← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 162

Sashe 48

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya zaro takobinsa ya nufi cikin gidan cikin sand’a...
Ubandoma dake faman bincike kaman b’era sai k’wak’ule k’wak’ulen rami yake sam bai aune da shigowar mutum ba sai jin sauk’ar takobi yayi a wuyarsa ana furta “Mik’e ka nuna fuskarka..!!!”
Muryar Majidad’i ya daki dodon kunnuwansa...
Take jikin Ubandoma ya d’auki rawa, karkarwa kurum jikinsa keyi ga gumi dake keto masa... Ya kasa tashi ya kasa d’ago fuskarsa da tuni ya jik’e da gumi...

Majidad’i ya capko wuyarsa da k’arfin gaske yana k’ok’arin d’agosa.. Daidai wannan lokaci Ubandoma ke kokawan danna layarsa saidai ga tsananin mamakinsa ko gizau layar tak’i dannuwa....

Majidad’i ya kwashe da muguwar dariya sanda layar ta fad’i k’asa... K’afa yasa ya shura layar yana fad’in “Kana tunanin laya tana tasiri a wannan gidan ne... Ai bari kaji ba Fada bane kawai takeda shiri ko wane gida nada nasa shirin... K’aramin munafuki tashi ka nuna kanka kuma ka fad’i waye Ubangidanka..!!” Ya k’arashe maganar yana mai fincike rawanin Ubandoma... Take fuskar Ubandoma ya bayyana gumi sai tsartsafo masa yake...

Baki sake Majidad’i Ke dubansa “Kai..!!! Kaine kenan... Kaine Bak’on Buzu...!!!”

Cikin rawar murya Ubandoma Ke fad’in “Allah shi taimakeka wllhi bani bane... Wllhi banida masaniya sahub b’arawo na taka kamin rai dan Allah..!”

Baikai aya ba Majidad’i ya kwahesa da wata irin jahilar mari wanda ya sanya Ubandoma zubewa k’asa yana mai ci gaba da rantsuwa yana fad’in bashi bane Bak’on Buzu baida masaniya kan Bak’on Buzu....

Damk’o wuyarsa Majidad’i yai yana fad’in “Ka shiga hannu kuma kenan ai... Sai ka sanar dani Ubanda kakema aiki...!!”

Ubandoma yaci gaba da magiya yana fad’in ai masa rai baisan komai ba...

**

A cen Fada kuwa hankulan Giwa da Waziri ne yakai k’ololuwa wajen tashi... Giwa bataga Ta zama ba, tabbas akwai wanda Taguwarsa tafi tasu Gudu cikin Masarautar ya zama dole a yau d’in ta gana da Tal’udu duk yanda za’ai... Wannan mummunan labari da Waziri ya kawo mata ba k’aramin barazana bane a gareta...

Waziri na tafiya Giwa da Jakadiya sukai shirin zuwa ganin Tal’udu...

Giwa tai zaune saman jar dardumanta mai d’aukeda tambarin masarauta na tsafi... Jim kad’an guguwa ya kaure mai cikeda jan hayak’i, nan take Tal’udu ya bayyana cikin shigarsa maras kyaun gani....

Yana fitowa Giwa ta kifa kanta alamun gaisuwa, tinda taga jan guguwa tasan yau ba kanta, tashin hankali ne take fuskanta...

“Turai kinyi kuskure..!” Tal’udu ya fad’i cikin tsananin huci...

Giwa Ta shiga girgiza kai tana fad’in “Babu laifina ko guda Uban tsafi... Na tabbata wani ne da yasan da batun K’undin nan ya rigamu isaga Wambai... Amma yanzu so nake ka duba min mai fitilar tsafi ta hasko maka gameda wannan K’undi... Shin ina k’undin yake a halin yanzu...?”

Cikin tsananin b’acin rai ya buga jan sandar dake hannunsa, lokaci guda yake furta “Har abada K’undin nan bazai tab’a dawowa hannunki ba Turai... Kin riga da kin tapka kuskure... Kuma iyaka abinda fitilar tsafi Ta hasko mana shine K’undin zaiyi nisan tafiya har ya isaga wannan yarinya SAUDATU... Ita kad’aice zata iya bud’e wannan k’undi domin idan baki mance ba K’ADDARAR MASARAUTAR nan yana ratayene a wuyarta... Da ace yaranki sunyi nasaran kasheta tun a wancan lokacin k’ila da K’addarar Ta iya sauyawa... Barinta a raye yafi muni fiyeda rashin tarewa da banyi da ita ba.... Turai kina cikin had’ari muddin baki nemo Saudatu yanda Ta shiga Ta fice ba...!!” Ya k’arashe yana mai kuma dukan k’asa da sandar hannunsa...

Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana.... A ina Saudatu take... A wane duniya Ta b’uya da har Tal’udu ya kasa gano yanda take rayuwa... Tabbas ya zama dole duk nisan duniyar data tafi ta nemo ta... Har abada bazata bari wulak’antacciya irin wannan yarinyar tayi sanadin mulkinta da duk wani Farin ciki nata ba...
Ta d’ago idanunta da sukai jazir tana duban Tal’udu
“A ina zan samo Saudatu Uban tsafi...?!”

Gashin girarsa guda d’aya ya tsinko ya aza saman tafin hannunsa yaceda Giwa matso nan ki gani... Babu musu ta matsa kusa tana Ware idanunta sosai... Ga tsananin mamakinta tsillin gashin taga ya kama da wuta yanaci sosai baka iya ganin komai sai bak’in hayak’i...

Tal’udu yaci gaba da fad’in “Yanda wannan wuta Ke ruruwa baki iya ganin alamun tsillin gashin nan Toh haka Saudatu zata k’ona rayuwarki ba tareda kin iya ganin koda alamunta ba....!!”

Giwa ta had’iyi miyau cikeda fargaba da kuma tashin hankali... Take ta kuma d’agowa tana duban Tal’udu.... Da tuni ya soma sakin murmushi... Lokaci guda yaci gaba da furta “Saidai akwai mutum d’aya wacce tasan yanda Saudatu take... Shiyasa na fad’a miki har abada bazaki iya kasheta ba domin itace kad’ai zata iya sanar dake yanda SAUDATU take... Ko ni ban sani ba amma ita d’in ta sani...!!”

Giwa da tai masa K’uri tun bai kai aya ba Ta furta “IZZATU..!!”

Tal’udu ya kuma murmusawa yace “K’warai kuwa Izzatu ce kad’ai tasan Duniyar da Saudatu Ke rayuwa a halin yanzu... Izzatu ce kad’ai makaminki na k’arahe akan wannan yarinya Saudatu... Wannan na d’aya daga cikin dalilin da yasa na hanaki kashe Izzatu, domin ita kad’aice fitilar tsafi ke hasko min a duk lokacin da na soma bincike kan Saudatu, hakan na nuni da cewa itace zatai maki jagoranci har ki isaga Saudatu...Lokacin da Izzatu zatai maki amfani yazo Turai..!!!” Yana ida fad’in haka guguwa ya kaure b’at ya b’ace daga cikin d’akin...

Tashin hankali wanda baa saka masa rana, waige waige Giwa ta soma tana kiran sunan Tal’udu lokaci guda take furta “Ta yaya matar da bata cikin hankalinta zata sanar dani wani gameda Saudatu..? Ta ya zan sami wasu amsoshi daga wajen matar da babu hankali a tattareda ita...? Ta yaya matar da babu harshe cikin bakinta zata iyayin magana..?!! Tal’uduuu...?!!” Ta k’arashe tana mai k’walla masa kira amma saidai babu Tal’udu babu alamunsa....

Giwa ta sauk’e nannuyan ajiyan zuciya kana ta mik’e ta nufo waje... Tai k’uri ma wannan d’akin da kullum yake nan a bud’e... D’akin da ya kamata ace Saudatu ke rayuwa ciki tareda Tal’udu... Tana ficewa daga cikin gidan Tal’udu ta tadda Jakadiya na jiranta...

Jakadiya tace da ita “Allah shi taimakeki ina muka nufa....?!”

Giwa ta kuma gyara bak’ar Alkyabbarta Ta rufe fuskarta sosai kana taceda Jakadiya “Wajen Izzatu muka nufa... Kiyi min kiran Ubandoma...!!”

Daga haka sa kai tai Ta wuce cikin sauri Jakadiya na fad’in “An gama Allah shi baki yawan rai...!!”

Take Jakadiya ta soma neman layin Ubandoma...

Muhibbah dake zaune haraban masauk’inta tana duba wani k’aramin littafi na addu’o’i lokaci guda tana karanta sak’onnin soyayya da Fu’ad ke Aiko mata tana sakin tsuka a hankali nan ta hangi alamun giftawan mutane cikin wane irin sauri tamkar zasu tashi sama... Ai take taji koma su wanene tana son ganin yanda suka nufa... Babu shiri ta mik’e ta gyara rufin kanta sannan ta fito cikin sand’a tabi hanyar da taga sunbi....

SameenaAleeyou 📚
[7/14, 7:36 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*033*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Cikin tsananin rud’ani da tashin hankali Giwa Ke duban Jakadiya “Jakadiya ban fahimceki ba.... Mai kike cewa...?!”

Jakadiya Ta kuma risinawa “Allah shi baki yawan rai kaman yanda kikaji na fad’i ba Ubandoma bane ya amsa kiran kuma ga dukkan alamu Uabdoma yana cikin had’arin gaske, dan wannan murya da naji cikin wayar salulan ba k’aramin tada min hankali yai ba Allah shi taimakeki...!” Ta k’arashe tana mai kuma sadda Kai...

Giwa ta fuzar da fuci kana tace “Shige ki bud’e mamu k’ofar...!”

Babu musu Jakadiya ta isa ta bud’e k’ofar da yake mai nauyin gaske, da k’yar take iya jan k’ofar... Koda gani wannan dadd’en gini ne mai matuk’ar k’argo da aminci...

Muhibbah dake gefe a lab’e tai K’uri tana dubansu har suka shige cikin d’akin... A hankali ta sad’ad’o ta k’araso had’ida rakub’ewa tsakankanin tapkeken k’ofar da yake mai kunnuwa biyu, tana iya hango Giwa da Jakadiya Ta tsakankanin ramin k’ofar yanda sukai tsaye gaban mahaukaciyar matar nan dake d’aure da manyan sark’ok’i....

Matar tana ganin Giwa sai ta soma k’ok’arin fincika tana san sance d’aurinda aka mata... Ita kad’ai sai fincika take tamkar zatayo kansu...

Dama Ubandoma ke bugunta idan tai yunk’urin kaiwa Giwa damk’a gashi yau babu Ubandoma... Jakadiya ce Tai ta maza ta janyo k’atoton dutsin dake gefe ta aza saman k’afafun mahaukaciyar wanda ya sanyata sakin k’aran azaba... sai kuma ta koma tai lak’was tana fidda numfashi a hankali sabida tsananin azaban nauyin dutsen da takeji saman k’afafunta...

Giwa Ta sami zarafin k’arasowa cikeda k’asaita... Lokaci guda Ta umarci Jakadiya data baza mata mayafinta Ta zauna bisa...

Jakadiya ta d’an dubeta da mamaki kana tace “Allah shi baki yawan rai zama a wannan k’ask’antaccen waje mai cikeda k’azanta da k’ask’asanci bai kamaceki ba...!”

Batakai aya ba Giwa Ta katseta cikin tsananin daka tsawa “Jakadiya har yaushe kika fara sa’insa dani... Umarni nake baki ba shawarinki nake nema ba...!!”

Babu shiri Jakadiya ta risina “Tuba nake ya Shugabata... Allah ya huci zuciyar Sarauniya tilo d’aya a Masarautar nan...!!” Ta k’arshe tana mai yaye mayafin kanta kana Ta baza ma Giwa a nan gaban mahaukaciya Izzatu... Giwa Ta tako Ta zauna irin zaman da masu mulki keyi kana tai k’urima Izzatu...

Daga yanda Muhibbah ke tsaye bata iya sauraron abinda suke fad’i dan d’akin nada matuk’ar zurfin gaske abinka da gini irin na gidan sarauta da ya kwashe shekaru aru aru, gashi dai tana iya hangensu da duk wani motsin da suke amma bata iya sauraren abubuwan da suke fad’i duk kalan kasa kunnuwan da tai kaw... Ga kukan hadari dake k’aruwa wanda ya dad’a taimakawa wajen hanata auraron abinda suke fad’i...

Giwa takai hannunta guda cikin tsananin b’acin rai ta damk’o wuyar Izzatu, kana iya ganin yanda jiniyoyin hannunta sukai rud’u rud’u sabida tsananin b’acin rai “Izzatu kinyi kad’an kiga baya mulki na... Ke k’ask’antacciya ki bud’e baki ki sanar dani wace duniya kika b’oye Saudatu..?!!”
Giwa Ta k’arashe tana mai kuma matse wuyan Izzatu da tuni Ta soma k’ak’arin amai sabida tsananin rik’onda Giwa tai mata..!!

Jakadiya gaba d’aya Ta razana ganin Giwa na shirin aika Izzatu lahira gashi Tal’udu ya sanar da ita cewa idan har tana k’aunar zaman lafiyarta toh bazata kashe Izzatu ba...!
Tuni Jakadiya ta zube tana dannan zuciyar Giwa kafin da k’yar Giwa ta sararawa Izzatu...
Chapter 48 · 0% Book details