← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 162

Sashe 81

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Kanada tabbacin zata cika maka burinka..? Kokuwa a iyaka tsawon lokacinda ka kwashe kana mata bauta Ta tab’a cika maka alk’awari...?!”

Ubandoma yai shiru yana juya kalamanta cikin sanyin jiki...!

Ganin yanayinsa ya kuma baiwa Muhibbah k’warin gwiwar ci gaba da magana...

“Babu cika alk’awari a duniyar da babu komai cikinta face zalunci... Shi azzalumi a koda yaushe hanyar da zai rud’eka ya cutar dakai ya kuma yaudareka yake nema.. Babu Aminci a duniyar da yarda da rik’on amana yai k’aranci cikinta..!” Ta kuma sassauta murya tana duban Dattijo Ubandoma tace “Baba lokaci bai k’ure maka ba, you can still do the right thing... Zaka iya zab’an tafarki mai kyau... Alk’awarin Allah gaskiya ne Baba... Shid’in yana tareda masu gaskiya ne..! Kai abinda ya dace ka juya bayawa azzalumai.. Kaji tausayin wannan Baiwar Allah da halinda Ta tsinci kanta ciki wanda idan son ranta ne bazataso ta ganta a yanayin da take ba..!” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka....

Allah sarki saiga Hawaye suna gangarowa daga idanun Ubandoma... Ya k’arasa jikin dakali dake wajen ya zauna yana mai ci gaba da matsan k’walla... Lokaci guda yana tuna abubuwan da Giwa ta umarcesa yayi marassa kyau, ya tuna babu alk’awarin da ta tab’a cika masa, ya tuna kalan wulak’acin da tai masa wanda bazasu lissafu ba ciki harda marin da Jakadiya tai masa, wanda tayi hakan ne bisa umarnin Giwa...
Muhibbah ta dubesa ta kuma duban Izzatu hawaye na gangaro masu gaba d’aya... Lokaci guda Ubandoma yaci gaba da fad’in “Kaico na! Kaicon son zuciya irin nawa..! Tinda nake ban tab’a jin kalaman da suka sanyar min da gwiwa suka sakani nadama ba irinta yau... Hak’ik’a na tafiyar da rayuwata ga bautawa zalunci da juyawa gaskiya baya... Ban tab’a danasanin abubuwan da nayi irinta yau ba.. Yarinya kinyi gaskiya da Kikace azzalumi bazai tab’a cika alk’awarinsa ba, hanyar da zai amfana dakai kurum yake nema... Babu lokacinda zan miki bayanin abubuwan da nayi marassa kyau bisag umarnin Gimbiya Turai amma da na baki labarin komai a yanzu basai anjima ba... Ina fata wad’anda na zalunta ta dalilinta zasu yafeni... Musamman Mahmood... Shid’in mutumin kirki ne... Kuma ina tsoron kasancewarsa cikin Masarautar nan da azzalumai sukai yawa dan rayuwarsa na cikin had’ari..!”

Kiran sunan Mahmood da yai ya sanya wasu hawaye kuma gangarowa Muhibbah tana mai tuna mummunar zato da tai masa a baya.... Tai saurin saka hannu Ta share hawayen da suka gangaro mata tace “Baba tinda ka fahimci haka Alhamdulillah, Ina mai tabbatar maka in sha Allahu bazan bari wani ya cutar da Mahmood ba... Yanzu ka taimaka mu fitar da wani rai da yake bayan ginin nan, mu kub’utar dasu daga wannan azzaluman masarauta..!”

Ubandoma ya dubeta yace “A ina kenan...?!”

Muhibbah tai saurin masa nuni da cikin d’akin kana ta basa labarin abinda ta tadda Izzatu nayi... Yai shiru kaman nazari kana ya murmusa yace “Hak’ik’a gidan nan yanada surkulle da k’ofofi wanda wasu ma iyayenmu basu San dasu ba... Abinda yasa nima nasan da wannan waje an tab’a rufe mahaifina a ciki ne lokacin sarki Baban AbdulJabbar, mahaifina sunyi wani laifi sunci amanan masarauta aka kawosu wanann waje shiyasa nasan da wajen, ba kowa ya sani ba cikin Masarautar nan... Kuma akwai ire iren wanann da dama cikin Masarautar nan... Kinga can..!” Yai mata nuni da wani ginin... Yace inada tabbacin a nan k’ofar d’akin yake, Zo muje...!” Ya k’arashe yana mai sab’a babban gare yayi gaba...

Muhibbah tabi bayansa cikeda mamakin yanda zasu samu k’ofa a wannan waje....
Aiko suna zuwa taga Ubandoma yasa hannu ya tab’a zanen Tanbarin Masarautar da akaima ginin kwalliya da ita... Aiko nan garun ya soma gaucewa... Ga tsananin mamakinta saiga k’ofa....

Suka dubi juna itada Ubandoma, lokaci guda yace da ita su shiga... Itadai da bismillah ta shige cikin d’akin Mahaukaciya Izzatu na biye dasu... Suna shigewa kuwa Ubandoma ya zaro tocilan dake aljihunsa wanda yake haska waje idan zai kawo wa Izzatu abinci ya shiga haska cikin d’akin... Ga tsananin mamakinsu k’aton k’arfe suka hango had’e da manyan sark’ok’i an dadd’aure mutum dashi ga kwanukan abinci ga syringe na allurai a warwatse a wajen... Mamaki ya cikasu, kallo guda zakai ka fahimci mutum ke rayuwa cikin buwayar Ubangiji a wajen... Tsoro da mamakin zalunci dake cikin wannan masarauta suka kuma kama Muhibbah... Cikin sauri Ubandoma ya k’arasa ga mutumin dake fidda numfashi da k’yar alamun ya gama galabaita sabida tsananin yunwa da k’ishin ruwa.. Kai a d’auke wannan ma mutum ya rayu wannan waje saidai buwayar Ubangiji wanda babu abinda ya gagaresa, bazaka mutu ba sai ranan da yace zaka mutu, duk tsanani kuwa idan lokaci baiyi ba shi zai raya abinsa.... Ubandoma jiki na rawa dan shima ya razana sosai... Yasa hannu ya d’an mirgino da mutumin wanda babu komai jikinsa sai ‘yar bante irinta bayin zamanin da turawa Ke d’iban bayi a k’asashen bak’ak’en fata.... Cikin yankewar zuciya ya furta “JA’AFARU...!!”

Sunan Ja’afar da ya ambata ya Sanaya Muhibbah dake bin syringe d’in kallo tana karantawa abinka da wacce Ta karanci wani fanni na kula da majinyata... Tuni ta daskare zuciyarta naci gaba da tsinkewa.....

SameenaAleeyou 📚
[8/24, 10:02 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*52*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Sunan Ja’afar dataji Ubandoma ya ambata ya sanyata mik’ewa jikinta na matuk’ar rawa ta nufo yanda yake a kwance tamkar marass numfashi... Tuni Ubandoma ya warware rawanin kansa ya suturta ma Jafar jikinsa... Muhibbah tai tsaye tana duban fuskar mutumin da Ubandoma ya ambata da Jafar, yau ahekaru goma sha hud’u da kwanaki kenan rabonta dashi... Tabbas ya canza koda kuwa bai cikin yanayin wahala da suka tsincesa ciki, girma ya k’ara canzasa saidai duba guda tai masa ta fahimci shine... Wasu irin hawaye suka gangaro mata, wannan masarauta cike yake da abubuwan mamaki... Tana nan tsaye tamkar statue ta sauraro muryan Ubandoma naci gaba da fad’in “Ja’afaru bawa ne a Masarautar nan wanda ya b’ace tsawon shekara guda yau... Ni nasan ba b’acewa yayi ba Dan a zatona Giwa ce ta gama dashi, ashe a wannan waje aka ajesa ba tareda sanin kowa... Lallai na yarda Giwa zata iya yin komai sabida Ta dawwama kan Karagar mulki... Mulkin duniya da batada tabbas wanda duk soyayyarka da ita dole ka barta..!”

Muhibbah ta duk’a a hankali hawaye naci gaba da gangaro mata... Ta dubi Ubandoma tace “Anya yanada rai...?!”

Ubandoma ya jinjina mata kai bayan ya tab’a wasu jijiyo a wuyansa “Yanada rai, zuciyarsa na bugawa... Bai mutu ba... Abinyi shine muyi gaggawan kub’utar dashi da kuma Izzatu daga cikin Masarautar nan kafin Giwa ta cimmamu Dan nasan duk yanda take yanzu hankalinta a tashe yake...!”

Muhibbah tai saurin jinjina kai tana mai mik’ewa tsaye tace “Haka ne wannan gaskiya ne... Kuma kaima idan tasan ga abinda kayi bazata k’yaleka ba.. Toh amma yanzu meye abinyi..? Ina zamu kaisu..?!”

Ubandoma yai shiru tamkar mai nazari sai kuma ya dubi Muhibbah yace “Akwai wani k’auye can gabas da Masarautar nan mai suna Galambi, k’auyen iyayen matata ne, yanzu haka na tura yarana can tun lokacin da Waziri da Yazeed suka soma min barazana da yarana kasancewar matata Ta rasu banida kowa sai yarana guda biyu... Shisa nake neman ‘yanci na bar bauta ya ko wace irin hanya domin na inganta rayuwar yarana guda biyu kada suma su taso cikin bauta.. Alk’awari na d’aukarwa mai d’akina shisa kikiga idanuna sun rufe bani gane daidai da abinda ba daidai ba burina na samu ‘yanci na cika mata burinta na fidda yaranmu daga k’angin bauta...!”

Muhibbah ta jinjina kai tace “Na fahimceka Baba... Toh yanzu ya za’ai mu kaisu garin matar taka...?!”

Ubandoma yace “Idan muka tafi gaba d’aya Ke za’a iya zarginki a Masarautar nan... Zaifi kyau ni na tafi dasu tinda nasan dole a nemeni kuma dole ayi tunanin ni ne na taimaka masu, sannan babu abunda zasu min barazana dashi a Masarautar nan tinda na tura yarana can da nisa yanda bazasu samesu ba... Ni zan tafi taredasu ayi masu duk wani jinya da ya kamata Dan iyayen matata sunada sani sosai akan abinda ya shafi cututtuka da kuma magani, Allah ya huwace masu wannan baiwar..!”

Muhibbah ta jinjina kai tace “Alhamdulillahi! Amma wani hanzari ba gudu ba Baba... Shin ya za’ai mu fice da Jafar yanda yake a kwancen nan ba tareda an ganmu ba...?!”

Ubandoma ya murmusa kad’an yace “Karki damu d’iyata wannan ai ba matsala bace, muda muka taso cikin bauta... Bari kiga yanda akeyi...!”

Ga mamakin Muhibbah dik girman jiki da tsawo da Allah ya huwace wa Jafar sai gani tai Ubandoma ya ciccib’esa ya azasa bisa kafad’arsa... Ya dubi Muhibbah yace ta fito da Izzatu su bi bayansa... Jinjina masa kai kurum tai kana ta janyo hannun Izzatu suka bi bayan Ubandoma sauri sauri gudun kada suyi artabo da wani...
Ga mamakin Muhibbah wani hanya taga sun nufa can yamma da Masarautar, itadai sai waige waige tsoron kada a gansu...
Ubandoma ya d’an dubeta yace “Ki kwantar da hankalinki babu wanda zai ganmu, wannan k’ofa da kike gani ba kowa ya san da ita cikin Masarautar nan ba... K’oface da dakarunmu suke kwanton b’auna ga abokan gaba musamman a lokutan da suke kokonton samun nasara... Tsohuwar k’oface mai tsohon tarihi wanda a mutanen wannan zamani dake rayuwa cikin Masarautar ba kowa yasan da ita ba...!”

Muhibbah ta jinjina kai suna ci gaba da tafiya tace “Baba da alama kanada ilimi sosai gameda wannan masarauta, kasan abubuwa da yawa k’unshe cikinta...”
Chapter 81 · 0% Book details