← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 162

Sashe 69

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna tafe suka hange Zuhra da Raheema harmada Umaima hankali tashe sun fantsama cikin Masarauta dan da alama labarin abindake faruwa ya gama karad’e cikin Fada...
Muhibbah tana hangosu Ta kuma janyo hannun Zahra had’ida canza masu hanya cikin sauri dan bata fata ta had’uda kowa cikin Masarautar a halinda Masarautar Ke ciki....
Gaba d’aya ranan Masarautar a yamutse take abubuwa ne da dama suka faru gashi uwa uba an nemi Mahaukaciya Izzatu cikin Masarautar an rasa... Neman duniyar nan anyi an rasa yanda Ta shige... Ga Jamal kwance rai hannun Allah kan kace mai dafin jikin Takobin da Majidad’i ya sara masa a k’afa tasa k’afar tayi bak’ik’irin tamkar ba’a jikinsa yake ba, shi kad’ai yasan azaban da yakeji... Cikin gaggawa aka nufi asibitin koyarwa dashi koda wani abinda za’a iya dan da alama cikin sakanni dafin Ke haurawa jikinsa kaman wani Saran bak’in kumurcin maciji, gaba d’aya k’afar ta sauya halitta ta koma tamkar bak’in gawayi Dukda kuwa hasken fata da Jamal kedashi.....
Duk wannan hali da ake ciki babu wanda yasan Fu’ad yana kwance cikin d’aki yana aman farin kumfa sakamakon drug overdose da yai... Tashin hankali ne dai wanda ba’a saka masa rana kowa cikin Masarautar hankalinsa a tashe yake....
Dole Mahmood da Turaki ma suka nufi asibitin koyarwa dan sanin halinda Jamal Ke ciki Dukda kuwa tashin hankali da shi kansa Mahmood d’in yake ciki bayan abinda d’iyarsa Zahra tai masa a bainar jama’an Masarauta....

Shi kuwa Yazeed tinda ya samu ya kub’uta daga hannun Majidad’i babu wanda ya kuma sakasa a ido dan tin lokacin yai ficewarsa gaba d’aya daga cikin Masarautar, bai zarce ko ina ba sai club d’in da suka saba had’ewa da watsattsun abokansa... Tinda ya isa wajen kuwa banda kwankwad’an Barasa baya aikin komai, harta abokan nasa saida suka razana da irin giyar da Yazeed Ke zubawa cikinsa... Bai masu magana ba bai ce masu komai ba tinda ya isa wajen shan barasa kawai yake ko zai mance tashin hankalin da ya baro cikin Masarautar su...

**

A b’angaren Muhibbah kuwa bata k’yale Zahra ba daidai da dak’ik’a guda, har saida bacci ya d’auki yarinyar, tai zaune a gefenta tana duban fuskarta cikeda tausayawa, taita tuna abubuwa da dama gameda yarinyar da mahaifinta tin farkon zuwanta Masarautar... Hoton Zahra rungume da Mahaifinta dake gefen bedside Muhibbah ta d’auko tana kallo hawaye tab idanunta, tasa hannu a hankali tana Shafa hoton hawayen na zirarowa daga idanunta... Ta lumshe idanunta a hankali sanda taji kuka mai k’arfin gaske na zuwa mata, a hankali Ta maida hoton yanda ta d’auko kana Ta fice daga d’akin cikin sauri... Masauk’inta ta tafi ta shige k’uryar d’aki ta fad’a saman gado tana shesshe’k’ar kuka mai tsuma zuciya... Tana ganin kiran Ansar na shigo mata amma sam bata iya d’agawa ba sai kuka dake kuma kufce mata mai ban tausayi.... Kaman wacce aka sinkaya ta mik’e ta soma shiri... Kayanta ta shirya cikin akwati da zimmar Washe gari idan Allah yakai rai asubahin fari zata d’auki hanyar Bauchi...

**
Babu yanda Mahmood baiyi ba Giwa ta koma masarauta amma fir tak’i tace bata barin cikin asibitin har sai likitocin da suka shiga aiki ma Jamal sun fito sun sanar da ita d’anta is stable, daga ita har Jakadiya sai faman kai komo suke, tana tafe Jakadiya na take mata baya sauran Hadiman nata na risine daga gefe...
Mahmood da Turaki harmada Waziri suma duk suna gefe suna jiran fitowar likita... Jim kad’an likitan ya fito ya nufosu, sukai masa chaa suna jiran ta bakinsa....

Da hak’uri likitan ya soma masu, Giwa ta shiga girgiza kai tana fad’in “Likita bana son jin irin wad’annan kalaman, ka bud’e baki ka sanar dani halinda d’ah na Ke ciki...!!”

Dogari guda ya bud’e murya yace “Hattara Bokan Turai, Giwar Amale bata jiran amsa daga bakin Talakawanta....!!”

Likita yai gyaran murya yace “Prince is stable now....But there’s something in his life that would remain irreversible... I’m sorry to say we did everything we could ganin gubar batai tasiri cikin jikinsa ba, a dalilin haka... we had to amputate his leg... Da ace bamuyi gaggawan cire k’afar ba tabbas da gubar ta haura zuwa zuciyarsa wanda hakan ka iya kawo sanadiyar mutuwarsa....!!”

Kuka ya kufcewa Giwa yayinda Mahmood ya lumshe idanunsa a hankali, yai saurin k’arasawa ga Giwa yana bata baki... Ya dubi likitan yace suna iya ganin Jamal... Likita ya jinjina kai yace “We’re moving him to the resting room in a bit... Zaku iya shiga can ku gansa Your Highness... Excuse me...!” Ya k’arashe yana mai shigewa...

Yarima Mahmood ya janyo hannun Giwa da har lokacin bata koma daidai ba ta k’asa yarda Wai Jamal d’inta ya zama mai k’afa guda, haka suka nufi d’akin da aka kwantar da Jama cikin matuk’ar sanyin jiki....

Giwa tana hango Jamal kwance da yankakken k’afa Ta rintse idanunta tana k’ok’arin danne kukan dake zuwa mata, Ta k’arasa jikin gadon tana shafa k’afar nasa take fad’in “Jamal d’ah na..!!” Tsananin rawa da muryarta keyi ya hanata ci gaba da magana...

Mahmood ya tsaya daga d’aya gefen yana duban d’an uwan nasa cikeda tausayawa...
A hankali Jamal ya bud’e idanunsa yana dubansu, lokaci guda ya yunk’ura zai tashi yaji tamkar babu k’afarsa guda a jikinsa... Yai saurin kai hannunsa maras cannula dan tabbatarwa ai kuwa babu k’afar an cire...
Cikin tsananin tashin hankali yake furta “No no no no... This can’t be happening... Maami what’s going on... Where’s my leg... I want my leg back... Tell them to bring me back my leg...!!”

Mahmood ne yai saurin dafasa cikin k’ok’arin bashi baki “Calm down please Jamal, everything will soon be alright kaji, just calm down kaji d’an uwana... Bayan takobi mai guda da Majidad’i ya sara maka is a miracle you survived... Ka gode ma Allah kaji da ya k’addari cewa akwai sauran rayuwa gaba gareka...!”

Cikin zuban hawaye Jamal Ke fad’in “Yaya shikenan na zama nakashashhe... Yaya ka dubeni fah ka gani... Ka dubi halinda nake ciki you could you except me to calm down...! I shouldn’t be in this position, maiyasa na karb’i fad’an Yazeed wanda shi bazai min haka ba... He should be the one here not me...!”

Mahmood yai saurin dafasa yana mai girgiza kai yake furta “Kar kayi magana haka Jamal kai musulmi ne kuma nasan ka yarda da K’addara mai kyau ko akasinta... Wannan itace k’addararka Jamal, koda ace Yazeed bai zama sanadi ba kasa a ranka hakan zai sameka... Bawa baya wuce k’addararsa kaji koh... Kayi fatan Allah ya baka ikon cinye wannan jarabawa taka...!”

Jamal da hawaye Ke gangaro masa k’uri yayima Mahmood yana dubansa lokaci guda yake furta “Yaya... Yaya I’m sorry... Please forgive me...!!”

Mahmood ya dubesa da mamaki yace “Jamal mai kai kake neman afuwa... Ni baka mun komai ba...!”

Wani irin duban da Giwa ta aikawa Jamal ya sanyashi lumshe idanunsa a hankali daidai lokacinda wayar Mahmood d’in ta soma ruri...

Excusing kansa yai ya fice amsa kiran dan da alama daga masarauta ake masa kiran...

Mahmood na ficewa Giwa ta dubi Jamal tace “Koda wasa kada kayi gigin sanarda Yayanka wani abu... Koda wasa Jamal...!”

Jamal na hawaye yake aika mata wani irin muguwar kallo da rinannun idanunsa, lokaci guda yake furta “Maami zunubaina ne suke bibiyata, shiyasa na tsinci kaina a halinda nake yau, na tabbata hakkin wannan yarinyar da duka ‘yanmatan da na lalatawa rayuwa suke bibiyata.... Wanda Duka ke kika umarceni kan son mulkin banza wanda ba tabbata zai ba....Yau ga halinda na tsinci kaina ciki...!!”

Saurin toshe bakinsa Giwa tayi tana fad’in “Rufe bakinka Jamal, duk abinda kayi sadaukarwa ne ma gidanku da ahalinka... Kuma abinda ya sameka ba laifin d’an uwanka Yazeed bane kaima ba laifinka bane laifin wancan tsinannen mahaukacin ne kuma nayi imani sai ya biya abinda ya aikata... Dan haka koda wasa kada na sake jin maganganu irin haka daga gareka...!”

Banda aika mata mugun kallo Jamal baya komai, lumshe idanunsa yai wasu hawayen suka kuma gangaro masa

Mahmood ne ya turo k’ofa ya shigo, yanayin da suka gansa ciki sosai ya kuma firgitasu....

Giwa ta tsaresa da ido tsoro bayyana saman fuskarta, duk a nata zaton yaji tattaunawarsu da Jamal ne.... Ta had’iyi miyau da k’yar kana tace “Sadauki lafiya na ganka haka...?!”

D’an satan kallon Jamal yai yaga idanunsa a lumshe suke kana ya matso kusan Giwa yai mata rad’a a kunne... K’unshe bakinta tai ba tareda ta iya furta koda kalma ba duniyar na neman juye mata... Mahmood ya isa ga Jamal dan baiso hankalinsa ya kuma tashi a condition d’in da yake ciki... D’an dafasa yai kad’an yace “We’d be around idan kana nemanmu, for now Likita yace ka sami hutu kaji...Akwai dogari guda da zaizo ya kula dakai, Allah ya baka lafiya kaji k’anina...!”

Jamal ya jinjina masa kai yana mai dubansa cikeda so da k’auna, ya rik’o hannunsa kad’an yace “Thank you Yaya..!”

Murmushi Mahmood ya sakar masa had’ida shafa sumar kansa kad’an kana yasa kai ya fice Giwa na biye dashi tamkar tayita kurma ihu haka take ji ko zata sami sanyin rad’ad’in da zuciyarta Ke mata...

Suna tafe take ceda Mahmood “Ina Fu’ad d’in... Oh ni Turai naga ta kaina wannan wane irin al’amari ne Ke faruwa da ahalina...?!”

Mahmood ya rik’ota kad’an yace “Maami ki kwantar da hankalinki, Fu’ad yana ER and he’s out of danger now... Turaki yana can wajensa taking care of everything...!”

Giwa na hawaye take duban Mahmood tace “Shi kuma mai ya sameshi...?!”

“Drug overdose...!”
Ta kuma rintse idanunta tana wasu hawayen na zubo mata tashin hankali daga wannan sai wancan...
Mahmood yaima Jakadiya alama da hannu tazo... Ta k’araso cikeda risinawa.. Nan yace Ta kula da Giwa zai k’arasa ya sami Likita...
Chapter 69 · 0% Book details