← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 162

Sashe 146

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryar Mahmood ya katse mata tianin nata sanda yake ci gaba da furta “Zahra, tarihin rayuwarmu zai iya canzawa gaba d’aya.. Inaso Ki sani a yau d’in zaki samu wasu amsoshi da kika jima kina nema tsawon rayuwarki..!” Ya k’arashe yana mai janyo wata doguwar envelope fara k’al...
Gaba d’aya Sai Zahra tama rasa mai yake fad’i, tunda taga ya janyo doguwar takardan nan tasan bazai shige takardan sakin Muhibbah bane... Shiyasa yace labarin rayuwarsu zai kuma canzawa... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un, Muhibbah gaskiya ta fad’i mata da tace aurensu da Paa d’inta bazai k’argo ba.. Gashi nan kuwa hakan ya tabbata...

K’ok’arin saita kanta ta d’anyi dan bata so ya fahimci tasan wani abu, muryarsa ne yankatse mata tinaninta

“Zahra..!” Ya ambato sunanta cikin dakewa... Lokaci guda ya mik’a mata doguwar takardan yace “Make sure kin damk’a mata a hannunta...!”

Bata amsa ba Sai tsananta fad’uwa da gabanta yake, tana son tambayarsa takardan ta Mecece amma yin hakan ba huruminta bane, wace ita ma da zata bud’i baki taima Mahaifinta tambaya makamanciyar wannan..
Ta kuma sinkayo muryarsa cikin dakewa yana furta
“Karb’a mana..!”

Jiki a matuk’ar sanyaye, hannunta na tsananin rawa Ta amshi envelope d’in da duka hannayenta biyu...
Mahmood yai gyaran murya ya furta “Tashi kije, ki bata hannu da hannu sak’o ne mai matuk’ar mahimmanci ciki wanda ban amince wani Ko wata cikin Hadiman gidan nan su bata ba face ke.. Dan haka kar kiyi wasa dashi Kin fahimta..?!”

Ta jinjina masa kai a hankali tace “Na fahimta Paa...!”
Lokaci guda ta kuma neman izinin tafiya yace tana iya tafiya kana ta mik’e jiki a matuk’ar sanyaye Ta nufi k’ofa..

**

Koda suka isa nan suka sanar sud’in bak’i ne zuwaga Gimbiya Muhibbah sannan wasu Dakaru daga cikin masu tsaron babban gate d’in Fada sun gane Ansar, hakan yasa ba’a wani tsaya tsananta bincike akansu ba..
Aka had’a Mommy da wasu Dogarai guda biyu sukai mata rakiya cikin Fada, a wani parlorn sauk’an bak’i aka sauk’i Mommy kafin aka tura wata Hadima taje ta sanar da sak’on bak’uwa da Gimbiya Muhibbah kedashi... Koda sak’on ya isa ga Muhibbah batai zaton Mommy bace, sanin cewa bata wani San mutanen garin sosai ba ya sanyata tinanin ko daga inane bak’in nata.. Da wannan tinani ta nufi parlorn bak’in.. Ga tsananin mamakinta Mommy ta gani.. Aiko sunan ganin juna Muhibbah ta taho a guje ta rungumeta... Suka rungume juna suna hawaye... Ai tuni Muhibbah tace ta k’araso daga ciki, sashenta suka nufa suka k’ule a d’aki suna kukan yaushe rabo... Nan Muhibbah ke sanar da Mommy watak’ila su koma tare idan har Mahmood ya sawwak’e mata... Aiko nan Mommy ta gyara zama ta ambato sunanta, Muhibbah ta amsa cikin sanyin jiki “Dama maganar ya kawo ni, dan ko ruwa bazan sha ba zan amo dashi... Sannan koda ace kina matsayin Gimbiya kuma Sarauniya ni zan miki fad’a a matsayinki na d’iyata..!”

Gaban Muhibbah ya fad’i tana mai duban Mommy da Ta had’e rai sosai, cikin rawar murya tace “Mommy mai nayi.. Kema kina zaton zan maku butulci ne..?!”

Kasteta Mommy tai da fad’in “Ashe bakida hankali ban sani ba..?”

Ta d’ago idanunta da sukai rau rau tana duban Mommy... Mommy taci gaba da fad’in “Ansar ya sanar dani komai kuma banji dad’i wannan rashin hankali da yayi ba.. Yau idan mun taimakeki sai kin saka mana.. Idan akace haka za’ake taimako don a rama maka abinda akai maka mai sunan abin kenan.. Ashe ba wajen Allah kake neman ladanka ba kenan..! Muhibbah Ansar ya fad’a miki k’arairayi ne kawai dan ki dawo cikin rayuwarsa amma ba gaskiya bane.. Mahmood masoyinki ne Muhibbah domin kaw ina mai tabbatar miki badon Allah ya k’addari aurenku ba da yanzu bamu San waye Yawale ya aura miki ba..!”

Muhibbah da gabanta yai wani irin tsinkewa ya fad’i d’agowa tai tana duban Mommy dake ci gaba da karanto mata duk yanda al’Amara suka kasance... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa wasu irin hawaye suna gangaro mata.. Abubuwan sai suna Zuwa kanta daki daki... Mommy ta k’arashe da fad’in “Koda wasa kar inji kin kashe aurenki akan shiriritar banza kinji koh...!”

Girgiza kai Muhibbah take tana hawaye take furta “Mommy I’m afraid it’s too late...! Mommy any moment Rankaidad’e zai iya sauwak’a min..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..

Baki sake Mommy Ke dubanta “Ban fahimceka ba Muhibbah..!”

Cikin rawar murya Muhibbah ta sanar da Mommy yanda sukaida Rankaidad’e... Mommy ta shiga tafe hannaye tana salallami... Yanzu duk yanda nake ganinki mai wayon nan Ashe ba haka bane.. Ina tunaninki ya tafi Muhibbah da har zakiyi irin wannan yarjejeniya da mijinki... Kin kuwa San girman zunubin mace Ta bud’i baki Ta nemi saki daga wajen mijinta..? Haba Muhibbah.. Ina karatunki ya tafi..?!”

Cikin zuban hawaye take furta “Mommy banso na cutar da kowa, a tunanina Ansar bai cancanci abinda Rankaidad’e yai masa ba.. Dan duk abinda kika sanar dani is a total opposite da wanda ya sanar dani.. I was so confused Mommy, dan Allah kada kiga laifina..!” Ta k’arashe cikin zuban hawaye murya na rawa sosai.. Bata ida rufe baki ba Hadimarta ta nemi izinin shigowa ta risina ta sanar da ita shigowar sak’on Gimbiya Zahrau wacce Ke zaune parlor tana jira..

Muhibbah dake k’ok’arin saita kanta, share hawayen da suka wanke mata fuska tai kana taceda Hadimar tana nan tafe...

Hadimar ta risina Tai godiya kana ta fice...

Jim kad’an Muhibbah ta fito waiting room d’in yanda Zahra Ke zaune saman wasu kujeru na alfarma tana jiran fitowarta...
Fuskar Zahran kad’ai Muhibbah ta gani ta fahimci babu lafia, domin kaw ta hango tsagwaran tashin hankali kwance saman fuskar nata.. Tasan bazai shige fushin da take da ita bane...

Murmushin k’arfin hali saman fuskarta Ta k’arasoga Zahran...
Saidai bata kaiga furta koda kalma guda ba Zahran ta mik’a mata envelope dake rik’e hannunta tana mai furta “Paa yace na baki wannan..!”

Muhibbah ta dubi Zahra da mamaki Ta kuma dubi takardan da take mik’a mata zuciyarta na tsananta bugawa...

Bata amsa ba saima duban Zahra data kumayi tana mai furta “Wannan kuma fah Zahra..?!”

A hankali Zahra ta girgiza kai tace “I’ve no idea, he just asked me to give it to you..!”
Lokaci guda Muhibbah ta shiga girgiza kai tana mai furta “Ni kuma..? Rankaidad’e..?”

Zahra ta kamo hannunta guda ta damk’a mata takardan cikin tafin hannunta.. Lokaci guda take furta “Bansan mai takardan Ke k’unshe dashi ba, amma ga dukkan alamu k’unshe yake da abu mai mahimmanci tinda har ya tsallake Hadiman gidan nan ya bani umarnin na kawo... Watak’ila burinki ya cika miki cikin Takardan nan..! Ina miki fatan alkhairi.. Tia..!”

Tana ida fad’in haka bata kuma tsayawa sauraren wata kalma daga Muhibbar ba tai saurin sa kai tana matsan k’walla...

Muhibbah dake tsaye wajen tamkar wacce ruwa ya shanye duban Zahra kurum take har ta b’acewa ganinta tana rik’eda takardan dake rik’e cikin hannunta..
Cikin tsananin bugun zuciya ta sauk’oda idanunta masu zuban ruwa tana duban takardan
tana kuma juyasa

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Takardan Saki Rankaidad’e ya bata,shikenan ya sauwak’a mata kaman yanda yace idan taci jarabawar zai sauwak’a mata... Batasan sanda sanda kuka ya kufce mata ba... Ta nufo cikin d’aki afufujajan tana kuka take fad’ida Mommy “Mommy Rankaidad’e ya sawwak’e min, shikenan ya rabu dani Mommy... Mommy dan Allah kice masa na fasa banso naci jarabawar kuma..!” Cikin tsananin kuka take maganar dunk’ule da takardan a hannunta... Mommy Ta taso da sauri ta rik’eta tana tambayarta ta nastu ta sanar da ita abinda ke faruwa.. Inaa kuka kurum Muhibbah take.. Lokaci guda Ta mik’e ta nufo waje da gudu alkyabbarta na biye da ita tana shek’ar kuka.. Babu shiri Mommy ta mik’e ta biyo bayanta.. Hadimanta suna tambayarta “Rankidad’e meke faruwa..?” Bata tsaya basu amsa ba suma ta shigesu tana mai ci gaba da kukanta ta nufi sashen Gimbiya Turai... Kan cinyarta ta fad’a tana kuka sosai dunk’ule da takardan a hannunta take fad’in “Ummi dan Allah kice masa na fasa, wllhi banson lashe jarabawar kuma..! Dan Allah Ummi kice masa yayi hak’uri ni na fasa yarjejeniyar..!”

Gimbiya da bata fahimci yanda Muhibbah ta dosa ba, d’agota tai tana kuma tambayarta abinda Ke faruwa.. Tace “Ki natsu kimin bayani Saudah, Wai meke faruwa..? Ina Sarakin yake..? Mai kuma ya faru yanzu..?!”

Cikin kuka Muhibbah Ke fad’in “Ummi cewa yayi ya sauwak’a min...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana...

Gimbiya Turai ta shiga karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ta kuma duban Muhibbah dake matsan hawaye tace “Shi ya sauwak’a miki..?!”

Cikin kuka ta kuma jinjina kai ba tareda ta iya furta komai ba sabida tsananin rawa da muryarta keyi...

Gani kawai sukai Gimbiya ta mik’e ta fice cikin tsananin b’acin rai...

Muhibbah ta rarrafa kusa da Mommy ta kwanta saman cinyarta tana ci gaba da shek’ar kukanta har lokacin takardan damk’e yake cikin hannunta...

Mommy sai bata baki take tana calming d’inta amma kaman cewa take ta k’ara, tinanin ‘yan kwanaki biyun da sukai matsayin ma’aurata take.. Beautiful moments da suka tsinci kawunansu ciki a ‘yan kwanakin gashi yanzu shikenan ya zama tarihi Rankaidad’e ya kufce mata na har abada, domin kuwa a tsarin Sarki baya komen mace, idan ya sauwak’a mata kafin nad’in sarauta shikenan bayan nad’in sarauta bazai kuma dawo da ita ba.. Sabon kuka ya kuma kufce mata labarin yanda al’amarin aurensu ya kasance da Mommy Ta sanar da ita na kuma Yawo a kwanyarta, Rankaidad’e is her savior, tin daga fari shi ya soma tsintarta a lokacin data b’ace ranan bukin sallah kuma badon Allah ya k’addari su Yazeed sai Sun cutar da ita ba tabbas da Rankaidad’e bai Tafi ya k’yaleta taredasu ba.. Sannan ya kub’utar da ita a hannun Yazeed a lokacinda yaso lalata mata rayuwa a karo na biyu.. Bayan wanann ya kub’utar da ita a hannunsu Giwa da Jamal wanda shima Jamal d’in yaso kuma lalata mata rayuwa a karo na biyu... Gashi da taimakon Allah shi ya kub’utar da ita bai bari Yawale ya aurarta ga duk sharan da yaso ba... Shin tayaya zataso rabuwa da irin wannan miji wanda a kullum burinsa shine ya zamto mata katanga... Shid’in ya zamto tamkar garkuwa ga rayuwarta.. Maiyasa bazatayi kukan abinda tai masa ba..
Chapter 146 · 0% Book details