← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 162

Sashe 38

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kwantar da murya yake fad’in “Ba nufina ba kenan Muhibbah... Nafi kowa so Ki samu adalcin da kika cancanta duk duniyar nan...!”

“Idan gaskiya kake fad’in then ka dena sare min gwiwa with your negative thoughts...!”

Ansar ya fuzar da huci, cikin b’acin rai yake furta “Ni ban hanaki aiwatar da komai ba... From the very start, I’ve done nothing but supporting you, amma abinda nakeso ki gane a nan shine dik abinda zakiyi do it the right way...think it through first Muhibbah.. Idan Ke baki damu da kanki ba wasu sun damu dake..!!”

Cikin tsananin b’acin rai take furta “You know what...! I should not have called you, you aren’t helping at all... Zanyi abuna yanda na tsara ba tareda neman shawarinka ba.. Goodnight.!!” Ta k’arashe tana mai katse kiran...

Shiru yai had’ida k’urama waje guda idanu... A hankali ya fuzar da fuci mai tsananin d’umi had’ida shafe fuskarsa da duka tafukan hannayensa biyu....

A b’angaren Muhibbah kaw zama tai dirshan saman gado tana tinanin mafita... Ita yanzu bama saka cameras a fada ba, mai zai faru idan Mahmood nada shakku da kokonto akanta ne..? Zahra..! Itace Ta fad’o ranta... Lokaci guda ta mik’e ta soma shiri kana ta nufi sashen Giwa.... Saidai a bakin k’ofan parlornsu Zahra taja ta tsaya sakamakon sauraro muryar Zahra cikin kuka tana fad’in “Paa you actually take that woman’s side..? Paa banifa na k’onata ba, bani naji mata ciwo ba... Ita da kanta taji ciwo ma kanta... and Paa...”

Cikin tsananin k’unan rai ya katseta da fad’in “Just shut up Zahra... Ban miki wannan goyon ba, rashin kunya ba d’abi’arki bane... First thing in the morning zakije ki baiwa Raheema hak’uri...sannan kiyi alk’awarin bazaki sake abinda kika aikata ba....!”

“Really now Paa... You believe that woman over your own daughter...? Paa that woman is a liar.. She is a hypocrite...”

“Zahraa..!!” Ya daka mata uban tsawa yana mai k’ok’arin d’auketa da mari... Muhibbah tai saurin shigowa ta shige tsakaninsu had’ida rungume Zahra lokaci guda take furta “I’m sorry your Highness, I didn’t mean to interfere...But please don’t hurt her she’s still a kid...!”

Tsaye kurum yai yana mai ci gaba da sakin huci, jijiyonsa sunyi rud’u rud’u sabida tsananin b’acin rai... Gaba d’aya itakam Muhibbah ma tsoro ne ya rufeta ganin yanda Mahmood ya koma lokaci guda, babu yanda Ta iya ne dole tai hakan badon haka ba da koda wasa batai gigin shigowa har ta shige tsakaninsa da Zahra ba...

Cikin tsananin huci yake nuna Zahra yatsa kaman zai magana sai kuma ya juya yasa kai ya fice daga d’akin gaba d’aya...

Zahra ta kuma shigewa jikin Muhibbah tana mai ci gaba da sakin kuka....

Muhibbah kuwa sosai ta rungumeta tana kuma lallashinta, cikin zuciyarta take ayyana cewa ko shakka babu goyon turai akaima Zahra, wannan zai bata dama ta shawo kan yarinyar cikin sauk’i ta tarwatsa mahaifinta.... Ta saki murmushi a hankali tana mai ayyana yanda Mahmood zaisha kunya ya kuma fad’i k’asa warwas a bainan jama’an sa....
Lokaci guda ta kuma janyo Zahra suka zauna saman gado tana mai furta “Is ok Zahra... Kukan nan ya isa haka, maza share hawayenki kinji koh....!”

Zahra ta d’ago tana dubanta da idanunta masu zuban hawaye lokaci guda take furta “My Paa has changed, bai tab’a d’aga min murya ba sai gashi yau har zai maren all because of that witch...!” Ta k’arashe tana mai kuma tintsirewa da wani kukan...

Bubbuga bayanta Muhibbah keyi a hankali tana fad’in “Kukan nan ya isa haka Zahra, karkiyi saurin yanke hukunci kan mahaifinki... Abinda ya fad’i maki gaskiya ne, ya kamata kije ki baiwa Raheema hak’uri.... Ba’a San d’iya Ta gari ‘yar babban gida da raina mutane ba kinji koh...!”

Da mamaki Zahra ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubanta kana tace “Kema kin zab’i kibi bayan wannan mayyar ne... Wllhi nayi imani ba tsakanida Allah take son Paa d’ina ba... I know she’s after something, sam bana son ya aureta...!” Ta k’arashe cikin rawar murya...

Dafa hannunta kad’an Muhibbah tai kana tace “I understand where you’re coming from, it’s natural for girls like you to get jealous idan mahaifinsu zai k’ara aure, ko dan taya mahaifiyarsu kishi.....Kiyima Raheema kyakkyawan zato kinji koh... Sannan kiyi kaman yanda Paa d’inki yace... Apologies to her kinji koh...And also to your Paa..!”

D’an kallon Muhibbah tai kana tace “Alright fine zanjeni amma sabida ke... Kuma tare nakeso muje...!”

Jinjina mata kai Muhibbah tai tana mai kuma dafa kanta take fad’in “Sure... Zan rakaki in sha Allah kinji koh... So ki kwantar da hankalinki....!”

Ta jinjina mata kai a hankali tana mai goge ragowar hawayenta...

Mahmood dake tsaye daga k’ofa yana saurarensu take yaji wane irin sanyi cen k’asar zuciyarsa, ji yake Zahra na cikin aminci muddin tana tareda Muhibbah... Can k’asar zuciyarsa yakejin kwanciyar hankali da tarrayan Muhibbah da kuma Zahra, bugu da k’ari wannan kyawawan shawari da Muhibbah ke bata su suka cancanci yarinya mai shekaru irin nata... Take tinanin matarsa Aliya ya fad’o masa, tabbas ko wace uwa wannan shekarun take jiyewa d’iyarta, wannan dangerous stage ne a rayuwa da yake buk’atan taka tsantsan, shekarun teenage... Idan har Muhibbah zata kasance da d’iyarsa a haka baida haufin cewa zai sami kwanciyar hankali da yin hakan... Ya saki murmushi mai taushi a hankali kana yasa kai ya fice...

Muhibbah dake satan kallon bakin k’ofan da wutsiyar idanunta murmushi Ta saki a hankali don ko babu komai tasan kwalliya ta biya kud’in sabulu, tarkonta ya d’anu.. Ta sami yardar Yarima Mahmood... Yanzu next move d’inta shine maganan dasa camera...! Taita faman sak’e sak’e cikin zuciyarta tana neman hanyar da zata b’ullowa Al’amarin...

Mutum guda ne ya fad’o zuciyarta Yazeed...! Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai ayyanawa cikin zuciyarta... Tabbas Yazeed ne kawai zai kawo cikas a wannan shiri na dasa na’urorin d’aukan hoto masu motsi cikin gidan....!
Da wannan shiri ta Kwana cikin zuciyarta da niyyan Washe gari zatai k’ok’ari ta riga Mahmood making move...

Sam Zahra bata bari Muhibbah ta koma cen masauk’inta ba, haka taita mata magiya saida suka kwana tare... Ko shakka babu SHAK’UWA CE mai tsafta ke shiga tsakaninsu a hankali....

Washe gari bayan Muhibbah ta nufi sashenta ta shirya dawowa tai ta jira har Zahra ta farka bayan ta sad’ad’a asibahin fari ta ajiye likankken takarda mai d’aukeda rubutu jikin k’ofar motar Yazeed yanda dole a gani... Koda ta ijiye takardan successfully murmushi ta saki a hankali tana mai furta “You’re the only person that can ruin his plan... After all kud’in baku jituwa.. Hakan dalili ne na kuma tarwatsa tsakaninku...Da sannu zaku rasa mulkin Masarautar nan gaba d’ayanku sannan ku fice a Masarautar cikin k’ask’anci da d’ibewa juna albarka....!” Tana ida fad’in haka tai saurin gyara alkyabbarta Ta rufe fuskarta kana ta fice daga wajen gaba d’aya...

Koda ta shigo duba Zahra nan Ta makara wajen taya Zahra shiryawa, daidaida kayan da Zahra zata saka Muhibbah ce ta tayata zab’e.... Gaba d’aya yarinyar ta cika da farin ciki gwanin ban sha’awa... A haka Umaima ta shigo ta taddasu tana mamakin yanda Sabo mai k’arfi ya shige tsakanin Zahra da Muhibbah lokaci guda, hakan sosai yaiwa Umaima dad’i ko dan ganin Zahra cikin Farin ciki bayan rasa mahaifiyarta da yarinyar tai... Dik mai k’aunar Zahra dole yaji dad’in kasancewar Muhibbah cikin Masarautar domin kaw ta maidowa yarinyar wani b’angare na Farin ciki data rasa sakamakon rashin mahaifiyarta da tai... Su duka ukun sukai karin kumallo Umaima Zahra da kuma Muhibbah a nan parlorn su Umaimar.... Idan ka gansu yanda suke gudanar da al’amransu del su birgeka... Muhibbah sai saka masu chapter take suna darawa kaman ba gidan sarauta ba, sosai suka baje suna jin dad’in moment d’in....

Giwa da Jakadiya ne suka taho zasu shige nan suka sinkayo hayaniyar su Zahra... Giwa ta dubi Jakadiya da alaman tambaya saman fuskarta...

Jakadiya tai gyaran murya tana mai furta “Allah shi baki yawan rai ai wannan yarinya bak’uwa da akai a masarauta mai suna Muhibbah itace ta dawowa Gimbiya Zahra’u da Farin cikin data rasa...!” Ta k’arashe tana mai kuma jinjinaga shugaban tata...

Giwa tai shiru tamkar mai nazari kana ta jinjina kai tace “K’warai yarinyar tanada saurin shiga zuciya banga laifin Zahra’u ba... Hakan zai kyau idan har zata zamto mai d’ebewa yarinyar kewa...!” Ta k’arashe k’asaitaccen murmushi saman fuskarta lokaci guda ta nufi parlorn su Umaima Jakadiya na biyeda ita...

Muhibbah ce ta soma hango Giwa tai saurin mik’ewa alamun girmamawa kana ta risina tana kwasan gaisuwa had’ida kambaba Giwa...

Giwa ta saki murmushin jin dad’i sanda su Umaima da Zahra sukai kaman yanda Muhibbah tai, abin sai ya kuma birge Giwa, tana matuk’ar son girma.. Tana son mutumin da zai bata girma ya kuma aza mata k’asa sam bata lamuntan raini shisa ba ko yaushe tasu ke zuwa d’aya da Raheema ba.... Sosai taji dad’i har k’asan zuciyarta tana mamakin yanda Muhibbah ta k’ware wajen koyi da d’abi’u da al’adun babban gida...

Daga Umaima har Zahra mamaki suke yau Giwa ce ta shigo har parlornsu, ita kaw Jakadiya sam zuciyarta bata aminta da wannan k’auna da Giwa ke nunawa Muhibbah ba yarinyar da sam basu wani San tushenta da asalinta ba, ita dai sam zuciyarta bai kwanta da yarinyar ba musamman ganin yanda zuciyar Giwa dana yarinyar suka had’e waje guda tun daga had’uwar fari...

Kaman daga sama suka sinkayo muryar Yarima Yazeed yana dokawa Jakadiya kira dik Kuyangin dake bisa hanya k’arewa suke suna kwasan gaisuwa wajen Yazeed...Jakadiya ta dubi Uwargijiyarta kana tai mata izini ta hanyar jinjina kai....

A hanyar matakala Jakadiya ta iske Yarima Yazeed, tai saurin zubewa tana kwasan gaisuwa...

“Jakadiya ina Maibabban d’aki...?!” Yai tambayar a hasale...

Jakadiya ta kuma risinawa zatai magana sai muryar Giwa suka sinkaya tana fad’in “Yazeed mai kake nema da safiyar nan....?!”

A cen parlorn su Umaima kaw tinda Muhibbah taji Yazeed na neman Jakadiya tasan tarkonta ne ya d’anu dan haka murmushin jin dad’i kurum ta saki tana mai tiniwa Zahra cewa anjima kad’an zasuje sashen Gimbiya Zeenatu domin neman afuwan Raheema...

**

Yazeed na matuk’ar huci yake furta “Your beloved Son, the perfect one among us all yana nema ya b’ata al’adun gidan nan tun kafin ya hau mulki...!”
Chapter 38 · 0% Book details