← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 162

Sashe 27

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tai alamawa Jakadiya suka soma Tafiya, ‘Yanmatan gaba d’aya masu sanye da tufafi iri guda su goma sha hud’u suka jera a layi sahu biyu kansu a k’asa har Giwa ta fice daga cikin wajen...

Koda Giwa ta iso d’aki hankalinta bai kwanta ba, kaman ko yaushe Yarima Jamal ta tadda zaune a d’aki yana jiran k’arasowarta.... Yanayinta da ya gani ya tabbata akwai abu mai girma dake damun Mahaifiyar tasa....

“Maami lafiya na ganki haka...?” Ya bid’a fuskarsa d’aukeda damuwa...

K’ak’aro murmushi Giwa tai dan har abada bata yarda ta nuna gazawarta ba kana tace “Lafia lou nake Ubana... Baka kwanta ba...?”

Jamal ya murmusa kad’an kana yace “Maami kinsan bazan tab’a kwanciya ba tareda naga kin kwanta bacci cikin aminci ba....!”

Tai murmushi cikeda jin dad’i kana tace “Allah shi maka Albarka Jamal, biyayyan da kake min kaima Allah shi baka yara masu yi maka irinta...!” Bata Kai aya ba tai saurin katse addu’ar tata kaman wacce ta tina wani abu...

Jamal ya tsareta da idanu yana jiran yaji k’arshen addu’an nata... Kaman ko yaushe yaji tayi shiru batai masa fatan samun yara ba... Mik’ewa yai ya k’araso gabanta had’ida duk’awa, ya d’ago kai yana dubanta kana yace “Maami mai ya hanaki k’arasawa...Shin baki so nima nai aure na haifi nawa yaran ne....?”

Tai masa K’uri tamkar mai tunani, kana ta shafi gefen fuskarsa kad’an, lokaci guda ta sakar masa murmushi kana tace “Tanadin da nai maka na musamman ne Jamal, K’warai Inaso naga ‘ya’yanka kuma wataran zasu gaji sarautar gidan nan... Toh amma Jamal idan Kai aure yanzu waye zaike kula dani yanda kake kula dani... Sanin kanka ne cikin ‘yanuwanka kaf ka fisu kula dani da kuma al’amra na... Kaine Gwarzo na Jamal, idan Kai aure hankalinka zai karkata zuwaga iyalinka.... Wa zai kula dani Jamal...?!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...

Jikin Yarima Jamal yai sanyi... Yana matuk’ar k’aunar mahaifiyarsa fiye da komai a duniya... Ko wace irin biyayya ne yai alk’awarin yi mata wannan biyayyar matuk’ar zai sanyata cikin Farin ciki... A hankali ya mik’e daga durk’ushen da yake ba tareda ya kuma juyowa ya dubeta ba yai ficewarsa zuciyarsa na matuk’ar masa zogi... Ya rasa gane dalilin da yasa sam mahaifiyarsa bata k’aunan ya kawo maganan aure cikin rayuwarsa... Maiyasa take masa haka, ya kasance mai tsananin biyayya a gareta, Bai tab’a sab’a umarninta ba tsawon rayuwarsa... Toh Maiyasa shi bazata barshi ya cika burinsa na ganin ya aje iyali ba...? Idan dan tsoron kar biyayyan da yake mata ya daina ne yayi imani babu macen da zatazo Ta hanasa biyayyawa mahaifiyarsa...

Da wannan tinanin ya nufo matakalan benen, idanunsa suka sauk’a zuwa b’angaren Umaima da Zahra... Yai K’uri yana duban k’ofan parlorn nasu... A hankali ya soma takawa har ya isa ya bud’e k’ofar parlorn cikin tsanaki.... Ya soma takowa cikin d’an madaidaicin parlorn yana mai k’arewa k’ofar d’akin Umaima kallo... Lokaci guda idanunsa suka sauk’a kan zanen gidan sarautar dake lank’aye wajen wanda shine ya baiwa Umaima ta lank’aya a wajen.... Ya tako har zuwa gaban zanen ginin gidan sarautar yana shafawa a hankali tamkar mai nazarin wani abu.... Lokaci guda ya maida dubansa zuwaga k’ofar d’akin Umaima, ya jima yana duban k’ofan d’akin kafin ya soma takawa a hankali cikin tsanaki ya isa jikin k’ofar ya tura a hankali, nan kuwa k’ofar ta bud’e....
Cikin sand’a yake takowa zuwa cikin d’akin har ya iso gaban gadon Umaima dake baccinta hankali kwance....

Yai mata K’uri yana dubanta, daidai lokacinda Umaima Ta d’anyi juyi cikin bacci bargon da ta rufa ya d’an janye ya yaye k’afafunta zuwa cinyoyinta suka bayyana... Zuciyar Jamal tai wani irin tsinkewa, yai saurin rintse idanunsa yana mai kauda Kai gefe... K’irjinsa bai daina bugu ya soma k’ok’arin Kai hannunsa da niyyan janyo mata bargon ya rufa mata, hannayensa sai rawa suke... Ba tareda ya kuma duban k’afafun nata ba ya janyo bargon ya gyara mata a hankali... Bayan ya rufa mata durk’usawa yai gaban gadon nata kana yai mata k’uri... Ya saki murmushi a hankali yana duban idanunta dake rufe ruf alamun bacci....

Cikin zuciyarsa yake fad’in “Ke tawa ce Umaima... Na rabaki da Ja’afar domin na mallakeki... Na kuma mallaki soyayyarki... Bazaki sake ganin Ja’afar ba har abada Umaima... Ja’afar bawa ne k’ask’antacce wanda bai cancanci soyayyarki ba... You’re mine Umaima... Kuma duk namijin da yai yunk’urin raba tsakaninmu zan b’atar dashi kaman yanda na b’atar da Ja’afar... Umaima, koda ace mahaifiyata bazata amince min da aurenki ba, toh kema bazan tab’a bari kiyi aure ba... Sabida ked’in tawa ce, na gwammaci nayita ganinki haka koda bazamu sami zarafin kasancewa da juna ba... Ina sonki Umaima.. Ina matuk’ar k’aunarki.. With all my heart..!” Ya k’arashe siririyar Hawaye na gangarowa Daga idanunsa guda... Ganin ta soma muskutawa alamun farkawa ya sanyashi saurin mik’ewa ya nufi k’ofa... Cikin sand’a ya fice kana ya janyo mata k’ofar a hankali ya nufi k’asa ya fice daga sashen gaba d’aya...
***

Washe gari ta kama asabar ranan hutun aiki sannan d’alibai ma suna gida babu makaranta... Hakan yasa koda Zahra ta tashi tai wanka ta shirya sai ta nufi cen b’angaren bak’i yanda Muhibbah take.... Muhibbah batai mamakin ganin Zahra zaune a parlor tana jiran fitowarta ba...

Suka sakar ma juna murmushi kana Zahra ta soma gaidata, Muhibbah ta amsa da sakin fuska ta k’arada “Yau mai nayi da na cancanci amsar bak’uncin kyakkyawar Gimbiya da sanyin safiyar nan... Gaskiya yau d’in ga dukkan alamu na tashi da sa’a...!” Ta k’arashe tana mai fari da idanu...

Zahra Ta murmusa kana tace “Zuwa nai na gayyaceki karin kumallo a cen b’angaren mahaifina...!”

Take annurin fuskar Muhibbah ya d’auke cak... Gabanta yai wani irin yankewa ya fad’i... Karin kumallo a b’angaren Yarima Mahmood... Wai kuma tareda ita Muhibbah...?!

Ganin yanayinta ya canza ya sanya Zahra sakin murmushi kad’an kana tace “Bakiso ko...?”

K’ak’aro murmushin yak’e Muhibbah tai kana tace “Ba haka bane Princess, kawai gani nai kaman bai dace ba... Maybe mahaifinki ma bazai so haka ba, or maybe hakan ya sab’a al’adu da d’abi’un Masarautar nan... Karki mance Zahra nan ba Spain bane yanda dik abinda kike ganinshi normal a can a nan ka iya zama akasin haka...” Ta k’arashe cikeda kulawa...

Zahra Ta d’anyi rau rau da idanu kana tace “But ni banga komai ba cikin yin hakan... You’re my only friend here... Har yanzu ko sch banyi k’awaye ba.... Kuma shi yace min nazo muyi breakfast taredashi, na tambayeshi idan zan iya zuwa da friend d’ita.. Ya tambayeni wacece friend d’in tawa nace mishi ke ce.... Bai hana ba, kuma ai abinci kawai zamuci tare duka ni banga wani kuskure a cikin hakan ba... Ko shima sab’a dokan gidan nan ne...?!”

D’an fuzar da iska kad’an Muhibbah tai kana ta k’araso ta rik’e hannayen Zahra cikin nata “Princess ba haka bane... But baki tunanin maybe Paa d’inki yanaso ku kasance ku biyu ne, to spend time together... Daughter and Dad bonding... Baki tinanin haka.?” Ta k’arashe tana kashe mata idanu guda....

D’an turo baki kad’an kana tace “Fine tinda kink’i zuwa... But promise me anjima zamu fita mu shak’ata a Lambun Masarautar nan sai muyi namu bonding time d’in...”

Murmusawa kad’an Muhibbah tai kana tace “I promise you...!” Ta k’arashe tana mai d’aga tafin hannunta alamun alk’awari....

Zahra na ficewa da kad’an Umaima ta shigo ta d’auketa suka tafi b’angaren Giwa domin karya kumallo daga cen kuma sashen Zuhra matar Yazeed suka nufa....

**

Sanda Zahra ta k’araso sashen mahaifin nata, samansa ta haura don sanar dashi ta dawo ya sauk’o suyi breakfast saidai wayan da taji yana yi ne ya sanyata tsayuwa ba tareda Ta iya ci gaba da tafiya ba...

Mahmood da sam baisan da isowar d’iyar tasa ba yaci gaba da fad’in “Must we talk about that Turaki... Sau nawa zance maka sanin gaskiyar babu wani amfanin da zaiwa Zahra... I cannot break my daughter’s heart, rashin mahaifiyarta da tai is enough... Zahra went through a lot already... Rasuwar Aliya, d’aukota daga Spain mu dawo Nigeria, rabata da rayuwar data saba, makarantar ta abokanta da sauransu don’t you think is enough for her... Bai kamata na kuma bijiro mata da wani tashin hankali ba... The only abinda na sani shine bazan tab’a bari tasan gaskiya ba muddin gaskiyan zai jefata cikin tashin hankali... I already lost my wife, I can’t lose my daughter Turaki...!”

Dukda k’arancin shekarunta hakan bai hanata k’ok’arin saita natsuwarta ba... Taji jiri na neman kada ita... Mai Paa d’inta yake b’oye mata... Meye ne wannan abin da baiso ta sani...? Meye a k’unshe da rayuwarta da yake b’oye mata...? Ta yarda da Paa d’inta tsawon rayuwarta, bata tab’a kawo akwai abinda zai b’oye mata mai girma har haka ba.... Ita zata iya cewa ma tafi shak’uwa dashi sama da mahaifiyarta... Toh meye ne ake mata rufa rufa akai... Toh kodai Paa d’inta nada masaniya ne akan mutuwar mahaifiyarta tinda gashi taji yana cewa ya rasa matarsa bazai kuma rasa d’iyarsa ba... Idan bata mance ba zuwansu Nigeria ne aka tsinci gawar Maama a d’aki... Toh ko Paa yasan wani abu ne gameda mutuwar mahaifiyarta shine yake b’oye mata...?! Take taji wasu k’walla suna kuma zuwa idanunta.. No Paa d’inta bazai tab’a yin wani abu mai kama da wannan ba, bama zata bari zuciyarta ta raya mata hakan ba.... Tayi nisa cikin tinani ta jiyo muryarsa yana fad’in “I guess my princess’s starving already... Forgive your Paa ya barki kinata jiranshi... Do you want me to serve you...?” Ya k’arashe yana mai k’arasowa jikin dining table d’in....

K’ak’aro murmushi tai kana tace “No it’s alright Paa... Just sit down I’ll serve you...!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye cikin tsananin sanyin jiki... Yarima Mahmood yai mata K’uri yana duban yanda yanayinta ya sauya gaba d’aya...
Ta k’araso tana k’ok’arin had’a masa shayi, har lokacin idanunsa akanta.. Hannunta ya d’an rik’e alamun dakatarwa kana yace “Are you sure you’re alright sweetheart..? Wait ina friend d’in taki... Why isn’t she here...?”

K’ak’aro murmushi ta kumayi na k’arfin hali kana tace “I’m fine Paa... Tace ba yau ba maybe some other time...!”
Chapter 27 · 0% Book details