← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 162

Sashe 126

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Neman duniyar nan cikin Masarautar sunyi babu Giwa babu Muhibbah balle Jamal ko Jakadiya..! Babu su Babu alamunsu... Idan Kaga Mahmood dole ka tausaya masa, gaba d’aya ya fice hayyacinsa harta Ansar saidai yasha mamakin kalan tashin hankalin da Yarima Mahmood ya shiga na rashin ganin Muhibbah... Ko shi da yake ikirarin yana sonta sai yaga nasa ashe wasan yara ne..! Saima ya soma tuhumar kansa anya yana sonta kuwa..? Ji yayi kaman ba soyayya yake mata ba tinda yaga yanda Yarima Mahmood ya gama susucewa cikin Masarauta na rashin ganinta da tinanin halinda zata iya kasancewa ciki..!
Allah ya gani Mahmood d’in sai ya basa tausayi sanin cewa ahalinsa ne suka cutar da matar da yake matuk’ar so irin haka...

Anyi searching anyi anyi babu su babu alamun su, idan aka soma tunanin dakatawa da nema Mahmood d’in yakan ce babu mai hutawa koda gari zai rufe ya kuma wayewa ne sai an zak’ulo yanda suke cikin Masarautar..!

Turaki ya dafe kansa kurum yana duban Mahmood d’in dake Ta k’ok’arin tokarin wani k’ofa da iyaka k’arfinsa wanda shida Turakin ne suka k’araso wajen..!

Bai sarara ba saida yaga ya bud’e k’ofar..! Suka ja sukai turus shida Turaki ganin kujera ajiye daga center Babu kowa akai sai handcuffs da sauran busasshen jini... Cikin sanyin jiki zuciyarsa na bugawa ya isaga Kujerar take ya zube ya duk’a saman gwiwoyinsa ya d’aga handcuffs d’in yana juyawa yana kallo... Turaki ma ya k’araso yana kallon kayan mamaki.. Da gaske dai mutanen nan bak’ak’en azzalumai ne.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Can ya hango hawaye daga idanun Mahmood suna d’agowa...

Baida daina juya handcuffs d’in ba yake furtawa cikin tsananin rawar murya “They tortured her..! Sun azabtar da ita Turaki...! They’re not humans..! Ta yaya d’an adam zai aikata haka..! Kodai akwai laifin da nake aikatawa ne Allah ya jarabceni da irin wad’annan ahali..! Tell me Turaki..! Please tell me..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..

Turaki ya dafasa yace “Mahmood kowa da irin jarabawarsa a rayuwar nan, wani a jarabcesa Ta iyalansa wani ta ahalinsa, wani ta wajen sana’arsa.. Wani ma da lafiyarsa za’a jarabcesa.. Duk dan a gwada k’arfin imaninmu..! Kada ka kauce hanya your Highness..! Ubangijinka yana gani kuma baya bacci da sannu zai kawo maka sauk’i iftila’in da ya Aiko maka..! Tashi muje.. Watak’ila sun fitar da ita daga cikin Masarautar nan muyi saurin cimmasu..!!” Yai k’ok’arin mik’ar da Mahmood d’in suka nufo waje dukda shi kansa Turakin baisan Ta inda zasu kuma nufa ba..!

Rik’o hannun Turaki Mahmood yayi yace “Kana tunanin sun kashe Muhibbah..?!” Yayi maganar cikin tsananin rawar murya..

Turaki ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali, dan duk abinda zai fad’iwa abokin nasa a halin yanzu yasan k’arya ne, amma babu yanda ya Iya Mahmood yana buk’atar a kwantar masa da hankali a kuma nuna masa akwai hope..! Nan Turaki yaci gaba da basa k’warin gwiwa yana nuna masa kada ya karaya da izinin Allah Muhibbah tana nan da rai kuma zasuyi rayuwa mai tsawo nan gaba tare..!

A tare suka nufo yanda suka baro su Ansar da sauransu, jikkunansu a matuk’a sanyaye daga Mahmood d’in har Turakin tun bayan da sukaga wajen dasu Giwa da Jamal suka aje Muhibbah...

Izuwa wannan lokaci cikin Masarauta ta gama rikicewa gaba d’aya, kama daga b’angaren masu sarauta har zuwa b’angaren bayi.. Zancen kenan guda d’aya ake.. Masu mamaki nayi masu jimami nayi... Illahirin Masarautar tausayin halinda Mahmood ya tsinci kansa ciki suke..! Su matan Wambai kuwa sai jinjina lamarin suke masu k’ara gishiri da onga nayi.. Harda masu cewa Giwa ce ta cinye ‘ya’yan Yarima Yazeed Wai mayya ce, ita ta cinye matar Mahmood ta cinye mai Martaba harma da Wambai itace Ta cinyesa Ta kuma cinye k’afar Jamal guda Ta cinye hannayen Yazeed..!

Juwariyya d’iyar Wambai da itace takaiwa su Raheema da Gimbiya Zeenatu labari gaba d’aya tsoron al’amarin ya gama cikasu.. Gimbiya Zeenatu jikinta yafi na kowa yin sanyi, zataso Ta sami Mahmood Ta sanar dashi yanda ta rufe asirin Giwa na kashe matarsa da tayi dan kawai k’anwarta Raheema Ta aure Mahmood d’in, akan idanunta Giwa Ta halak’a Matar Mahmood, Ta kuma ce ta halak’ata ne dan Mahmood ya auri k’anwar Zeenat d’in Raheemah... matuk’a Aliya nada rai tasan d’anta Mahmood bazai tab’a kallon wata mace ba balle ya aureta, Anya bazat sami Mahmood Ta sanar dashi gaskiyar batun ba..? Ta k’arashe tunanin nata tana mai mik’ewa tsaye cikin tsananin sanyin jiki..

Juwariyya dake ci gaba da labartawa Raheema yanda abubuwan suka kasance dakatawa tai suna duban Gimbiya Zeenat da Ta mik’e jiki babu k’wari..!

Raheema tace “Aunty Ina kuma zakije.. Kinaji ance cikin Masarauta babu lafiya Dakaru ne ta ko ina.. Salon Ki fice wani tsautsayin ya ritsa dake, Allah ya gani Masarautar nan ya soma bani tsoro asubahin fari gobe zan tattara na koma Masarautar mu saidai duk abinda za’a fad’i a fad’i..!”

Gimbiya Zeenat da har lokacin jikinta a matuk’ar sanyaye yake tace “Raheemah Mahmood nake son gani akwai abinda nake matuk’ar son sanar dashi.. Gwara na sanar dashi bazan iya ci gaba da rik’ewa a cikin zuciyata ba..!!” Ta k’arashe tana mai rufa alkyabbarta ta nufi k’ofa...

Raheemah na kiranta inaa ko tsayawa batai ba..

Juwariyya Ta dubeta tace “Ahtoh dai ki tafi ki bar Masarautar nan kafin ta iso kanki..!”

Raheemah Ta dubeta da mamaki tace “Ban gane ba..?! Wai mai Giwan tayi yanzu ake nemanta haka..?!”

Juwariyya ta tab’e baki tace “Tabb! Yanzu ne duk labarin da nake baki ina hankalinki yake..! Ance miki ta sace matar d’anta zata cinye..!”

Raheemah ta girgiza kai tace “Ban fahimceki ba..! Wai kina nufin Zuhra..! Zuhra kam ai tana asibiti inji..!”

Juwariyya Ta dubeta shek’ek’e tace “Wata Zuhrar..! Ana miki maganan matar Yarima Mahmood..!”

Mamaki ya kuma kama Raheemah..! “Matar Yarima Mahmood fah kikace..? Yaushe Mahmood d’in yayi auren..?!”

Juwariyya Ta yab’e baki tace au ashe fah bakida labari kina nan kina jimamin rashin aurensa da bakiyi ba, gashi kin kasa zuwa asibiti kiga yanda mijinki Yazeed ya koma...!”

Cikin tashin hankali Raheemah ta katseta da fad’in “Ke ni k’i k’yaleni da zancen Yazeed, duk halinda ya tsinci kansa ciki ba matsalata bace tinda shine ya jefa kansa ciki..! Tambayarki nake shin Yariman nawa shine yayi Auren...Mahmood ne yayi aure...? Yaushe kuma a ina..?!!” Ta k’arashe idanunta na firfitowa waje hannuwa dafe da k’irji...!

Juwariyya da tai sakare rana dubanta jinjina mata kai tai tace “K’warai kuwa Rankaidad’e yayi aure, ranan da ya d’aura miki aure da Yazeed ranan yayo aurensa shima...! A yanda naji labari na Yawo cikin Masarauta babu wanda yasan yayi auren sai abokinsa Turaki da Hadiminsa, ke ko Giwa bata sani ba, naji ana cewa ya b’oye mata auren gudun kada Ta lashe masa matar tasa ne kaman yanda ta lashe matarsa ta farko, Aiko gashi data fahimci yayi auren Ta lashe sabuwar amaryar tinda babu wanda yasan k’anda suke yanzu.. Labari fah nata Yawo cikin Masarauta gashi ance Sosai Rankaidad’e ya rikice da neman matar tasa da alama yana matuk’ar k’aunarta..!!”

Gaba d’aya Raheemah bama Ta gane mai Juwariyya Ke fad’I saima hawaye dake k’ok’arin ambaliya a fuskarta..! Babu shiri Ta mik’e ta nufi waje cikin kuka..!
Juwariyya Ta mik’e tabi bayanta tana kiran sunanata...! Inaa Raheema bata tsaya ba burinta kawai ta isaga Mahmood ta tabbatar da gaske aure yayi ta kumaga matar da ya aura...

**

Ana tsaka da wannan kwanacala Yazeed ya iso Masarauta....

Ganin yanda ake satan kallonsa ana k’usk’us cikin Masarautar sosai ya kuma tunzura Yazeed, Wato yanzu ya zama abin nunawa da baki.. Wasu bayi da suka kasa janye idanunsu daga barin duban nasa suka kuma kasa duk’awa gabansa wane irin tsawa ya darara masu yana fad’in Shine Yarima Yazeed wanda ya kuma cancanci gadon mulki ko ba’a sarki maras hannaye za’a soma a kansa..!

Shidai Waziri gaba d’aya yasha jinin jkinsa da ganin yanda Masarautar take a hautsine.. Duk basu kawo komai ba dan duk sunyi zaton dalilin tsautsayin da ya afkawa Yazeed da iyalansa ne Masarautar Ke yamutse...

Duk wanda yaga Yazeed sai ya kuma dubansa kafin ya risina...

Sai sakin huci Yazeed yake yana ayyanawa cikin ransa duk Mahmood ne ya janyo, da ace ya auri Raheemah Sun tafi k’asar Spain duk da hakan bata faru dashi ba, da yanzu hannayensa da ahalinsa duk suna nan, wani irin tsanar Mahmood d’in ya kuma tokare masa k’irji... Inama yanada hannuwa biyu da ya shak’e Mahmood a yau ya mutuwa ya huce takaicin ganinsa a doron k’asa...

A daidai mashiga babban k’ofar da zai sadaka da cikin Masarauta su Yazeed suka had’uda tawagar Mahmood.. Da alama ficewa neman su Giwa zasuyi...

Gaba d’aya illahirin jama’an dake wajen suka maida dubansu ga Yazeed wanda tuni ya isa gaban Mahmood yana mai sakin huci... Waziri yana k’ok’arin sallaman wad’anda ba ahalin gidan ba Yazeed ya bud’e murya yace kowa ya tsaya, ayi a gaban kowa susan wanene Mahmood..!

Shi kuwa Mahmood kalaman Ansar ke ci gaba da buga zuciyarsa cewa ‘yanuwansa su suka lalata rayuwar Muhibbah, ya tuna Fu’ad ya sanar dashi Yazeed ne ya soma..! Zuciyarsa taci gaba da bugawa musamman da yaga Yazeed tsaye gabansa... Sai dunk’ule hannayensa yake yana murzasu wani irin gumi na tasowa tun daga tsakar kansa yana bin goshinsa har zuwa saman karan hancinsa yana gangarowa... Ji yake idan ya rik’e wuyan Yazeed tabbas zai iya kaisa lahira... Muryar Yazeed d’in suka sinkaya yana furta “Kaji dad’i..! Nace kaji dad’I Mahmood..!! Yanzu da kake ganin sarauta takace kai kad’ai dan ba’a Sarki muskini..! Idan ba’a Sarki muskini Toh ka sani ba’a sarki k’ask’antacce...! Yes na fad’a ba’a Sarki k’ask’sntacce, jinin Bauta wanda bai gaji komai ba face Bauta..!!”
Chapter 126 · 0% Book details