Sashe 60
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tai masa K’uri tana mamakin har yanzu kallon k’ararramar yarinya yake mata, bata kuma cewa komai ba sai jinjina masa kai da tai... Murya can k’asan mak’oshi tace “Que pases una buena noche paa..!” (Na barka cikin dare mai aminci Paa)
Ya jinjina mata kai a hankali alamun amsawa kana Zahra tasa kai ta shige jiki a matuk’ar sanyaye...
Ya bita da kallo har Ta b’acewa ganinsa... A hankali ya lumshe gajyayyan idanunsa yana mai shak’an iskar Ubangiji...
**
Yazeed ya kuma duban Ubandoma a karo na biyu kana ya gyara tsayuwarsa yana mai maida hannayensa duka biyu baya “Ka shirya kayi magana...?!”
Ubandoma ya d’ago jigataccen fuskarsa yana duban Yazeed, ya had’iyi miyau da k’yar cikin rashin sanin abinyi.... Lokaci guda ya kuma kauda fuska gefe....
Yazeed ya tako gabansa cikeda k’asaita “Kar ka damu kanada daga nan zuwa wayewar gari, karka mance gobe kake cika kwanaki uku rufe a wannan fursunan da bakada ranan fita muddin baka yanke shawarin da zai ceceka ba... Idan kuma kaga ka fice daga Fursunan nan ka tabbata gawanka aka fitar, dani dakai munsan yanda al’amara ke gudana cikin Masarautar nan... So shawari ya rage naka Ubandoma..!” Ya k’arashe shu’umin murmushi saman fuskarsa....
Yazeed yana ficewa Ubandoma yaci gaba da matsan k’walla, shin da waye zai Yarda Mahmood ne kokuwa Yazeed ne..? Yasan babu mai ciresa a ukun da ya shiga face Allah... Toh waye zai sanadin fitarsa Mahmood kokuwa Yazeed... Sarai yasan shirin Giwa akan Mahmood ya kuma san idan yayi gigin sanar da Mahmood wani abu toh fah saidai wani bashi ba dan ko shakka babu Waziri da Giwa har lahira zasu aikasa... Toh amma Yazeed fah... Yace zai basa muk’ami a mulkinsa, ya masa alk’awra masu yawan gaske... Amma zai cikasu..? Amsar da baida tabbas akai...
Wata zuciya tace tabbas idan har kai sanadin hawansa mulki zai baka duk wani muk’ami da kake so cikin Masarautar... Zai ‘yantaka k’ila ma har ka zamto Wazirinsa...
Idan kuwa ka tsayaga Mahmood tabbas koda ka fice a gidan Yari zaka tabbata ne matsayin bawa k’ask’antacce ‘yanci da kake mafarkin samu har abada bazaka tab’a samu ba....! Ya k’arashe tinanin basa yana mai aza kafad’arsa saman katifa da aka sak’ata da buhu da ciyayi....
Can bayan ya kwanta da kad’an yaji ana kokawa jefa kansa cikin buhu.... Ubandoma ya mik’e firgit daga baccin da yake yana k’ok’arin k’watan kansa yana ihu neman d’auki....
Cikin azama yake kokawan k’watan kansa.... Kaman daga sama saiji yai b’at mutanen sun b’ace alamun sun danna layun zanansu... Bai ankara ba saiji yai an d’aukesa cak an fice dashi daga cikin furaunan gaba d’aya...
**
Washe gari ta kama juma’a ranan da masu sarautun gargajiya na cikin Fada Ke shirin shirya zama ta musamman dan tabbatar da Yarima Mahmood matsayin sarki mai jiran Gado....
Waziri sai safa da marwa yake cikin zauren nasa, ya kasa ficewa Fada... Shi kad’ai yakai mari yakai gwauro... Can wasu maza guda biyu k’arfafa suka shigo kawunansu a k’asa....
A d’ari Waziri ya nufesu yana furta “Yaya yaya menene labari... Kada kuce min bakuyi nasaran kashe Ubandoma ba...!”
Matansa sai duban juna da ido kurum suke wannan ya kalli wannan suna kifa kawuna a k’asa suna sosa k’eya....
Daga impressions d’insu kawai Waziri ya fahimci basu cika aikin da ya basu ba... Wasu jahilan mari ya dinga d’aukesu dashi, cikin tsananin k’unan rai yake furta “Ashe ku sakarkaru ne... Ta yaya za’a ce bawan nan shi kad’ai ya gagareku....?!”
D’ayan yace “Tuba muke mai Girma Waziri, gaskiya bashi kad’ai bane cikin d’akin wani ne ya taimaka masa...!”
Waziri ya danna masa harara yace “Ban gane bashi kad’ai ba... Duk kuyi nasaran sakawa masu tsaronsa maganin bacci amma ku kasa kashesa...? Wai mai kuke nufi ne ma...?”
D’ayan yace “Duk munyi haka mai girma Waziri, Ina mai tabbatar maka masu tsaronsa mun barbad’a masu hodar gusar da hankali amma mun iske wani cikin d’akin wanda bamu iya tantance fuskarsa ba shi ya taimakawa Ubandoma...!”
Gumi ya shiga ketowa Waziri, sai faman kama gefen babban garensa yake yana kece gumin...
Cikeda b’acin rai ya furta “Ku b’ace min da gani Bana buk’atar sake ganinku... Sakarkaru marassa amfani...!!”
Suna ficewa ya kuma iza babban garensa kana ya fice ya nufi Fada a fujajan....
**
Turaki yai tsaye gaban paint work d’inda Mahmood yai a daren jiya yana kalla yana sakin murmushi a hankali.... Daidai nan Mahmood d’in ya fito cikin shiri farar jampa k’al sai k’amshin Dolce & Gabbana ke tashi a jikinsa lokaci guda yana k’ok’arin saka cuff links yake fad’in “Muje mu samu ayi addu’ar nan damu, and banso na rasa hud’uban juma’a...!”
Juyowa Turaki yai yana duban abokin nasa har lokacin murmushin ne saman fuskarsa....
Mahmood da gaba d’aya hankalinsa kega mak’ala links d’insa jin Turaki yai masa banza ya sanyashi d’agowa yana duban Turakin....
Ya k’arasa abinda yake kana ya furta “I hope dai lafiya kake tsaye wajen kanata faman sakin murmushi... Ko Hidaya na hanya ne yau d’in...?!” Ya k’arashe cikin sigan zolaya...
Turaki yai taku kad’an ya k’arasoga Mahmood d’in, har lokacin murmushin bai bar saman fuskarsa ba... “Rankaidad’e akwai abinda ake b’oye mana ne ba’a so mu sani...?!” Yai maganar cikeda zolaya...
Girgiza kai kad’an Mahmood yai kana yace “Kaga babu lokacin hayaniyar nan naka Turaki...!”
Bai kuma cewa komai ba yasa kai ya nufi downstairs cikin sassarfa...
Turaki ya fad’ad’a murmushinsa yana furta “Allah huci ran Sarki mai jiran Gado tuba nake... Inama sarki zaimin izini na fad’i wani abu da ya tsaya min a mak’oshi....!”
Shidai Mahmood bai amsasa ba har suka nufo parlor, yanda Turaki Ke ci gaba da fad’in “Yarima I can see you’re in love..!”
Cak Mahmood ya tsaya ya kasa ci gaba da tafiya... Lokaci guda ya kaikaito yana duban Turaki, girgiza kansa kad’an yai yana mai furta “Where is that coming from..?!”
Turaki ya gyara tsayuwarsa yace “You paint in the middle of the night when you’re in love... And this is exactly what happened when you fell for Marigayiya, Allah yai mata rahama... Musamman kake neman waje maras hayaniya ka keb’e kaita zanen abubuwa masu ban sha’awa a tsakiyan dare, Sannan zanan can da kai yayi shige da wanda kayi lokacin Aliya...!” Ya d’anyi fasali kana yaci gaba da takowa a hankali “Mahmood tell me wacece Ta kuma sace zuciyarka haka dan dai na tabbata ba Raheema bace...?!”
Gajeren tsaki yai kana yace “Stop talking nonsense, will you..! You talk too much...!” Yaci gaba da tafiya dukda heart d’insa dake beating very fast... Lokaci guda yake furta “Banida lokacin shiririta nan naka Tukraki...!” Yai maganar yana mai ficewa daga parlorn...
Turaki ya rakasa da ido hannayensa sakale cikin aljihu kana ya d’an fuzar da fuci kad’an had’ida tab’e baki murmushi saman fuskarsa... Mahmood kenan, shid’in yasan abokinsa Farin sani kuma ya san abokin nasa needs him now more than ever...! Ya kuma murmusawa a hankali kana ya takewa Mahmood d’in baya...
**
Giwa ta kuma kece gumin da ya sauk’o mata.. Cikin tsananin tashin hankali take furta “Waziri bamuyi haka dakai ba, kayi alk’awarin bazaka bani kunya ba toh mai kuma nakeji haka... Ubandoma na raye...? Kenan duk wanda Ubandoma Ke masa aiki yafimu saurin motsawa kuma ko shakka babu shine bak’on Buzu, ina tsoron kada wannan bak’on Buzun ya rigamu isaga Mahmood... Dani dakai duka mun sani idan har ya rigamu isaga Mahmood toh fah kashinmu ya bushe cikin Masarautar nan...!” Ta k’arashe cikin tsananin huci tana hura hanci...
Lokaci guda ta tako zuwa gaban Waziri, bata daina huci ba take furta “Waziri tun wuri ka gyara wannan al’amari... Matsaloli sunmin yawa ko kasan Jamal ya auka soyayya da yarinyar nan Umaima...? Sannan har yau Izzatu tak’i sanar dani yanda Saudatu take... Kodashike ta yaya zan tsammaci samun amsoshi daga wajen matar da babu hankali tattareda ita cikin sauk’i... Na bijiro mata tako ina amma babu wani canji, na mata da k’arfi na mata da lallama na mata da hauka duka babu canji... Waziri kar ka k’ara wani abin kan matsalolin da suke kaina, ka ida abinda ka riga ka soma... A binciko Ubandoma da mai taimaka masa yanda suka shiga suka fita idan kuma ba haka ba kana iya mancewa nid’in TAKACE....!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji....
D’ago idanu yai yana dubanta, lokaci guda yake furta “Zan gyara abinda na b’ata na miki alk’awari... Sabida Ke Turai babu abinda bazanyi ba..!!” Ya k’arashe cikin tsumewa yana sakin huci....
Giwa ta murmusa a hankali kana tace “Inaso naga Mahmood saman karaga Sati mai zuwa...!”
Waziri ya jinjina kai “An gama Allah shi taimakeki...!!” Daga nan ficewa yai waya manne kunnensa...
**
Fitowarsu daga gidan Wambai suka nufi fursunan da Ubandoma ke rufe ciki dan yau ne wa’adin da Mahmood d’in ya d’ibar masa ya gama duk wani tunanin da zai kafin masarauta ta yanke masa duk hukuncin da zata yanke masa... Toh amma labarin da suka tadda wajen masu tsaron fursunan shine ya d’aure masu kai...
Mahmood ya tsaresu da idanu yana karantarsu sai sosa Kai suke suna neman afuwansa.... Ya d’an taka kad’an zuwa cikin d’akin yana k’arema d’akin kallo... Ya kaikaito yana duban guard guda “Kace baku San yaya akai ya fice ba..?”
Guard d’in ya jinjina kai cikeda risinawa “Allah shi baka yawan rai bacci ya d’aukemu daga nan bamu kuma sanin komai ba sai farkawa mukai muka tadda babu Ubandoma..!”
Mahmood ya fuzar da fuci a hankali yana mai binsu da idanu.... Tsaban takaicin da suka sakasa ciki bai iya cewa komai ba saima fitowa daga cikin fursunan da yai Turaki na take masa ba....
Waya ya ciro ya kirawo Sankira yace a sanar dasu Galadima akwai zama yau d’in na gaggawa a nan cikin Fada... Kan kace mai masu sarautun gargajiya sun hallara...
Waziri sai muzurai yake kaikace baisan meke wakana ba....
Gaba d’aya suka had’u a babban Zauren zama na musamman dake a cikin Masarautar...
Waziri ne ya soma yin gyaran murya yace “Allah shi taimaki Yarima kuma Sarkin mu mai jiran Gado... Mun amshi sak’on kira na gaggawa daga bakin Sankira...Allah yasa dai lafiya...!” Ya k’arashe cikeda risinawa...