, tabbas tayi kama da matan masu mulki.... Wayar Rahima ne yai ringing, ta d’an d’aga yatsarta guda alamun excuse kana ta matsa gefe ta d’auki wayar ganin ba kowa Ke kiranta ba face aminiyarta Zuhra.. Aiko tana d’agawa ta sinkayo muryar Zuhra cikin kuka... Gaban Rahima ya yanke ya fad’i, lokaci guda take furta “Zuzu meke faruwa... Please talk to me... Yazeed ya miki wani abu ne....?!”

Cikin muryar kuka Zuhra Ke fad’in “Rahima na gaji, na gaji da wulak’ancin Yazeed, dan Allah kizo I really need you...!” Ta k’rashe cikin shesshek’an kuka...

Fuzar da fuci Rahima tai a hankali kana tace “Alright ya isa haka Ki daina kukan nan, gani nan zuwa...!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin saita kanta yayinda kacaukam hankalin Muhibbah ke gareta tinda ta soma wayar, gaba d’aya hankalinta baiga Umaima daketa faman karanto mata bayani yawa malamar makaranta gaban d’alibai...

Rahima ce ta K’araso yanda suke tsaye kana tace bara taje sashen Zuhra, gaba d’aya yanayinta ya sauya ko takan motar ma batabiba ta shige cikin sauri... Muhibbah tabi bayanta da kallo har ta b’ace mata kana ta maido da hankalintaga Umaima, ta riga da ta samu information d’in da take buk’atan sani gameda Ja’afar dan dama hakan ne yasa tace suzo sashen bayi...ta d’an langab’e kai tana fad’in “Gaskiya mu juya haka nan your highness, na gaji sai wani lokaci kuma....”

Umaima ta murmusa kana tace “Da wuri haka...Dik San sanin Masarautar naki....?”
Murmusawa itama Muhibbar tai kana tace “Fada da fad’i take your highness bazan iya zagayawa ba...!”
Umaima ta kuma murmusawa kana tace “Toh mu k’ara gaba kad’an na nuna miki Rumbur sarki....”
Muhibbah ta jinjina kai tana mai murmusawa kana tace “Idan kince haka...”

**

Sauri sauri Rahima ta nufi b’angaren Zuhra tamkar zata tashi sama, dik kuyangin da zata gifta sai sun risina Sun gaidata, alla alla take ta isa taji wata uwar yau kuma d’an maras mutuncin nan yaiwa k’awarta... Aiko tana isowa ta hangesa tsaye k’ofar sashen cikin shiga irinta alfarma, yai tsayuwa irinta wanda keji da tsananin mulki da izza hasken rana ya haske kyakkyawar fuskarsa, kaman kullum babu alamun rahama ko fari’a a fuskar tasa... Ta sauk’e fuci a hankali tana girgiza kai kana taci gaba da dosowa sashen.... Tana hango dogaransa suna jinjina kai suna darewa a wajen alamun sallamansu yai, ta K’araso had’ida risinawa alamun gaisuwa... Har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya ya k’urama waje guda idanu... A zahiri zakai zaton gaisar dashi Rahima keyi...
Bai amsa gaisuwar nata ba sai cewa da yai “What brought you here...?” Yai maganar idanunsa na duban wani b’angaren...
Ta d’an saci dubansa kada’an kana tace “Prince what happened to Zuzu, is she well...?” Tai tambayar cikeda damuwa
Shu’umin murmushin nasa ya saki a hankali kana ya d’an kaikaito yana k’are mata kallo daga sama zuwa k’asa....
“Maiyasa bazaki shiga ba and find out yourself... After all, abinda ya kawoki kenan... !” Tana gani yai alamawa Hauni cewa ya k’araso, lokaci guda tasa kai ta shige tasan koda taci gaba da tsayuwa wajen ba samun amsa zatai ba....

Tana fad’awa cikin gidan ta haye d’akin Zuhra... Kwance ta taddata saman gado sai kuka take hannunta dunk’ule da wani abu...
Rahima na shiga Zuhra ta taso a guje ta rungumeta tana kuka sosai mai ban tausayi...
Jikin Rahima a matuk’ar sanyaye ta rik’e Zuhra suka zauna saman sofa, lokaci guda take furta “Zuzu Kukan nan ya isa haka... Mai kuma ya faru....?”

D’aga mata wuyarta tai taga alamun shati yayi jajazir, bata iya magana ba sai wani kukan da ta kuma fashewa dashi... Rahima ta zaro idanu waje...
“Zuzu kina nufin kice min Yazeed ne yai maki wannan tabon..? Zuzu mai ya faru....?”

Zuhra tai k’arfin halin share hawayen dake idanunta kana ta soma fad’in “Yazeed baida imani Rahima...Yazeed mugu ne, azzalumi ne.... Yazeed ya maidani tamkar shara cikin gidan nan, wllhi ko kuyanga ta fini ‘yanci cikin gidan nan... A duk lokacin da yaga dama zai d’ebo dik wani wulak’ancinsa ya zuba akaina... Rahima mai nai masa da tsanani...? Laifi ne don Allah ya jarabceni da soyayyarsa... Rahima na baro masarautarmu da Gata na da komai na, na zabi na zauna dashi... Amma kiga irin wulak’anci da cin kashin da yake min wanda ko kuyanga bazata d’auka ba... Daren jiya bai dawo gidan nan ba sai tsakiyar dare kuma na tabbata bai samu yanda yake so bane wajen ‘yanmatan nasa shiyasa ya dawo gareni ya sauk’e gajiyarsa da dik wani takaicinsa akaina... na tabbata da ya sami yanda yake so bazan ganshi ba sai Washe gari...wannan wace irin rayuwa ce...?” Ta k’arashe tana mai kuma share hawayenta...

Cikeda kulawa Rahima ta dafa hannayenta kana tace “Shine yai maki wannan tabon don Kinyi magana...?”
Zuhra na hawaye take jinjina mata kai, lokaci guda taci gaba da fad’in “Dama zai k’ara auren da yafi min sauk’i... Ni ba fita aiki nake ba balle hakan ya d’ibe min kewa, bana zuwa ko ina, kullum ina kulle cikin gidan nan ina cazagan bak’in cikin mijina... Shin haka auren masu sarauta yake...? Ba haka na tashi naga mahaifina nayiwa iyayena ba... Maiyasa ni zan tadda haka cikin gidan aurena...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

Sauk’e ajiyan zuciya Rahima tai kana tace “But kin tabbata biye biyen wasu matan yakeyi, kodai Kawai zarginsa kike...?”
Dubanta Ta d’anyi had’ida yin murmushi mai ciwo “Rahima kenan... Yazeed ne fah ba wani ba, wanda idan na hanasa kaina yakance yanada dubun wanda suka fini... Wllhi badon yana matuk’ar son mulkin Masarautar nan ba, nayi imani da a cikin gidana zai dinga aikata fasik’anci da matan banza, kawai yasan yin hakan ka iya shafa martabansa ne shisa...!” Ta k’arashe wasu hawayen na kuma gangaro mata....

Rahima ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “K’awata zan baki shawari, kici gaba da hak’uri wataran komai zai wuce ya zamto tarihi... Wataran macen da ya raina, Ke d’in da ya raina sai Allah ya jarabcesa akanki... Ki kwantar da hankalinki k’awata kima daina saka ma ranki damuwarsa kiji da yaranki kawai kinji koh... Kuma koda wasa kada Ki bari wannan batu ya isa Masarautar ku don kimanki ne zai zube...”

Zuhra ta jinjina kai a hankali kana tace “Na gode K’awata... Allah ya bar min Ke, zanyi dik yanda kikace in sha Allah...!”
Rahima ta murmusa kana tace “Yauwa yanzu naji batu K’awata, share hawayen ki ki kuma cancad’a kwalliya, ki nuna masa kaman ma ba’ai komai ba kinji koh...”

Zuhra ta jinjina mata kai kana ta mik’e ta fad’a bathroom dan wanke fuskarta....
Tana shigewa Rahima ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’ida kishingid’a cikin kujeran...

***

Kishingid’e suke k’asar wata ‘yar bukka dake wani b’angar a haraban Masarautar, anyi ado da kwalliya ma wajen da dardumai da kuma manyan pillows na alfarma, ko wannensu sanye cikin shiga irinta alfarma, kallo guda zakai masu su birgeka...
Yazeed, Jamal saiko Fu’ad, an K’awata gabansu da kayan marmari...
Chapter 14 · 0% Book details