Sashe 65
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babban Zauren taro ya cika fam da masu sarauta... Yazeed ya k’araso gaban Fu’ad dake binsa da muguwar kallo tun shigowarsa, murmushin nan nasa ya saki da gefen baki, yayi tsayuwa irinta masu ji a Mulki gaban Fu’ad, hannayensa hard’e yake dubansa kana yai gyaran murya kad’an yace “Aren’t you gonna congratulate me little brother... Ko har yanzu kana shakkun ni ne nan zan zama Sarki...?!”
Fu’ad ya d’an murmusa had’ida shafe fuskarsa da tafukan hannunsa biyu wanda yin hakan d’abi’arsa ce, ya k’arewa Yazeed kallo daga sama zuwa k’asa ya d’an kauda kai gefe yana kuma sakin murmushi yace “Ai banga Sarkin ba balle nai maka murna... B’ata lokacinka kawai kake don na tabbata kai d’in har abada bazaka tab’a zama Sarki ba muddin za’a bi cancanta da kuma dacewa...!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya...
Yazeed ya kai k’ololuwar b’acin rai... Sai faman sakin huci yake yana tururi yake duban Fu’ad ji yake tamkar ya kai masa naushi sai faman dunk’ule hannunsa yake... Bazai iya jure kalaman Fu’ad ba... Ya yunk’ura zai kai mai naushi Jamal dake gefe yai saurin rik’esa a hankali yake furta “Don’t make a scene here please Yazeed..!”
Fu’ad na murmushi yake fad’in “Barshi... Please do it... Go ahead, do it Yazeed... Ka nuna musu asalin kaid’in ba wanda kake faking ba... Just do it...!” Ya k’arashe cikin huci....
Jamal ya janye Fu’ad yana fad’in “Ya isa haka Fu’ad, karku bamu kunya dan Allah... Martaban gidanmu zaku tab’a...!” Fu’ad ya d’an dubi Jamal had’ida fincike hannunsa ya koma gefe ya zauna yana sakin huci dan dukansu biyu da Yazeed d’in har Jamal d’in haushi suke basa idan ya tuna tilasta masa da sukai ya aikata laifin da har yau yake danasanin aikatawa tsawon rayuwarsa.. Laifin da ya zama silan rugujewar rayuwarsa da Farin cikinsa....
Yazeed kaw k’arasawa yai yana ci gaba da taku cikin babban Zauren masu muk’amin cikin Fada na kawo masa caffa (Gaisuwa irinta masu mulki) kai kace an riga an nad’asa... Shi kad’ai sai wani cika yake yana ayyana hukunci mai tsauri da zai yanke wa Mahmood da zaran an nad’Asa Sarki.... Tabbas Mahmood zai zama abin kwatance cikin Masarautar, sai ya d’and’ani kud’ansa Ta yanda sunan Sarki Yazeed kawai yaji an ambata zai daburce hankalinsa ya gushe... Ya murmusa kad’an yanajin badon Shid’in yanzu sarki bane da tuni ya fashe da dariya tsaban tsananin munin horon da ya tanadarwa Mahmood d’in.... Yana tsaka da tinanin ne yaji cak sautin algaita da tambura sun tsaya kaman daga sama ya hango Majidad’i ya shigo cikin Zauren kai kace jeho sa akai... Doguwar takobinsa rik’e a hannunsa sai faman huci yake tamkar wani zaki....
A d’ari Yazeed ya mik’e tsaye yana ware idanu tabbas wannan mahaukacin ne rik’eda takobi....
Majidad’i na dariya yake fad’in “Wow wow wow..! King Yazeed AbdulJabbar ai ban zanci har munyi wasan Takobin har kaci har an nad’aka ba.... Ka mance ne na tuna maka...? Agreement d’in namu ba haka bane Dark Prince... Bayan mun kai Mahmood k’asa Wasa za’ai d’aya ya fille kan d’aya wanda yai nasara shine zai zama Sarki..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji yana mai zaro Takobin daga cikin gidanta...
Gaba d’aya illahirin jama’an dake wajen suka mik’e tsaye suna kallon kayan Al’ajabi wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan....
Ana tsaka da wannan yanayi kururuwa da hayaniya had’ida ihu ya gauraye cikin Fada ana fad’in bayyanar Mahaukaciya... Dogarai sai faman guje guje suke ana kokawan Kamata amma sun kasa....
Giwa Alkyabba a hannu ta nufo k’asa dan ita kanta kururuwan da hayaniyar har tsakan kanta takeji ga hannunta dake tsananin mata k’aik’ayi wanda bata tab’a jin irinsa ba.... Tafiya kurum Giwa take ba tareda sanin yanda take jefa k’afafunta ba... Bayi sai k’amewa suke suna bata hanya ... lokaci guda take doka kiran Jakadiya a hargitse...
Masarauta babu lafiya...
*Toh fah yau akeyinta ga Izzatu ta bayyana....Ga kuma Yazeed da Majidadi ko yaya wasan zata kaya.....???
SameenaAleeyou📚
[8/13, 7:34 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*44*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A daidai mashigar sashen nata suka had’uda Jakadiya jikinta sai karmami yake, illahirin jikinta rawa yake... Cikin tsananin tashin hankali Giwa taceda Jakadiya “Jakadiya mai nakeji... Shin da gaske Izzatuce ta bayyana...?!”
Jakadiya tai saurin jinjina kai tana mai zubewa saman gwiwoyinta “Allah shi taimakeki gaskiya ne Izzatu...Izzatu itace Ta bayyana cikin Fada...!”
Giwa ta zaro idanu waje tana dafe da k’irji take fad’in “Jakadiya hakan ba mai yuwa bane... Sanin kanki ne bayyanar matar nan tashin hankali ne tsantsa da musiba cikinta... Bayyanar Izzatu yana nufin za’ai babban rashi cikin Masarauta... Jakadiya ina Ubandoma... Shi kad’ai yake iyawa da Izzatu ta k’arashe cikin wane irin yanayi mai gauraye da d’imauta....
Jakadiya Ta had’iyi miyau da k’yar tace “Allah shi taimakeki kin mance cewa Ubandoma yana tsare hannun Masarauta... Bamuda hurumin tunk’aransa a halinda ake ciki...!”
“Jakadiyaa!!” Giwa ta darara mata wani irin gigitaccen tsawa wanda ya sanyata mik’ewa tsaye zumbur ba tareda tasan tayi hakan ba...
Giwa taci gaba da fad’in “Mune Masarauta, mune Fada Jakadiya babu Uban da ya isa ya hanani aiwatar da dik abinda naga dama cikin Masarautar nan, ba’a haifa ba kuma baza’a haifesa ba... Badon mahimmanci da rayuwar Izzatu kedashi a gareni ba da yau d’in Ta bak’unci lahira kowa ya huta...!! Jakadiya inaso Ki nemomin Ubandoma yanda ya shiga ya fita..!!”
Cikeda risinawa Jakadiya tace “An gama rankishidad’e..!!” Daga haka sa kai tai Ta famtsama cikin Masarauta tana tinanin Ta yanda zata soma neman Ubandoma gashi babu Waziri babu dalilinsa, duk tulin kiran da Giwa Ke masa sam bai d’aga ko guda d’aya ba... K’irjin Giwa yaci gaba da bugawa ba tareda tasan dalili ba... Hankalinta bazai kwanta ba muddin bataga Izzatu a hannunta ba... Ya zama tilas Ta canza ma Izzatu ma’ajiya idan ba haka ba tabbas duk wasu abubuwan da ta jima tana ginawa tsaf zasu rushe, sadaukarwar data jima tanayi zai tashi a aikin banza ita kuwa sam bazata tab’a barin hakan ya kasance ba...! Ta k’arashe tinanin nata tana mai fitowa daga sashen nata...
Ganin Masarautar a cike mak’il yasata tina cewa ashe akwai taron cikin Masarautar sam sabgogin gabanta sun sa ta mance hakan... K’irjinta ya kuma bugawa tamkar an sauk’e mata guduma... Lallai kuwa Izzatu bata zab’i rana mai kyau ba... Bazai yuwu yau d’in tayi shawagi cikin Masarauta ba hakan barazana ne Babba gareta... Babu shiri ta koma sashenta yanda ta umarci Hadimanta guda biyu su fiddo mata sutura na mulki da k’asaita dole ta nufi babban Zauren taro zama a fadarta bai ganta ba yau d’in....
Muhibbah da fitowarta kenan daga b’angaren su Umaima tayi rakiyawa Zahra ta barota tareda Umaiman bayan taceda Umaiman ta kula da ita dan har lokacin Zahra bata wani dawo dai dai ba nan ta hangi wilk’awan Giwa tamkar giftawan walk’iya... Koda ganin irin tafiyar da Giwa take kasan babu lafiya... Tai d’an jim tana mamakin meke faruwa dan su sam basuji duk hayaniyar da ake cikin Masarautar ba...
Wasu bayi dake kakkab’e babban parlorn Giwa na k’asa ta sinkayo suna fad’in tashin hankalin dake cikin Fada na bayyanar mahaukaciya... Gabanta ya yanke ya fad’i kenan mahaukaciyar nan ta kuma bayyana... Cikin d’an sassarfa Ta iso yanda bayin suke... Suna ganinta suka had’iye sauran maganganun nasu suka risina alamun girmamawa...
Muhibbah ta bisu da kallo ba tareda tacedasu komai ba tasa kai tai shigewarta... Zama bai ganta ba, dik yanda za’ai ya zama dole tasan yanda zatai taga mahaukaciyar nan k’ila wani haske ya kuma yaye mata....
Dik yawon da tai cikin Fada babu mahaukaciya Izzatu babu alamunta... Hango Giwa da tai ta nufi wata hanyar cikin shigata alfarma Hadimanta guda biyu biyeda ita hakan yasa Muhibbah tai saurin take masu baya....
Shigewarsu Giwa da kad’an Jakadiya ta iske Waziri da Ubandoma had’ida wasu dogarai majiya k’arfi dake rik’eda Ubandoman... Yanayinda Waziri ya ganta ciki ya tabbatar mata babu lafiya... Jakadiya ta dakatar dasu ta buk’aci ganin Waziri a keb’ance... Nan take sanar dashi abindake faruwa... Babu shiri Waziri ya umarci dogaran su kwance Ubandoma... Sukai yanda yace, ba tareda b’ata lokaci ba Waziri ya sanarda Ubandoma abindake faruwa... Kan kace mai sun fantsama neman Izzatu cikin Fada Ta yanda sukeda tabbacin zasu sameta....!
**
Matawalle ne ya mik’e a fusace yana fad’in “Kai Majidad’i haukar nan taka Ta ishemu kar ka kawo mana shashashanci nan...!”
Majidad’i ya d’ago Takobin sama ya nuna Matawalle dashi yace kana k’arasowa nan zan farke cikinka har lahira.... Wllhi na rantse da Ubangijin dake busan numfashi bani barin wajen nan sai na kara da wannan d’an tayin marassa kunyan... Sai na nuna masa ba’a cin amanata a kwana lafiya... Fad’a ni sayenta ma nake balle nawa... Zamu kara... Ko ni...Ko kai.... Wanda ya riga fille wuyan d’an uwansa Sarautar tasa ce..!!” Ya k’arashe yana mai duban D’angundan da suka shigo tare dashi yace “Fara aikinka..!”
Babu musu D’angundan ya soma busa irin nasu na ‘yan dauri yanayi yana wasa Majidad’i had’ida ihu irin nasu....
Daga Jamal har Fu’ad ganin abin suke tamkar mafarki... Meke faruwa ne haka... Wannan wane irin al’amari ne... Jamal yasan Majidad’i yasan ko wani kalan mahaukaci ne shid’in... Bayayiwa Majidad’i kallon cikakken mutum mai lafiya yasan sarai aka k’yalesa da d’an uwansa ko shakka babu zaiyi halin dabbobi ne ga d’an uwansa Yazeed tinda kaf abokan Majidad’i ‘yangunda ne da ‘yandauri hasalima Majidad’i yasha maganin k’arfe Takobi bata kamasa, trap shima ya had’awa Yazeed kan cewa su amince a gwada k’arfi da Takobi wanda duk yai nasaran kashe d’aya shi zai zama Sarki, yasan yasha na k’arfe dan haka a sauk’ak’e zai fille wuyan Yazeed mulki ya dawo gidansu....
Jamal yai tsalle ya raba tsakaninsu, yana mai duban Majidad’i yake fad’in “Babu wani wasan da za’ai... An jima da daina irin wannan jahilcin a Masarautar nan, addini ya wadata bazaku kawo mana abin fad’i a sauran masarautu dake kewayenmu ba...!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji....