Sashe 73
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yarima Mahmood ne ya katseta da fad’in “Maami kinada masaniyar cewa d’anki is a criminal... He almost raped someone’s daughter... Tir da hali irin naka Yazeed, kuma kada kaji da Wai baka sha ba ni nan zan damk’aka wa hukuma a k’watar ma wacce kaso zalinta hakkinta... Maras mutunci kawai...!!”
Giwa da duniyar Ke juye mata gaban Mahmood Ta k’araso ta rik’e hannunsa tana fad’in “So kake ka tozartamu ka b’ata Martaban gidanmu... Shin ka kuwa San abinda kake k’ok’arin yi Sadauki... Ka tab’a ganin an kira hukumar ‘yansanda cikin Fada...!”
Cikin k’unan rai yana mai girgiza kai ya katseta da fad’in “Sabida Fada ba’a gayyato hukuma shine ya baiwa mutanen cikinta dama su ci zarafin sauran Al’umma... Shin Maami ki fad’a min wata dokace ta baiwa ‘ya’yan Masarautar nan daman su ci zarafin sauran bayin Allah... Shin wannan shine mulkin adalci..? Idan har baza’a baiwa kowa dama da ‘yanci irinta mutanen cikin masarauta ba bana tunanin wannan sarauta an gina sa ne kan adalci...!”
Giwa da takaicinsa ya gama k’ulle mata mak’oshi ji take kaman ta fincikosa ta shak’esa ya mutu har lahira ko zata huta, saurin katsesa tai a hasale da fad’in “Wane adalci kake magana...? Adalcin da zai tab’a Martaban gidanku... Adalcin da zai sakaku jin kunyar duniya... Adalcin da zai zamto tozarci a gareku.. Shine kake magana Mahmood..? Ince da bakinka kace attempting yayi bai aikata ba... Toh kan wane dalili zaka Sa Jami’an tsaro su shigo har cikin Fada su kama d’an uwanka... Shin wannan shine irin sarautar da zaka gudanar Mahmood... Ka rusa Martaban Gidan nan ka wulak’anta mutuncin rawani...?! Idan har kuwa kayi hakan Ina mai tabbatar maka saidai ka nemi wata mahaifiyar amma bani ba..!!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata...
Shaye da tsananin mamaki Mahmood Ke duban mahaifiyar tasu ganin yanda b’aro b’aro ga gaskiya gabanta amma Ta zab’i ta rufe idanunta... A hankali yake girgiza kai kana ya soma fad’in “Ban tab’a tsammanin zanji haka daga bakinki ba Maami a matsayinki na shugaba ga Al’umma sannan kema mace ce Maami, na zaci ciwon d’iya mace na d’iya mace ne... Maami sanin kanki ne babu abu mafi muni da zai auku ga d’iya mace tamkar wani yaci zarafinta Ta hanyar fyad’e... Tashin hankali ne da zai rayu da ita tsawon rayuwar da zatayi a duniya...Maami fyad’e k’azamin laifi ne mafi muni wanda duk wanda zai aikata irin wannan laifi bai cancanci a kirasa d’an Adam ba don babu mutum mai hankali da yake cikin hayyacinsa da zai aikata k’azamin laifi irin fyad’e... Maami koda ace duka yaranki maza ne ya kamata ki tuna ita wacce yaso zalunta d’iyar watace... Maami kiyi tunani da ace Yazeed ya aikata laifin nan wane irin k’unci da tashin hankali Mahaifiyar yarinyar zata tsinci kanta ciki...Fyad’e k’azamin laifi ne, mummunan aiki ne wanda duk mutum mai hankali zai k’yamace shi..!”
A hasale Yazeed dake rik’eda bakinsa da jini ya b’ata ya mik’e yana fad’in “Really Your Highness... Shin laifin ka k’yamata kokuwa dai kanada wani abu ne a zuciyarka... Why can’t you just admit it already, son yarinyar kake shiyasa duk hankalinka ya tashi kake ganin kaman na rigaka saninta saurana zaka samu..!!” Ya k’arashe shu’umar murmushin nan nasa saman fuskarsa...
Mahmood dake tsananin sakin huci da yatsa ya nunasa yace “Idan ka sake magana cikin d’akin nan zan tako har wajen na kikkifa maka mari... Mutumin banza kawai, Allah ya wadaran hali irin naka...!” Ya k’arashe yana mai ficewa daga sashen gaba d’aya...
Yana ficewa Giwa ta k’arasoga Yazeed tana aika masa muguwar kallo, shid’inma muguwar kallon yake aika mata.. Tsuka yai ya mik’e sosai yana furta “What..? Ai na zaci zaki bari Mahmood ya mik’ani ga hukuma ne tinda duk kin fifitasa akanmu and especially me... Da kuwa kinyi gigin barin hakan ya kasance wllhi da na tono baya na sanar dashi wacece ta koya mana aikata laifin fyad’e tun bamu Kai haka ba...!” Yai muguwar murmushin nan nasa
Giwa tai saurin Kai hannu ta toshe bakinsa tace “So kake ahalinmu ya tarwatse...?!”
Yazeed ya fincika hannunta ya bud’e bakinsa yace “Tarwatsewa na yaushe, ga can halinda kika baro ‘ya’yanki ciki and you’re losing Mahmood too dan na tabbata bayan juya baya da kikaiwa gaskiya a yau zai wuya yaci gaba da miki irin biyayyar da yake miki a baya Gimbiya Turai... Kuma barikiji na fad’a miki muddin kikaci ba da goyon bayan Mahmood yai sarauta wllhi kinji na rantse miki sai na tono baya... Sai na sanar dashi mummunan aikin da kika sa muka aikata..!!” Ya k’arashe yana mai jifarta da muguwar kallo kana yasa kai ya fice...
Saiga Giwa tayi zaune dirshan saman gwiwoyinta hawaye na gangaro mata... Bataci ta zama ba da irin babubuwan dake faruwa da ita, dole ta ziyarci Tal’udu taji a ina ya makara tulin abubuwan nan suke faruwa da ita wanda ko ta ina babu wani sauk’i... Jakadiya ce ta shigo tana mata Fadanci dan ranta yayi sanyi amma tsawan da Ta dakama Jakadiyan ya sanyata komawa da baya babu shiri har tana karo da k’ofa... Giwa ta zube wajen sosai tana kuka da gaske ko zata samu taji sanyi cikin zuciyarta...
**
Duk yanda Yazeed zai wuce kowa idan ya dubesa saidai ya kauda fuska sabida yanda halittar fuskar tasa ta sauya, gashi babu rawani balle ya rufe fuskar tasa da ita, banda harara baya aika wa mutanen cikin Masarautar komai, wasu bayi guda biyu da suka kasa janye idanunsu daga barin dubansa ya daka masu tsawa da fad’in “What are you looking at..! Ku b’ace daga nan kafin ku rasa rayuwarku.. K’ask’antattu kawai.!!!” Ya k’arashe yana mai shigewa sashensa...
A parlor ya tadda Zuhra da Raheema suna fira irinta k’awaye...Aiko suna hangosa haka suka mik’e babu shiri... Bai tanka kowa a cikinsu ba saima kallon banza da ya rakasu dashi kana yayi hayewarsa sama....
Zuhra da Raheema suka dubi juna, Raheema tace “Zama bai ganki ba Zuhra, tashi tashi maza kije kiji abinda ya sami mijinki Ina tunanin had’arin mota ya samu...!”
Zuhra ta jinjina kai kana ta mik’e a sauri Ta haye sama d’akin Yazeed... Tana haurawa Raheema ta mik’e cikin sand’a ta waiga gefe da gefe kana ta lallab’a ta haura saman itama, daidai jikin k’ofar d’akin Yazeed ta lab’e tana sauraren tattaunawarsu...
Cikeda tsoro Zuhra ta k’arasa zata amshi ice block d’in dake nad’e cikin towel hannunsa da niyyan taimaka masa, kallon wulak’anci ya aika mata kana yace “Kika k’araso nan sai na fasa miki k’ank’aran nan akai...!”
Tai tsaye daga yanda take tana mai shanye k’uncinta, jinjina kanta tai a hankali kana tace “Naji bakaso na taimaka maka but please ka sanar dani Ina ka sami raunin nan, a matsayina na Matarka ya kamata na sani Prince, kodai had’arin mota ka samu...?!”
Murmusawa yai da gefen bakinsa kana ya shiga k’are mata kallo daga sama zuwa k’asa a gadarance, duba irinta k’ask’anci “Su matata manya..! Dan Ke matata ce sai akace sai dole kisan komai gamedani...? Kin zata dan kina matata kinada wani k’ima ko daraja a idanuna ne... Kin San mai na d’auki mata...! Abun holewa ne kawai da shak’atawa, nothing more nothing less...! So dan kina a matsayin matata hakan bai baki wani kima ko daraja a idanuna ba..Now get out of my sight..! Fita nace kafin Ranki ya b’aci...!!” Ya k’arashe cikin karaji...
Babu shiri Zuhra da tuni hawaye sun wanke mata fuska ta fice a guje tana toshe kukan da yazo bakinta gadan gadan kana Ta fad’a d’akinta tai ma k’ofar key ta haye gado tana canzan kuka...
Raheema dake mak’ale bayan k’ofa Zuhra na ficewa daga d’akin Yazeed tai wuf ta shige ta maidoda k’ofar ta rufe....
Kallo guda yai mata ya watsar yana mai ci gaba da abinda yake cikin ko in kula...
Gabansa ta k’araso ta tsaya tana huci take fad’in “You’re not a man Yazeed... How could you say those horrible things to your wife.... You disgust me..!!”
Da idanu guda yake dubanta daga sama zuwa k’asa kana yace “Did you say I disgust you..? What if I take my anger out on you..!!” Ya k’arashe yana mai zabura kaman zaiyo kanta..
Raheema tajada baya cikeda tsoro lokaci guda Yazeed ya koma ya zauna yaci gaba da abinda yake, murmushi saman fuskarsa yake furta “And the loyal best friend come to the rescue..! Ke har kinada bakin da zakiyi magana dan an wulak’anta Zuhra...Tell me duk fad’in duniyar nan akwai wanda ya wulak’anta Zuhra sama da wulak’ancin da Ke kika mata ne...?!”
Raheema ta katsesa da fad’in “Yes nasan naci amananta in the most painful way but bana goyon bayan ka wulak’anta ta ka aibata Ta, ka k’yaleta taji da cin amanarta da kake da matan banza a waje... Wait speaking of matan banza, don’t tell me garin biye biyen matan Naka ne akaji maka wannan raunin...?!”
Ya kafeta da idanu murmushi saman fuskarsa, lokaci guda ya mik’e yana takowa gabanta sosai har saida suka isa jikin gini, fuskarsu dab kusan na juna yake fad’in “Why... Why do you care..? Tell me are you jealous...?!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa...
Raheema dake sakin huci a hankali k’ak’aro murmushi tai tace “Me.. Jealous of you..? Allah ya sawak’e min Kaima kasan zuciyata na Mahmood ne shi kad’ai...!”
Wannan karon murmushi mai bayyana hak’wara Yazeed yai kana ya saita idanunsa cikin na Raheema ya kuma gyara tsayuwarsa yana mai furta “What if na sanar dake cewa Yarima Mahmood shine yaji min wannan raunin kuma ba akan kowa ba sai akan mace kaman yanda kikai zato...!”
Ta d’ago firgitattun idanunta tana dubansa a razane “Yazeed mai kake son cewa ban fahimceka ba...?!”
Yazeed ya kuma murmusawa yace “Zama ki fahimceni... Your beloved Prince is in love with another girl... Ke barin fad’a miki Mahmood bai k’aunarki coz I can see it in his eyes wannan yarinyar yake so kuma akanta ne yamin jina jina dan yana tsoron na rigashi saninta... Now that you know get out of my room kafin nima na sauk’e takaicina akanki na miki jina jina a wajen nan..!!”