← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 162

Sashe 1

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

 *MUHIBBA*

*001*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Daga yanda take zaune cikin mota tana iya hango dogon ginin gidan, gidan da ko ba’ace ba Kai tsaye zaka kirasa da gidan sarauta sabida yanda aka tsara ginin ga kyau ga girma had’ida tsawon gini.... A iyaka shekarun da tai bataga gidan ba tabbas ba wani abu muhimmi da ya canzu da tsarin ginin gidan saiko fenti da abinda ba’a rasa ba... Idan bata b’ata lissafi ba yau shekaru ak’alla goma sha biyar kenan rabonta da wann masarauta mai bak’in tarihi a gareta... Shin ta yaya ma zata mance shekarun, bacin dik wani iftila’in rayuwa da gwawarmaya data fuskanta wannan Masarauta shine sila... Masarautar dake tafe da K’ADDARAR rayuwarta a cikinta, Masarautar da ta canza labarin rayuwarta, Masarautar da take tamkar Kurkuku a idanunta, Masarautar da aka ginata kan mulkin zalinci a zahiri kuma ana rud’in mutane da yaudararsu da kyawawan d’abi’u na k’arya... Masarautar da babu tausayi balle jin k’ai cikinta....

Lokaci guda Ta saka bayan hannunta Ta goge hawayen da suka d’igo mata.... Matashin saurayi dake zaune gefenta wanda a k’alla bazai gaza shekaru 30 a duniya ba, girgiza kansa yai kad’an had’ida fuzar da huci a hankali.... Lokaci guda yake furta “HIBBAH da zaki bi shawarina Ki janye wannan k’udiri naki, Ki mance komai ki fawallawa Allah lamuranki da sannu zai saka miki, na tabbata bayan abinda suka miki Keda iyayenki Allah bazai barsu ba, Wllhi sai ya saka maku... So please Ki janye wannan k’udiri naki...Mulkin duniya bamai dawwama bane suma wataran zasu tafi yanda mahaifanki suka tafi... So please ki janye wannan k’udiri naki....!”Ya k’arashe cikeda kulawa.....

Murmushi mai ciwo budurwar mai kimani shekaru 29 tai kana tace “Ansar wllhi wllhi bazan janye k’udirina ba... Wllhi sai na tozarta su a idon duniya... Sai na ruguza mulkin zalunci da sukeyi... Sai na nunawa duniya su wasu irin mutane ne... Wllhi bazan barsu haka nan ba, yanzu ne daidai lokacin da ya kamata na dawo, daidai lokacin da suka rasa mahaifinsu, na tabbata yanzu ne zasu soma yak’in neman mulki ni kuma zanyi amfani da wannan daman...!” Cikin tsananin karaji tai maganar tana mai duban Ansar kana ta maida dubantaga ginin masarautar, lokaci guda ta kuma sakin murmushi mai ciwo kana ta soma fad’in “Iyalan Sarki AbdulJabbar na dawo gareku, saidai wann karon ban dawo a matsayin Saudatu ba, bak’ar yarinya mummuna abin wulak’antawa...MUHIBBAH, a matsayin Muhibbah na dawo, abar soyuwa a gareku... Ku yi shirin tarban rugujewarku, k’uncinku da kuma tashin hankalinku... Zan zame maku musiba da annoba, zan zamto yunwarku na kuma zamto abincinku, kaman yanda zan zamto k’ishin ruwanku na zame maku ruwan shanku.... I’ll take you down to the ground, all of you... D’aya bayan d’aya... Wllhi sai na jefaku cikin tashin hankali had’ida k’uncin rayuwa fiyeda yanda kuka jefa nawa da na iyayena ciki... Wllhi sai na tarwatsaku da duk wani mulki da sarauta da kuke tak’ama dashi.... Alk’awari ne..!!!” Ta k’arashe tana mai kuma yarfe wasu hawayen da suka zubo mata....

Suna nan zaune cikin mota daga cen gefen kwalta yanda Ansar yai parking suka soma jiyo sautin siren... Gaba d’aya Unguwar ya d’auka da k’uwa sai kaucewa ake ana bada hanya, kana iya hango motoci na alfarma sun doso babban gate d’in Fadar, ko wata mota d’auke take da lambar Jos Emirate Council.... Ga wani zabgegen mutumi da jajayen kaya irinta dogarai ya zarkwad’o tuk’ek’iyar dorina daga waje yana korin mutane yana fad’in Ku gafara ‘ya’yan talakawa... Yarima MAI JIRAN GADO ya iso mahaifarsa.....”

Duban Ansar tai kana ta maimaita abinda bafajen nan yake fad’i...
“YARIMA MAI JIRAN GADO...?” Tai maganar d’aukeda alaman tambaya...

Jinjina mata kai Ansar yai kana yace “From what I heard, yau ake saka ran isowar Babban d’an Sarki AbdulJabbar mai rasuwa, Wato Yarima MAHMOOD AbdulJabbar Mahmood... Shine babba cikin yaran Sarkin, da alama ya iso kenan daman yau ake saka ran dawowarsa daga K’asar Spain cen Madrid....”

Katsesa tai da fad’in “Na riga nasan shine Babba cikin asararrun yaran Sarki AbdulJabbar, saidai tambayar da zan maka Wai dama dik tsawon shekarun nan baya k’asar nan...?”

Fuzar da iska kad’an Ansar yai kana yace “K’warai baya k’asar nan, kuma na tabbata rikicin karb’an Mulkin gidansu ya sanyashi dawowa don ba don haka ba, Yarima Mahmood bazai tab’a dawowa Nigeria ba, shekarunsa kusan goma sha biyar kenan a turai...”

Gabanta ya yanke ya fad’i lokaci guda.... D’agowa tai tana kuma duban Ansar dake ci gaba da kwararo mata bayani kana ta dakatar dashi da fad’in “Wait, kace shekara sha biyar baya Nigeria...?”

Jinjina mata kai yai kana yace “K’warai shekaru goma sha biyar baya Nigeria, yana cen k’asar Spain tareda marigayiyar matarsa da d’iyarsa mai kimanin shekaru goma sha hud’u..”

Muhibbah Ta kuma katsesa da fad’in “Marigayiyar Matarsa...?”

Amsar ya jinjina kai yace “Shekara guda kenan da rashin matarsa da yayi, ‘Yar k’asar nan ne saidai daga yanda naji labari ita matar tasa d’iyar talakawa ce ba d’iyar masu mulki ko sarauta ba, hasalima tsangwamar matar tasa da iyayensa sukai ya sanyashi yanke shawarin barin k’asar da iyalinsa gaba d’aya, a nan Nigeria ya aureta suka tafi Spain tare, Allah ya albarkacesu da yarinya k’wara d’aya mace, and last year sunzo Nigeria sai tsintar gawarta akai a cikin d’aki har yau ba’a San cause na mutuwarta ba, ba’a San mai ya kasheta ba, kawai dai gawarta aka tsinta a d’aki .... Bayan watanni kad’an ya kuma rasa mahaifinsa Sarki AbdulJabbar the same shekaran da ya rasa matarsa Gimbiya Aliya, shekaran ta zamto shekarar k’unci ga Yarima Mahmood, toh tin daga nan ya d’auki d’iyarsa suka koma k’asar Spain bai kuma lek’o Nigeria ba sai yanzu da batun mik’a Mulki ya taso... Kaman yanda kika sani Sarki AbdulJabbar yanada k’anne ‘yan Uba wanda suma harin wannan kujera ta sarauta suke... And na tabbata Hajiya Turai Giwar Sarki AbdulJabbar bazata tab’a bari sarautan nan ya subce daga hannun yaranta ba....”

Ambato Hajiya Turai da yai ya kuma sanyata jin wani irin tuya a k’irjinta tamkar ana barbad’a garwashin wuta....

A hankali ta furta “Ya isa haka banson jin labarinsu, balle sunayensu....”

Ansar ya d’an dubeta a kaikaice kana ya girgiza kai yace “Kuma a hakan kike cewa kin shirya rayuwa cikin masarautarsu... Tell me Hibbah, Ta yaya zaki fuskanci mutanen da ko sunayensu baki sonji balle har kiyi rayuwa taredasu under same roof, Hibbah na rok’i arzikin ki Dan Allah Ki janye k’udirinki, let’s focus on our relationship please...” Ya k’arashe cikin marairaice mata murya....

Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Doc, please not now... Dan Allah kamin wnn alfarmar, ka barni na cika burina, na tarwatsa ahalin Sarki AbdulJabbar kaman yanda suka tarwatsa nawa ahalin, nai maka alk’awari da zaran na cika wannan buri nawa, zan sanar da Mummy da kaina a saka mana rana.... Nidai kawai babban taimako da zaka min shine ka shigar dani wannan masarauta na sami gurbin zama cikinta....!”
Yanda tai maganar ya sanyashi d’an dubanta kad’an kana yace “Naji, zan shigar dake Masarautar nan, zaki sami gurbin zama cikinta, amma da sharad’i....”

D’agowa Ta d’anyi had’ida dubansa kad’an kana tace “Mecece sharad’in...?”

Ansar ya d’an daidaita zamansa kad’an kana yace “Nurse, sharad’ina shine randa na kawoki Masarautar nan zaki sanar dani abinda Iyalan Marigayi Sarki AbdulJabbar suka miki da har kike yunk’urin tarwatsa tsakaninsu....”

Gabanta ya yanke ya fad’i, ta sani tina wannan bak’in labari na nufin tashin hankalinta ne, amma batada zab’i idan har hakan zaisa Ansar ya shigar da ita wannan masarauta toh zata tuno baya, za kuma ta waiwayi bak’in shafin rayuwarta da a kullum idan Ta bud’esa sai ta shiga matsanan cin tashin hankali domin kaw duk wani k’uncinta daga nan ya soma....

Ansar ya katse mata tinaninta da fad’in “Do we have a deal...?”

K’ak’aro murmushi tai kana Ta jinjina masa kai a hankali kana tace “Zan sanar daki My Dr....!”

Murmushi yai a hankali kana yayi key wa motar yana fad’in “Ya kamata mu d’auki hanyar Bauchi kafin Mummy Ta soma kiranmu....”

Muhibbah Ta d’an murmusa a hankali itama kana tace “I’m sure inada missed calls d’inta ma Dan wayata throughout kashe take...”

Jinjina kai yai idanunsa naga kwalta yake fad’in “Kunfi kusa ai, though idan anyi dare fad’an wa ni za’ai dukda cewa Kece na kawo Ki rubuta jarabawa...”

D’an b’ata fuska tai kad’an kana tace “Naji dai, Babu mai shiga tsakaninmu da Mummy ta...”

Murmushi yai wnn karon kana suka d’auki hanyar Bauchi....

***

JOS(FADA)

Zaratan mazaje ne guda Uku tsartsaye a bakin Kamfacecen parlor na alfarma, ko wannensu sanye cikin shiga irinta mulki da sarauta, rigar Kufta da wandonta harmada da hula da takalmi, Dik yanda mazaje masu kyau suke wad’annan mazaje zasu amsa sunan... Hannayensu hard’e suna duban Mutumin dake k’arasowa garesu mai tsananin kamanni dasu saidai shi ya d’ara masu a shekaru, hannunsa na dama rik’e da hannun matashiyar budurwa mai kimanin shekaru 14 da suke tafe tare... Fadawa kuwa sai ci gaba da kod’asa suke suna wasashi....
_Allah ya yika Sarki... Mahamuda jikan Mahamuda, Dan na gada kafi Dan na koya... Allah ya baka gidanku, Mahamuda yayi sarauta Mahamuda zai kuma yi... Gaba salamun baya salamun, Allah yaja zamanin Sarki Mai jiran gado..._

Ire iren kirarin da suke masa kenan... Biyu daga cikin samarukan nan masu jiran k’arasowarsa murmushi ne fal fuskokinsu yayinda guda d’aya ya had’e Rai tamkar yaga ajalinsa, dan kirarin nan da Fadawa keyi jinsa yake tamkar ana yaryafa masa narkarkiyar dalma cikin k’irjinsa....

_Tafiya mai cikeda sark’ak’iya, rud’ani, tausayi, Fansa, sadaukarwa had’ida soyayya_

SameenaAleeyou📚
[5/20, 10:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*002*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 1 · 0% Book details