Sashe 105
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A parlor ya tadda Mahmood d’in alamun isowarsa yake jira... Kasancewar dare ne yana damk’a masa bai wani zauna ba ya juya abinsa... Mahmood kaw da kansa ya nufi b’angaren dan Dama sashensa da yayi zaman aure da Aliya nan ya aje Muhibbah ciki, yanada mabud’an ko wani k’ofa a sashen... Abinka da dare k’afa ya d’auke babu wanda ya kula da fitowarsa har ya isa shashen... Da mabud’an hannunsa yayi amfani ya bud’e ko wacce k’ofa har ya isa d’akin da Muhibbah take...
Yayi tsaye yana jin yanda ruwa Ke zuba daga bathroom alamun har yanzu dai bata fito daga wankan ba... Can gefe ya hangi abincin da aka kawo mata ko tab’awa batai ba, babu abinda taci ko ruwa bata sha... Yasan bazai wuce tsoro takeji ba, hannu yasa cikin aljihun jallabiyarsa ya ciro ‘yar k’aramar pen ya isa jikin paper bag d’in yayi rubutu...
Ita kaw Muhibbah har lokacin tunanin Ansar da Mommy take hawaye na ci gaba da zuba mata tasan dukansu biyu hankalinsu ba’a kwance yake ba da tashinta duk yanda suke...
Duk azzalumin da ya d’aukota ya aje a nan ya cuceta ya kuma cuci ahalinta, har abada bazata tab’a yafe masa koma wanene.. Balle ma tasan Bazai wuce aikin Giwa azzaluma ba, tasan wani tanadin mugunta take mata, kafin Ta cimma burinta akanta zata San yanda zatayi ta guje daga wannan kurkukun da izinin Allah...
Tana wannan tunani Ansar yana can ya kuma bud’e idanunsa ya dubi Mommy ya dubi Hameedah... Mommy Ta taso da sauri ta dafasa tana fad’in “Ansar a kira Dr ne... Ansar d’ah na talk to me..!”
Lumshe idanunsa ya kumayi sai yace “Mommy Muhibbah... Take me to her... I want see her... Please take me to her...!” Tin daga haka bai kuma cewa komai ba sai kuma rufe idanunsa da yayi... Kukan da Mommy Ke k’unshewa ya kuma kece mata... Kuka take tana fad’in “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Oh ni Murjah yau naga takaina... Na halak’a d’ah nah da kaina...! Ansar duk abinda ya sameka Bazan tab’a yafewa kaina ba... Domin kuwa ni ce sila..!” Ta k’arashe cikin kuka sosai...
Hameedar ma kuka take sosai Ta isa Ta dafe hannun Mommy tace “Mommy Kiyi hak’uri in sha Allah Ya Ansar zai sami lafiya, ki daina fad’in maganganu haka... Bawa baya wuce k’addrarsa a rayuwa..! Allah ya k’addari hakan sai ya faru.. Kiyi hak’uri kiyi masa addu’a kinji mommy... Addu’arki shi Yafi buk’ata a yanzu..!”
Jinjina kai kurum Mommy take bata ko iya amsa mata, Yarinyar ta kamo hannun Mommy ta k’araso da ita saman sofa dake daga can gefe cikin d’akin tace “Mommy ki kwanta a nan, kinga Kema d’azu Dr yace jininki ya hau, ya kamata ki huta Ya Ansar baziji dad’i ya tashi yaga kema kin kwanta rashin lafiya ba.. Ki huta Kinji mommy..!” Ta k’arashe tana taimakawa Mommyn ta kwantarta...
Hameedar bata bar gefen Mommy ba har saida taga Ta lumshe idanunta irinta mai bacci.. Ta mik’e ta komo kusan Ansar Tai masa K’uri hawaye na ambaliya a fuskarta...
Lokaci guda take masa fatan samun lafiya had’ida sauk’in al’amarin da suka tsinci kansu ciki gaba d’aya...
**
Koda Muhibbah ta fito mamaki ne ya cikata ganin shopping bag aje saman gado, kaman mai jin tsoro haka ta isa jikin ‘yar jakan... Gabanta sai fad’uwa yake dan a iya saninta Kuyangin sun tafi bacci Toh waye ya shigo ya aje wannan jakan... Tsoro ya kuma kamata, Ta shiga ‘yan waige waige bataga kowa ba... Toh kodai kuyangin basu tafi bane..? Ta lek’a cikin jakan a hankali nan taga sanitary pads ne cike cikin ‘yar jakan... Gabanta ya kuma tsinkewa... Ya akai Kuyangin suka San tanada buk’atan wannan... Saikace masu aiki da iskokai... Kodai matsafan Giwa ne suka sanar da ita..? Toh amma Maiyasa Giwa bata fara mata azaba ba har yanzu saima treating d’inta nicely da takeyi... Zuciyarta ta raya mata babban ukuba take tanadar miki shiyasa take binki a sannu..!
Ta d’ago jakan tana binsa da kallo nan gefe taga wani rubutu mai d’an karan kyau gashi dai da biro akayi rubutun balle tace bugun company ne masu k’era jakan ne suka rubuta... Sam bai yi kama da ace hannu ne ya rubuta ba, abinda aka rubuta shine yafi tafiya da hankalinta..
_Kina tareda kariya a nan fiyeda yanda kike zaton zaki fi samun kariya.. Rashin cin abincin ka iya janyo miki rashin lafiya_
Ta karance sak’on yafi sau abinda yafi... Tinda ta tab’a jakan hannunta ya kamata k’amshin dake jikin jakan... Ta rasa a ina tasan irin k’amshin kuma wannan k’amshin shine taji duk ya dabaibaye jikinta sanda ta farka a bacci... Tasan irin k’amshi but she couldn’t figure out ina tasan k’amshin... Wani ikon Allah bayan karance sak’on nan da tai sai taji natsuwa ya d’an sauk’o mata kad’an, Ta d’auki bag d’in ta bathroom dan kintsa kanta... Lallausar doguwar riga ta zira ta bar kanta a bud’e dan ya ida bushewa, k’anan kitson aurenta da aka mata ya bi wuyanta ya kwanta luf...
Tinda Ta fito a haka daga closet d’in ya kasa janye idanunsa daga dubanta, hab’arsa d’aure saman hannunsa yake kallon duk wani motsinta yacce kasan mai kallon shirin film da yayi matuk’ar tafiya da hankalinsa da tunaninsa baiso yayi missing koda scene guda ne... Yanda take tafiyar kaman wata mai tsoron taka k’asa haka ta k’araso saman darduman ta zauna a hankali tana mai bin kayan abincin da kallo... Ta hard’e k’afafunta ta zauna tana bud’e dishes d’in...
Allah ya gani batada appetite bazata iya cin komai ba... Maida murafen tai ta rufe kana Ta rapka uban tagumi tana duban jerin abincikan dake gabanta...
Ji yake bazai iya bacci ba har sai ta tabbata ta saka wani abu a cikinta, duk abinda ya sameta Ta dalilin yunwa zai zamto laifinsa tinda shi ya d’aukota ya ajeta... Ya lumshe idanunsa a hankali yana tunanin kodai yaje ya turasasa mata cin abinci ne... Amma yin hakan na nufin ya tona kansa kuma bazata bari ya fahimci ainihin motive d’inta gameda Masarautar ba harma da rayuwarsa da na d’iyarsa da taso tarwatsawa... Idanunsa a lumshe yake tinanin kaman ance ya bud’e ya dubeta nan yaga Ta janyo farantin fruits Ta lumshe idanunta had’ida furta bismillah a hankali... Nan Ta soma cakalan fruits d’in dan rabonta da abinci tun had’inda gudidi ta bata tace ta shanye kuma idan har tana so ta cimma burinta na gudu daga wannan kurkuku she needs to maintain her strength idan ba haka ba bazata iya guduwa ba dan haka cin abinci ya zamto mata dole koda bata so... Haka Ta rintse idanunta taita tura abincin tana b’ata fuska tamkar mai cin magani... Yanda take da fuskarta sosai yaso basa dariya... Can k’asan zuciyarsa yana jin sanyin ta saka wani abu a cikinta at least, yanzu zai iya kwanciya...
Da wannan tinanin ya mik’e ya nufi band’aki ya d’auro alwalais yazo ya tada sallah nafilfili wanda d’abi’arsa ce duk dare before going to bed...!
A b’angaren Muhibbah kuwa tunda ta d’an saka wani abu a cikinta bacci ya kuma yin gaba da ita... Nan cikin baccin nata take mafarki da Mahaifinta...
Tana kuka tana sanar dashi azzaluman Masarautar Sun kuma kamata zata nemi hanyar guduwa Ta ko wani hali ta gudu... Mahaifinta ya girgiza mata kai yace “Nan shine gidanki Saudatu..! Bazaki bar gidan nan ba... Akwai mutane da suke buk’atar kasancewarki a nan ciki harda k’annenki guda biyu...!” Daga haka Mahaifinta ya b’ace bata kuma ganinsa ba...
Da salati saman bakinta ta farka zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Wannan wane irin mafarki tayi da Abbanta... Mai yasa yace nan shine gidanta..? Su waye k’annenta guda biyu... A iyaka saninta batada k’anne... Kuma k’anwarta d’aya ce mai suna MUHIBBAH kuma ta rasu tana jaririya a lokacinda wuta ya cinyesu itada Mahaifiyarsu a sansanin ‘yan gudun Hijira da suka fake a Sansanin dake Yalawan Shandam..! Hasalima sunan k’anwar tata Muhibbah ta maida wa kanta...Toh su waye k’annenta da Babanta yace suna nan cikin wannan masarauta..?!!
SameenaAleeyou 📚
SameenaAleeyou📚
*MUHIBBAH*
*65*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
NOT EDITED!
Ta lumshe idanunta a hankali mafarkin bai b’ace mata a kwanyarta ba, Toh kodai Taswiran nan abinda yake nufi kenan... K’ila akwai wasu mutane b’oye cikin ginin azzaluman cikin Masarautar nan sun b’oyesu Babanta yanaso ta taimaka masu amma baya ga haka bata tunanin akwai wani jininta cikin wannan masarauta... Toh mi zatai menene abinyi gashi ta baro zanen a gida, hasalima batasan yanda ta jefar ba...! Ta dafe kanta a hankali zuciyarta na ambaton Allah ya warware mata wannan al’amari cikin sauk’i...
**
Safiyat Washe gari a d’aki Jamal ya tadda Giwa sai faman kaiwa da kawowa take tana sak’awa tana warwarewa... Yau kam jikin Jakadiya da d’an sauk’i dan tare suka shigo da Jamal d’in Dama isowarsu Giwa take jira... Suna shigowa Giwa ta dubi Jakadiya tace “Kin tabbata Zahra’u ce ta baki mayafin nan..?!”
Jakadiya ta jinjina kai tace “Allah shi taimakeki wllhi Allah nayi imani Gimbiya Zara’u itace Ta bani mayafin nan..!”
Jamal da Giwa suka dubi juna, Jamal zai magana Giwa ta k’araso gabansa tace “Kada ka damu d’ah na kaje kaji da Amaryarka, so nake ka tareda kyakkyawar Amaryarka a yau... Kaga kai sabon ango ne bai kamata wani hidimar ko wani damuwa yasha gabanka ba, I can handle Zahra I promise..!”
Jamal yai shiru ya tsareta da idanu sai kuma yace “Maami gobe nakeda ganin Dr a asibiti yace k’afar roba da aka min ya zama ready... Ni a nawa tsarin nafi so idan aka zaka min sabuwar k’afata na tareda Amaryarta dan banaso ta ga k’afata a haka..!”
Giwa Ta k’ak’aro murmushi tace “Toh banda abinka Jamal ai a haka da yankakken k’afar taka ta ganka tace tana sonka, Umaima sam bazata damu dan taga k’afar angonta guda d’aya ba dama tasan abinda ta aura ai... So wannan ba abin damuwa bane... Tuni nasa an gyara maku sashen da zaku zauna, an zuba komai na buk’ata ciki... Gida ya tsaru masu shi kawai yake jira...Ni nafi so ka bada himma ga batun tariyarku dan Farin cikinka shine gaba da komai a wajena..!” Ta k’arashe tana shafa b’angaren fuskarsa guda cikeda kulawa wanda zaka rantse har cikin ranta Farin cikin d’an nata ne ya dameta...