Sashe 61
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mahmood yai gyaran murya kad’an daga yanda yake zaune “Haka ne Waziri, na umarce Sankira ya kirawoku gaba d’aya dan na sanar daku abindake wakana cikin Masarautar...!”
Wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan haka suka dingayi....
Suna iya hango tsagoron b’acin rai kwance saman fuskar Mahmood... Waziri ya kuma duk’awa yace “Allah shi huci zuciyan Sarki mai jiran gado...!”
Mahmood yaci gaba da fad’in “Na sani ko baku fad’i ba wasu daga cikinku zasuyi kokonton cewa ba ni ne na tura Ubandoma gidan Wambai ba sabida Ubandoma Hadimina ne..!”
Basu iya furta komai ba sai duba da ido da suke dan gizonsa bazai bari su katse zancen nasa ba...
Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Magana Ta gaskiya bani na tura Ubandoma gidan Wambai ba... Hasalima ni Mahmood banida masaniyar yayi hakan har sai bayan da aka kamashi..!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya hannayensa hard’e ta baya yayi tsayuwa irinta masu mulki..
Gaba d’aya suka shiga jinjina kai Waziri na fad’in “Wannan gaskiya ne Yarima... Kuma muna masu tabbatar maka duk mun aminta bazaka aikata wani abu mai kamada wannan ba... Dole a hukunta Ubandoma na cin amanan da yaima Masarautar nan...!”
Mahmood ya kuma yin gyaran murya cikin muryarsa mai amo wanda kana iya sauraron dirin sautin nasa na amsa babban Zauren yake ci gaba da fad’in “A daren jiya Ubandoma ya gudu daga fursunan da aka ajesa wutin gadi.... A sabida wannan zanso ku gama duk wani shawarin da zakuyi zuwa gobe a nad’a sarki a wannan masarauta namu dan bazai yuwu muyita zama haka babu shugaba ba kowa yayi abinda yakeso... Sannan dole a zak’ulo Ubandoma yanda ya shiga ya fita...!”
Rufe bakinsa Keda wuya suka sinkayo murya na fad’in “Basai kunsha wahalan neman Ubandoma ba... Gashi nan zai bayyana gabanku ya kuma fad’i wanda yake ma aiki dan hallak’a rayuwar Wambai... Sannan da akai rashin sa’a aka kamashi sai wannan mutumi ya tura a kashe Ubandoma a daren jiya... Ni ne nan na ceci rayuwar Ubandoma, da yanzu ya zama tarihi kaman yanda saura suka zama...!” Ya k’arashe yana mai k’arasowa gaban Yarima Mahmood su duka biyu suna duban idanun juna...
Yazeed ya sakar masa shu’umar murmushin nan nasa kana ya maidoda dubansaga masu sarautun gargajiya dake faman jifan juna da kallon mamaki, gyaran murya yai kad’an yana mai takowa gaba garesu cikeda k’asaita yake furta “Kuna mamaki ne...? Well, gaskiyar kenan mutumin da kuka d’auki yarda kuka d’aura masa shid’in ba mai gaskiyar bane kaman yanda duk kukai zato...”
Waziri dake faman muzurai ne gumi na kuma keto masa yai azaman katse Yazeed da fad’in “Hattara Yarima Yazeed, kasan cewa Sarki ne gaba gareka...!”
Yazeed ya watsawa Waziri jahilan kallo kana ya matso dab gaban Wazirin, ya tsaresa da idanu kaman zai magana sai kuma ya saki murmushin nan nasa... “Waziri kenan, ai a iyaka sanina ba’a nad’a Muk’amin Sarki a Masarautar nan ba tun bayan mutuwar mahaifina... Saidai kuma ban sani ba idan Kai ka nad’a... Kuma ma ka d’an dakata kad’an... Ai a iyaka sanina duk mutumin da aka kamasa da laifi mai girma irin na kisa da cin amanan masarauta bazai tab’a yin mulki ba haka nan jinjinsa bazasu tab’a gadan sarauta ba... Shin nayi gaskiya..?!” Ya k’arashe cikin sigan tambaya yana mai tsare Waziri da firgitattun idanunsa...
Waziri bai iya furta komai ba sai muzurai da yake yana k’ok’arin had’iye ragowar tuk’in goro da ya tsaya masa a mak’oshi...
Yazeed ya kaikaito cikeda iko kana yaci gaba da fad’in “Wai aka ce wak’a bakin mai ita tafi dad’in saurare... Hakimai masu daraja Zan bada izini a shigo da Ubandoma domin ya fayyace maku komai da bakinsa...!”
Lokaci guda ya dokawa Hadiminsa Hauni kira yace a shigo da Ubandoma... Ga mamakinsu sai hango Ubandoma sukai na shigowa kai a k’asa hannayensa a d’aure waje guda....
Manyan masu muk’amin cikin Fada suka ci gaba da kallon kallo suna ‘yar k’usk’us tsakaninsu... Masu aza babban gare daga zaune nayi....
Ubandoma ya k’araso ya zube a k’asa ba tareda ya iya d’ago idanu ya dubi jama’an dake wajen ba....
Yazeed yai gyaran murya kad’an yace cikeda isa “Kai muke saurare Ubandoma..!”
Zauren yai tsit gaba d’aya ana jira aji daga bakin Ubandoma wanda ko motsi k’wakk’wara bai iyayi sai had’iyan miyau da yake da k’yar....
Ganin yayi shiru ya kasa magana yasa Mahmood soma takowa gaba gareshi cikin salo irinta masu mulki... Saida ya d’ibi wasu dak’ik’ai yana duban Ubandoma dake duk’e wajen yana muzurai daga zaune kana yai gyaran murya kad’an...
“Karkaji tsoron kowa kuma kada kaji shakkan kowa... Ka sanar damu abinda Yarima Yazeed Ke k’ok’arin fad’i...!”
Zuciyar Ubandoma yaci gaba da bugawa musamman yanda ‘Yay’an Sarkin guda biyu suka sakashi gaba... A hankali ya d’ago ya saci kallon Yazeed dake ci gaba da aika masa mugun kallo lokaci guda na sakar masa wannan murmushin nasa da gefen bakinsa...
SameenaAleeyou📚[8/7, 8:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*41*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kallon ina binka bashin ceton rayuwarka da nayi Yazeed Ke aika masa... Gumi yaci gaba da tsartfsafowa Waziri, ya kasa koda duban b’angaren da Mahmood yake balle su had’a idanu, hasalima bazai iya duban cikin idanun nasa ba....
Gyaran muryar da Mahmood yai ne wanda saida ya amsa illahirin Zauren ya sanya Ubandoma k’ok’arin had’o kalamai saman harshensa....
“K’warai... K’warai Wannan gaskiya ne Yarima Yazeed shi ya ceci rayuwana a daren jiya da aka kawo min farmak’i har cikin fursuna... Badon Yarima Yazeed ba da yanzu na zama tarihi nabi sahun Wambai....!” Ya k’arashe cikin rawar jiki....
Mahmood da tinda ya soma magana ya tsaresa da idanu cikin dakewar murya yace “Baka amsa tambayar da masarauta tai maka ba Ubandoma.... Shin wanene yake baka umarni... Wanene jagoranka a wannan laifi da kuka aikata...?!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya mai amo....
Ubandoma ya kasa magana sai k’ok’arin ware idanunsa da tin bugun da Majidad’i yai masa ya sauya masu kamanni...
Ubandoma ya kasa cewa uffan sai muzurai da yake... Ya jima yana ha’intan Yarima Mahmood duk bai isheshi ba ace yanzu kuma ya k’ago babban k’arya ya lak’a masa.. Muryar Yazeed ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yai nisa ciki “Kai magana Ubandoma.. Ka fad’i waye yake baka umarni..?!” Ya k’arashe yana jifan Ubandoma da kallon Karka mance na ceci rayuwarka you owe me that one..
Ya kuma had’iyan miyau da k’yar kana ya d’ago hannayensa dake d’aure yana k’ok’arin pointing Mahmood cikin tsananin rawar jiki, hannayen nasa sai b’ari suke ya k’arashe nuna Mahmood yana mai furta “Gashi nan... Gashinan.... Shine wannan...Yarima Mahmood ne..!”
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum Mahmood ke nanatawa cikin zuciyarsa... Yayinda sauran masu muk’amin Fada suka shiga tsananin shock, sai duban juna suke cikeda tsananin mamaki....
Mahmood ya lumshe idanunsa a hankali had’ida fuzar da fuci... Ya tako gaban Ubandoma ya tsaresa sosai da idanu, kan Ubandoma a k’asa ya kasa d’agowa sai matsan k’walla yake....
Waziri ya mik’e a birkice yana sab’a babban gare ya isaga Ubandoma dake duk’e wajen yana furta “K’arya kake la’ananne bawa... Ba’a haifi Bawan da zai tozarta jinin mulki a Masarautar nan... Tsinuwar Allah ya tabbata kanka Ubandoma... Allah ya kwashe maka k’ask’antaccen bawa..!!”
D’aga hannu Mahmood yaiwa Waziri alamun dakatarwa cikin wane irin yanayi da basu tab’a ganinsa ciki ba.... Ya tako ya k’araso gaban Ubandoma... K’afafunsa dake rufe cikin bak’ak’en Lacoste cover shoe kurum Ubandoma ya gani yaji k’irjnsa yai wani irin bugawa kaman an sauk’e masa guduma...Jikinsa yaci gaba da karkarwa, ya soma yunk’urin d’ago idanu da zummar duban Mahmood saidai yana d’ago kai yai saurin maida idanunsa k’asa... Yazeed na jifansa da wane irin kallo... Take Ubandoma ya zube a wajen sunamme tun kafin Mahmood yakaiga masa magana....
Yazeed yai saurin duk’awa yana jijjiga Ubandoma lokaci guda yake cewa a kawo ruwa a yayyafa masa... Take d’akin taron ya hautsine... Waziri sai tokarinsa da k’afa yake yana fad’in suman k’arya yai ya tashi ya k’aryata abinda yace cewa Mahmood ne ya turasa gidan Wambai.... Waziri baiji bai gani sai tokarin Ubandoma yake, ta ko ina kai naushi yakewa Ubandoma dake zube wajen tamkar maras numfashi...
A fusace Yazeed ya mik’e yana sakin wane irin huci yake nunida Waziri lokaci guda yake furta “Waziri..! Idan kayi sanadin mutuwar Ubandoma a wajen nan karkaji da Wai zan zaro takobi na fille wuyanka kaima take a wajen nan..!!” Yanda yake maganar k’irjinsa na sama na k’asa idanunsa a waje zai tabbatar maka cewa tsaf zai aika abinda ya furta...
Waziri ya zaro idanu waje jin Yazeed na cewa har lahira zai kashesa muddin yayi sanadin rayuwar Ubandoma....
Take Waziri ya kifa kansa yana fad’in “Tuba nake Yarima..!”
Yazeed ya kuma watsa masa wata muguwar kallo take ya doka kirawa Hauni, babu shiri Hauni ya k’araso tareda wasu dogarai guda biyu... Yazeed yace ya d’auki Ubandoma a wuce dashi asibitin cikin Masarauta a basa kulawa na musamman...
Bayan ya gama bada wannan umarnin an kwashe Ubandoma an fice dashi ya maidoda dubansaga masu sarauta....
Gaba d’aya risinawa sukai gaba ga Yazeed saikace wani Sarki... Abin ba k’aramin dad’i yayiwa Yazeed ba ganin yanda masu muk’amin cikin Fada har sun soma basa girma tamkar an nad’asa Sarkin... Musamman da ya waiga yaga babu ko k’yallin Mahmood wajen... Murmushin nan nasa ya kuma sakewa, cikin zuciyarsa yake furta “Good... Bravo Prince Yazeed..! You actually did it... In no time zaka zama Sarkin wannan Masarauta... Burinka yana gab da cika... Kai d’in baka saka abu gaba Kaga kasawa...!!” Ya k’arashe tinanin nasa yana mai sakin muguwar murmushi lokaci guda kuma ya tsime sosai tamkar wanda ya tina wani abin....
Gyara tsayuwarsa yai had’ida yin gyaran murya ya dubi Waziri da gaba d’aya tamkar ba’a hayyacinsa yake ba kana ya kuma takowa dab gaban Waziri ya d’ibi wasu ‘yan dak’ik’ai yana duban Wazirin... Saida yai gyaran murya kad’an yace “Waziri... Na tabbata bakaso kai wasa da muk’aminka... Toh ina mai shawartanka da kai hattara kafin soyayyar da kake nunawa criminal irin Yarima Mahmood ya kaika ya baroka....!” K’asa k’asa yai maganar yanda Waziri ne kad’ai ka iya sauraro...
Waziri ya had’iyi miyau da k’yar musamman da yaga yanda Takororinsa masu Sarauta tuni kaman sun soma goyawa Yazeed baya....
**