← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 162

Sashe 63

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su duka biyun sukai tsaye suna duban juna... Fu’ad ne ya soma sakar masa murmushi kana yace “You’re a loser Yazeed...! Sarautar da kake so bazaka tab’a samu ba, kanaji kana gani Yaya zai d’ale Karagar nan... Kuma kasan maiyasa na kiraka da loser...” Ya murmusa kad’an kana yaci gaba da fad’in “Sabida dik abinda ka sa gaba baka samun nasara... How about our bet... Nasan maybe ka mance sabida ta yab’a maka magana ta ajeka a yanda ya kamaceka... Kuma kasan menene zaifi maka ciwo Prince Yazeed... Ni da ita d’in masoya ne, she chose that psychopath over you...you lost to me Yazeed and too bad kana cikin Masarautar nan zakaga aurenmu... To cut it short, Na d’agaka na bugaka da k’asa a wannan wasan kaman yanda Yaya zai kuma bugaka da k’asa a wasanka dashi... So now tell me Yazeed AbdulJabbar... Among the two of us who’s a failure..?!” Ya k’arashe yana mai sakar masa murmushi da gefen baki...

Yazeed yaci gaba da tururi yana aikawa Yazeed muguwar kallo... Hannu ya d’aga zai kai masa mari “How dare you Fu’ad!!”

Fu’ad ya damk’e hannun nasa shima cikin huci yake furta “Kada ka kuskura ka sake kwatanta wannan kuskuren dani Yazeed... If not...!” Ya murmusa kad’an sai kuma ya saki hannun Yazeed d’in ya fice gaba d’aya daga parlorn....

Yana ficewa Yazeed yasa kai ya fice cikin sassarfa zuciyarsa naci gaba da k’una....

Zuhra na ganinsa haka tai saurin sallaman kuyanginta tana mai k’arasawa garesa cikin tsananin tashin hankali... “Prince lafiya... Mai ya faru dakai..?!” Ta k’arashe tana mai rik’e baki ganin wuyansa yayi shati kaman ya tara jini..
Bai amsata ba hasalima kota kanta baibi ba yayi hayewarsa sama, sai sakin fuci yake, gaba d’aya zuciyarsa a jagule take... Haushin komai da kowa yake, Zuhra ta turo k’ofa ta shigo cikin sand’a kaman mai tsoron kada ta tada jariri mai bacci...

Ta saci dubansa kad’an ta d’an had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’oshi tana yunk’urin k’arasawa gareshi da zummar duba ciwonsa... Cikin k’arfin hali Ta d’an fuzar da fuci a hankali kana ta nufi yanda yake tana k’ok’arin massaging wuyarsa da towel...
Cikin daka tsawa yace da ita “Get out..! Tashi ki fita nace bana buk’atar kulawarki...!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci..

Jiki a matuk’ar sanyaye Zuhra ta mik’e ta fice hawaye masu d’umi na gangaro mata....

Tsaki ya buga tana ficewa ya maida k’ofan ya rufe yana ci gaba da fuzar da huci mai tsananin tururi... Yana sosa wuyarsa yanda Mahmood ya shak’esa kalaman Fu’ad na dawowa kwanyarsa.. Wato Muhibbah take ko waye ta sanar da Fu’ad kalan wulak’ancinda ta masa, Yana nan yana faman famkam famkam Fu’ad na masa kallan k’ask’antacce wanda mace Ta yarfa... How dare she..! Wllhi sai ya koya mata hankali, this isn’t over, in fact is far from over... He must teach her a lesson, a very good one...! Babu macen data kai ta wulak’anta Prince Yazeed AbdulJabbar....! Ya k’arashe tinanin fuskan mutum biyu da yafi tsana na masa gizo cikin idanunsa, Mahmood da kuma Muhibbah....

A b’angaren Zuhra kuwa tana fita parlor ta tadda Raheema ta shigo, ganinta haka ya tabbatarwa Raheema cewa plan d’inta yayi aiki tasan Mahmood ya confronting Yazeed ko babu komai tasan yanzu Mahmood zai soma yarda da ita.... Tai saurin k’arasawa fuska fal damuwa ta kamo Zuhra tana tambayarta meke faruwa.... Zuhra bata iya cewa komai ba saima kukan da take k’ok’arin dannewa ne ya kufce mata....

Cikin nuna kulawa Raheema ta kamota suka zauna saman kujera tana k’ok’arin comforting d’inta... Lokaci guda san jin meke faruwa da Zuhran...

**
A b’angaren Fu’ad gaba d’aya yinin ranan yinta yai yana tinanin abinda su kaiwa wa yarinyar shekarun baya... Yana so ya mance komai ya soma Sabon rayuwa musamman da yanzu Muhibbah ta shigo cikin rayuwarsa saidai baijin zai iya yin hakan sabida Shi kanshi baijin zai iya yafewa kansa balle ita yarinyar da suka zalunta da ahalinta... Fu’ad ya dafe kansa dake tsananin sara masa had’ida rintse idanunsa, lokaci guda yake furta “No no no I don’t want to Yazeed...! Just let me go... I don’t want to do it....!” K’ara ya kuma sakewa shi k’ad’ai yana mai watsi da k’wayoyin dake cikin tafin hannunsa yake furtawa da k’arfi “Just leave me alone... Please leave me alone, bana son yin abinda kuke umartana... Just leave me alone.. Leave me alone..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai tak’urewa can k’arshen gado...
Yanda Fu’ad yaga rana haka yaga dare, gaba d’aya tashin hankalin ya dawo masa Sabo tamkar mai tab’in hankali haka ya dinga yin abubuwa....

Gaba d’aya Masarautar ma abubuwa sun kuma tab’arb’arewa, a b’angaren Waziri da Giwa basuyi k’asa a gwiwa ba dan koda wasa bazasu bari Yazeed ya soma d’alewa Karagar nan ba maganar Tal’udu ya tabbata kaman yanda ya sanar dasu cikin yaran Sarkin duk wanda ya soma zama Sarki shine gawan fari don fitilar tsafi ta hasko masa mutuwa a Masarautar...
Tuni sun samo mafita yanda Waziri ya tafi asibiti cikin shiga na b’adda kamanni tufafi irinta bayin Masarautar mata ya saka sannan ya d’auki farantin abinci tamkar wanda zaikaiwa fursunan abinci yanda babu mai zarginsa....

Yana shigewa d’akinda Ubandoma Ke kwance ya maida k’ofa ya rufe...

Ubandoma yai k’uri ganin ba likita bane ya shigo.... Yai Saurin mik’ewa ganin mutumin da yai shiga irinta mata na kuma nufosa... Kafin yai yunk’urin gudu Waziri ya damk’osa ya yaye mayafin daya rufe fuskarsa dashi... Zuciyar Ubandoma ya tsinke ganin Waziri ne... Waziri ya sakar masa murmushi yana mai furtawa cikin sigan rad’a “Kwantar da hankalinka Ubandoma bakada wajen gudu... Kuma idan har kanaso ka tsira da rayuwarka data iyalanka toh kayi yanda nace..!” Ya k’arashe yana sakarwa Ubandoma murmushi mai muni....

Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar yana mai furta “Waziri kamin rai dan Allah kada ka kasheni ko ‘ya’yana wllhi Yarima Yazeed ne ya tilasta min fad’in duk abubuwan dana fad’a a Masarauta... Amma ko kad’an babu hannun Mahmood cikin abinda nayi, hasalima na sinkayo tattaunawarku da Giwa ne cewa akwai abinda kuke nema gidan Wambai ni kuma naga abinda nada matuk’ar mahimmanci wajenku sannan idan na rigaka samo abin watak’ila Giwa ta ‘yantani na sami ‘yanci na bar bauta abinda na jima Ina burin mallaka tsawon rayuwata... Kaji dalilina Allah shi taimakeka...!” Ya k’arashe jiki na matuk’ar rawa...

Waziri ya saki wata bazawar murmushi yace “Shege Ubandoma... Ni dama nasan za’a aika... Wato ki gaka mai wayo koh... Haba Ubandoma kana bawa yaushe har zakai tunanin kaid’in shirinka zai aiki akan namu... Toh kana jina...”
Ubandoma yai saurin jinjina kai alamun eh....

Waziri yaci gaba da fad’in “Zan k’yale wannan ya shige Ubandoma amma da sharad’in zaka k’aryata abinda ka fad’i gaban Masarauta... Zaka sanar da Masarauta cewa Yazeed ne ya tilasta maka fad’in hakan Ka fahimta...!”

Ubandoma yai saurin jinjina kai sai kuma ya d’anyi jim tamkar yana tuna wani abin...

Waziri yace “Ya naga kayi shiru..?”

Ubandoma ya muskuta kad’an yace “Toh Yarima Yazeed fah Rankashidad’e kasan halinsa idan na janye abinda na fad’i gameda Yarima Mahmood hakan ka iya janyo min matsala wajen Yarima Yazeed..!” Ya k’arashe fuska fal damuwa...

Waziri yace “Bakada matsala Ubandoma Yazeed bazai maka komai ba ina mai tabbatar maka... Kaidai kawai kayi yanda na umarceka...!”

Ubandoma ya jinjina kai cikeda girmamawa yana mai tabbatarwa Wazir cewa zai yanda yace....

**

Yazeed ya gama tunanin Ta yanda zai b’ullowa Mahmood ya d’auki Fansarsa, ya saki murmushin nan nasa a hankali had’ida furta “His daughter... Itace weakness d’in Mahmood kuma da ita zai amfani ya tarwatsa Mahmood... Lokaci guda ya mik’e ya fice daga sashen nasa... Zuhra na hango fitarsa ta window ta lumshe idanunta tanai masa addu’an shiriya cikin zuciyarta...

**

Zahra Ta ida shirin baccinta kenan taji ana knocking a k’ofarta... D’an jim tai tana duba time kafin ta saki murmushi dan tasan bazai wuce Paa d’inta ba tinda yau d’in duka basu had’u ba ta dubashi a sashensa da duk yanda take tinani cikin Masarautar zata sameshi bata sameshi ba... Tasan bazai iya bacci bai ganta ba, cikin sauri ta isa k’ofa ta bud’e tana mai furta “I thought yau bazan ganka ba Paa...!” Birki tai ganin Uncle Yazeed tsaye bakin k’ofar cikin wane irin yanayi...

“Uncle.. Lafiya...?!” Ta tambaya tana dubansa fuska d’aukeda damuwa...

Yazeed ya sakar mata murmushi mai kyau yace “Princess... Aren’t you gonna let your Uncle in....?”

Cikin sauri ta matsa gefe ta basa hanya tana mai furta “Sorry Uncle... Please come in...!”

Yazeed ya kuma sakar mata murmushi kana yasa kai ya shigo...

Yana tafe ne Zahra ta hango wuyansa yayi shati jajazir kaman ciwo.... Ta taresa da fad’in “Uncle wait... What happened to you... Mai ya sameka..?” Ta k’arashe cikeda kulawa....

Yazeed ya d’an shafi wuyansa yace “Oh this...” Yai maganar yana mai zama saman doguwar kujera dake cikin d’akin lokaci guda Zahra ta K’araso ta zauna gefensa duk ta damu da ciwon da ta gani wuyarsa...

Yana mai sosa wuyan yake ci gaba da fad’in “Someone tried to kill me Zahra...!” Yai maganar yana mai duban cikin idanun yarinyar...

Ta zaro idanu waje “Kasheka Uncle... Waye kenan... Maiyasa ba’a kamashi ba... Whoever did this to you needs to pay Uncle..!”

Ya murmusa kad’an yace “You think so..?!”

Zahra tace “Haka ne ya kamata Uncle...”

Yazeed ya fuzar da fuci kad’an sai kuma yace “Zahra’u mai kike tunani a duniyar da babu adalci..? Mai kike tunani a Masarauta mai cikeda azzalumai wanda suka d’auki kashe rai ba komai ba...?!”

Kalamanta sunyi mata nauyi, gaba d’aya kwanyarta sai yana neman juyawa, lokaci guda tunanin mutuwar mahaifiyarta yazo mata, k’walla suka ciko idanunta.... Cikin rawar murya take furta “Uncle bana son rayuwa a irin wannan Masarautar... What if... What if this kingdom is cursed... I lost my Maama here... Bana so na sake rasa wani cikin iyayena Uncle what’s wrong with this palace...?”

Janyota yai ya rungumeta yana lallashinta lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Kar ki damu Princess, that won’t happen kinji koh... Amma inaso kisan waye yamin wannan abun Princess...”

Ta d’ago tana dubansa had’ida share hawayen idanunta “Uncle who attempted to kill you..?”
Chapter 63 · 0% Book details