← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 162

Sashe 135

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cak ya tsaya da abinda yake sanda ya soma sinkayo muryarta cikin tsananin tsoro tana fad’in kada su cutar da ita alamun mafarki take na abubuwan da suka faru da ita..! Tai wani irin k’ara tana mai k’ank’ame jikinta waje guda, juyin da zatai Ta jita cikin jikin mutum ya mata runfa had’ida matseta tsam cikin jikinsa, tanajin hucin numfashinsa alamun yana karanto mata add’u’o’in tsari yana tofa mata..! Zuciyarta yaci gaba da yankewa, tanajin yanda k’irjinsa yai mata rumfa.. Meke faruwa da ita.. Shin Rankaidad’e ne yake bibiyarta haka..? Toh mai hakan yake nufi..?! Take taji zuciyarta naci gaba da tsinkewa abinda ya faru da ita shekaru goma sha hud’u baya ya shiga dawo mata.. Tsoro da firgici suka cikata..! Ya fahimci yanayin da take ciki na tsananin tsoro da firgici, hakan yasa ya kuma rufeta sosai da k’irjinsa, saitin kunnenta yake rad’a mata “bani daga cikin shaid’anun mutane, bani daga cikin wad’anda suke keta haddi kan abinda damarsu bai mallaka ba..! I’m here now, kiyi bacci cikin aminci.. Bazan bari wani abu ya cutar dake ba... I’ll watch you sleep the whole night..!!” Ya k’arashe yana mai rufa masu bargo da d’aya hannun nasa har lokacin bai saketa ba yana rik’eda ita cikin jikinsa...!

Cikin yanayin tsoro take furta “Rankaidad’e.. Shin kaine..? saida maka ni sukai..?!” Cikin tsananin rawar murya take ci gaba da furta “Kaji tsoron mahaliccinka wanda yake iya ganinka komin duhun daren nan... Kada ka cutar dani..!”

Ta sinkayo muryarsa kaman mai rad’a yana furta “Do you have to keep on buzzing..? Stop asking questions..! Just close your eyes and go to sleep now...!”

Samun kanta tayi tana mai bin umarninsa, Ta rintse idanunta da k’arfin gaske zuciyarta bata daina tsinkewa ba, wannan murya Ta Rankaidad’e ne..! Toh mai yake nufi da kalamansa da yace baya daga cikin shed’anun mutane wanda suke keta haddi kan abinda damarsu bai mallaka ba..? Toh kodai siyar masa ita Baffah Yawale yayi shiyasa ya kawota cikin Masarautar ya aje... Kardai a matsayin Kuyanga ya sayota, kardai ba’a d’aura mata aure da Ansar ba..! Shin Wai meke faruwa ne..?!! Toh kodai ma ba Rankaidad’e bane..!? Idan bashi bane Wanene...?

Ta lumshe idanunta har lokacin tsoron bai saketa ba, tanajin yanda zukatansu Ke bugu cikin na juna, bata San ya akayi bacci ya saceta a yanayin da take ciki ba, farkawa tayi da asuba taga baya nan... Tai saurin kunna side lamp zuciyarta na kuma tsinkewa bataga kowa ba sai wannan musulmin k’amshin nasa dake tashi a hankali kama daga jikinta zuwa yanda ya kwanta..! Ta lumshe idanunta a hankali tana ambaton Allah.. Kalaman mutumin yana dawowa kanta wanda tafi bada k’arfin zaton Rankaidad’e ne..! Meke faruwa..? K’ila dai sayota yayi matsayin Kuyanga..! Wannan tunanin shine yafi tsaya mata a zuciya..! Ta lumshe idanunta hawaye na kuma gangaro mata... Sai tana ganin abin tamkar a mafarki ne ya kasance..! Sosai Ta shiga rud’u da damuwa... Ta shiga lalumen magungunan data sha daren jiyan tana tinanin anya batayi overdose ba..!

**

A b’angaren Mahmood kuwa tinda ya dawo nasa b’angaren ko wane juyi zai sai ya tuna daren jiya, da yanda sukayi bacci cikin jikkunan juna, inama hakan ya kasance ko yaushe, yasan ya barta cikin tarin rud’u da tunanin abinda Ke faruwa tinda har wannan lokaci bai fito fili ya sanar da ita dalla dalla abinda ya faru ba..! Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai tuno k’amshin da ya shak’a cikin jikinta, shikad’ai sai sakin murmushi yake... Yana jan cazbahan dake rik’e hannunsa yana kuma sakin murmushi sanda ya tuna kalamanta a garesa wanda sosai sukaso basa dariya amma ya gimtse... A fili ya furta “So innocent..!!” Tunowa da yayi Muhibbah zata iya kasancewa ‘yaruwar Zahra ya sanyashi mik’ewa zaune sosai yana tuno abubuwan da suka faru...

Ya jima yana zaune wajen yana tuna abubuwan da suka faru sai faman sak’awa da warwarewa yake, dole ya gwada k’wayar halittarsu cikin gaggawa domin tabbatarwa idan sud’in ‘yanuwan juna ne, saida gari ya d’an soma wayewa kana ya fito domin ya nufi k’abarin mahaifinsa.. A hanya ya had’uda Ja’afar da alama shima k’abarin MaiMartaba mahaifinsu ya nufa..!
Ja’afar yana ganinsa ya k’araso suka gaisa, a tare suka jera suka nufi k’abarin mahaifinsu.. Suka jima sosai suna masa addu’a kafin daga bisani suka nufi b’angaren mahaifiyarsu...

A parlor suka taddasu itada Baba Nomau yana karanto mata Alk’ur’ani tana biyawa..!

Cikin jin dad’I suka k’araso suma suna sauraro, saida suka ida karatun kana Mahmood da Ja’afar suka risina suka gaisheda mahaifiyarsu... Suka isa can saman Darduman da Baba Nomau Ke zaune bisa sukai masa musabaha had’ida gaisuwa..!

Baba Nomau ya kamo hannun Ja’afar yace suje Bargan Dawakai ya nuna masa Doki mai Fararen sawaye da yake basa labari kafin ya koma gida..!

Ja’afar na murmushi ya amshi jakan fata ta Alk’ur’an d’in Baba Nomau suka nufo waje yana fad’in “Baba ashe dai baka mance ba..!”

Baba Nomau yace “Yarima ina zan mance, bayan abinda nake son gani ne..!”

Ja’afar ya kuma murmusawa yana mai furta “Aiko wajensu na nufa dan nayi kewan Dawakan gaba d’aya..”

Suka jera suka nufi Bargan Dawaki, Hadiman Masarautar duk yanda suka gansu sai Sun risina Sun gaidasu, abinda Ja’afar yakema wasu a baya yau sai gashi ana Yi masa..! Allah kenan mai juya al’amaransa a lokacin da yaso..!

A can parlorn Gimbiya Turai kuwa gyaran murya tai ta ambato Mahmood da fad’in “Saraki..!”

Mahmood ya amsa mata cikeda girmamawa..

Gimbiya taci gaba da fad’in “Dama inaso nai maka magana kan Saudah...!”

Ya d’ago a hankali yana duban mahaifiyar tasa sai kuma ya maida kansa k’asa...

Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Tinda ga yanda auren naku ya kasance, kafin Ayi shelanka matsayin Sarki.. Kafin ai maka nad’i ina son sanin matsayin auren naku tunda kasan sharud’a da k’aidojin al’adu da dabi’u na cikin Masarautar nan..! Idan har Saudah bata k’aunarka a matsayin miji da zatai rayuwa dakai bazanso Ta kuma wani rayuwar k’unci nan gaba ba... Ta cancanci Farin ciki bayan tulin iftila’i na rayuwa data fuskanta..! Shiyasa nace kafin ayi maka nad’i a ambaceka a matsayin Sarki, Ina son sanin matsayin wannan auren naku..!!” Ta k’arashe cikeda kulawa..

Wai ance ba’a San Sarki da fad’uwan gaba ba sannan ba’a Sarki rago amma shikam tabbas wannan tambaya da mahaifiyarsa tai masa ya d’auresa gaba d’aya had’ida haifar masa da fad’uwan gaba wani na bin wani...!

D’an gyaran murya yai yace “Ummi dama akwai wani alfarma da nake so..!”

“Alfarma kuma Saraki..?!” Ta nanata a hankali tana mai dubansa...

SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*

*78*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Kafin Mahmood yakaiga furta wani kalma amintacciyar Hadimar Gimbiya Turai ta nemi izinin shigowa, saida ta duk’a cikeda risinawa ta gaida Yarima da mahaifiyarsa kana tace “Allah shi baka yawan rai Barde yana k’ofa yace a sanar dakai isowan Turaki..”

Mahmood ya jinjina kai a hankali alamun amsawa, Ta kuma risinawa ta nemi izinin fita...

Maidoda dubansa ga mahaifiyarsa yai kaman zai magana sai ta katsesa da fad’in.. “Yanayin dana ganka ciki Allah yasa lafiya...? Ina saurarenka wane alfarma kake magana..?”

Shiru ne ya d’an biyo baya kafin yai gyaran murya kad’an yace “Kan batun d’iyata Zahra ce... Inaso ki bani lokaci kad’an, nayi alk’awarin zanzo miki da bayanin komai a dunk’ule..”

Maganan Muhibbah suke ba Zahra ba, amma da alama so yake ya kawar da zancen shiyasa ya kawo batun Zahra, shiru ne ya ratsa tsakani kana ta jinjina kai tace “Ba damuwa, Allah ya kaimu lokacin... Kaci karin kumallo ne..?” Ta tambaya tana dubansa cikeda kulawa..

Wani irin sanyi mai gauraye da rahama yakeji cikin zuciyarsa, tinda yake da Giwa bata tab’a tambayarsa lafiyarsa ba, yunwarsa ko k’ishin ruwansa damuwarta kawai ya cika mata burinta ya d’ale Karagar mulki... Yau ga mahaifiyarsa Ta asali tana kula dashi irin yanda akema k’aramin yaro Dukda yawan shekarunsa..

Ya jinjina kai a hankali yace “Naci Dibino da ruwan shayi kafin na shigo..”

Kanta a k’asa irin kunyar nan da akewa yaran fari ta murmusa domin kuwa ba kowa ya tuno mata ba face Mahaifinsa, hakan yakeyi wasu lokuta.. “Ka zama Bak’on Buzu da gaske kenan..” Ta fad’i murmushin bai bar saman fuskarta ba...

Shima d’in d’an Murmusawa yai kad’an yana mai k’ok’arin mik’ewa

Ya risina kad’an yace “Na barki lafiya Rankidad’e..!” Harda ‘yar d’aga babban yatsa yai mata alamun jinjina... Sai yana tuno mata da lokutan baya lokacin tana can masarautarsu kafin tayi aure... Hak’ik’a lokaci yayi da zasu waiwayi gida...

**

A parlornsa ya tadda Turaki yana jiran k’arasowarsa... Bayan sun gaisa Turaki yai gyaran murya yace “Wai lafiya ka d’add’agoni da sassafen nan... Kodai Gimbiya turned Rankaidad’e down ne..” Ya k’arashe cikin sigan wasa..

Mahmood yai masa wani duba da gefen idanu had’ida girgiza kai, shidai Turaki ba’a rabasa da jin baki, ba tareda ya furta komai ba ya nufi upstairs.. Jim kad’an ya dawo rik’eda sealed ledoji guda biyu a hannunsa, ya mik’awa Turaki yace “Gwajin k’wayar halittar samples d’in nan nake so... If possible kar ya shige cikin satin nan kafin ayi nad’in sarautar nan...”

Turaki ya dubesa da mamaki yace “DNA test your Highness..? Samples d’in su Yazeed ne ko kuwa na su waye..?”

Fuzar da huci yai kad’an ba tareda yace komai ba saima juya ledojin yake a hannunsa wanda d’aya toothbrush d’in Zahra ne ciki d’aya kuma sumar Muhibbah ne da ya tsinko jiya akanta a ciki...

Murmusawa Turaki yai yace “Mahmoodu hadari sa gabanka yanda kake so.. Tambihi gagari fasahar yaro... Idan tayi tsami dai zata fito Fada Sank’ira ya mana shela..”

Murmusawa yai kad’an wannan karon suna duban juna su duka biyun sanda Turaki yasa hannu ya amsa...

A hankali ya furta “Thank you..”

Murmusawa kurum Turaki yai had’ida furta “An gama Rankaidad’e.. Zanyi k’ok’ari na tabbata an samu within the week..”

Mahmood ya jinjina masa kai, har zai fice ya dawo da baya yace “Aff kaga na mance Rankaidad’e.. Tare muke da Dr Ansar zai shigo yai maka sallama idan anyi masa izini, sannan a bashi dama yayi sallama da Gimbiya Muhibbah, yau yake son komawa garinsu...”

Take ya had’e rai sosai yana duban Turaki k’asa k’asa, kaman wanda baison magana ya soma fad’in “How Many times do I have to tell you.. I don’t trust that Dr, especially around my wife..!”
Chapter 135 · 0% Book details