← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 162

Sashe 37

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zuciye Raheema dake tsananin fuci ta juyo tana duban Zahra kana Ta soma fad’in “Shut your mouth you little brat, this is all your fault...How could you... Ta yaya zaki katse min hira da mijina ki kirawo mana wannan shu’umar wajen nan... Just who do you think you are..!? Na jima da sanin baki so na auri mahaifinki, but ban zaci munafuncinki yakai har haka ba, tell me so kike Ki lik’awa babanki ita ko mai da zaki gayyato mana ita...? Toh bari kiji na fad’a miki, Yarima Mahmood is mine, he’s mine... I don’t care if you’re his daughter... The next time da kika sake yunk’urin aikata wani abu mai kama da haka ni da kaina zan hukuntaki, maras kunya kawai...!”

Zahra da tuni ta soma huci da hawaye, lokaci guda take furta “You’ve no right to talk to me that way..! You are not my mother, you can’t punish me... You’ve no right over me...I hate you, I hate you.... And yes I never liked you, I don’t want you for my father... To hell with you..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin daka tsawa hawaye na sauk’o mata....

A zuciye Raheem Ta mik’e zatakaiwa yarinyar mari Muhibbah tai saurin rik’e hannun Raheema tana mai sakin huci itama...
“Don’t you dare lay a finger on her...!!”

A guje Zahra ta nufi upstairs tana kuka sosai take kiran mahaifinta....

Raheema ta dube Muhibbah shaye da mamaki kana tace “Excuse me...! Wacece Ke... How dare you interfere..! Sakar min hannuna kafin na sakaki kiyi nadaman da baki tab’a irinsa ba tsawon rayuwarki.... Munafuka mai bin mazan mutane..!!”

Wannan karon murmushi Muhibbah tai kana tace “Why...? Tsoro kikeji...? Baki yarda da kanki bane...? How many times do I have to tell you babu abinda zanyi da Yarimanki... Ni inada Sarki already... Bana buk’atan Yarima, amma ga shawari guda d’aya... If you’re scared of losing your prince... Then ki sami igiya mai k’arfi ki d’aure zuciyarki dana d’iyarsa waje guda... Aikin banza kike idan har yarinyar nan bata k’aunarki... Shawari ce..!!” Ta k’arashe tana mai sakin murmushi saitin fuskar Raheema... Tana ida fad’in haka tasa kai tai ficewarta daga sashen gaba d’aya, tana tinanin mai zatai gameda batun dasa cameras a cikin gidan da Mahmood Ke k’ok’arin yi, she really needs to come up with something, dole tasan yanda zatai tasa a datse batun saka cameras cikin gidan....

Haka Raheema tabi bayan Muhibbah da kallo har ta b’acewa ganinta, kumafa abinda Muhibbah ta fad’i mata gaskiya ne... Idan har tana son samun kan Mahmood da gaske toh fah dole tai hak’uri da wannan sangartacciyar yarinyar har ta samu ta mallakesa, idan yaso daga baya sai tasan yanda zatai da yarinyar.... Tana ida tinanin ta d’aga idanu tana duban benen, lokaci guda ta kuma sauk’e huci a hankali kana ta soma jan k’afarta mai ciwo ta nufi benen da d’ingishi...

Tana haurawa ta hango Zahra zaune parlorn saman ta tak’ure waje guda ta kifa kanta cikin gwiwarta tana kuka mai tsuma zuciya....

Ta gallawa yarinyar harara tana mai yatsina fuska, lokaci guda tai k’ok’arin saita kanta kana ta nufi cikin parlorn cikeda k’issa, gefe da Zahra ta isa ta zauna had’ida kwantar da murya “Daughter I’m sorry... Believe me I didn’t mean to... Kiyi hak’uri dan Allah... Please don’t tell your Paa about this... Kiyi hak’uri rainane ya b’aci amma bana nufin dik abinda na fad’i kinji koh....!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin rungumo Zahra...

Idanunta masu zuban hawaye ta d’ago tana duban Raheema dashi kana tace “Don’t touch me... Karkizo kusa dani... Bana sonki da Paa d’ina... Bana so ya aureki... Ke muguwa ce... Ni Ki k’yaleni... Just go away..!!” Ta k’arashe tana mai kuma kifa kanta cikin k’afafunta...

Takaici ya kuma turnuk’e Raheema a mak’oshi, batasan Mahmood da matarsa wane irin goyo sukaiwa d’iyarsu ba, shakka babu goyon turai Mahmood yai mata shisa bata ganin mutane da gashin ido, an gama sakalta yarinyar sai abinda take so... Ji take kaman ta d’add’auketa da mari amma sai tai k’ok’arin saita kanta sanda ta tuna kalaman Muhibbah... A hankali ta mik’e tana kuma duban Zahran kana ta fice daga parlorn ta nufo k’asa...

Gimbiya Zeenatu na kwance saman kujera mai lilo na sarauta, gefe da ita kuyangace ke rik’eda parantin kayan marmari tana d’auka d’aya bayan d’aya tana ci cikeda kmasaita da mulki... Tamkar wacce aka jefota haka suka hango Raheema na shigowa na sakin huci... Kuyangin suka shiga sadda kawunansu suna gaidata, sai faman sakin huci take tana jan k’afarta dake ciwo...

Gimbiya Zeenat ta tashi daga kishingid’en da take ta zauna sosai tana duban Raheema...

“Ke kuma fah... Miye haka...?”

Raheema taja Ta zauna kujera mai duban ‘yar uwarta kana tai alamawa bayin kan cewa su fice... Babu musu suka risina suka fice gaba d’aya....

Gimbiya Zeenat tace “Ke nake saurare Raheemah, mai kuma ya faru... Ya na ganki kin dawo cikin fushi keda kika tafi zance da masoyinki.... Sannan mai ya sami k’afarki na ganki haka nan...?”

Huci kawai Raheema ke sakewa tamkar tafashesshen kunu....

Gimbiya Zeenat tace “Ke Raheema ki bud’e baki kimin magana Bana san shashashancin banza...!!” Tai maganar cikin hasala....

Raheemar ma a hasale take fad’in “Aunty ni fah na gaji, na gaji da wannan shed’aniyar d’iyar Mahmood d’in... Wannan yarinyar da kike gani sam babu alkhairi a tattare da ita....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin huci...

Mik’ewa tsaye wannan karon Gimbiya Zeenat tai kana tace “Bani labari mai ya faru...?!”

Tas Raheema ta kwashe dik abinda ya faru ta sanar da ‘yar uwarta... Da mugun mamaki Gimbiya Zeenat ke dubanta kana ta d’an girgiza kai alamun rashin yarda tace “You mean to say Mahmood baisha miyar nan da muka gama masa had’i ba..?!!”

Sai sannan Raheema ta tina ashe fah miyar da aka shirya musamman dan Mahmood an gama masa had’i da komai shine ta tuntsirar dalilin ganin Muhibbah... Ta dafe kanta cikin sauri tana mai furta “Na shiga uku Aunty wllhi baici ba...!”

Saukan wane irin jahilin mari taji a k’uncinta, ta d’ago tana duban Auntyn tata dake sakin hucin b’acin rai... “Ashe ke shashasha ce ta bugawa a jarida ban sani ba... Ashe Ke doluwace Ta k’arshe.. Kinsan da yaya aka had’a maganin nan... Kinsan kwanakin maganin nan nawa a tsibirin iskokai... Shine dan dak’ik’anci da shashashanci zaki zubar kuma dik zaman nan baki San yanda duk kikai kika basa yaci ba..?? Dak’ik’iyar inace Ke Raheemah..!!?” Ta k’arashe tana mai jijjiga Raheema dake kuka dafe da k’uncinta....

Raheema na kuka take fad’in “Aunty wllhi ba laifina bane laifin shegiyar Muhibbar nan ne.... Aunty makirar nan ta shige dik tinaninki...!”

Hankad’ata gefe Gimbiya Zeenat tai tana mai ci gaba da sakin tururi “Bazamu tab’a rasa Mahmood ba, dole ya zamto yana k’ark’ashin ikonmu.... Amma kafin nan sai mun b’atar da wannan yarinya Muhibbah dake k’ok’arin kutso Kai cikin rayuwarsa data d’iyarsa..!!”

Raheema ta dubeta da mamaki kana tace “Aunty ya za’ai mu b’atar da ita, bayan ko idanunta tsoro suke bani...!”

K’asaitaccen murmushi Gimbiya Zeenat tai kana tace “Na b’atadda wad’anda suka fita balle ita... Akan mulkin nan babu abinda bazanyi ba... Juwariyya..!!!”

Raheema ta kuma dubanta da mamaki kana tace “Mai ya kawo Juwariyya cikin batun nan Aunty..?!”

Murmusawa Gimbiya Zeenatu Ta kumayi kana tace “Itace solution d’inmu... Itace zamu umarta ta bincika mana komai gameda Muhibbah... Idan muka San ko wacece ita kaita k’asa bazai mana wuya ba, dan ni ban yarda da wannan Muhibbar ba...!”

Raheema ta saki murmushi cikeda jin dad’i “Gaskiya Aunty Ke d’in ta dabance, badon Giwa ta rigaki shigowa gidan nan ba da anyi shu’umar Sarauniya.! Toh amma do you think we can trust Juwariyya..?!”

Murmusawa Gimbiya Zeenat ta kumayi tana mai zama cikin kujerar lilonta, tana juyi bisa take fad’in “Ai a halin yanzu babu wacce zamu yarda da ita samada Juwariyya tinda har ta juyawa ahalinta baya dan cikar burinmu... Karki mance duk wani information kan Yayanta ita ke kawo mana, so na tabbata bazamu samu matsala da ita ba....!”

Murmusawa Raheema tai kana tace “K’warai kuwa Aunty shawarinki yayi..!”

Suka kuma duban juna a tare suna masu sakin murmushin cin nasara....

***

Zagaye d’akin take faman ci gaba da yi waya manne kunnenta tana mai ci gaba da fad’in “Ansar please pick up... Pick up please... Ina tsananin buk’atar shawarinka...!!”

Har saida wayar ta kusan katsewa Ansar ya d’aga yana mai furta “I can see someone’s already missing me, Sorry wanka na shige ban jima da isa masauk’i ba na tsaya restaurant nayi takeaway... Do you want some... Na kawo miki...?!” Yai maganan teasingly...

Katse wasan nasa tai da fad’in “Ansar akwai matsala....!”

SameenaAleeyou 📚
[7/1, 10:39 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*026*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Gathering natsiwarsa yai waje guda yana mai furta “Ina saurarenki... Meke faruwa...?”

Fuzar da fuci tai a hankali tana mai zama cikin gado “Ansar Mahmood yana so ya dasa cameras in every angle cikin Masarautar... I mean he can’t do that... Zai b’ata min shirina, bayan babu abinda na fara...” Ta k’arashe cikeda damuwa...

Lokaci guda ya isa ya zauna bakin gado yana mai furta “What..! Hibbah you need to leave that place right away, muddin aka saka cameras you’d definitely get caught..!”

Jinjina masa kai tai kaman yana kallonta kana tace “What do I do now Ansar... Mai zanyi na hana yuwar hakan...?!”

Fuci ya fuzar a hankali kana tace “Muhibbah ki bar maganan mission d’in nan naki... Abubuwan da suke faruwa sign suke nuna miki cewa akwai matsala gaba... Before everything gets out of hands let’s leave, tun ban bar cikin garin nan ba... Zanzo ni na d’auki, mu koma gida...!”

Katsesa tai da fad’in “Haba Ansar, kai saikace ba namiji ba, sai gashi kaman ka cire tsoro da shakku cikin sai kuma ka sake komawa ruwa..!”

Shima ya katseta da fad’in “Dik abinda ya shafeki Muhibbah bazan masa tinani d’aya ba.. I’ll think through and think through and think it through... Karkiga laifina sabida banso ki shiga matsala ne....!”

“Are you saying na ajiye makamaina na bika mu koma gida, what about the justice that I deserve..? So kake na tafi na mance komai..!?”
Chapter 37 · 0% Book details