← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 162

Sashe 122

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai bata bari ya fice ta shiga janyosa tana basa hak’uri yana fuzgewa.. Ya juyo yace “Kika kuma tab’ani wllhi zan rabza miki sandar nan kinji na rantse..!!”

Giwa na kuka taceda Waziri ya dakatar dashi yana hanasa ficewa...!

Da k’yar Waziri ya rik’o Jamal dake faman bige bige yana kuka yana fad’in ya tsani Giwa...!

Saman wata kujera Waziri ya zaunar dashi ya rik’e sandar nasa wanda babu hali yayi tafiya babu ita..

Waziri ya duk’a gaban Jamal dake ci gaba da sakin huci yana murza tafukan hannayensa sabida tsananin b’acin rai... Lokaci guda Waziri Ke furta “Jamal basai kayi gwajin k’wayoyin halitta ba dan kasan wanene mahaifinka... Kasa a ranka cewa mahaifiyarka itace k’wal d’aya taka domin kuwa tayi sadaukarwa da dama a sabida ku ‘ya’yanta...Duk abubuwan da take, duk fad’i tashin nan sabida kai da ‘yan uwanka take..!”

Cikin karaji Jamal ya katsesa da fad’in “Can’t you see she’s ruining us... Duk abubuwan da take babu wani alfanun da suka mana saima d’aid’aita rayuwarmu da sukayi... Ka gaya min cikin yaran nata wanene ya taka matakin nasara,,, Yazeed dake kwance babu hannuwa babu iyali ne..? Ko kuwa ni da nake dogarawa da wannan sandar ko Fu’ad dake kwance gadon asibiti wanda tasa muka maidasa mahaukaci da k’arfin gaske..! Ka gaya min wanene zai gaji kujeran dataci burin cikinmu..?!!” Ya k’arashe sabbin hawaye na gangaro masa..!

Waziri yace “Dukda haka dai, yanzu idan ka juya mata baya zaku tafi k’aaa tare ne gaba d’aya ko ince dukanmu gaba d’aya..!”

Giwa dake gefe tana hawaye Ta shiga jinjina a masa kai tana furta “Ni d’in mahaifiyarka ce Gwarzona, ko mai Nayi bazaka gujeni ba, domin kuwa ba’a sake mahaifiya, bamu San waye mahaifinka ba amma nid’in nice mahaifiyarka..! Jamal karka guje ni da bazan iya k’arasa yak’in nan ba tareda kai ba d’ah nah..!!” Ta k’arashe cikeda kissa tana kuka tana dafe k’afan d’an nata...

Lokaci guda Jamal yasa hannuwansa ya d’agota zaune... A hankali yake furta “What’s done is done Maami...! Naji zan tsaya tareda Ke mu k’arabs abinda kika riga kika soma... Nima ina cikin yak’in nan already...! Now that I know sarautar na namu bane zanyi komai domin naga ahalinmu basu tagayyara ba..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci da zafin zuciya...

Giwa Ta saki murmushi tana dubansa, lokaci guda take furta “Hak’ik’a kai d’in ka cika d’ah na kuma jinina..!!”

**

Iyaka jigata Umaima Ta gama yi, da k’yar da tura k’afa da nishi da komai ta samu ta janyo wayar da babban yatsarta.... Ta had’e k’afafunta tana k’ok’arin d’ago wayar zuwa hannunta, nanma wani jan aiki... Sai ta kama kaman zata iya d’aukowa sai ya fad’I k’asa... Ga dare na kumayi, k’arshe haka ta hak’ura ta maida jikinta baya tana nishin wahala da k’yar... Firgit Ta farka Ta hango hasken hantsi alamun gari ya soma wayewa.... Taci gaba da k’ok’arin d’aukan wayar da k’afafunta har Allah ya bata sa’an d’aukan wayan... Saidai tana samun nasaran d’aukar wayar taji kaman shigowarsa, zuciyarta ta yanke... Cikin Sauri ta tura wayar ta zauna bisa... Tai saurin gyaran kwanciyarta ta lumshe idanu tamkar mai bacci zuciyarta bata daina tsinkewa ba...!

K’arasowa gareta yayi ya zauna gefenta had’ida k’ura mata idanu... Yakai hannunsa a hankali yana shafa goshinta zuwa fuskarta, lokaci guda yake furta “I’m sorry my love..! Ba’a son raina na d’aureki na barki kika kwana d’aure daren da ya kamata mu rayasa cikin faranta ran juna... Please forgive me Umaima... I promise zan kula dake... Zan baki Farin ciki a gidan aurenki, zan zamto the most loving and caring husband da ko wace mace zatayi fatan samun irinsa....Dukda cewa a yau labarin rayuwana ya canza... Amma na miki alk’awari soyayyar da nake miki bazai tab’a canzawa ba..! I love you so much Umaima..!” Ya k’arashe yana mai sumbatar goshinta..!

Hawayen da take mak’alewa suka shiga gangaro mata... Lokaci guda Jamal yai k’ok’arin saita kansa yana dubanta... “My love kin tashi..! Akwai abinda kike so..! Tell me ko menene zan kawo miki..!”

Yananyin data gansa gaba d’aya kaman bashi ba harga Allah tun bayan abubuwan data gani mugun tsoronsa take.. Amma dole tasan yanda zatayi Ta kub’utar da kanta da kuma Muhibbah daga hannun wannan mahaukacin mutumin tinda har Allah ya bata Sa’an d’aukan wayar salulansa..! Dole tayi acting very smart idan tanaso Ta cimma burinta..!

Cikin rawar murya take furta “Ya Jamal meke faruwa..?! Maiyasa ka d’aureni..! Na gaji, bathroom nake son shiga dan Allah ka kwanceni kaga ko sallah banyi ba..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..!

Dubanta yayi duk a rikice sai yace “Are you sure..! Zafi kikeji da gaske.. where does it hurt.. Nuna min ina Ke miki ciwo.?!” Ya k’arashe yana kai hannunsa jikinta..

Ta had’iyi miyau da k’yar tace “Ko inama ciwo yake min a jikina... I spent the whole night like this.. Maiyasa ka d’aureni.. Ina sonka bazan tab’a gudunka ba... Please untie me..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

Kaman wanda yaji maganarta ya soma yunk’urin kwanceta, sai kuma ya dakata yana furta “No... Zaki gujeni, sabida munafukar nan Ta fad’a miki k’Arya akaina... No Umaima bazan kwanceki ba har sai na tabbata ked’in kin zama tawa gaba d’aya... Zanje na kashe wancan munafukar na dawo na d’aukeki mu bar Masarautar nan..!”

Yana ida fad’in haka ya mik’e ya nufi k’ofa...!

Aiko yana ficewa, cikin rawar jiki Umaima ta d’auko wayar ta soma k’ok’arin bud’eta Allah yasa k’aramar wayace ba’a kulle take ba... Babu lambar kowa a gidan saita Giwa cikinta, da alama Giwa kawai yake kirada layin... Ta soma tunanin bayan lambar Jamal d’in lambar waye Ta had dace a gidan..! Lambar Zahra kawai ta had dace hakan yasa ai Saurin latsa lambobin Zahra....

Zahra da tashinta kenan tana k’ok’arin shiryawa ta fito Fadar Giwa taji meke faruwa cikin Masarautar da yasa tin jiya da dare bataga kowa ba nan taga kira da bak’on lamba na shigo mata kaman bazata d’aga ba dan har Ta kusan matsewa tinda tsirarun mutane ta sani a gaba d’aya k’asar zai wahala ace wani bak’on lamba da ba na ahalin cikin gidansu ba na nemanta, sai kuma ta dai taji ta d’aga kiran... Aiko tana d’agawa ta sinkayo murya kaman ta Aunty Umaima tana fad’in “Zahra ki saurareni...!”

Zahra cikin wane irin yanayi tace “Aunty Umaima is that you..! Meke faruwa...?!”

Cikin sauti Umaima dake k’ok’arin saving chajin wayar dan ta kusan mutuwa gaba d’aya battery d’in... Nan taci gaba da fad’in “Follow your Uncle Jamal, and save Muhibbah..! Zahra don’t ask questions kawai kiyi yanda nace.. Ki bi bayansa kiga yanda ya b’oyeta and run straight to your Paa..! Ki sanar da Paa d’inki..!!” Bata ida maganar ba d’iff wayar ta katse chaji ya k’are...

Cikin rawar jiki Zahra Ke juya wayar hannunta....

Sauri sauri ta fito daga d’akin kota kan Hadimatarta dake sanar da ita abincin karin ta ya kammala bata bi ba..! Zuciyarta sai tsinkewa yake... Tana ficewa taga Masarautar babu wani mutane sosai kaman anyi shara, kodashike safiya ne sosai garin bai ida wayewa ba....

Cikin sand’a Ta fito Ta soma tafiya, zuciyarta sai bugawa yake, can kusan sashen Jamal ta hangosa ya fito cikin shiga ta kayan sanyi bak’ar riga mai hood, yanayin data gansa ciki sosai ya bata tsoro tai saurin bin bayansa kaman yanda taji Umaima tace....

Abinda ya bata mamaki shine hanyar da taga yabi mutane basu faye bin wajen ba, hasalima tamkar abandoned waje ne a cikin Masarautar... Dukda zuciyarta dake matuk’ar tsinkewa bata fasa bin bayan Jamal ba....

Tafiya mai nisa sukayi tanayi tana lab’ewa jikin Gini har dai taga ya tura wani k’ofa ya shige... Ta sad’ad’o a hankali ta nufo k’ofar da taga ya shige...!

Zuciyarta ne tayi wani irin tsinkewa sanda Ta hango Uncle d’inta Jamal tsaye gaban Muhibbah dake daure saman kujera kanta a kife a lamun takai mak’ura wajen jigata..! Akan idanunta Jamal ya d’auke Muhibbah da wata irin jahilar mari yana furta “Wake up..! Tashi munafuka it is morning already..!!”

Muhibbah ta d’ago kanta da k’yar tana k’ok’arin bud’e idanunta sukai luhu luhu dan tsananin azaba, ga wane irin tsami da jikinta Ke mata, kwana a zarge saman wannan kujera da ko motsawa baka iyawa ba k’aramin azaba bane...!

Jamal ya sakar mata murmushi yace “Good morning Beautiful..! How was your night..?! Na tabbata kinji dad’i...!”

Wayar salulansa ne da tai ringing ta katsesa..! Ganin Giwa ce mai kiransa abin ya basa mamaki dan shida ita sunada wayan da su kad’ai suke kiran juna da... Toh ina ya bar wayan... Wata zuciya tace tsakanin asibiti zuwa d’aki..

Yana d’agawa ya soma fad’in “Maami nifa van samu naje jana’izan yaran Yazeed ba, na taho direct zuwa wajen yarinyar nan..! Kuma banaso na had’u da Ya Mahmood can wajen jana’izan..!”

A hautsine Giwa tayi da fad’in “Kai Jamal ba wanne bane dalilin kiranka... Karka bar kusan yarinyar nan... Itace ta dawo..!!”

Baiji mai tace ba network ya katse cikin sauri ya fice neman service...

Hakan ya baiwa Zahra daman shigowa, a tsorace take duban Muhibbah dake zuban hawaye... Cikin rawar jiki ta isa da zummar kwance Muhibbah saidai babu hali domin kuwa da handcuffs Jamal ya d’aureta bada igiya ba babu key babu halin Ta kwanceta..! Ta d’ago a razane tana dubanta lokaci guda Muhibbah ke girgiza mata kai domin kuwa ta hango Jamal na dosowa... Take ta tuna sunyi Spanish classes da Zahra, Zahran ta koya mata wasu kalmomi daga cikin yaren... Sannan har Ta bata wani littafi na koyon yaren wanda ta tsinci wasu kalmomi ciki...

A hankali take furtada Zahra cikin Spanish “Zahra, Pon tu mano dentro de mi camisa..!” (Zahra ki saka hannunki cikin rigana.) “Papel..!” (Takarda) Zahra ta gane kalman Papel takarda yake nufi da spanish..

Muhibbah taci gaba da fad’in “No tengas miedo..!” (Karkiji tsoro)
“Solo haz lo que te digo..!” (Kiyi yanda nace)

Zahra Ta jinjina mata kai a hankali kana tayi yanda Tace dukda tana Iya jin sautin sandar Jamal a bayanta alamun ya kusa cimmata..!
Zahra ta ciro takardun Taswiran Muhibbah ta had’esu waje guda Allah yaso ruwan daka watsa mata bai jik’e cikin takardun ba sai gefe gefe...

Muhibbah Tace “Esconderlo..!” (Ki b’oye)..

Zahra Ta kuma jinjina mata kai a hankali kana tayi saurin turawa cikin rigarta...!
Chapter 122 · 0% Book details