← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 162

Sashe 56

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Giwa ta k’araso ta rik’o hannayensa cikin rawar murya itama take furta “Zakai naka family d’in d’ah nah believe me... Kawai so nake ka k’ara hak’uri kaji...!!”

Ya d’ago rinannun idanunsa yana dubanta, lokaci guda yake sakin murmushin da za’a iya kira da na takaici “Oh really..! Na k’ara hak’uri... Wai mai kike tsoro Maami... Na fad’a miki ko nayi aure bazan daina miki biyayya ba ki k’yaleni nayi aurena kafin na sanar da Ya Mahmood cewa kin hanani aure...!”

Saurin toshe bakinsa tai tana mai furta “Kul ahir d’inka, na haneka... Idan ka sanar da Mahmood shikenan asirinmu ya tonu kasan shi bazai fahimci komai ba... Toh naji kanaso kai aure wacece matar daka samu... D’iyar wace masarauta ce..? Ko kuwa d’iyar wani mai mulki ne...?”

Jamal ya saki murmushi a hankali yana mai dubanta kan ya isa saman gado ya zauna “Maami kinfi kowa kusanci da ita...”

Giwa ta gyara tsayuwarta tana mai dubansa “Ban fahimceka ba.. Wacece ita..?”

Murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake furta “Your niece Umaima...!”

K’iris ya rage Giwa batakai k’asa ba... Tashin hankali ana wata ga wata... Umaima dai... Umaima Jamal Ke so...Take annurin fuskar Giwa ya d’auke cak... Ta shiga nunasa da yatsa tana mai furtawa da k’yar “Koda wasa kada ka kawo min wannan rainin hankalin a gidan nan... Bazaka auri Umaima ba.... Na gama magana...!” Tana ida fad’in haka ta fice fuu tamkar zata tashi sama...

Jamal yaci gaba da sakin fuci yana mai jifa da pillow... Lokaci guda ya mik’e ya nufi bathroom... Muhibbah dake mak’ale bayan cottons Ta fito a hankali tana goge gumin dake goshinta... Cikin sand’a tabi Ta hanyar data shigo.... Shakka babu ta bangaji tubalin flower Wanda hakan ya janyo hankalin Jamal... Babu shiri ya fito yana lek’en meke faruwa... A hankali yake bin alamun k’fafu har ya iso yanda ya jiyo sautin... Baiga kowa ba amma yaji alamun fad’uwan abu.... Yai saurin saurin isa jikin gini yana lek’a k’asa.... Ya k’urama waje guda idanu yanda ya tsinci k’aramin k’yalle kaman an fincika ne ya rage saura... D’aukan k’yallen yai a yatsun hannunsa yana juyawa a hankali.... Idanunsa suka kuma sauk’a kan alamun shatin jini yanda ta kuje gwiwar hannunta... Jamal yai saurin k’arasawa had’ida k’urama wajen idanu... Hannu yakai ya d’an shafi jini yana duba... Tabbas jini ne... Kenan hakan na nufin wani na bibiyarsa a Masarautar... He needs to find out koma wanene...! Ya murmusa kad’an yana mai furtawa a fili “You chose the wrong prince.. Ko wanene kai I’d hunt you down myself...!!” Ya k’arashe yana mai gimtse fuska had’ida sakin huci...

**

Tareda yaran Sarki AbdulJabbar gaba d’aya akai komai idan ka cire Jamal wanda ya tafi amsa kiran mahaifiyarsa

Daga bisani aka kai Wambai cikin Fada yanda ake bisne sarakuna da ‘ya’yayensu nan aka bisne Wambai...

Kowa ya watse aka bar Mahmood da Majidad’i suna tsaye kan k’abarin suna addu’o’i ga Wambai...

Majidad’i ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Mahmood... Murmushi ya saki da gefen bakinsa yana mai furta “Aikin banza kenan idan kana tunanin add’u’anka zai isaga mutumin da kai ajalinsa... Da zaka matsa daga kan mahaifina da ya fiye min komai domin tsayuwarka a nan ba amfanansa da komai yake ba... Kuma bari kaji na sanar dakai Billahillazeem sai na d’au fansar mutuwar mahaifina... Kuma sai na amshe mulki ya koma gidanmu koda hakan zai zamto abinda zan aikata na k’arshe kenan a rayuwata..!!” Daga haka sa kai yai ya shige cikin tsananin huci tamkar zai kifa k’asa...

SameenaAleeyou 📚
[7/30, 7:10 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*38*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Da idanu Mahmood ya rakasa har ya b’acewa ganinsa kana ya maidoda dubansaga k’abarin Baba Wambai, abubuwa ne jibge cikin zuciyarsa da zaiso amo dasu amma saidai babu halin yin hakan... Ya kuma lumshe idanunsa a hankali kana yasa kai ya nufi k’abarin mahaifinsa wanda ratan dake tsakaninsa dana Wambai kad’an ne... Ya jima yana tsaye wajen yana karantowa mahaifinsa addu’a kana ya nufi na matarsa itama addu’an yai mata had’ida sauran mutattun dake kwance wajen cikin harda kakanninsa...

Daga nan fitowa yai ya nufi sashen Giwa yanda ya tadda ta fito tana shirin tafiya Gidan Wambai Jakadiya na biyeda ita da kumburarren fuska sai muk’arabbanta na cikin Fada dake take masu baya, Mahmood na k’arasowa suka zube suna kwasan gaisuwa, Jakadiya sai faman b’oye kumbararren fuskarta take cikin mayafi...

Mahmood ya kuma duban Jakadiya dake ci gaba da k’ok’arin janyo mayafi tana kare fuskarta... Sunanta ya ambato wanda ya sanya gabanta fad’uwa... Cikin ‘yar daburcewa Jakadiya Ke k’ok’arin amsawa tana mai kuma risinawa “Allah shi taimaki Yarima mai jiran Gado...!”

Mahmood ya gyara tsayuwarsa kad’an “Jakadiya mai ya sameki... A ina kika samu rauni...?”

Jakadiya ta d’an saci duban Giwa dake jifarta da muguwar kallo... K’ok’arin saita kanta tai had’ida furta “Allah shi baka yawan rai k’aramin had’ari na samu amma da sauk’i...!”

Yai shiru tamkar mai nazari sai kuma yace “Likita ya dubaki....?”

Wannan karon Giwa ce ta basa amsa da fad’in “Karka damu Sadauki lafiya lou take wannan raunin ba komai bane, na riga masa likita ya dubata...”

Jakadiya ta had’iyi k’uncinta jin abinda Giwa ta gama fad’iwa Mahmood, lallai ta yarda Giwa tayi nisa a makirci tinda har ita da take ta hannun damarta bata k’yale ba...
Jinjina kansa kad’an Mahmood yai had’ida mata fatan samun sauk’i Giwa na fad’i masa zasu wuce gidan Wambai gaisuwa...

Jinjina kai yai cikeda girmamawa yace a sauk’a lafiya... Tawagar Giwa suka sa kai ana ci gaba da wasa Giwa duk wani taka k’afarta da zatai a k’asa..

**

Video call yau d’in yaji ya kirata sabida kewarta da yai sosai, yana zaune Office d’insa saman kujerarsa na duba marassa lafiya yai mata K’uri ta fuskar wayar nasa yanda take ci gaba da goge gwiwar hannunta data karje with cotton wool... Lokaci guda take ci gaba da fad’in “I couldn’t believe what I saw either, I mean... Mai ya kawo sunana rubuce jikin k’yalle, and what worries me the most shine k’yallen da sunana Ke rubuce bisa anyi crossing... Mai ahalin AbdulJabbar suka aiwatar da sunana...”

Katseta Ansar yai da fad’in “Wait what’s that... Are you injured...?”

D’an fuzar da fuci tai a hankali tana mai gyara zamanta take kuma duban hannun nata kana tace “Oh! Just a small scratch but I’m okay... Kar ka damu likita...”

Fuzar da huci yai a hankali yana mai kauda kai gefe cikeda damuwa “Hibbah bamu yi haka ba... You promised me you won’t put yourself in harm ways.. You promised me you’d take good care of yourself... Toh mai nake gani yanzu...!” Ya k’arashe cikin d’an tsawatarwa...

Fuzar da huci tai a hankali kana tace “I’m sorry..Okay, it won’t happen again...I’d be more careful next time...Yayi maka..!” Ta k’arashe cikin raunin murya...

Shafa fuskarsa yai da duka hannayensa biyu kana yace “Do I have a choice..!”

Dariya yaso bata ta d’anyi kad’an yayinda Ansar ke fad’in “Aw Wato ma dariya na baki...!”

Muhibbah tace “Gani nayi Likitana ya fini damuwa da lafiyata...!”

“Of course you’re right... Na fiki damuwa da lafiyarki... My next patient zai shigo Hibbah.. Do you want me to attend to them...?!” Yai tambayar cikin kashe murya...

Murmusawa tai kad’an tace “Likita bakada dama... We talk later.. Take care.. Bye..!”

Katseta yai da fad’in “I love you...!”

Murmushi kurum tai cikin tsananin sanyin jiki wanda ita kanta bata San dalilin jin hakan ba kana Ta katse kiran ta koma cikin kujera ta zauna sosai tana mai lumshe idnunta.. Abubuwa ne da dama cunk’ushe cikin zuciyarta...

**

A can gidan Wambai kuwa yanda aketa karb’an gaisuwa Gimbiya Zeenatu ma da tata tawagar Sun halarta... Raheema sai faman aikawa Juwariyya muguwar kallo take, dik itace ta janyo Mahmood yanzu bai kulata, gashi ta kula sam maganinsu baiyi tasiri akan Mahmood d’in ba tinda gashi shiru shiru har yanzu babu wani canji tun ranan data barbad’a maganin a sashensa... Tai k’wafa tana mai kuma hararan Juwariyya...
Ga mamakin Raheema Murmushi Juwariyya Ta sakar mata kana ta tura mata sak’o ta waya
_Haba mutumiyar ko gaisuwa babu, ai ya kamata Kimin ta’aziya for old time sakes... How about idan muka keb’e Ta baya, I’ve something special for you..!_

Raheema ta karance sak’on ta kuma d’agowa tana duban Juwariyya dake ci gaba da sakar mata murmushi tana mai mik’ewa tsaye kana ta shige wata k’ofar.. Tana shigewa Raheema ma ta mik’e tana mai gyara mayafinta had’ida satan idanun mutane musamman Su Zuhra da Zahra da Umaima dake zaune daga can gefe... Ta d’an rank’wafo taceda Zuhra “Best bara na d’an amsa waya...”
Zuhra ta jinjina mata kai tana mai ci gaba da jan cazbaha dake hannunta Raheema tasa kai tabi k’ofar da taga Juwariyya tabi...

Raheema na shigewa Juwariyya ta maida k’ofar ta rufe... Raheema ta finciko wuyan Juwariyya tana fad’in “How dare you... Laifinki ne Mahmood bai kulani yanzu, you messed everything up...!”

Fincikewa Juwariyya tai tana fad’in “Ki saurareni Raheema shisa na kiraki wajen nan to make it up to you.. Amma idan bazaki saurareni ba fine kina iya tafiya...!” Ta k’arashe cikin huci...

Gyara tsayuwarta Raheema tai tana fad’in “Fine, tell me mai kike son sanar dani... Wani amfani abinda zaki sanar dani zai min...?!”

Juwariyya ta murmusa kad’an kana tace “Zai muku amfani both you and Mahmood, it might help you win him back.... Shi kuma Ya Mahmood zai masa amfani yasan yanda zai ya kare kansa da mulkinsa...!”

Raheema ta d’an gyara tsayuwarta tana fad’in “Mai kike nufi...?”

Juwariyya ta fuzar da iska kad’an kana tace “You know nafi kowa san Ya Mahmood ya d’ale Karagar nan... Banson Yaya na ya d’ale...”

Raheema ta katseta da fad’in “Ke naji naji... Just go straight to point da Allah bansan iyayi...!”

Juwariyya tace “I saw my brother and Ya Yazeed together at the hospital before my father passed away...!”

“So, sai mai dan kin gansu tare..Ta yaya hakan zai taimaka min win Mahmood back...?”
Chapter 56 · 0% Book details