← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 162

Sashe 93

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigewan Muhibbah da kad’an Ansar ya shigo gidan ya taddasu Mommy nan a parlorn suna ci gaba da sorting kayayyakin... Aunty Salamatu Ke zolayarsa da fad’in angon wani sati ita kaw Aunty Gudidi sai yatsina baki kurum take dan Allah ya gani bata fata ayi wannan aure, ita da zata samu sarari ma zata kuma ziga Yawale koda wasa kada ya biyewa Murjanatu na aurawa d’an d’an uwansa tsinatcciyar mage...

Aunty Salame ke sanar dashi Muhibbah ta dawo tana ciki... Ai tuni ya mik’e yana sosa kai tana ci gaba da zolayarsa mai tagwayen mata...

Silalewa yai ya nufi corridor, yana k’ok’arin knocking kenan Ta bud’e k’ofar alamun zata fito... Sukai tsaye suna duban juna, sosai shigar manyan kayan ya amshesa dashike ba gwanin saka manyan kayan bane.... Tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi kana Ta matsa Ta basa hanya ya shigo... Daga can gefe ta zauna Shiko na tsaye jikin k’ofa, Muhibbah ta gaishesa babu wani walwala tattareda ita... Harga Allah kalaman Aunty Gudidi ya tsaya mata a rai, sai tana jin tabbas Ansar bai cancanceta ba...

Gyara tsayuwarsa yai yana mai tsareta da idanu “Mun d’aura auren k’awarku Azeema yau wata sati kuma a d’aura naki...!”

D’an Murmusawa tai tace “Aw Wai dama auren Azeema ake..?!”

Ansar ya jinjina kai yace “Eh Musbahu ya zama Ango...”

Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Allah sarki, Allah yasa albarka... Ai Azeema da Musbahu sun dace da juna..!”

(Azeema da Musbahu dukansu ‘yan Estate d’in ne kuma Musbahu aminin Ansar ne Azeema kuma islamiyansu guda dasu Muhibbah.. Taron aurensu Muhibbah ta tadda..)

Ganin yanayinta yasa Ansar d’an nusawa yace “Kema Rana itiyau an d’aureki...!”

Ta d’an dubesa da mamaki tace “Next week fah kake magana..?!”

Ansar ya jinjina kai yace “Bakiga su Mommy a parlorn suna had’a lefe ba..”

Ta jinjina kai a hankali tace “Na gani... Amma sai inaga next week kaman yayi kusa...!”

Ansar ya d’an tako kad’an ya jinginu jikin dressing mirror yana mai karantar ta “Mai yasa zakice yayi kusa bayan cikan burinmu kenan mu kasance tare...”

Gyara zamanta tai tana mai duban wani b’angaren, lokaci guda Ta fuzar da fuci a hankali tace “Ba haka nake nufi ba, ai inaga aure yana buk’atan shiri balle ma Amarya wacce aka santa da wasu ‘yan kintse kintse...!”

Yana murmushi ya furta “Relax Amarya Ta to be, Baffah Yawale ne ya matsa a d’aura auren gaba d’aya next week tarewa Mommy tace ba yanzu ba sai ta gama shirin bukinta, kinga auren kawai za’a d’aura ba wai tarewa zakiyi yanzu ba... Nima gidan nawa akwai fittings da ba’a gama ba, Ki kwantar da hankalinki kina nan tareda Mommy har nan da wata guda... Ku gama duk wani shirye shiryenku da zakuyi Keda Mommy, wata guda ai ya isheku..!”

Ta murmusa kad’an har lokacin babu walwala tattareda ita... Gyaran murya yai kad’an yace “Hibbah kalleni nan..!”

Ta d’ago idanunta masu rauni tana dubansa “Maiyasa nake ganinki haka..? Ko baki Farin ciki ne..?!”

Hawayen da ya gangaro mata tasa hannu Ta share, lokaci guda take furta “Ba haka bane Yaya Dr, gani nake kaman baka cancanceni ba... Kar ka mance Mommy batada masaniyan gaskiyar abinda ya sameni, idan nayi shiru na aureka a haka Anya na kyautawa Mommy..? Kai d’aya ne d’anta.. Mommy Ta cancanci sanin komai kafin aurenmu..!”

K’arasowa yai ya d’an duk’a gabanta yana kallon yanda hawaye ke gangaro mata... Lokaci guda yake girgiza kai “Hibbah no... Ba lallai sai Mommy tasan abinda ya sameki ba, ni ne zan zama mijinki kuma naji na gani nayi accepting d’inki yanda kike... I don’t care if you’re a rape victim... Ba son ranki bane hakan ya faru dake, Maiyasa zan k’yamaceki bayan nasan k’addara na kan kowa... Su wad’anda suka aikata laifin sune ya kamata suji kunya... Hibbah I...!”

Cikin kuka Ta katsesa da fad’in “Kana fad’a min haka ne dan naji sanyi a zuciyata... Amma bazan tab’a zama kaman ko wacce mace ba... Sun cuceni Sun zalunceni Sun d’auke min abinda yafi komai mahimmanci da daraja a gareni... Ansar ko baka fad’a min ba nasan dole can k’asan zuciyarka kana jin zafin abin... Maza har Uku sun lalata rayuwar macen da zaka aura lokaci guda..!!”

Daidai nan Anty Gudidi Ta shigo tana tafe hannaye had’ida salallami “Na shiga uku ni Gudidi mai nake ji... Maza har uku, d’aya biyu uku... Sauransu zaka aura Ansar... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Yau na shiga uku ni Gudidi ka kaita ina... Wllhi Allah ya tsari gatari da saran shuka..!!”

Ansar ya tareta da fad’in “Aunty ki dakata, ki saurareni..!”

Bata dakata d’in ba sai ci gaba da tafe hannaye take tana salallami tana doka kira wa Mommy “Murjah..! Murjah!! Na shiga uku ni Gudidi Toh kizo kiji abinda nakeji a nan..!!”

Daidai sanda Mommy da Aunty Salame suka k’araso a firgice suna tambayan Gudidi meke faruwa...

Nuni tai masu da Muhibbah dake zaune saman stool kanta kife tana hawaye Ansar tsaye gefe idanunsa sunyi jazir yana aikama Gudidi muguwar kallo..

Mommy tace “Gudidi meke faruwa kike salati haka kaman anyi rashi..!”

“Yo ba gwara mutuwa ba da abinda naji... Gata nan Munafuka ta bud’e baki ta fad’i maki... Ta wane sinne kai zatai rufa rufa Ta aure miki d’ah..!”

Ansar ne ya katseta da fad’in “Ya isa haka Aunty... Bai kamata Ki saka Muhibbah gaba kina aibatata ba... Babu abinda ta miki na aibu..!”

“Kai rufe min baki shashasha.. Wannan ai aurenta da kake k’ok’arin yi shine babban aibu... Ace namiji ba d’aya ba ba biyu ba har uku sun gama watsewarsu da ita kai kuma da yake hidahumi ne shashasha zaka yarda ka aureta a haka har kana wani cewa ba son ranta bane..!”

Cikin tsananin k’unan rai Ansar ke fad’in “Eh Aunty I don’t care idan duka mazan duniyar nan ne suka lalata mata rayuwa sabida ba laifinta bane, itama bata tab’a fatan hakan ya faru da ita ba... Akan mai za’a dinga nuna k’yama da tsangwama ga wad’anda tsautsayi da k’addarar fyad’e ya auka masu.. Shin son ransu ne..? Shin suma bazasuyi fatan su kasance kaman ko wacce mace bane..? Aunty rape victims sunada ‘yanci da zasu rayu kaman ko wata mace a fad’in duniyar nan.. Tunanin k’yama da tsangwama da zasu fuskanta tsakanin Al’umma shi yake jefa da yawa cikinsu cikin hali na ha’ula’i wasu a garin haka har kashe kansu suke sabida tsoron tsangwama daga sauran mutane... Maiyasa baza’a jasu jiki ba a nuna masu cewa rayuwa bata k’are masu ba... Zasu iya samun Farin ciki kaman ko wata mace.. Instead ki tsaya a nan kina aibata Ta a matsayinki na matar cikakken Alk’ali da taimakawa kikayi aka capke wad’anda suka aikata laifin, dan rashin hukuntasu shi zaisa gobe su kuma..!”

Mommy Ta katsesa da fad’in “Ansar Wai maganan da nakeji gaskiya ne..?! Kenan Muhibbah tai mana k’arya da tace b’arayin daji Sun halak’a ahalinta...?!”

Ansar ya d’an fuzar da huci yana shafa kansa yace “Mommy Ki tsaya kiji I’ll explain everything..!”

Girgiza kai Mommy tai tace “Shikenan kuma ai... Kasan ni bana son mak’aryaci ko yaya ne... Balle yanda naji kana maganan fyad’e kenan Allah kad’ai yasan B’arayin daji nawa ne sukai mu’amala da ita..!”

Anty Gudidi tace “Alhamdulillah abinda nake nufi kenan... Ta yaya zaki bari d’anki k’waya d’aya tol a duniyar nan ya auri wannan abar.... Wayasan mai wad’ancan kmazaman b’arayin dajin suka gama yi da ita kawai d’anki yazo ya kwashi ragowarsu... Wllhi Allah ya sawwak’e wannan ai sai ki zama abin nunawa tsakanin k’awaye...!”

Mommy na tsananin huci take duban Muhibbah dake duk’e a wajen tana sharb’an kuka mai tsuma zuciya....

“Ke.. D’ago ki kalleni dan daga yanzu bazan kuma kiranki da sunan Muhibbah ba... Allah kad’ai yasan menene asalin sunanki da abubuwan da kike b’oyewa... Na rik’eki da zuciya d’aya ashe Ke ba haka kika d’aukemu ba.. Kin b’oye mana wannan babban al’amari... Toh kiji da Wai d’ah na bazai auri mace irinki ba...!!”

Muhibbah ta d’ago a firgice tana duban Momy da idanunta masu zuban ruwa... Ko saurarenta Mommy bata tsayayi ba tasa kai Ta fice daga d’akin a tsananin fusace yayinda k’awayenta suka take mata baya... Ansar yai saurin bin bayanta yana ambato sunanta inaa ko tsayawa batai ba.... Muhibbah kaw tana ganin sun fice Ta maida k’ofan d’akin Ta silale a wajen tana cazgan kuka mai tsuma zuciya...

Ansar ya dawo yana bubbuga k’ofar inaa bata bud’e ba sai ma shesshek’an kuka da take...

**

A can Masarauta kuwa daren jiya kusan gaba d’aya mafarkai ya dingayi sarara marassa kan gado... Mafarkinsa na k’arshe ne ya tsaya masa a rai yanda suke tsaye shida ita cikin Babban Zauren ajiya na masarauta... Su duka biyu Suna rik’e da wannan Taswiran ya rik’e b’angare guda itama ta rik’e b’angare guda, kowa a cikinsu yana so ya amshe Taswiran daga hannun d’an uwansa ga Wambai daga gefe yana sakin murmushi yana kallon kokawan k’wace wannan Taswiran da Mahmood keyi hannun Muhibbah... Dik k’ok’arin Mahmood ganin ya amshe wannan Taswiran daga hannunta bai iya amshewa ba dukda cewa ya dage k’arfinsa gaba d’aya... Yana juyawa yana kallon Wambai yana cewa ya taimakesa kada ta gudu da Taswiran, Wambai sai murmushi yake masa lokaci guda yana cewa ya bita duk nisan duniyar da zatai itace zata zamto fitilar haska masa duhun dake gaba garesa... Haka ya dinga binta a guje har ta shige wani k’ofar... K’ofar tana gab da rufewa ya isa ya saka hannayensa duka biyu yana k’ok’arin janyota yana son k’wace wannan Taswiran amma bata sakar masa ba... K’iris ya rage k’ofar bai rufe ba ya farka daga baccin...!

Shafe Fuskarsa yai da duka hannayensa biyu daidai lokacin da sallaman Zahra ya daki dodon kunnuwarsa...

Zahra ta bisa da kallon mamaki dan bakinta na uku kenan tana sallama mahaifin nata baiji ba....

Ta k’arasa ta zauna daga can kusan k’afafunsa, Ta risina tana gaidashi...

Saida ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ya amsa mata...

Zahra Ta d’an muskuta tace “Paa are you alright..? You seem deep in thoughts...!!”

K’uri yai mata sai kuma ya nusa kad’an ya kirawo sunanta da siga mai firgitarwa...

Zahra ta d’ago a d’an tsorace tana dubansa “Paa..!”

Mahmood yaci gaba da fad’in “Tell me what really happened, kuma kada kimin k’arya...!!”
Chapter 93 · 0% Book details