← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 162

Sashe 160

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mahmood ya jinjina kai a hankali yace “Masha Allah.. Ubangiji yayi jagora, I trust you Fu’ad..! Nasan zaka iya, and zamanka a can zaisa ka d’an mance wasu abubuwan.. I know there’s nothing we can tell you that will ease the pain you’re going through.. So the best solution shine kayi nesa da Masarautar nan na d’an wani lokaci...Just focuss on your studies kaji koh..!”

Fu’ad ya jinjina kai a hankali yana amsawa lokaci guda ya k’arada “Dama inason alfarma Your Highness.. Inaso naje na duba Maami a asibiti kafin na wuce..!”
Mahmood ya jinjina masa kai a hankali yace “Kafin driver ya wuce da kai airport sai ka tsaya kai mata sallama ko...”
Ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Godiya nake Rankaidad’e..!” Ya nemi izinin tafiya.. Har ya mik’e ya soma tafiya Mahnood ya ambato sunansa, ya dawo da baya kad’an...
“You take care and study hard..!”
Mahmood ya fad’i yana duban Fu’ad d’in...
A hankali Fu’ad ya saki murmushi had’ida jinjina kai... Lokaci guda yasa kai ya fice fadawa na masa fatan alkhairi.. Mahmood kaw yabi bayansa da kallo har ya b’ace masa zuciyarsa cikeda k’aunan d’anuwan nasa.. Iyakacin gatan da zai masa kenan ya fitar dashi daga wannan environment for the mean time...
Fu’ad yana fita ya tadda Ja’afar na jiransa, suka sakar ma juna murmushi suka nufi Mota a tare, Zahra da Umaima dake tsaye daga can saman bene suna hangensu.. Zahra taci gaba da fad’in “He’s my favorite you know.. I feel sorry for him... Ace ga halinda mahaifiyarka ke ciki ‘yanuwanka babu ko guda d’aya.. Jamal ya kashe Yazeed ya kuma kashe kansa wannan tashin hankali da yawa take gwara yayi nesa da wajen nan hakan sai yafi masa sauk’i fiyeda zamansa a nan.. Koda kuwa muna son kasancewarsa a nan tareda mu..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..
Umaima Ta jinjina kai a hankali idanunta naga su Fu’ad d’in take furta “Yeah.. Zaifi kyau yayi nesa da wannan Masarautar na d’an wani lokaci..!”

Daidai lokacin kaman ance Fu’ad ya d’aga kai sama... Ya hangosu tsaye suna dubansa hawaye saman fuskar Zahra... Ya murmusa kad’an had’ida Girgiza mata kai alamun banda kuka, lokaci guda ya d’aga mata babban yatsa cikin salon da suke ma juna.. Ta saki murmushi mai bayyana hak’wara itama tai masa irin yanda yai mata... Umaima da Ja’afar suka murmusa suma kafin Fu’ad yai masu waving suma sukai masa suna masu sakin murmushi had’ida masa fatan alkhairi har suka nufi yanda aka paka hamshak’iyar SUV d’in driver na jiran isowarsu... Dogarai suka bud’e masu motan Ja’afar da Fu’ad suka shige tare Dan har airport Ja’afar d’in yai masa rakiya... Kafin su k’arasa airport d’in saida suka biya yai sallama da Giwa dake asibti tana ci gaba da jinya... Abubuwa goma da ishirin sun taru sun mata yawa Ta wayi gari yau babu kowa nata a tareda ita.. Babu Yazeed babu ‘ya’yan Yazeed sannan babu Jamal ga Fu’ad ma ya tafi nisan duniya wanda bata San ko su sake had’uwa ko ba su sake had’uwa ba... Giwa Ta koma bata kowa bata da komai daga ita sai ko Jakadiya wacce itama a halin yanzu Ta kanta take ba Ta Giwa ba.. Koda aka sallamesu a asibti Basu San yanda zasuje ba Dan basu san yaya zasu kwashe da ahalin Masarauta ba... Ta yaya ma zasu soma shiga cikin Masarautar..? Da wasu idanu zasu dubi ahalin wannan gidan wad’anda suka masu bak’in zalunci a baya...

Jakadiya taja Ta tsaya tana haki Dan harga Allah ta gaji da tura Giwa saman wheelchair.. Lokaci guda take furta “Ke Izzatu nifa ba baiwarki bace ki barni najida ciwon jiki dake damuna wanda kece kika jaza min.. Kowa ta kama gabansa cikinmu Dan Allah ya gani bazan iya d’awainiyar Ki ba ehe..!”

Giwa na hawaye take furta “Jakadiya ni ce fah Giwa..!”

A wulak’ance Jakadiya Ta dubeta kana Ta shek’e da wata irin muguwar dariya tace “Giwa a ina.. Giwa ko b’arauniya.. Kin dai sace sunan asalin Giwa kin rad’a ma kanki.. Nida Ke babu maraba.. Ke har gwara ni na rik’i matsayin Jakadiyar Sarki Ke kuwa Baiwa ce tukuf wacce a cikin bayin ma ina tsamman ke Bakida cikakken asali.. A nan zan barki kema kiyita kanki.. Ai na gama miki mai wuyan tunda na fito dake nan..!”

Giwa na hawaye taci gaba da fad’in “Yanzu idan kika barni a nan naje Ina Jakadiya..? Kema babu yanda zakije Don bakida wajen zuwa, kina tunanin Idan kin koma masarauta zasu karb’eki ne.. Jakadiya bamuda Kowa sai mu biyun... Gwara mu taimaki juna..!”

Jikin Jakadiya yayi sanyi Dan gaskiya Giwa Ta fad’i basuda kowa sai su biyun.. Lokci guda Jakadiya tace “Toh Ina kike so muje Izzatu.. Tinda dai masarauta yafi k’arfin shigarmu yanzu...”

Giwa tace “Haka zamu sad’ad’a mu shiga ta k’ofar bayi mu samu wani waje mu fake tunda duk duniyar nan babu yanda zamuje da ya shige Fadah..”

Jakadiya tai shiru sai kuma ta jinjina kai tace “Haka ne Izzatu bamuda wajen zuwa da ya wuce masarauta a yanda kike d’in nan idan na shiga gari dake gudu za’ai gashi ni kaina ba wai lafiya bane ya isheni Tabbas mafaka muke nema a halin yanzu..”

Giwa tace “Naji dad’i da kika fahimci haka, yanzu mu San yanda zamuyi mu shige cikin Masarauta koda da dabara ne..”
Jakadiya tace “Hakan bazai yuwu ba sai cikin dare lokacin k’afa ya d’auke tinda ta k’ofar Bayi zamu samu mu shige...”
Suka tsaida shawari akan cikin dare zasu saci k’afa su shige Masarauta.. Hakan ce ta kasance... Suka saci k’afa suka bi Ta k’ofan Bayi abinka da wanda suka San kan gidan...
A wani tsukin d’aki da ya gama rub’ewa ciki babu komai a nan suka samu suka yada zango.. Babu komai cikin d’akin sai wata mutacciyar tabarma.. Haka Jakadiya ta watsar da Giwa saman tabarman... Kafin safiya Giwa ta gama b’ata wajen da k’azanta.. Wanda hakan yasa Jakadiya tashi tana fad’in gaskiya bazata iya rayuwa Inuwa guda da Giwa ba Allah ya gani bazata iya mata jinya ba.. Saidai Ta rub’e a wajen... Giwa na kiran Jakadiya ko sauraronta Jakadiya batayi.. Saidai Jakadiyar na ficewa taga gungun Bayi suna fad’in saidai ta koma cikin d’akin ta fito da Giwa su shige su bar cikin Masarautar dan basu buk’atan annoba taredasu kokuma su had’asu gaba d’aya itada Giwan su cinna masu wuta su ida k’onewa.. Haka babu yanda Jakadiya ta iya ta shiga ta zuba Giwa saman wheelchair d’inta daga ita har k’azantarta, ga wani irin d’oyi da takeyi.. Jakadiya sai toshe hanci take ta fito da Giwa.. Aiko nan gungun Bayin nan suka shiga toshe hanci masu gudun gananin yanda halittar Giwa ya koma nayi... Take yaransu suka shiga jifanta suna kiranta dodanniya... Kan kace mai Bayi sun cika dam a wajen ana kallon abin Al’ajabi yanda Giwa Ta koma..

Muhibbah da Umaima harma da Zahra suna zaune gefen Gimbiya Turai a Fadarta tana basu labarin masarautarsu da d’an uwanta mahaifinsu Sabuwar Jakadiya tai sallama Ta risina ta kwashi gaisuwa..

Yanayinta kad’ai ya tabbatar masu babu lafiya..
Gimbiya Turai tace “Lafiya Jakadiya..? Meke tafe dake..?!”
Gaba d’aya su Muhibbah suka zuba mata idanu suna duban yanda take a birkice gaba d’aya.. Lokaci guda Jakadiya Ke fad’in “Allah shi taimakeki cikin Masarauta ne babu lafia...!”
Su Umaima suka dubi juna cikeda mamaki, rabonsu da ace cikin Masarauta babu lafiya tun bayan ficewarsu Giwa a Masarautar..
Gimbiya Turai tace “Ina saurarenki Jakadiya.. Meke faruwa cikin masarauta..?!”

Jakadiya tace “Allah shi taimakeki Tsohuwar Jakadiya mai murabus tareda Baiwa Izzatu sune a cikin Masarautar nan, gashi can gungun bayi sai jifansu suke dasu da yaransu..!”

A tare Su Umaima suka mik’e da jin wannan batu.. Giwa a cikin Masarauta..? Gimbiya Turai taceda Jakadiya ta tsaya su tafi tare.. Jakadiya ta jinjina kai har Gimbiya ta mik’e ta kintsa, su Muhibbah ma suka rufa Alkyabbarsu kana suka nufo bayan Gimbiya Jakadiya na masu jagoranci har suka iso yanda Giwa da tsohuwar Jakadiya suke a wulak’ance sai jifansu yaran Bayi suke suna fad’in basa son dodanniya su fice masu..
Chapter 160 · 0% Book details